Free chapter · Read without an account
The Matriarch’s Exodus
by NorthernAngel · His Rose
Muryar Baffa a buɗe ya yi sallama cikin parlour’n Yemma inda duk suke zaune suna tattauna abun da Zara ta yi, sai zuga Yemma suke yi. Ganin Baffa a cikin parlour’n yana doso su ya sa duk suka yi shiru. Mutane irin su Hajiyar Sudan da Malika, ƙawar Yemma, ranar ne suka fara ganinsa a zahiri a duniya, mamaki ne ya bayyana a fuskokinsu. Sai dai ganin Zara a bayansa ya sa suka shiga mamakin gaske, suna kallonsu har suka ƙaraso. Baffa na isowa inda suke, kai tsaye ya je sofa ɗin da Yemma ke zaune ya miƙa mata hannu a gaggauce yana cewa, “Bani, bani!” Nan fa kowa ya tsit ana kallon ikon Allah, daidai isowar su Zafar da Muazzam da su ma sun ji abun da Baffa ya faɗa, sun kuma ga yadda ya taro hannu, duk sun gane Jasmine yake nufin a ba shi. Zara dai na tsaye a bayansa, ta yi folding arms ɗinta a ƙirji tana turo baki gaba, holding her ground with an understated yet triumphant presence. Yemma kuwa da wani irin mamaki take kallon Baffa, sannan ta kalli Zara. Baffa ya sa hannu ya karɓi Jasmine, yayin da ita kuma Yemma ta sakar masa ita ba shiri don kar su yi abun kunya a gaban mutane. Yana karɓarta ya juyo yana cewa, “Zara? Ina Zarar take ne?” Zara da ta matsa daga nesa ta ƙaraso tana cewa, “I’m here, Baffa.” Miƙa mata yarinyar ya yi yana cewa, “Maza, ku tafi gida before it starts raining.” Daga haka ya juyo yana kallon Yemma, “Daga yau kar wanda ya sake ɗauko yarinyar nan ya kawo ta nan.” Daga nan ya kalli Zafar da ke tsaye daga can ɓakin ƙofa yana kallon komai, Baffa ya fara magana cikin faɗa yana nuna shi: “Kai, ka na ji na? Kar a sake ɗauko yarinyar nan a raba ta da mahaifiyarta. This is pure insanity! In ba hauka ba, a ina aka taɓa yin haka? She is just a newborn baby! Yaushe ta yi girman da za a ɗauko ta a kawo ta nan for more than one hour without her mother's consent?” Ya sake juyawa yana kallon Yemma cikin tsantsar ɓacin rai, “Kuma mahaifiyarta ta zo ɗaukarta kin ce ba za ki bayar ba, duk kin tara mutanen banza kuna ta zaginta. A kan me? Saboda kawai ta ce ki ba ta ƴarta? Be honest with yourself for once, Aziza! If you were in her shoes, would you ever tolerate this? Ke ce zaki bar wani ya raba ki da jaririyar ɗiyarki har tsawon wannan lokacin? No way! You would have burned this entire place down to the ground! Shi ne yanzu saboda ita surukar ki ce, you think you can just walk all over her and insult her maternal rights? Toh daga yau kar a sake kawo yarinyar nan nan muddin ba ita Zaran ce ta ga dama ta kawo miki ita ba. This disrespect ends today! If you want to see her so badly, learn to respect her boundaries and go over to their place!” Ya kuma kalli duka ƙawayen nata cikin faɗa da zallan ɓacin rai, dominance ɗinsa gaba ɗaya na cika parlour’n yana cewa: “Sai kace ba ku haihu ba? Yanzu idan yaranku mata da ke gidan miji aka yiwa irin wannan cin zarafin za ku zuba ido? This is absolute wickedness and complete madness! Amma ba laifin ku bane, Aziza ce ta kasa sanar da ku wacece Zara acikin gidannan dukda da yawa acikin ku kun san Maryam. Or do you think because she’s an orphan, nobody has her back? Daga yau, kar wanda ya sake kuskuren shigo min gida yana cin zarafin yarana. Zagin Maryam kuma da kuka zauna kuka yi, ku da Allah! Amma Aziza, kar ki sake tara mutanen banza a gidan nan suna cin zarafin