Free chapter · Read without an account
BABI NA UKU
Na yi tsammanin magana ta ƙare, sai ji na yi ya ce.
“Muhammad Zaid ya kira ni yanzu ya ce gobe zan yi tafiya Kano za ki raka shi.”
Gabana ne ya faɗi a hankali na ɗago idona.
Mama ma ta ɗan kalle Abba da ya ci gaba da magana.
“Ya sanar da ni tafiyar da zai yi Kano, kuma na ce Allah ya kiyaye sai ki shirya ko?”
Numfashi na sake a hankali, ina cewa.
"To Abba Allah ya kai mu."
Kasa haƙuri Aunty Mansura ta yi sai da ta yi magana ta ce.
"Abba kuma daga shi sai ita za su tafi?"
Shiru Abba ya yi kamar ba zan yi magana ba, sai ya ce.
"A'a ya ce min tare da waye ɗalibai ne, to amma ke ina ruwanki?"
Shiru falon ya yi, babu wanda ya sake magana, abinci na ci sannan na yi musu sai da safe.
**************
Dare.
Ina zaune akan gado ina duba wayata.
Tun bayan sauke ni da ya yi a gida bai kira ni ba.
Bai yi text ba, babu kira.
Ni kuma na kasa kiransa. A haka na kwanta ina tunanin shi, ga kuma abin da yake damuna, wai Kano da zan bishi.
Can ƙarfe goma da rabi na dare,wayata ta yi haska.
Da sauri na ɗauka, ina dubawa
My Zaid️
Da na gani ne yasa wani irin farinciki ya rufe ni, amma hausawa sun ce mai hali baya fasawa.
Sai da na bari ta yi ringing sau biyu kafin na ɗaga, ciki ciki na ce.
“Assalamu alaikum.”
Muryarsa a kasalance, ya ce.
“Wa alaikum salam.”
Shiru na ji ya yi na gane har yanzu yana fushi,na ciza leɓena, ina kashe murya na ce.
“Prof...”
“Hmm?”
Ya ce kamar an yi masa dole.
“Ka yi fushi da ni ne?”
Na faɗa ina turo baki kamar yana gabana.
Shiru ya yi na wasu dakiku.
Sannan ya ce.
“Ke da gaske kin ɗauke ni wani Namiji ne daban ko?”
Kunya ce ta kama ni, na yi ƙasa da murya na ce.
“Ba haka nake nufi ba fa.”
“Amma abin da kika faɗa kenan.”
Ya faɗa, da alama fushi a muryarsa.
Shiru na yi can dai na ce.
“To ka yi haƙuri.”
Numfashi, ya sake a hankali ya ce.
“Ki sake faɗa.”
Da mamaki na ce.
“Me?”
“Ki sake cewa yi haƙuri.”
Dariya ta kusa kufce min, na ce.
“Prof fa...”
“Na ce ki sake.”
Ya faɗa, da ɗan zafi.
Murmushi na yi kaɗan na ce.
“Yi haƙuri.”
“Again.”
Na rufe fuskata, na sake cewa.
“Yi haƙuri.”
Sai ya yi dariya a hankali, ya ce.
“Allah Noor."
“Me?”
Na faɗa ina turo baki cikin shagwaɓe.
“Kin san ba zan iya yin fushi da ke ba.”
Wani irin daɗi na ji, ya kama ni, sosai, kafin in yi magana...
Na ji wata muryar daga bayansa.
“Professor!”
"Yes."
“An kawo takardun meeting.”
Na gane ba shi kaɗai ba ne, a hankali na ce.
“To ka je aikinka.”
“Kin kore ni?”
Ya faɗa da ɗan murmushi a murya shi.
“Ni kuma?”
“Wallahi ba zan kashe wayar ba.”
A yadda ya yi maganar sai da dariya ta kwace min, na ce.
“Prof!"
Shi ma ya yi dariya.
Cikin sanyin murya, ya ce.
“Noor...”
“Hmm?”
Na faɗa ina gyara kwanciyata.
“Na yi missing ɗinki, ban ji daɗin abin da ya faru ba."
Ban san me zan ce masa ba, sai kawai na yi shiru.
Shi ma ya yi shiru na ɗan lokaci kafin cikin sanyin murya ya ce.
“Kin yi shiru kuma.”
