Free chapter · Read without an account
BABI NA HUƊU
*************** Aunty Mansura.
Kuwa da kuka ta shiga gida bayan tafiyarmu, sosai Ummah ta bata haƙuri, a ranar bata je Makaranta ba.
Iya Khadijah ce ta shiga Makarantar.
A ɓangaren su Hafsat da Samiha ma sun kira wayata bata shiga, dole sai haƙura suka yi.
*************
Lokacin sallah ne ya tashe mu, tare da shi muka yi, sannan ya fita, bai jima ba ya shigo mana da abinci.
A falon muka ci abincin, sannan muka zauna yana ba ni labarai iri-iri, har na saki jikina, na fara dariya, ya ji daɗin ganin na saki jiki ina dariya, ya cigaba da ba ni labarai sosai.
Sai yamma sannan ya fita, ni kuma na kwanta ina amfanin da wayarsa da ya ba ni, har bacci ya kama ni, a wajen.
Sai ku san sallah magriba sannan na farka da na buɗe idanunna na ji gidan shiru, babu motsin kowa, sai na ɗan tsorata.
A hankali nake kallon kyawawan kayan da aka kawata gidan da su, duk da gidan ya yi min kyau, amma zuciyata ta kasa samun nutsuwa gabaɗaya saboda wannan ce tafiyata da farko da na taɓa yi da wani Namiji.
Wayarta ce ta ɗauki ƙara,da sauri na duba, sunan Hafsat da na ganin ne yasa na ɗan sauke ajiyar zuciya.
“Ke! Har yanzu baki kira ni ba. Yaya tafiyar?”
Murmushi na yi kaɗan kafin na amsa mata da cewa.
“Alhamdulillah, na iso lafiya.”
Na faɗa ina kallon ƙofar falon da na ga za'a buɗe.
"Ke! Lafiya na ji duk kin yi sanyin ko wahalar tafiyar ce?"
Zama ya yi a kusa da ni, yana rungume ni, na yi saurin cewa.
"Eh zan kira ki."
Ni ce na fara kashe wayar ina kallon fuskarsa na ce.
"Sannu da dawowa."
"Yawwa Noor, mu yi sallah ko? Dan ina so mu fita yawo."
Ban yi magana sai tashi da na yi, kamar yadda ya buƙata. Yanzu ma tare muka yi sallah, sannan ya yi wanka, ina zaune na ga yana ƙoƙarin saka kaya a gabana na tashi da gudu zan fita na ji ya riƙe hannuna.
"Kafin ki gudun ki fara shiga wanka."
Idona a rufe na shiga toilet ɗin.
Kafin na fito ya gama shiryawa, kasa fitowa na yi, daga toilet ɗin, na manta ban shiga da hijabi ba, ina tsaye a toilet ɗin tsawon lokaci.
Buɗe ƙofar na ji ya yi na yi saurin ɓuya a bayan ƙofa, hannunsa kawai yasa yana janyo ni, fuskata na rufe da ɗaya hannuna.
"Noor."
Baki na turo gaba na ce.
"Uhm."
Dariya ya yi tare da cewa.
"Amma kin yi kyau sosai a hak."
Da sauri na kwanta a gadon ina rufe jikina
Wata doguwar rigar ya ajiye min yana fita daga ɗakin ya ce.
"Ki shirya, ina zuwa."
Da sauri na shirya na zauna ina jiransa, ashe babu inda ya fita, kawai ya bani waje ne na shirya.
A gaskiya mun yi kyau sosai kayamu iri ɗaya, yau ban saka hijabi ba, mayafin rigar kawai ya nuna min na saka.
Kuma na yi kyau sosai, ban san haka mayafi yake da kyau ba, hannunsa cikin nawa haka muka fita.
Wani hotel muka shiga, iska mai daɗi ta bugi fuskata. Na ɗan matso kusa da shi ina kallon wajen cikin mamaki, wai ni ce a hotel.
“Kin yi shiru.” Ya faɗa yana kallona.
Ɗan murmusawa na yi na ce. “ban taɓa zuwa irin wannan wajen ba ne.”
Kai ya girgiza yana murmushi ya ce.
“To yau gashi Mijinki ya kaho ki, ki manta da komai, ki ji daɗin lokacinmu kawai.”
Ban san dalilin da yasa kalamansa suke shiga raina haka ba. A hankali muka ci gaba da tafiya tare.
Wurin wani lambu mai kyau muka tsaya. Akwai fitilu masu kayatarwa da furanni iri-iri.
Mutane kaɗan ne a wajen saboda dare ya yi.
Na saki murmushi ba tare da na sani ba.
“Ga shi nan.” Ya faɗa,yana murmushi.
“Menene?”
Na faɗa ina gyara tsayuwata.
“Murmushin da nake son gani, mana."
Da sauri na sunkuyar da kai, na ce
“Prof...”
“Hmm?”
“Ka cika son bani kunya.”
Dariya ya yi, tare da cewa.
“Ni kuma ina son ganin yadda kike rikicewa idan na faɗi gaskiya.”
Harare shi na yi amma hakan ya sa ya ƙara dariya.