yarinyata under my roof. I will never tolerate such malice in this compound! Aƙalla ita Maryam ɗin ta gama lafiya ta bar muku duniyar cikin mutuncinta—ku da kuka zauna kuna aibanta macen dake ƙasa, ku kuka san amsar da zaku bawa Ubangijinku. Mutanen banza kawai! I will not allow anyone to destroy the peace of my family. Not today, and definitely not in my home!” Ya kalli Yemma, “Ki bi su can idan za ku yi irin wannan, not here.” Daga nan ya kalli Zafar cikin tsawa da kaifin ido yana cewa, “My friend, zo ka wuce ka kai iyalanka gida! Look at you standing there like a statue while all this disrespect is unfolding! Me kake tsaye kana kallo? Move your legs now, take your wife and daughter back to your house, and from today, make sure she is completely protected from all this toxic drama!” Zafar na tsaye yana kallon komai, fuskarsa nan a ɗaure ya sha mur, hannunsa na cikin aljihu yake bin kowa da kallo with a heavy, unreadable gaze. Ƙarasowa ya fara yi ba tare da ya ce komai ba. Zara kuwa Baffa ta kalla tana cewa, “Sai da safe, Baffa.” Cikin kulawa ya amsa mata yana sa mata albarka. Ta yi gaba ta nufi ƙofa, yayin da Zafar ya fara binta a baya yana ɗan satar kallon mahaifiyarsa cikin damuwa, saboda sosai ya ji ciwon abun da Baffa ya yi mata a cikin ƙawayenta. Sai da Baffa ya ga ya fice sannan shi ma ya juya, ya nufi ƙofar da za ta sada shi da private garden ɗinsa da zai koma ɓangarensa. Yana ficewa, Muazzam da Ahmad da ke tsaye kamar an dasa su suka bi bayansa, jikinsu duk a sanyaye—saboda ko a mafarki ba wanda ya taɓa tunanin Baffa zai iya yi wa Yemma haka. Tabbas idonsa ya rufe saboda ɓacin rai, wanda hakan ke nufin akwai abun da Zara ta faɗa masa da ya harzuƙa shi haka. Shi dai Muazzam tuni jikinsa ya sake sanyi da auren nan, saboda ya san ba yadda za a yi irin abubuwan nan na faruwa a ce Zafar na goyon bayan Zara, musamman yadda yake da mahaifiyarsa. Wani irin tausayin ƙanwarsa ne ya kama shi, wondering what else she was enduring in silence. Bayan fitar kowa, kamar babu abin da ya faru, Yemma ta ce a ci gaba da hira just to save face. Ta ma ƙi yarda sam a dawo kan maganar abin da ya faru dan kar zuciya ta ɗibeta ta samu baffa gaban jama’a. Sai dai su duka matan, jikinsu ya yi wani irin sanyi ƙalau, basu daɗe ba suka tashi suka ce za su tafi, they all made polite excuses and left. Daga ita sai Hajiyar Sudan da aminiyarta Malika aka bar su a cikin gidan, cike da makirci suka hau saka da warwara. A ɓangaren Zafar da Zara kuwa, ko da suka fito, Zara ta sa Jasmine da ke ta baccinta cikin pram ɗinta suka fara tafiya suka nufi gida. Wani nauyayan tension na shiru ne ke yawo a tsakaninsu—babu wanda ya ce wa wani uffan har suka isa gida. Zafar ya dakata a bakin matakalan entrance ɗin part ɗin Zara. Yayyafi ake sama-sama lokacin, dan haka da sauri Zara ta yi unclipping carrycot ɗinnan daga frame ɗin, and carried Jasmine straight inside. Shi kuma Zafar ya maida stroller ɗin zuwa parking space inda ruwa ba zai taɓa ba. Ai kuwa Zara na shiga, the light drizzle turned into a heavy downpour. Zafar sai motar Zaran ya shiga, ya kuma koma manor...
Zara na shiga ciki, ta shimfiɗe ƴarta completely unbothered, taje ta sauya kaya zuwa wani relaxed loungewear. Ta dawo ta kwanta a kan sofa in her bedroom, switched on the TV, ta fara kallo—completely at ease. Sai da aka kira Maghrib ta tashi tayo alwala tayi sallah….
