Free chapter · Read without an account
HERTURN TO WAIT
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER 107*
*HER TURN TO WAIT*
*JIDDAAH BARKUM*
—————
Ummie ta ɗan ajiye hankalinta a kansa, tana nazarin fuskarsa kamar tana son gano wani abu da ya ɓuya a zuciyarsa, bayan ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta tambaye shi cikin murya mai taushi, “Habibi, babu dai wata matsala ko? Duk kuna zaune lafiya?” Zayd ya ɗago kansa ya kalleta, sannan ya jinjina kai a hankali, “Babu komai, Ummie, everything is fine,” ta sauke numfashi, tana jin daɗin amsar da ya ba ta, duk da cewa a zuciyarta tana fatan Allah Ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin iyalinsa, “Toh, Allah Ya sa haka, ka dai yi ta haƙuri, habibi, ka kuma koyi ɗauke kai, musamman a kan ƙananan abubuwa, ba komai ba ne za ka dinga magana a kai ko ka ɗauki mataki a kai, sometimes, keeping quiet is better than reacting to everything,” Zayd ya saurare ta cikin nutsuwa, ba tare da ya katse ta ba, “Allah Ya ba ku zaman lafiya gaba ɗaya, ya sanya albarka a aurenku, ya kuma sa ku fahimci juna,” a hankali ya jinjina kai, “Ameen, Ummie,” ta miƙa hannu ta shafa masa fuska a hankali, “Allah Ya baka ikon adalci, habibi,” “Ameen,” ya sake amsawa, kafin ya koma cin abincinsa, bayan ya gama, ya zauna tare da Ummie na ɗan lokaci suna hira, ba ya son yin gaggawar barin gidan mahaifiyarsa, musamman a irin waɗannan lokutan da yake samun damar zama da ita ba tare da wata matsala ta office ko ta gida ta katse musu hirar ba, sai da ya yi sallar Maghrib sannan ya shirya tafiya, ya yi wa Ummie sallama, ya sumbaci hannunta, ta kuma yi masa addu’ar Allah Ya kiyaye shi a duk inda zai je, “Drive safely, habibi, and please, don’t overwork yourself,” Zayd ya ɗan murmusa, “I will, Ummie, don’t worry,” daga nan ya fice daga gidan, ya nufi motarsa, a wannan karon, shi kaɗai ne a cikin motar, babu convoy da ke biye da shi, ya shiga, ya kunna injin, sannan ya bar harabar gidan a hankali, bayan tafiyarsa, gidan ya ɗan yi shiru.
Sai dai ba a daɗe ba, Suhaila ta sauko daga sama, sanye da well ironed hijab dinta har kasa ta nufi falon inda Ummie take zaune, ta zauna a gefenta, ta gyara zaman hijab ɗinta, sannan ta juya ta fuskanci mahaifiyarta da wata irin fuska da ke nuna cewa akwai abin da ya daɗe yana damunta, “Ummie, yanzu na faɗa miki yadda Mommy ta yi welcoming Anty Rayy amma bakice komai ba haryanzu Wallahi, ba ki gani ba!” Ummie ta zuba mata ido tana kallonta amma batace komai ba, Suhaila ta buɗe baki, ta sake rufe shi, kamar har yanzu tana ƙoƙarin fahimtar abin da ta gani, “Wallahi har yanzu abin nan bai bar kaina ba, I’m still trying to process everything! Abin ya kasa sinking into my brain, Ummie,” Ummie ta yo Shiru kawai, tana sauraron ta, Suhaila ta ci gaba da magana cikin ɗan sauri, “Mommy ta yi wa Anty Rayy maraba sosai, kamar wadda ta daɗe tana jiranta, kuma ba nan abin ya tsaya ba, ta ma yi wa Seeyama kacha-kacha a gaban akhie, har da Anty Rayy!” Ta ɗan dakata, tana kallon Ummie don ganin ko ta fahimci abin da take nufi, “Which is very unusual for her, Ummie! Kin san Mommy fa ba ta cika ganin laifin Seeyama ba, duk abin da Seeyama ta yi, sai dai ta nemi hujjar kare ta, amma yau sai ga shi tana gaya mata a fili cewa ba ta iya komai, dole Rabi ta zo ta dinga kula da ita!” Suhaila ta girgiza kai, tana jin mamaki ya ƙara mamaye ta, “Abin ya ba ni mamaki sosai, Ummie, gashi kuma ta ce za ta samo mata yar aiki, ta kuma faɗa wa Akhie ɗin, amma shi bai ce komai ba!” Ta matsa kaɗan kusa da Ummie, “Gashi ni ma na zo na faɗa miki, amma ke ma ba ki nuna wata damuwa ba, haka za a zuba ido kawai? What if she has something in mind? What if all this is part of a bigger plan? Sai lokaci ya ƙure, sannan a fara cizon yatsa,” Ummie ta sauke numfashi a hankali, ta juya ta kalli Suhaila da nutsuwa, “Suhaila, ya kike so na yi?” Suhaila ta ɗan yi shiru, Ummie ta ci gaba da magana, muryarta har yanzu a sanyaye, “Zan kira ta in ce kada ta kawo yar aikin ne? Ko kuma in je in yi wa Zayd magana, in ce ya hana ta? In gaya masa cewa bai kamata ya amince da shawarar da ta bayar ba?” Ta ɗan girgiza kai, “Ban san abin da kike so na yi ba, Suhaila, maybe tana yin haka ne da good intentions, perhaps tana son taimaka musu ne kawai, we should think positively, because positive thoughts will keep us from assuming the worst about people,” Suhaila ta sauke idanunta, tana sauraron mahaifiyarta, amma har yanzu ba ta gamsu ba, Ummie ta miƙa hannu ta riƙe nata, tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali, “Please, Suhaila, kada mu yi gaggawar yanke hukunci a kan abin da ba mu da cikakken sani a kansa, idan akwai wani abu da ya kamata mu sani, lokaci zai nuna mana,” ta ɗan dakata, kafin ta ƙara da murya mai laushi, “Abin da nake so shi ne zaman lafiya, ba na son a riƙa kallon kowane abu da shakku, har ma abin da zai iya zama alheri,” Suhaila ta jinjina kai a hankali, amma daga yanayin fuskarta, a bayyane yake cewa har yanzu abin dai bai kwanta mata a rai ba, ba don tana son ta yi wa Hajiya Hauwa mummunan zato ba, sai dai ta san irin yadda take ɗaukar Seeyama a matsayin wadda ba ta yin kuskure, don haka ganin yadda ta canza halinta kwatsam, ta fara nuna wa Raihana kulawa, har ta kai ga tsawatar wa Seeyama a gabanta, ya sa ta kasa yarda da cewa komai ya faru ne kawai saboda kyakkyawar niyya, amma da ta kalli Ummie, sai ta ga yadda mahaifiyarta ta nutsu, ba ta son ƙara tsawaita maganar, ta san Ummie ɗin nan da take gabanta, mace ce mai haƙuri, wadda ba ta son shiga tsakanin mutane ba tare da hujja ba, kuma ko da ita kanta ta lura da abin da ya faru, ba za ta fara zargin wani ba sai ta ga abin da ya tabbata, Suhaila ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta jingina da sofa, “Okay, Ummie, I hear you,” amma a zuciyarta, tambayar ba ta daina kasancewa ba, me ya sa Hajiya Hauwa ta sauya halinta kwatsam? Kuma me ya sa take ganin cewa dole ne raihana ta samu yar aikin da za ta riƙa kula da ita? Suhaila ta girgiza kai a hankali, tana ƙoƙarin kawar da tunanin daga ranta, ko dai Ummie tana da gaskiya ne, kuma ita ce take overthinking komai, ko kuma akwai wani abu da ba su sani ba tukuna, a wannan lokacin, ba ta da amsa.