Can kuma muka zauna a wani wajen hutawa.
Shiru ne ya ɗan ratsa tsakaninmu kafin ya ce.
“Noor.”
Kai na ɗago, ina kallon fuskarsa.
“Kin san wani abu?”
“A'a.”
“Tun ranar da na fara ganinki na fara tunanin wata rana zamu zauna haka ina hira da ke ba.”
"Amma da kika fara guduna, sai na fara karaya.
Sai yanzu na tuna yadda nake gudunsa a kwanakin baya.
Dariya ce ta kubce min, na ce.
“Ba gudunka nake ba.”
“To me kike?”
“Tsoronka nake ji.”
Na faɗa ina kwantar da kaina a kafaɗarsa.
“Ni?”
Kai na gyada, tare da cewa.
“Eh mana.”
Ya haɗe gira kamar bai yarda ba.
“Ni da kike tsoro?”
“Eh.”
Na faɗa ina murmushi.
“Yanzu fa?”
Ya tambayeni yana shafa fuskata.
Na ɗan yi shiru, na ce.
“Yanzu ba sosai ba.”
Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskarsa, ya ce.
“Alhamdulillah.”
Na kalle shi.
“Me yasa ka yi farinciki haka?”
“Dole na yi farinciki saboda Matata ta fara sabawa da ni.”
Da sauri na ka1u da kai ina dariya.
Sai wajen ƙarfe tara na dare muka fita daga hotel ɗin.
A gajiye muka koma gida, amma zuciyata cike take da farinciki,
******"
Bayan mun ci abinci dare ne, muna zaune a falo yana duba wani abu a laptop ɗinsa, ni kuma ina wasa da wayata.
Sai wayar tawa ta fara ringing.
Da sauri na duba.
Mama ce, cike da kunya na amsa kiran.
“Assalamu alaikum Mama.”
“Wa alaikum salam ya kike?”
“Lafiya lau Mama.”
Muryarta ta yi sanyi, ta ce.
"Kun sauka lafiya? Ina Muhammad Zaid ɗin."
Ban san dalili ba amma sai na ji ƙwallah na son cika idona, na ce.
"Lafiya Mama shi kuma yana masaukin sa."
"To sai da safe."
Wayar na kashe ina kallon fuskarsa da yake dariya.
Baki na turo na ce.
“menene?"
Cikin dariya ya ce.
"Noor ƙarya ko? To ba na kiranta na faɗa mata muna tare.
Tashi na yi, daga falon na komai bedroom, wanka na fara yi sanan na yi shirya kwanciya, cike da tsaro na kwanta, har na yi bacci ban jin shigowarsa ba.
Sai da asuba ya tashe ni na yi sallah, tare muka yi, na zauna yin azikar, taɓa ni ya yi na kallon fuskarsa ya nuna min alamar na tashi.
Tashi na yi, na ga zan tada wata sallar, dole ba dan na so ba, na bi bayansa muka sallar, addu'a sosai na ga ya tsaya yi bayan mun idar da sallar ni kuma na tashi zan kwanta na ji ya riƙe hannuna.
Riƙe kaina ya yi yana addu'a, shiru na yi ina sauraronsa, yana gamawa, na tashi kwance na yi, ban ko yi masa magana ba.
A bayana na jiki ya kwanta yana janye abin da na rufe jikina da shi, hannunsa na kama ina ƙoƙarin tashi ya kwantar da ni cikin sanyin murya ya ce.
"Kwanta Noor bacci za mu yi."
Kwanciya na yi ina jin duk abin da yake min, hannunsa yasa yana cire min kayan baccin jikina, shiru na yi ban iya magana ba, ko motsi na kasa yi.
Rufe idona na yi da sauri jin ya cire min duk kayan jikina, ina so na motsa ko na hana shi abin da yake yi min amma naka magana.
Ba zan iya faɗa muku irin abin da ya faru a lokacin ba, saboda da ni ma, ban gama tabbatar da abin da ya faru da ni gaske ne ko mafarki ne.
Sai bayan wani lokaci da komai ya gama wakana, ban yi tunanin irin wannan ranar na kusa ba, ban kuma yi tunanin irin haka ake ji ba. Kawai dai na buɗe idona na ganni kwance a kujerar falo da wata mata akana, da alama likitace.
A hankali na ɗago kaina ina kallonsu, sai yanzu na fara tunanin irin abubuwan da suka faru da ni, ban san lokacin da fashe da kuka ba.
Jiki na rawa Muhammad Zaid ya riƙe min hannu cikin kwantar da murya ya ce.
"I'm sorry Noor, ban san haka za ta faru I'm so sorry."
Tureshi na yi daga kusa da ni ina cigaba da kukana, wannan matar ce ta ce.
"Sorry sister, babu wata matsala fa, kina shiga ruwan zafi, komai zan.."
"Babu ruwanki."
Na faɗa da muryata da bata fita sosai.
Murmushi ta yi tare da ya masa sallama, har bakin ƙofa ya rakata, sannan ya dawo yana aikin ba ni hakuri.