A hankali na ce. “Ni ma ban ji daɗin abin da ya faru ba I'm sorry."
Numfashinsa na ji ya sauka a hankali, sannan ya ce.
“Da gaske?”
“Eh.”
“Amma kin sa na fara tunanin ba ni da wani matsayi a zuciyarki.”
Da sauri na ce. “Ba haka ba ne fa.”
“To yaya ne?”
Shiru na yi.Ban san yadda zan faɗa masa ba.
Dariya ya yi kaɗan sannan ya ce.
“Ki bar shi. Na ji.”
Sai wani irin kunya ta kama ni.
Can ya ce.
“Kin shirya tafiyar Kano?”
“Ban ma fara shiri ba.”
Na faɗa ina tashi zaune.
“Ki fara.”
Ya faɗa kai tsaye.
“Me zan?”
Na kasa ƙarasa maganar ina yin shiru.
“Duk abin da kike buƙata. Ba za mu daɗe ba.”
Kai na gyada kamar yana ganina, na ce.
“Okay.”
“Good girl.”
Da sauri na rufe fuskata da pillow.
Wannan mutumin yana da wata hanya ta musamman da yake sa zuciyata farin ciki.
Maganar Mama ce tasa ya kashe wayar, tashi na yi ina buɗe mata ƙofa.
Kallon fuskata ta yi tana cewa.
"Kin shirya kayanna ki ne?"
Ƙasa na yi da kaina na ce.
"Ni ban san irin kayan da zan shirya ba, kuma fa dama na faɗa masa ni ba zan bishi ba, shi ne ya faɗawa Abba."
Zama ta yi a gefen gadona ta ce.
"Oho ashe kin san da tafiyar ko?"
Shiru na yi ina rubuta wa Hafsat message akan tafiyar da zan, amma ban sanar da ita Kano zan tafi tare da Prof Muhammad Zaid kawai na ce zan yi tafiya garinmu.
Ina gama rubuta mata na ga Mama ta shirya min kayana, na yi farinciki sosai, bayan ta gama shirya kayan ne, ta zuba min ido tana kallona.
Ƙasa ta yi da murya ta ce.
"Don Allah Uwata ki kula sosai, ba na so ki ɓata masa rai, duk wani rashin mutuncinki ki ajiye sakin dawo gida."
Murmushi na yi na ce.
"To Mama dama ai shi bana masa rashin mutunci."
"To sai da safe."
Har ta je baki ƙofa na ce.
"Mama me kike so na taho miki da shi?"
"Dama kina da kuɗi ne?"
Jin abin da Mama ta faɗa ne yasa na yi ƙasa da murya na ce.
"Ba shi ne ya ce duk abin da nake so na tambayeshi ba."
"To bana son komai, kuma ban ce ki tambayeshi wani abu ba."
"Allah ba da haƙuri."
Ina faɗar haka na kwanta ina ƙananun maganganun, akan me za'a ce ba zan tambaye shi wani abu ba, bayan shi ne ya ce na tambaye shi.
Washegari tun da asuba da na yi wankan tsarki na yi sallah, na zauna ina addu'a.
Tun kafin na tashi na ji messages ɗinsa suna shigowa har guda biyu, hanuna na miƙa na ɗauko wayar.
"Ki tashi ki yi sallah."
Shi ne abin da ya rubuta a farko.
Na biyu kuma:
"Kar ki manta da breakfast."
Murmushi na yi ina kallon wayar.
Replying na yi masa da.
"Na gani Prof."
Nan take ya dawo min da.
"Good."
Wayar na ajiye na fita, domin yin aiki, a ranar duk ni ce na yi aikin komai, sai bayan na yi wanka na shirya ne, sannan su Aunty Mansura suka fito.
Sai bayan kowa ya fito ne, sannan muka fara cin abincin, sosai na ci abincina, Umar ne ya yi dariya yana kallona ya ce.
"Aunty Maryama ta yi kyau Abba."
Dariya duk muka yi sannan na kama kumatunsa na ce.
"Ashe Umarun Mama kallona yake yi ban sani ba."
Kafin wani ya yi magana Prof Muhammad Zaid ya yi sallama, amsawa Abba ya yi yana murmushi, kusa da Abba ya zauna, ya gaida su Mama.