Gurin 7:15pm Jasmine ta tashi daga bacci, lokacin ruwa ake tsugawa a waje ba ƙaƙƙautawa. Zara na cikin feeding ɗinta sai ga Zafar ya shigo, tsab-tsab da shi—looking completely untouched by the rain outside. Da waya a kunnensa ya shigo, ya wuce kai tsaye kan gadonta ya zauna yana ta wayarsa cikin yaren su. Har sai da Zaran ta gama ba Jasmine abincinta, sannan ya yi snapping fingers ɗinsa yana kallon bayanta. Ta juyo tana kallonsa. Hannu ya miƙa mata alamar ta ba shi Jasmine. Ba musu ta tashi ta je ta miƙa masa ɗiyarsa, sannan ita kuma ta koma sofa section ta ci gaba da kallonta. Sai da aka kira Isha’i ya tashi ya kai mata Jasmine inda take zaune, ya juya ya fice zuwa masallaci without uttering a single word. Har lokacin, no words were exchanged between them. Itama lura da yanayinsa yasa ta kama kanta, daman tasan he was bound to be bitter over the way she called out his mother—the untouchable matriarch da babu mai taɓa ta. Ita uwarsa shikenan duk abun da tayi taci bulus? Tunanin haka ya sa ta jan wani dogon tsaki, ta miƙe tsaye tana taɓe baki in sheer defiance. Nan ta hau shirin yi wa Jasmine wanka, ta danna intercom ɗin ɗakinta ta kira ɗaya daga cikin doulas ɗinta don ta taimaka mata. Tsab ta yi mata wankan, ta shafe ta da oil ɗinta, sannan ta shirya ta cikin pajama ɗinta tare da smart socks da sleeping sack. Ta hau ba ta nono, amma har ta gama yarinyar ba ta da alamar bacci. Haka ta yi ta kwantar da ita tsakiyar gadon tana ta mata wasa har guraren ƙarfe goma na dare. high-profile silence ɗin ya ci gaba lokacin da Zafar ya sake shigowa. Ya hau gadon ya ɗauki Jasmine dake kwance kusa da mamanta, daga nan ita kuma Zara ta tashi ta wuce bathroom ta yi wanka, ta gabatar da sallar isha, sannan ta shirya cikin comfy sleepwear ɗinta. Ko da ta dawo, ta karɓi Jasmine ta hau ba ta nono, inda nan da nan kuwa yarinyar ta yi nauyayan bacci. Bayan ta shimfiɗe ta, ta fice zuwa downstairs don ta yi dinner. Har ta sauka stairwell ɗin, sai ta tsaya ta sake wani tunani, sannan ta juyo ta dawo sama. A zaune inda ta bar shi a kan sofa ta tarar da shi—shiru shi kaɗai. TV ɗin a kunne yake yana haske bedroom ɗin, amma kansa na ƙasa ya dafe shi da hannayensa biyu, deep in his own heavy thoughts. Zara ta ƙarasa kusa da shi tana kallonsa cikin rashin fahimtar dalilin mood ɗinsa, ta kira shi a hankali: “Obim.” Ɗagowa ya yi yana sauke nauyayyen ajiyar zuciya, sannan ya ɗaura idonsa da suka yi jajir a kanta. Da mamaki, Zara ta isa gaban inda yake ta zauna a kan hannun sofa ɗin, tana tambayarsa cikin sanyayyen sautin murya, “Are you okay, honey?” Gyaɗa mata kai kawai ya yi, kafin ya koma ya ci gaba da dafe kansa, not even trying to hide his ruined mood. Sake tambayarsa ta yi, “Did you get a chance to eat?” Gyaɗa mata kai kawai ya yi a karo na biyu, amma a zahiri, rabonsa da abinci tun breakfast ɗin da suka yi tare da safe. Tun ɗazu bayan Maghrib da waɗannan baƙin suka tafi, ya wuce part ɗin Yemma da ke ta faman kiransa a waya. Tun lokacin yake aikin ba ta haƙuri yana lallashinta, amma sam Yemma ta tubure! Ta ce a yau sai dai ya zaɓi ɗaya—ko ita ko Zara. In kuma ba haka ba, za ta bar musu estate ɗin ta koma inda babu wanda yasani gobe. Hakurin duniyar nan ya ba ta, amma ta ƙi saurara masa. Ta rantse cewa indai bai saki Zara a yau ba, gobe da safe za ta wuce wata ƙasar, kuma kar ya sake kiranta mahaifiyarsa. Tun bayan Maghrib har aka yi Isha'i ya fita ya yi