Free chapter · Read without an account

BABI NA SHIDA

by Maryam Usman · MATAR AURE CE

***********

Tun ranar da muka zo ban sake bacci cikin kwanciyar hankali ba, kullum ina fargaba, har tsawon kwanaki biyar ɗin da muka yi yau.

Sosai Prof Muhammad Zaid yake ba ni horo tun ina ganin kuka shi ne mafita har na gane in dan ina kukan ma zugashi nake.

Kullum sai na yi zazzaɓi, na rame ga tunanin da na saka a raina, na yi haske sosai babu komai a fuskata sai hanci, amma fa na yi kyau sosai.

Ina kwance ya shigo, da kayayyaki a hannunsa, tashi zan yi ya yi saurin cewa.

"A'a Noor ki kwanta."

Kwanciyata na yi ina kallonsa, sai bayan ya gama shigowa da kayayyakin da ya zo da su ne, ya zauna kusa da ni yana taɓa jikina.

"Noor ko za mu sake kwana biyu, ko jikin naki zan yi sauƙi, ba na so mu koma gida a haka, hankali su Mama zan tashi."

Tashi na yi ina cewa.

"Ni dai a'a gaskiya mu koma gida, ai na san ko mun sake kwana biyun ba haƙura za ka yi ba, kawai mu koma gida ni ya fi min."

Murmushi ya yi tare da shafa kansa ya ce.

"Yanzu dai ni ake gudu ko?"

"Eh, ai kai ne baka da tausayi."

"Shi kenan, ai za mu koma gidan kuma kullum da da dare zan zo."

"Ina, amma ba gidanmu ba ko?"

"Eh ba gidanku ba, ɗakin Matata zan zo."

Dukansa na yi a ƙirji, ina kuka, dariya ya yi yana riƙe hannayena.

Sai biyar na yamma muka shirya, har mun kai kayanmu motar ya ce na zo zai nuna min wani abu, ban yi tunanin komai ba, na bishi har cikin bedroom ɗin.

Zama na yi kusa da shi domin ganin abin da zai nuna min ɗin, ɓata fuska ya yi kamar zai yi kuka ya ce.

"Noor, ba na jin daɗi ko zamu fasa tafiyar nan sai gobe."

Ido na zaro na ce.

"Sai gobe kuma? A'a wallahi ni gaskiya a gida zan kwana."

"Ni ma ina so ki kwana a gidan saboda alƙawarin da na yi wa Abba, amma don Allah Noor ki taimakawa Mijinki mana."

Baki na taro na ce.

"Da me kuma? Ni fa Allah ba na so kana marerecewar nan, kamar wani almajiri ko Maraya."

"Ai ni maraya ni, a gabanki oho Noor help me."

Wayo ya yi min da daɗin baki, ya biya buƙatarsa, sannan muka yi wanka, ganin lokacin sallah yasa muka fara yin sallar magriba sannan na yi saurin shiga mota kafin ya sake cewa wani abu.

Tsakanin Kano da Jigawa babu wani nisa sosai, shi yasa kafin tara na dare muna gida.

Na san halinsa, shi yasa muna zuwa gida na sauka har ina haɗawa da gudu, duk sun zaune a tsakar gida, na shigo da sauri.

Tashi Abba ya yi tare da cewa.

"Lafiya Uwata me ya faru kike shigo gida babu sallama."

Kunya ce ta kama ni na yi ƙasa da kaina na ce.

"Abba ka yi haƙuri na yi sallama ji ne ba ku yi ba."

Zama ya yi tare da cewa.

"To bismillah, zama na yi kusa da Mama muna gaisawa da su, tun shigowata Aunty Mansura take kallona, na yi murmushi na ce.

"Aunty Mansura ya kike kallona?"

Kafin ta yi magana ya shigo, zama ya yi kusa da ni suna gaisawa da su Abba, tashi na yi ina cewa.

"Mama da akwai abincin?"

Da kallon Mama ta bi ni tana cewa.

"Eh, ki zubawa Muhammad Zaid ɗin ma."

"Ya ƙoshi, ba zai ci abinci ba."

Ɗago da idanunsa ya yi tare da ɗaga min gira, hararar sa na yi ina cewa.

"Sai da safe Mama ka da wanda ya shigo min ɗaki."

Dariya ya yi yana tashi ya ce.

"Abba sai da safe, Khadijah ku zo."

Fita ya yi su Khadijah da Asiya har Aunty Mansura suka bi bayansa.

Kayayyakin da muka zo da su, ya basu, ni kuwa wanka na fara yi sannan na shiga ruwan zafi da na saba da shigarsa sannan na fita na ci abincin ko hirar da suke ban sa baki ba na koma ɗaki.

Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali na yi bacci a ranar, dan ko da asuba ma, sai da na makara.

****************

Sai da ya je gidan Prof Ahmad Zayyan sannan ya tafi gida, babu komawa a falon, shi yasa ya wuce nasa ɓangaren.

Sai da asuba Papa ya ganshi, rungume juna suka yi, sosai Ammyy take dariya, gaisawa ya yi da su, yana zama a falon suna hirar duniya shi da Papa.

Takwas na yi ya yi wanka, tare da yin breakfast sannan ya fito, tun a wajen breakfast ɗin Siyama da Sauban suka kalla juna.

Yana fita Sauban ya kama hannun Siyama suna fita waje.

"Yaya Sauban ba ka ga abin da na ganin ba?"

Dariya Sauban ya yi tare da cewa.

"Ai Siyama har so nake ya fita mu yi zancen."

"Yaya Sauban ko yawon amarci ya tafi ne?Ka ga yadda ya yi kyau da wani tunbi kai gaskiya sai na binciko mana."

Dariya Sauban ya yi tare da cewa.

"Yawwa ashe Siyama kainki yana ja, wallahi ni ma na ga, amma don Allah ki yi sauri kin ji sister."

**********

Ammyy ce ta kalle fuskar Papa ta ce.

"Wai ina Muhammad Zaid ya je ne?"

Kallon mamaki ya yi mata yana cewa.

"Wacce irin tambaya ce wannan, ko ban faɗa miki Kano aka tura shi meeting ba?"

Girgiza kai ta yi tana cewa.

"Allah ya kyauta."

"Amin."

****************

Har takwas da rabi ina bacci, sai da Khadijah ta buga min ƙofa sannan na fito dariya ta yi tana cewa.

"Aunty Maryama ko ba za ki je Makaranta ba ne?"

Hamma na yi ina cewa.

"Wallahi ba na jin daɗi jikina ne."

Aunty Mansura ce ta zo ƙofar ɗakina tana kallon fuskata ta ce.

"Kuma Maryama a Kano ɗin tare da Prof Muhammad Zaid kuke kwana?"

Gabana na ji ya faɗa na yi saurin cewa.

"A'a shi fa a hotel ya sauka ni kuma gidan wani abokinsa ya kaini."

Ashe Ummah ita ma tana tsaye sai ji na yi tana cewa.

"Ai muna nan sai tunani muke, ashe dai yaron nan Muhammad Zaid yana da hankali, to ki dai ki faɗa masa gaskiyar abin da yake zuciyarki, kin san sai ya sake ki, zai aure Mansura tun kafin wani abu ya shiga tsakanku."

Bana so jan maganar shi yasa na ce.

"To Ummah."

Ina rufe ƙofar ɗakina.

Zama na yi a bakin gadon ina tunanin irin rayuwar da muka yi a garin Kano, sai murmushi ya suɓuce min, da na tuna irin wahalar ni da Prof Muhammad Zaid yake yi sai da gabana ya faɗi, har yanzu ban sabo ba.

A duk lokacin da na tuna sai na ji faɗawar gaba, wanka na yi sannan na kwanta domin wani zazzaɓi na ji mai zafi zai rufe ni.

Ina kwance, na ji Mama tana kirana, a hankali na fito ina aro jarumta, gaisawa muka yi da ita ta ce.

"Ke ba za ki je Makarantar ba ne?"

Ba zan iya faɗa Mama bana jin daɗin jikina ba, yasa na ce.

"Yanzu zan fito."

Kallon fuskata ta yi tana cewa.

"Wai ko baki da lafiya ne? Duk kin yi sanyi."

Murmushi na yi ina cewa.

"Wallahi Mama gidan da yakai ni ne suka da AC, shi ne na kwasu sanyin tun da na ji nake mura da zazzaɓi."

Alamun tausayi na ga akan fuskarta ta ce.

"Sannu, ba na dafa miki ruwan zafi mai cita na san za ki daɗi."

Tana tafiya na sauke ajiyar zuciya, ina kwancinya dole ce za ta sa na je Makarantar nan.

Wayata na ɗauka na kiransa har sau goma, sai messages ɗinsa, iya message ɗin na duba, na ɗauko jakata da wayata sannan na rufu ɗakina.

Zama na yi har Mama ta dafa min tea ɗin sannan ta zuba min a tea flasks, kuɗin na karɓa a hannunta sannan na fita, sai tara da rabi na isa department ɗinmu, hakan ma sai da na zauna na ɗan huta a bakin baranda.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol