Free chapter · Read without an account
BABI NA BIYAR
Dare na yi, na burkice masa ganin yana ƙoƙarin sake maimaita abin da ya faru, sosai nake kuka da turashi amma ina yafi ƙarfina, sai bayan kammalar komai yake ba ni haƙuri.
Yanzu dai na ji jiki sosai dan zama gagarata ya yi, shi ma da kansa ya tausaya min, shi ne ya yi min wanka tare da ba ni tea, ina sha na dawo da shi.
Sosai hankalinsa ya tashi, asibiti ya kai ni, aka saka min ruwa, tare da allurai, kuma Alhamdulillah! Na ji sauƙi.
Muna dawowa gida aka kira shi ya fita, sai a lokacin na samu nutsuwa, domin ganinsa ma faɗewar gaba yake saka ni.
Tun fitarsa yake kira, gajiya na yi da kira na ɗaga.
"Assalamu alaikum Noor ya jikin? Ya yi sauƙi? Ko na zo mu koma asibitin?"
Haushi tambayoyinsa saka ba ni, na ƙi yin magana, ina jinsa ya yi murmushi ya ce.
"Ni nake magana kike yin shiru ko Noor? Shi kenan zan dawo ai, za mu haɗu.."
Jin abin da ya ce ne yasa na ce.
"Me za ka yi min in ka dawo ɗin Allah ni sai na gudu gida, haka ake wai babu hutu?"
Dariya ya yi tare da cewa.
"Ai ke ɗin ce Noor in dan aka bari kika huta da matsala ki yi haƙuri za ki huta amma sai mun koma gida, ki fahimta?"
Kuka na fashe masa da shi ina cewa.
"Allah ba zan yadda ka kashe ni ba."
Dariya ya yi sosai sannan ya ce.
"Ta ya ma Muhammad Zaid zai kashe Noor in dan na kashe ki to wai zan na ba ni daɗin da kike ba ni."
Kashe wayar na yi ina cilli da ita, tsakanin da Allah ina shan wahala a hannunsa, amma na ga kamar shi ba ya fahimta.
Zuwa yamma na ɗan jin sauƙi, Mama na kira muka yi waya, sannan na kira Abba, Khadijah ce ta kira ni, kamar ba zan ɗaga ba sai kuma na ɗaga.
"Assalamu alaikum Aunty Maryama ya Kano ɗin."
A hankali na ce.
"Lafiya Khadijah ya Makaranta?"
"Lafiya Aunty Maryama amma ba ki da lafiya ko?"
"Eh Khadijah zazzaɓi nake yi."
"Subbahallahi! Zazzaɓi kuma, ina Yaya Muhammad ɗin?"
"Yana masaukinsa."
Magana za ta sake na yi saurin cewa.
"Zan kwanta Khadijah sai an jima."
Wayar na kashe ina shiga toilet wanka na yi ina sake shiga ruwan zafi kamar yadda wata likita ta faɗa min a asibiti.
A cikin kayana da na zo da su na zaɓi ɗaya na saka, sosai na yi kyau fuskata ta yi fayuu da ita, na ɗan rame, amma na yi kyau sosai.
Ina zama ya shigo duk a gajiye, ruwa na kawo masa yana bina da kallo, kusa da shi na ajiye masa na ce.
"Sannu da dawowa."
Ban magana sai bakinsa kawai na ji, a saman laɓɓana, yana tsotsa kamar zan cire min, shiru na yi ina rufe ido.
A hankali ya cire bakinsa ya ce.
"I Love you. Noor ina sonki sosai ban san lokacin da sonki ya shigeni haka ba, ke ce rayuwata iya kallon fuskarki tana sani nutsuwa."
Sosai na ji daɗin kalamansa, ina lumshe idona, na ce.
"Kuma haka ake son mutum ba'a tausayinsa, jiya ma sai da na yi maka kuka amma baka tausaya min ba, ni babu ruwana da kai ai."
Murmushi ya yi zan rungume ni na tashi, ina guduwa, dariya ya yi tare da shiga ɗakin, yana shiga na fito da sauri, rabu ya yi da ni.