sallah ya dawo, su biyun suna kan abu ɗaya. Har ƙarfe goma ta shige bedroom ɗinta ta rufe ƙofa tasa locks ta bar shi a zaune a parlour, shi ne ya taso ya dawo gida rai a ɓace. Sosai Zara ta ba shi haushi, saboda irin wannan yanayin yake guje musu shiga tuntuni, gashi yanzu an kai gabar da ya fi tsana ya kuma ta gujewa a rayuwarsa. How on earth could his mother pack her bags and leave her husband’s house over his marriage? What kind of son will that make him? Gaba ɗaya kansa ya ɗauki zafi, ya rasa inda zai sa ransa ya ji sanyi. Zara da ke kallon yadda yake furzar da numfashi akai akai, ta ɗan shafa kansa tana sa yatsun hannunta cikin soft curls ɗinsa, ta ce, “What’s wrong, Obim? Are you sick?” Bai ɗago ba, kuma bai ce da ita uffan ba. Zuciyarsa gaba ɗaya ta rufe, babu wani ɗan spote na jin daɗi. Shi ya san halin da ya ga Yemma a ciki, ya kuma san ko wace ce ita. Ya san lokacin da take barazanar ta, da kuma lokacin da take da gaske—and tonight, he knew she wasn't playing at all. There was zero bluff in her threat. Zara kuwa, ganin ya share ta completely, ya sa ta miƙe tsaye sum-sum ta fice daga bedroom ɗin, ta koma ƙasa zuwa dining room ɗinta. Nan ta zauna ta yi dinner ɗinta cikin kwanciyar hankali, saboda duk a tunaninta, haushinta kawai yake ji a kan abin da ya faru a ɓangaren mahaifiyarsa ɗazu. Ta gama cin abinci kenan ta fara jin yar hayaniya—a continuous, aggressive barking sound da ya cika parlor ɗin. Haushin karnukan da ta fara jiyowa ba ƙaƙƙautawa ya sa ta tashi da sauri ta buɗe ƙofar dining room ɗin. Ko da ta fito, daga ƙofar kitchen ta fara hango su. Tana isa ta tarar da mai aikinta Jummai, wata maid ɗinta Fatii, da kuma wannan maid ɗin da ta gani da safe wadda ba ta gane ba. Sai kuma Panther da Ghost da ke ta zazzaga haushi non-stop, yayin da Jummai ke ta magana tana nuna ƙofa, amma ba a jiyota saboda haushin da karnukan ke yi. Da mamaki Zara ta ƙarasa, amma sai ta fara ƙoƙarin calming the dogs down tana jan su har suka fito foyer, inda ta tarar da Yeti a gurin shi ma yana gurnani softly. Abun mamaki ya ba ta, dan duk sun saba da maids ɗin. Ko da ta dawo lokacin da aka kawo su, duk ba su wannan halin in suka gan su. Hakan ya tabbatar mata da ɗayar nan da ba ta gane ba sabuwa ce—shi yasa ɗazu ta ga Ghost na ta muzurai ya hawo saman yayin da maid ɗin ta hawo. Bayan ta fita da su ta dawo, Ghost ya sake biyo ta, sai dai shi ba ta hana shi ba dan ta san he’s harmless compared to the rest. Tana dawowa ta gansu still staye gurin Jummai na ta faɗa: “Ki ka ce ta ce cikin gida zaki riƙa shigowa ki zauna? Toh ba nace miki ki dakata sai an yi magana da ita mai gidan ba? Kuma ya zaki riƙa shigowa anyhow bayan ba a yi assigning ɗinki ki yi aiki a nan ba? Gashi dogs ɗinnan duk ba su saba da ke ba suna ganinki suke fara haushi, na ce miki ki dakata da shigowa amma kin ƙi ji! I don't even know what brought you here this late at night!” Zara ta ƙarasa inda suke tana ɗaure short robe ɗinta da kyau tana rufe ƙirjinta. Da tsantsar mamaki ta tambaya, “What’s going on here, Aunt Jummai?” Juyawa Jummai ta yi ta kalli Zara ta fara mata bayani a tsanake. “Tun kwana huɗu da suka wuce, last zuwan madam Galado gidan nan, ta zo da wannan yarinyar a kan za ta riƙa aiki a nan.” Ta nuna ɗayar maid ɗin tana cewa, “Fatii gata nan, ita ta tambaya wacece head of maids aka ce mata Lucy ce, ta ce a kira mata Lucy. Kina sama a lokacin. Da Lucy ta zo, sai ta