Asiya ce ta fara gaida shi tana tashi domin tafiya Makaranta, sai bayan su Aunty Mansura sun gaida shi ne, na ɗago kaina na ce.
"Good morning."
Hannun Umar ya kama ba tare da ya amsa min ba, a hankali Umar ya ce.
"Yaya ka ga Aunty Maryama ta yi kyau sosai kuma anguwa za ta tafi."
Murmushi yake yi wa Umar sai ya ɗago kaina ya ce.
"Ina so zan yi breakfast."
Abincin da nake ci na tura masa gabansa ina tashi daga wajen, murmushi ya yi zan fara ci Ummah ta yi saurin cewa.
"Haba Muhammad Zaid, da girmanka za ka ci sauran abincin, a'a ba za'a yi haka ba Ke! Mansura zuba masa wani."
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Is okay, thanks."
Haushi ne ya kama Ummah, ganin Abba ban ce komai ba, akan abin da na yi, kasa haƙuri ta yi ta ce.
"Ai dama Uwar masu gida, ba mutunci ne da ita ba, yanzu sabo da Allah dan ka ce zaka ci abinci shi ne za ta turo maka nata kamar wani almajiri."
Katse mata maganar ya yi yana cewa.
"Abba za mu tafi, amma kawana biyar kawai za mu yi."
Dariya Abba ya yi tare da cewa.
"Allah ya kiyaye hanya, sai kun dawo, ni ma ka ga fita zan yi."
Tashi Abba ya yi suna yin sallama da shi, sai bayan ya gama cin abincin sannan ya kira wayata akan na fito, a lokacin muna tare da Khadijah ita ce ta fito min da kayana, sannan na shiga ɗakin Mama, sosai ta yi min faɗa.
Kuma na ɗauki duk abin da ta faɗa min, har ɗakin Ummah na shiga na yi mata sallama, Aunty Mansura kamar ta yi kuka haka ta biyo ni waje.
Shi ne ya buɗe min ƙofa sai bayan na shiga muka yi sallama da Khadijah da ta riƙe hannuna.
Ina kallon Aunty Mansura a tsaye ta kasa tafiya har muka fita daga layin gidanmu.
Muna hawa titi na kallon fuskarsa na ce.
"Good morning My Zaid."
Murmushi ya yi yana kama hannuna ya ce.
"Morning Noor ya aiki, dan na san ke ce ki yi abincin nan."
Murmushi na yi ina cewa.
"Eh, ni ce ya yi daɗi ne?"
Wayarsa da Ahmad Zayyan ya kira ne ya hana shi magana.
Da murmushi akan fuskarsa ya ɗaga.
"Ahmad Zayyan na fito fa."
Ban san abin da Ahmad Zayyan ɗin ya ce amma na ga ya yi dariya yana kallon fuskata, sai kuma ya tsaya a gafen titi.
Ɗago idanuna na yi domin ganin dalilin tsayawa, sai na ga Ahmad Zayyan ya fito daga motarsa, yana murmushi.
Dariya Ahmad Zayyan ya yi tare da cewa.
"Amarya ya gida?"
Kunya ce ta kama ni, na rasa abin da zan ce kawai na kawar da kaina gefe.
Ban san abin da ya ba shi amma na ga yasa abu a aljihunsa, sannan Ahmad Zayyan ɗin ya yi masa magana a kunne suka yi dariya.
Rufe motar ya yi yana cewa.
"Sai mun yi magana."
Cikin dariya Ahmad Zayyan ya ce.
"To amma a kula mana da amarya fa, dan na ga rawar ƙafa kake."
Kallon fuskata ya yi yana kunna motar, sai bayan mun yi nisa da Ahmad Zayyan ɗin ne, na ji yana matsa min hannu.
Shiru na yi ina tunanin wannan tafiyar kamar da abin da Prof Muhammad Zaid ya shirya, message A'isha ta yi min, kamar ba zan duba ba, sai kuma na duba.
"Assalamu alaikum Maryama ya hanya, ashe tafiya yawon amarci kuka yi, to Allah ya kiyaye hanya amma a dawo mana da tsaraba."
Da sauri na rubuta mata,
"Ke! Waye ya faɗa miki? Ni fa cewa ya yi aiki aka turashi Kano."
Minti biyu tsakani ta sake rubuta min.