Kafin Zayd ya isa gida, sai ya tsaya a hanya, yana tunanin abin da ya kamata ya saya ya shigar wa matansa da shi, ya ɗan jingina bayansa da kujerar motar, yana kallon hanyar da ke gabansa, kamar yana ƙoƙarin warware wata matsala mai muhimmanci, a ƙarshe, sai ya ɗauki wayarsa ya duba lokaci, “Hmm…” Ya rasa abin da zai saya, sai kawai ya yanke shawarar tsayawa a wani wuri da zai samu abubuwan da yake nema, da farko ya nufi wani shago da ake sayar da fura da nono, ya sayi wanda aka shirya masa sosai, daga nan sai ya wuce wani reshen Cold Stone Creamery, inda ya ɗauki ice cream da wasu snacks da ya gani suna da kyau, bai tsaya nan ba, da ya ga wani mai sayar da kayan marmari a gefen hanya, sai ya tsayar da motar, ya fito, ya zaɓi fruits different varieties ya saye su da uban yawa kamar dai zai raba wa jama’a, kowanne nau’in kayan marmari kuwa, aka saka shi a leda daban, bayan ya gama, ya koma motarsa, ya ajiye kayan da kyau, sannan ya kunna injin ya nufi hanyar gidan, da ya isa gidan, sai ya fara da ba wa maigadi nasa kayan da ya saya, ya bar na Seeyama a cikin motar, ya ɗauki sauran ledojin da zai kai wa Raihana, sannan ya nufi part ɗinta, yana shiga falon, sai ya tsaya na ɗan lokaci, babu Raihana a falon, amma komai yana cikin tsari, kujerun sun zauna yadda ya kamata, babu wani abu a warwatse, hatta kayan da ke kan stool da centre table an gyara su, falon ya yi tsaf, kamar ba wanda ya zauna a ciki tun safe, Zayd ya ɗan zuba wa wajen ido, sannan ya shaƙi iskar falon, wani irin ƙamshi mai daɗi ne ya cika wajen, ƙamshin turaren wuta da Raihana ta kunna, Zayd mutum ne mai matuƙar son ƙamshi, a wurinsa, ƙamshi mai kyau yana da ikon daidaita yanayin zuciyarsa, ko da ya shigo gida da gajiya ko kuma wani abu ya ɓata masa rai a waje, ya ɗan lumshe idanunsa na wasu daƙiƙu, at least, someone knows how to make a place feel welcoming, ba tare da ya ƙara ɓata lokaci ba, ya nufi hanyar da za ta sada shi da part ɗinsa.
Da ya isa ƙofar ɗakin, sai ya ɗora hannu a kan handle ɗin, ya buɗe ƙofar a hankali, Raihana ce kwance a kan doguwar sofa, ta idar da sallar Isha’i kenan, tana sanye da doguwar rigar material mai kyau, sai wani ƙaramin mayafi da ta yafa a kanta, duk da sauƙin kayan da take sanye da su, ta yi kyau sosai, wayarta tana hannunta, tana yawo tsakanin Instagram da Snapchat, lokaci-lokaci tana tsayawa kan wani abu da ya ja hankalinta, jin motsin ƙofar ne ya sa ta ɗago kanta, a daidai lokacin, idanun Zayd ma suka sauka a kanta, sun yi kallon kallo na wasu seconds kafin Zayd ya janye nasa idanun, ya rufe ƙofar, sannan ya ƙarasa cikin ɗakin, ya ajiye ledojin a kan ƙaramin stool ɗin da ke gefen sofa, ba tare da ya ce komai ba, sannan ya fara cire tie ɗinsa, Raihana kuwa, kawai binsa take da kallo, kamar yanzu ne ta fara ganinsa, tana kallonsa yana kwance tie ɗin, tana kallonsa yana ajiye shi, tana kuma kallonsa yayin da ya ɗauko wayarsa daga aljihunsa ya ajiye ta a gefe, daga ƙarshe ta tuna cewa ya dawo, sai ta gyara zamanta kaɗan, “Sannu da zuwa,” ta faɗa cikin sanyayyar muryarta, Zayd bai juyo ba, “Yauwa, sannu da gida,” daga nan ya wuce kai tsaye zuwa bathroom, Raihana ta ɗan yi shiru, idanunta na bin sa har ya ɓace cikin bathroom ɗin, bayan ya shiga, sai ta sauke idanunta a kan ledojin da ya ajiye, da sauri ta ɗauke hankalinta daga kan ledojin, ta miƙe, sannan ta nufi hanyar fita, duk da cewa har yanzu akwai ɗan tsoro a zuciyarta saboda abin da ya faru da macijin, ta