damƙa mata yarinyar ta ce ta ba ta aiki a cikin gidan nan. Har ta nuna mata waccan ɗakin na cikin foyer ta ce ta sa kayanta a nan. Ni ina gurin, da kaina na ce mata ɗakin dogs ɗin gidan nan ne, na kuma yi mata bayanin akwai ɓangarenmu masu aikin gidan nan, amma sai ta ce a cikin nan take so ta zauna. Ta nuna mata ɗakin da ke nan parlourn ta kai kayanta nan.” Jummai ta goge gumin da ke tsattsafo mata tsabar masifar da take tun ɗazu, kafin ta ɗora, “Ko da ita Madame ɗin ta tafi dare ya yi, shi yasa ban sanar miki ba, kuma ma duk mun yi zaton dole ta sanar miki da kanta. Bayan tafiyarta, da kaina na samu ita yarinyar nan na faɗa mata ba mai yiwuwa ba ne, ba maid ɗin da ke kwana cikin gidan nan, dan haka ta taso mu je can ɓangaren masu aiki. Da ƙyar na samu ta yarda, saboda har rashin kunya ta yi min wai ita nan mahaifiyar mai gidan ta kawo ta ta ce ta zauna! Bayan na samu ta koma can, sai na kai ta ɗakin Fatii dan ita ce ba ta da roommate. Washe gari tana tashi ta yo nan, sai dai karnukan suka yi ta haushi da su ka gan ta. Da Fatii ta sanar da ni, sai na gaya wa Lucy. Da Lucy ta sa a kira ta, sai ta yi mata warning a kan shigowa nan ɗin. Nan ma ta yi taurin kai ta ce nan mahaifiyar mai gidan ta ce ta riƙa zuwa tana zama. Lucy ta jaddada mata a kan dole sai an sanar miki kafin ta fara aiki a nan ɗin, amma ta ƙi ji! Kullum sai ta shigo nan kuma babu aikin da take yi; sai ta ga karnukan ba su nan take shigowa ta kunna TV ta zauna, ba ta jin maganar kowa! Yanzu Fati ta sanar min da ta gan ta ta fita daga ɗaki cikin daren nan ta biyo ta ta ga ta shigo nan. Shi ne na zo na tarar da ita, gashi karnukan nan sun jita sun fito sai barking suke suna ma neman kai mata hari ko da nazo.” Tunda Jummai ta fara magana, Zara ke kallonta tana jin abun kamar wani surreal nightmare. Yaushe Yemma ta kawo yarinya cikin gidan ta, kuma ba ta sani ba? What on earth was her motive for planting a random house girl right inside her personal space? Cikin rudani da tsantsar shock, ta kalli yar aikin da ke kallonta ido a tsai-tsaye—completely unbothered da irin bayanin da ake yi a kanta. Zara ta ma ƙasa cewa komai, sai kallon yarinyar kawai take yi with her heart pounding. Fatii ta kalla, muryarta na ɗan rawa ta ce, “Call Lucy for me.” Daga haka ta juya, jikinta na rawa ta shiga dining room ta ɗauko wayarta da ta bari a ciki. Sannan ta sake fitowa, her hands visibly trembling as she dialed Zafar’s number. Ya na ɗagawa, kai tsaye ta ce masa, “Come downstairs.” Daga haka ta yanke kiran, ta hau safa da marwa a livingroom ɗin, tana kallon yarinyar da ke tsaye completely unbothered kamar ma tana cikin gidan babanta. Zafar ne ya fara saukowa kafin Lucy ta iso. Yana zuwa gurin, idonsa ya sauka kan maid ɗinnan. Tun kafin Zara ta ce komai, ya yi magana yana kallon yarinyar, “What are you doing here?” Da sauri Zara ta kalle sa tana cewa, “You know her?” Gyaɗa kai ya yi, idonsa na kan yarinyar ya ce, “She’s Yemma’s maid. Me ya faru?” Daidai lokacin Lucy ta shigo, ta hau gaishe su. Zafar ya sake tambayar abun da ke faruwa saboda ya rasa yadda aka yi yar aikin Yemma ta zo gidan, kuma sanye da uniform ɗin maids ɗin Zara a jikinta. Zara dai ta ƙasa magana; gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan dalilin Yemma yin wannan zallan iskancin da ikon banzan. Wuce su ta yi ta nufi ciki ta bar sa tsaye a gurin. Zafar kuwa hau tambayar Jummai daya shaida me ke faruwa, inda