"Waye ya faɗa miki? To wallahi amarci ya tafi ci,🤣🤣."
Da sauri na juyo na kalleshi, murmushi ya yi min tare da kashe min ido.
Muryata na rawa na ce.
"Wai da gaske dama ba aiki aka turaka ba?"
Shagwaɓe min fuska ya yi tare da cewa.
"Uhm uhm ni aiki zan yi kuma tare da sauke nauyin Matata da yake kaina, kin fahimta."
Hawaye ne suka zubo min, bakina na rawa na ce.
"Allah sai ka maida ni gida, dama haka ake yi."
Sauka ya yi daga kan titi sannan ya tsayar da motar yana murmushi ya ce.
"Haba Noor, hawaye fa kike yi, ni ne ba kya son? Kuma da kika ce ba haka ake yi ba, ai ba laifi ba ne, ke fa Matata ce."
Kasa magana na yi sai kuka da yake son yafi ƙarfina, hannunsa na ji, a cinyata ya ɗauke wayata, sannan ya rungume ni sosai, har sai da na yi shiru ina sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce.
"Noor don Allah ki rufa min asiri, Allah ba na son wannan hawayen."
Cikin kuka na ce.
"Don Allah Yaya Muhammad ka maida ni, gida, ni gaskiy.."
"Ke! Gaskiya me?
Ya faɗa rai a ɓace, shiru na yi ban yi magana ba.
Motar ya ja da mungun gudu, har muka isa garin Kano bai sake magana ba, wani gida ya shiga, gida ne mai kyau sosai, ya haɗe sosai.
Shi ne ya buɗe min ƙofa, tare da kama hannuna, cikin nutsuwa yake jana, dan jikina duk ya yi sanyi, bana iya tafiyar ma.
"Ma sha Allah."
Shi ne abin da na faɗa a zuciyata lokacin da muka shiga cikin falon gidan ya yi kyau sosai.
Zama ya yi tare da yi min masauki a cinyarsa, shiru na yi jikina ya rawa, Allah ya sani na gama tsorata, na san da za'a tsaga jikina a lokacin da wuya a samu jini.
"Noor"
"Uhm"
Na ce, ina sake riƙe hijabin jikina.
Kwantar da kansa ya yi a ƙirjina yana sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Noor ki sake jikinki, babu kowa a gidan nan daga ni sai ke, don Allah ka da ki ɓata min tsari, na shirya abubuwa da dama, a wannan tafiyar."
Gyara zama na yi a cinyar tasa ina kasa magana domin ban san abin da zan ce ɗin ba.
"Noor, tashi mu shiga ciki, mu huta dan bacci nake ji, kuma zuwa yamma zan shiga meeting."
Shi ne ya ɗaga ni, yanzu ma ya ja hanuna har cikin bedroom ɗin gidan.
Daga bakin ƙofa na tsaya, ina kasa shiga, kwanciya ya yi, tare da cewa.
"Zo mu kwanta Noor, wai lafiya duk jikinki ya yi sanyi haka?"
Kuka ne ya kama ni da gudu na faɗa kansa ina kuka na ce.
"Ni don Allah ka maida ni gida, ai ba haka ake yi ba."
Rungume ni ya yi yana murmushi ya ce.
"Yawwa Noor, mu yi bacci ko? Zuwa yamma sai mu fita."
Dukan kafaɗarsa na yi ina cewa.
"Wai baka ji abin da nake faɗa ba ne?"
Dariya ya yi tare da riƙe hannuna ya ce.
"Na ji Noor, amma babu batun komawa gida, sai mun huta kamar yadda kowane Miji da Mata suke yi."
Kafin na yi magana ya matsi ni sosai a jikinsa, numfashi na a hankali nake yi.
Na jima a jikinsa, sannan ya rufe min baki da nasa, ban san tsawon lokacin da ya ɗauka yana tsotsar bakina ba, amma ni ma kaina na ji sanyi a cikin zuciya.
Yana fitar da bakinsa na kwanta a gefe ina sauke numfashi jikina ya sake yin sanyi, ko magana na kasa yi, ina jin sa yana cewa.
"Noor, tashi ki cire hijabin nan, ka da ki kwanta da shi."
Amma na kasa tashi, shi da kansa ya cire min hijabin, sannan ya saka ni a jikinsa ban san lokacin da na yi bacci ba.