daure ta fita zuwa kitchen, tana shiga, sai ta fara haɗa masa abincin da ita da Maryam da Bintu suka dafa kafin su tafi, sannan ta shirya shi a tray mai kyau, ta ƙara ruwan sha, ta gyara komai yadda ya kamata, kafin ta ɗauki tray ɗin ta koma ɗakin, ba ta daɗe da zama ba sai Zayd ya fito daga bathroom, jikinsa a nade da towel a ƙugunsa, Raihana ta ɗauke kanta gefe da sauri, tana pretending kamar ba ta ganshi ba tun lokacin da ya fito, shi kuwa, bai nuna ya lura da komai ba, ya ƙarasa gaban dressing mirror, ya fara shafa lotion a hannunsa, sannan ya buɗe wani drawer yana neman brush din gashin shi, sai a lokacin idanunsa suka sauka kan kayan amfanin Raihana da suka mamaye saman dressing mirror ɗin, ya tsaya, ya ɗan zuba musu ido, man shafawa, turare, kayan gyaran fata, da wasu ƙananan abubuwa sun cika wajen, wasu daga cikin kayansa da suka saba kasancewa a kan mirror ɗin an matsar da su gefe domin a ba kayan nata gurbi kamar dai shine yazo ma dakin cin arziki, Zayd ya ɗaga gira a hankali, interesting, sai ya juya wajen wardrobe ɗinsa, da ya buɗe ta, sai ya ga wasu daga cikin kayansa an matsar da su gefe, yayin da kayan Raihana suka samu gurbi a ciki, ba wai kawai ta saka kayan nata a gefe ba, ta shirya su cikin tsari, har kaamr dai dakin ya zama nata gabadaya, ya ɗan tsaya yana kallon wardrobe ɗin, so, she has officially moved in, ba abin da ya ce, kuma bai tambaye ta komai ba, ya ci gaba da shirinsa cikin nutsuwa, kamar bai ga wani abu na daban ba, Raihana kuwa, tana zaune ne tana kallon tray ɗin abincin da ta shirya masa, lokaci-lokaci tana ɗan leƙen inda yake, ta ga yadda ya ɗauki wasu kaya, ya koma wardrobe, sannan ya sake fitowa, a ƙarshe, sai ya rufe wardrobe ɗin ya nufi inda ya ajiye kayansa, ya shirya cikin doguwar jalabiya mai kyau da wando, sannan ya ɗauki wayarsa, Raihana ta koma ta kwanta a kan sofa, ta ba shi baya, tana pretending cewa ba ta damu da duk motsin da yake yi ba, sai da Zayd ya gama shirya komai tsaf, ya saka wayarsa a aljihu, sannan ya fara takawa zuwa ƙofar da niyyar fita, a wannan karon, Raihana ta kasa yin shiru, ta miƙe zaune da sauri, “Ina za ka je kuma?” Zayd ya tsaya, ya juyo a hankali ya kalleta, yana Sauke lumshashun idanunsa a kanta, Raihana ta nuna tray ɗin da ke gefenta, “Ga abincin da na kawo maka nan, ba ka ci ba fa!” Zayd ya sauke idanunsa kan tray ɗin, ya ɗan tsaya yana kallon abincin da ta shirya masa a nutse, kafin ya ɗago ya sake kallonta, “Zan kwanta ne, kuma na ci abinci a wajen Ummie, I’m full, thank you,” Raihana ta miƙe tsaye gaba ɗaya, ta matsa kusa da shi, “Ban gane ba, za ka kwanta ba? To, ba gadonka nan ba? Ka kwanta mana!” Zayd ya zuba mata ido, ita kuwa ta ci gaba da magana kamar ba ta lura da kallon da yake mata ba, “Ai dama ya kamata ka kwanta ka huta, ka sha aiki sosai yau, kuma maybe gobe ma za ka sake fita, you need your rest,” Zayd ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe su a kanta, “Yeah, abin da zan yi kenan, but not here,” Raihana ta zaro ido kaɗan, “Kamar ya ba nan ba?” Ya ɗan daga gira, “Exactly what you heard,” da sauri ta girgiza kai, tana matsowa kaɗan kusa da shi, “Amma fa ka san ina tsoron kwana ni kaɗai!” Ta yi maganar ne da wani irin shagwaɓa, amma tana cikin furucin sai ta ɗan lumshe idanunta, domin a wannan lokacin ne ta fahimci yadda maganarta za ta iya fitowa, wayyo Allah na! Ta rufe baki na ɗan lokaci, amma duk da kunyar da ta ji, ba ta janye maganarta ba, ta