Har dare ina wasan gudu, yana zama a kusa da ni, zan gudu ƙarfe goma na yi na rufe ɗaki.
Ina jinsa yana bugawa na ƙi budewa, ranar sai a falo ya kwana, sai bakwai na safe na buɗe ƙofa, a falo na sameshi yana aiki.
A hankali na ce.
"Ina kwana Yaya Muhammad."
Da murmushi akan fuskarsa ya ce.
"Lafiya Noor ya jikin ya yi sauƙi ko?"
Ganin ya sake fuskarsa yasa na zauna kusa da shi, na ce.
"Na ji sauƙi sosai, ya aikin?"
"Alhamdulillah! Me za ki ci?"
Jikina ne ya yi sanyi na ce.
"Ni zan dafa mana, ai yau ina da lafiya."
Ban sake magana sai murmushi da ya yi, sai bayan ya gama aikinsa ne muka fita a can muka ci abincin
Can ya kalle ni ya ce.
“Noor.”
“Na'am?”
“Yau akwai wani waje da nake son kai ki.”
Na ɗan haɗe gira.
“Ina kuma?”
Murmushi kawai ya yi, tare da cewa.
“Surprise ne.”
Na haɗe gira ina kallonsa.
“Prof, ka faɗa min mana.”
Kaisa ya girgiza yana murmushi, ya ce.
“A'a. Idan na faɗa miki ai ba surprise ba ne.”
Na turo baki gaba.
“Ni ban son irin wannan.”
“Ƙarya kike.”
Ya faɗa yana ɗaukar mukullin mota, a hankali muka fita daga hotel ɗin.
Tun a cikin mota nake ta tambayarsa amma ya ƙi cewa komai.
Can muka shiga wani babban shopping mall.
Na kalle shi cikin mamaki, na ce.
“Nan za mu shiga?”
“Eh.”
Ya amsa yana riƙe hannuna.
Ciki muka shiga.
Tun daga ƙofar shigowa mutane suke gaishe shi cikin girmamawa.
Na lura da hakan amma ban ce komai ba.
Kai tsaye wani shago ya kai ni ina shiga na gane kayan mata ne kawai a ciki.
Nan take na tsaya.
“Prof...”
“Hmm?”
“Me za mu yi a nan?”
Na faɗa ina turo baki.
“Za ki zaɓi duk abin da kike so.”
Idona na buɗe sosai, ina kallon fuskarsa na ce.
“A'a na gode.”
“Me yasa?”
“Saboda ba na buƙatar komai.”
Na faɗa ina gyara tsayuwata.
Ya ɗan matso kusa da ni, ya ce.
“Noor.”
“Na'am?”
“Tun da muka yi aure ban taɓa ganin kin nemi wani abu a wurina ba.”
Ban ce masa komai. Ya ce.
“Saboda haka yau ni zan saya miki abin da nake so.”
Da sauri na ce.
“Amma”
“Ba gardama na ce ki min ba.”
Dole sai shiru na yi.
Sama da awa ɗaya muna cikin shaguna.
Duk wani abu da ya yi masa sai ya ce.
“Ki ɗauka.”
Gajiya na yi na ce.
“Prof, wallahi ya isa.”
Ya ce.
“Bai isa ba.”
Can kuma muka shiga wani shagon turare.
Ina kallon turaren ne kawai.
Sai ya ɗauki wani ya miƙa min.
“Wannan ya dace da ke.”
Na karɓa ina ɗan murmushi.
“Ka san turaren mata ne dama?”
“Na sani.”
“Yaya ka sani zai dace da ni?”
Sai ya ɗan yi shiru kafin ya ce.
“Saboda duk wani abu mai kyau idan na gan shi na san zai dace da ke.”
Da sauri na kau da kaina, shi kuma ya yi murmushi.
Bayan mun gama siyayya muka shiga wani restaurant domin cin abinci, rana dan lokaci har biyu da rabi.
Muna zaune muna jira a kawo mana abinci.
Sai na lura da wata mata daga can gefe tana ta kallon Prof Zaid.
Ban kula ba da farko.
Amma daga baya sai na ga ta taso ta zo wajenmu.
Tsayawa ta yi tana murmushi.
“Dr. Zaid?”
Kansa ya ɗago, tare da cewa.
“Maryam?”
Mamaki ne ya bayyana a fuskarsa.
Ni kuma zuciyata ce ta ɗan bugawa, jin ya kira sunanta.
Murmushi matar ta yi, tana cewa.
“Ban yi tunanin zan haɗu da kai a nan ba.”
“Ni ma haka.”
Ya faɗa yana kawar da kansa gefe.
Ta kalle ni sannan ta sake kallonsa. Ta ce.
“Ba za ka gabatar min da ita ba?”
Murmushi ya yi ya ce.
“Matata ce, Noor.”
Nan take murmushin matar ya ɗan sauya kaɗan.
“Matarka?”
“Eh.”
Ya amsa a taƙaice.
Sai ta yi murmushin yaƙe.
“Masha Allah.”
Ni kuma na yi mata sallama.
Ta amsa amma idonta yana kan Prof.
Can ta ce.
“Da alama dai ka yi saurin mantawa da tsoffin abokanka.”
Ya ɗan yi murmushi kawai, ya ce.
“Rayuwar kenan.”
Abincin da aka kawo mana ne yasa ta yi mana sallama tana tafiya.
Amma tun bayan tafiyarta zuciyata ta kasa samun nutsuwa.
Na lura da yadda suke sanin juna, na lura da yadda ta kalle shi.
Kuma na lura da yadda ta canza lokacin da ta ji ni matarsa ce, sai tsoron ya kama ni.
Bayan mun fito daga restaurant ne muna tafiya zuwa mota.
Sai ya lura da shiruna, ya ce.
“Noor.”
Ban amsa ba.
Ya sake kira.
“Noor.”
“Na'am.”
Na amsa ba tare da kallonsa ba.
Tsayawa ya yi cak, ya ce.
“Me ya faru?”
“Babu”
Na faɗa ina kawar da kaina.
“Tabbas akwai wani abu.”
Kai na girgiza, na ce.
“A'a.”
Sai ya matso kusa da ni.
“Ko saboda Maryam ne?”
Nan take na ɗago ido na kalle shi.
Shi kuma ya yi murmushi, ya ce.
“Kenan saboda ita ne.”
Na haɗe fuska, na ce.
“Ba ruwana da ita.”
“Da gaske?”
“Eh.”
Dariya ya yi, tare da cewa.
“Allah ya taimake ni.”
“Me ya sa?”
“Saboda matata ta fara kishina.”
Da sauri na buɗe bakina na ce.
“Ni ba kishinka nake ba!”
Dariya ya sake yi tare da cewa.
“Shikenan Noor.”
Ya faɗa yana buɗe ƙofar mota.
Amma yadda yake murmushi ya nuna sarai cewa bai yarda da maganata ba.
Muna shiga falon na kwanta, ba na jin daɗi jikina kawai dai ina haƙuri ne.
Bai zauna falon ya shiga ɗakin, ya jima sosai sannan ya fito daga shi sai wani gajeren wando ko na ce pantis, kawai da kaina na yi na ce.
"Subbahallahi! Wai kai don Allah ba ka jin kunyata ne?"
Cak ya ɗaga ni tare da cewa.
"Ni ma ban sani ba, yanzu dai nake son tabbatarwa."
Ɗakin na ga ya nufa da ni ne, yasa na fara turashi na ce.
"Allah ka sauke ni."
Ban kula ni ba sai da ya kwantar da ni a gado shi ma ya hau sannan ya ce.
"Jiya fa kike rufe min ƙofa amma yau ki hana ni yin abin da nake so, ai hutu kika nema kuma jiya kin huta."
"Ni fa Allah ba na son wannan abu ya ishe ni..."
Shiru na ban ƙarasa maganar ba, jin yana yaga kayan jikina.
Ina dai aka ce min Prof Muhammad Zaid baya tausayi min ni ma zan ba da shaida, gabaɗaya a lamarinsa ban ga alama ta tausayi ba, duk kukan da magiyar da zan yi baya ji, har sai ya gay cima burinsa.