ta fara koro masa bayani tiryan-tiryan kamar yadda ta yi wa Zara. Bayan ta gama, ya hau kiran Yemma a waya ɗan ya ji ko da gaske ne da kuma dalilin yin hakan da ta yi, sai dai har ta ƙatse ba ta ɗaga ba. Nan ya kalli Lucy ya hau yi mata faɗan dalilin da yasa ba ta sanar wa Zara ba. Sosai ya yi masifa in sheer frustration, inda daga ƙarshe ya ce daga yanzu Jummai ce shugabansu—tunda daman tana ɗaya daga cikin masu shekaru a ƴan aikin gidan, kuma ya ga Zara ta yadda da ita tun tafiyarsu Saudi da ita. Daman dalilin da ya sa aka sanya Lucy saboda ita ta san tsarinsu ta kuma san komai a kan Zara, amma yanzu tunda duk sun yi adapting, ai ya kamata a sanya babba mai tunani. Nan kuma ya juya kan Jummai ya hau mata ƙashedi: kar a sake kawo wata daga main manor a ce wai za ta yi aiki a nan, ko waye ya kawo ta, dole a sanar wa Zara tukunna. Bayan ya gama, ya ce wa yar aikin Yemma ta biyo shi. Zuwa lokacin ruwan ya rage sosai, sai yayyafi ake yi. Main manor suka je har ɓangaren Yemma, inda ya hau ya tarar da Fadma da ke sanar masa a kan Yemma ta ce kar wanda ya dame ta, ta riga ta shiga bacci. Juyawa ya yi ya koma ƙasa, inda ya yi wa yarinyar stern warning a kan kar ta sake kuskuren takawa zuwa gidan nasa. Daga haka ya fice gaba ɗaya ya koma gidan. Ko da ya koma, duk sun watse. Sama ya hau, sai dai yana shiga ya tarar da Zara sai safa da marwa take ita kaɗai a private lounge ɗinta. Tana ganinsa, ta hau magana da sauri cikin ɗagawa murya. “Your mother wants to get rid of me, Zafar! She literally wants me dead! Who knows what instructions she gave that strange girl? What if she paid her to slip poison into my food or hurt my baby?! Ni kam na gaji wlh! That woman will never stop, she won’t rest until she sees my blood or drives me completely insane! I know it!” Cikin tsawa Zafar ya katse ta, “That’s my mother you’re talking about, Zara! Watch your damn mouth! Yemma can be mean, she can be unbearable, but she is NOT a killer! How dare you accuse her of something so insane? I’m sure she doesn’t mean that kind of harm, so stop inventing wild stories in your head!” Ɗakatawa Zara ta yi tana kallonsa. Kana ganinta ka san she’s very distressed—duk ta rikice ta tsorata, ɗan har zuciyarta gani take Yemma na son kashe ta ne. Cikin ɗaga murya ta ce, “Oh please, save those sweet lies for someone who actually believes them! We both know your mother is capable of anything just to get rid of me! Ni dai ba zan zauna a kashe ni ba, I won’t take any stupid chances with my life or my baby’s! I am leaving for my father’s house this exact night!” Daga haka ta juya ta shiga ɗaki. Jikinta na rawa ta shiga praying corner ɗinta, ta saka doguwar rigarta da ta yi Isha'i da ita, ta fito tana ta ƙoƙarin reaching Muazzam a waya amma sam ba ta samun sa. Ko da ta fito, Zafar na tsaye bakin ƙofa yana kallonta. Cikin zafin murya ta ce, “Give me way!” Kai tsaye ya sha gabanta tare da jefa mata kallo mai cike da tsananin gargadi da bacin rai, ya ce, “Stop being so utterly overdramatic, and don’t you dare drag a third party into this, Zara! I am positive if there’s any reason Yemma sent that girl here, it was simply to keep tabs on us and figure out what’s going on in this house—nothing more! Stop making up wild stories in your head!” Cikin halin ko-ta-kwana da rashin sauraronsa, Zara ta ce, “Look, I don’t give a damn about whatever excuses you’re making for her! All I