ci gaba da tsayawa a gabansa, tana kallonsa da idanunta masu ɗauke da roƙo, “Yinin da na yi yau fa, ka san yadda ya kasance ni kaɗai, kuma yanzu ka dawo, amma za ka sake barina ni kaɗai?” Zayd ya ɗaga gira kaɗan, yana kallonta, a hankali wani ɗan murmushi ya yi ƙoƙarin bayyana a gefen bakinsa, amma ya danne shi kafin Raihana ta lura, “Oh, really?” Raihana ta jinjina kai da sauri, “Eh mana!” Zayd ya ɗan karkatar da kansa, “Na gama miki kwanakinki ai, ko ba ki kirgawa ne?” Raihana ta yi shiru, ya ci gaba da magana cikin nutsuwa, kamar dai yana magana ne a kan wani abu da ba shi da wani muhimmanci, “Seven days, cif, kuma ina fatan yau ba za ki ce na yi miki satar kwana ba,” ya ɗan dakata, idanunsa a kanta, “Na kai miki kwanakinki, as budurwa kwana bakwai, so, what’s the problem now?” Raihana ta buɗe baki, amma ba ta samu abin faɗa nan take ba, Zayd kuwa ya ci gaba, “Kuma don Allah, kada ki gaya min kina tsoro bayan da na fita yau, kin shiga ɗakinki har kin kwashe kayan amfaninki kin dawo da su nan, I thought you were brave enough to handle the room,” Raihana ta zaro ido, “Ni fa—” Ta tsaya, Zayd ya ɗan karkatar da kansa, yana jiran ta ƙarasa maganar, “Ke fa me?” Raihana ta haɗiye yawu, ta ɗan karkata kanta gefe, “Ni dai… kayan amfanin ne kawai na ɗauko,” “Exactly,” ya faɗa cikin nutsuwa, “Kuma ba ƙaramin kaya kika ɗauko ba, you practically moved half your room into mine,” Raihana ta ji kunya, amma saboda ba ta son ya ga ta rasa abin cewa, sai ta ɗan ɗan turo baki, “To, ai kayan amfanin nawa ne!” Zayd ya ɗan yi shiru, sai kuma ya sauke idanunsa a kanta, yana ƙoƙarin ɓoye murmushin da yake son bayyana, “Of course they are,” ya matso kusa da ita kaɗan, “Just make sure you lock your door properly before sleeping, hmm?” Raihana ta ɗan yi shiru, ta sauke idanunta, sai dai Zayd bai gama ba, ya ƙara matsowa kusa da ita har ta ɗan ɗago kanta domin kallonsa nan idanunsu suka hadu suka fara kallon juna ba ko kiftawa zayd ya zuba makale idanunshi cikin nata kamar zai cinyeta ta ido, a hankali ya ɗaga hannunsa ya shafa kumatunta da tafin hannunsa, Raihana ta tsaya cak, duk wata magana da take shirin yi ta tsaya a maƙogwaronta, Zayd ya ɗan karkatar da kansa, idanunsa a cikin nata haryanzu, kafin ya sauke muryarsa sosai, “Goodnight,” ya ɗan dakata, sannan ya ƙara da wata murya mai taushi wacce tayi kasa sosai, “And sleep like a baby,” Raihana ta kasa amsawa, ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta na bugawa da sauri, yayin da Zayd ya janye hannunsa daga kumatunta, bai jira ta ce komai ba, ya juya, ya buɗe ƙofar, sannan ya fita ya ja mata ƙofar a hankali, Raihana ta tsaya a wurin kamar wadda aka dasa, har Zayd ya daɗe da ficewa, sautin rufe ƙofar ne ya dawo da ita daga tunanin da ta faɗa, ta tsaya a inda take, idanunta a kan ƙofar da ya rufe, sai ta ɗaga hannunta a hankali ta taɓa kumatunta, a daidai inda ya shafa, sai kuma kamar an taɓa ta, ta juya da sauri ta nufi window, ta yaye curtains ɗin, nan ta hango shi, riƙe da ledoji a hannunsa, yana tafiya a hankali zuwa part ɗin Seeyama, idanunta suka bi shi without blinking, har ya isa bakin part ɗin, ya buɗe ƙofar ya shiga, sannan ya ja ƙofar ya rufe, ta daɗe tana kallon ƙofar, kamar tana jiran ya sake fitowa, but nothing happened, a hankali ta saki curtains ɗin, ta juya ta dawo bakin gado, sannan ta zauna a hankali, ta zuba wa wuri guda idanu, her mind suddenly filled with thoughts she couldn’t explain.