Shiru na yi ina cigaba da kuka, duk haƙurin da yake ba ni, ba jinsa nake ba, har ya gaje ya yi shiru yana kallona.
Ban san lokacin da bacci ya yi gaba da ni ba, sai bayan na yi bacci ne ya samu nutsuwa.
Bedroom ɗin ya maida ni, sannan shi ma ya kwanta, sosai muka yi bacci, shi ne ya fara farkawa, ido ya zuba min yana kallona.
Kiran sallar ne yasa ya tashi, wanka ya yi, ya fita, a masallacin kusa da gidan ya yi sallah, sannan ya tafi nemo mana abinci.
Ban jima da fita ba, na farka kallon ɗakin na fara yi, sai abubuwan da suka faru suka fara dawo min, idona na rufe da sauri tuna irin yanayi da muka kasance.
A hankali na tashi ina ciza baki, domin ni ɗaya nasan halin da nake ciki, ina dafa bango na shiga toilet,a cikin toilet ɗin ma sai zama na yi, ina hawaye na yi wanka, har zan fito sai na tuna dole zan yi wankan tsarki jikina na rawa na yi, na fito domin wani zazzaɓi ne yake shirin kamani.
Wayata na duba na ga lokacin, sallah azahar na yi ina kwanciya a kan sallayar, gabaɗaya Prof Muhammad Zaid ya gama tafiya da garkuwar jikina, ba na jin wani ƙarfi, ga zazzaɓin da ya rufe ni daga yin wankan.
A hankali ya shigo da sallama a bakinsa, ko ɗago kaina ban yi ba, amma na amsa sallamar a zuciyata.
Kayayyakin hannuna ya ajiye yana zuwa gabana, jikinsa na rawa ya ce.
"Sorry Noor, ni ne ko? Sorry but.."
Katse shi na yi ta hanyar cewa.
"Don Allah ka daina yi min magana, na haƙura shi kenan?"
Murmushi ya yi tare da rungume ni, zame jikina na yi daga nasa ina kwanciyata.
Da sauri ya taɓa jikina jin ya yi zafi sosai ya ce.
"Subbahallahi! Noor zazzaɓi?"
Shiru na yi ina sake rufe jikina da hijabi, wata leda na ga ya ɗauko yana zama kusa da ni, a hankali ya ɗaga ni, na zauna abinci ya fara ba ni, na ci dama ina jin yunwa sosai, ɓata ka irin wannan lokacin ban ci abinci ba.
Ina gama cin abincin ya ba ni magani, shi ma babu musu na sha domin so nake na jin sauƙi abin da nake ji.
Kwanciya na yi a jikinsa ina kallon fuskarsa na ce.
"Don Allah ka maida ni gida, ba ni da lafiya ko'ina ciwo yake min, kum..."
Kuka ne ya kama ni sosai, a hankali ya goge min hawayen fuskata cikin sanyin murya da kwantar da hankali ya ce.
"Zan mai da ke, amma sai kin daina wannan kukan."
Shiru na yi ina nuna masa na yi shiru, murmushi ya yi yana ɗaga wayarsa da ake kira tun ina cin abinci.
"Assalamu alaikum wai kai in ka kira sau ɗaya ba zaka haƙura ba?"
Jin abin da ya ce ne, na tashi daga jikinsa dan na san da Ahmad Zayyan yake magana.
A hankali ya dawo da ni jikinsa yana murmushi da alama wata maganar Ahmad Zayyan ɗin ya faɗa masa.
"Kai ba haka ba ne, ni yau ma ban fita Noor ce take zazzaɓi, amma na yi musu message ai."
Dariya ya yi yana shafa bayana ya ce.
"Ina ruwanka da abin da yake damunta ba dai na ce maka zazzaɓi take ba."
Dariyar Ahmad Zayyan na ji daga cikin wayar, yasa na tashi ina turo baki, kallon fuskata ya yi tare da cewa.
"Sai mun yi magana ina wani aiki ne."
Wayar ya kashe yana kama hannuna ya ce.
"Ko kin son wani abu ne?"
Hawaye ne suka zubo min daga idona na ce.
"Ai ina ji kana faɗawa Prof Ahmad Zayyan abin da ka yi min."
Idonuwansa ya zaro ya ce.
"Yaushe kuma Noor ni ɗin, haba wannan fa sirri ne tsakaninmu daga ni sai ke sai Allah, amma ban sani ba ko za ki faɗawa Ƙawayenki?"
Rufe fuskata na yi ina juya masa baya na ce.
"Ni kunya nake ji Allah yasa Mama ba za ta gane ba."
Dariya ya yi tare da dawowa gabana ya ce.
"Ba za ta gane ba, in dan ki saki jikinki, na sake yi, kin saba kafin mu koma gida, babu mai ganewa."
Turashi na yi daga gabana ina cewa.
"Ni ba mahaukaciya ba ce."
Dariya ya yi sosai jin abin da na faɗa, ranar dai tare muka zauna a gidan babu inda ya fita, sosai ya kula da ni, komai shi yake min, kuma cikin nufin Allah na ji sauƙin abin da nake ji.