know is that your mother is actively targeting me, and I am going to report every single detail to my family right now—just in case something terrible happens to me!” Bai ce mata komai ba. Cikin sauƙi ya duƙa ya ɗauke ta sama—bridal style—bai ɗire ta ko'ina ba sai kan gado. Kai tsaye ya fara smooching ɗinta yana ƙoƙarin undressing ɗinta. Tun tana fighting ɗinsa har ta ƙyale shi, saboda ta lura he’s completely not himself tonight. Ko daga yadda ya ƙi biye mata su yi faɗa ma ta sani. Shi kuwa gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake da maganar da Yemma ta yi masa a kan sai dai ya zaɓa—ko ita ko matarsa. Ga kuma wannan sabuwar drama ɗin da Zara ta ɓullo da ita, har tana yi masa barazanar za ta koma gida, duk da ya san ba za ta iya ba duk bige ce. Amma sam baya so ta sako ko wane ɗan uwa a cikin maganar don kar a ƙara tunzura Yemma. So this was the only way to calm his nerves down—this raw distraction. He desperately needed it! Wata duniyar daban suka shilla cike da tsantsar desire, nutsuwa, da kuma ƙaunar juna mai ban mamaki—a completely raw and mesmerizing passion. Musamman shi Zafar, da a wannan daren yake jin wani sabon sonta mai zafi na ratsa duk wata jijiya da kafar jikinsa, impossibly deep. Duk wannan overwhelming stress ɗin, suffocating tension daga threats ɗin Yemma, da kuma heavy family drama just melted away the moment he held her close. A wannan daren, ba wai kawai don ya rabu da damuwa yake nemanta ba; he was clinging to her like his very life depended on it. Ko wanne stroke, ko wanne breath, and ko wanne touch felt like a desperate vow to protect what they built—wani unspoken promise akan no matter how chaotic the world outside became, she was his absolute anchor, his home, da kuma center of entire existence ɗinsa...
Washe gari bayan ya fito daga masallaci, ya shiga wing ɗin Yemma. Amma tun a parlour’n ƙasa ya tarar da Noor a zaune ta yi tagumi, ta rungume Imaan da ke ta faman kuka a jikinta. Da tsantsar mamaki ya ƙarasa ciki yana tambayar, “What’s going on here?” Noor ta ɗago tana kallonsa, kai tsaye ta ce masa, “Yemma left! Since 4:00 this morning ta tattara kayanta ta fita, wai airport za ta je! She didn’t even deign to tell us where she’s going, but she gave Imaan a message for you—that if you ever want her back in this house as your mother, you know exactly what sacrifice to make! And honestly, Yaya, none of this toxic nonsense is worth it! Imaan went to Baffa in tears to break the news, but Baffa just coldly dismissed it and said we should let her walk away! Do you seriously think keeping Zara in your life is worth destroying our mother’s marriage and completely fragmenting this entire family?! How on earth does Zara have the sheer audacity to go behind your back, report Yemma to Baffa, humiliate our mother, and still sit comfortably in your house playing the precious wife?! Do you even care about your own mother’s dignity at all, or has that girl completely blinded you?!” Ta ƙarasa maganar cikin ɗaga murya tana miƙewa tsaye in pure anger and disrespect. Bai kula ta ba, ya juya kai tsaye saboda idan ya tsaya, zai iya yi mata abin da bai taɓa yiwa wata mace ba a rayuwarsa. Yana fita, ya hau kiran P.A ɗinsa a waya ya sa a bincika masa ko Yemma ta riga ta tashi a ɗaya daga cikin family pjs ko flights ɗin safe. Daga haka ya koma gida, bai shiga ciki ba, ya shige motarsa ya bar estate ɗin gaba ɗaya...