Free chapter · Read without an account
BABI NA BAKWAI
*************
Tara na yi Prof Muhammad Zaid ya shiga class ɗinmu, babu walwala a fuskarsa yake koyarwar, duk wanda suka zo bayan shigar babu wanda ya bari ya shiga.
Sai tara da arba'in na tashi ganin babu kowa a bakin ƙofa ne yasa na shiga kaina tsaye, da sallama a bakina.
Tsayawa ya yi da bayanin da yake yana ɗago idanunsa ya zuba min.
Kowa kallona yake wasu suna magana ƙasa ƙasa, a hankali na ga ya nufu inda nake na juya da sauri, murmushi ya yi tare da ciro wayarsa message ya yi min akan na shigo.
Ni ma message ɗin na tura masa.
"Ba na so ka ɓata ni, kai kuma na ga kamar haka ne nufinka."
Yana duba message ɗin ya ce.
"Excuse me."
Fitowa ya yi, yana murmushi a gabana na ganshi a tsaye yana rungume da hannayensa.
"Ina kwana."
Na faɗa ina juya masa baya.
"Lafiya amma me yasa kika makara?"
Hawaye ne suka cika min ido na ce.
"Ni fa ba ni da lafiya kuma ba na so Mama ta sani shi ne da ta yi min magana na fito."
Ɗan matsowa ya yi kusa da ni, tare da sa hannunsa a fuskata ya ce.
"Wai zazzaɓi ne har yanzu."
Matsowa na yi daga kusa da shi na ce.
"Eh."
Ajin ya nufa yana cewa.
"Ina fitowa za muje asibitin ban yadda da wannan zazzaɓi ba, yau kwana biyar kina fama da shi."
Ban ce masa komai ba, har ya shiga Ajin, ganin ban shigo ba ne ya yi min message kan na shigo.
Ina ganin message ɗin na tashi ina shiga yan class ɗin ne suka bi ni da kallon, Samiha ce ta ɗaga min hannun tana cewa.
"Hey Maryama Ahmad."
Dariya na yi ina zama kusa da su surutu aka fara ganin na shigo har na zauna bai kore ni.
"Ya isa."
Shiru kowa ya yi, yana cigaba da koyarwarsa duk da ba na nan ya fara amma na fahimci wani abu.
Goma na yi ya tattara kayansa zan fita amma sai ya tsaya yana nunawa ɗaliban hanyar fita.
Fita aka fara yi Hafsat ta ce.
"Prof Muhammad Zaid fa ke yake jira."
Ido na ɗago ina kallon fuskarsa magana na yi masa da ido akan ya fita zan zo, amma ya ɗaga min kafaɗa.
Dole sai tashi na yi ina zuwa gabansa da nufin na yi masa magana, amma ya kama hannuna yana fita da ni, duk son na ƙwace na kasa, saboda ba ni da karfi yanzu.
Inda Allah ya rufa min asiri, motarsa tana gaban Department ɗinmu, motar ya buɗe min sannan shi ma yasa shiga.
Kuka na fara ina cewa.
"Shi kenan burinka ya cika ka kunyata ni a gaban mutane ko?"
"Eh."
Ya faɗa yana jan motar da gudu, wani asibitin kuɗi ya kai ni, sosai likintan ta duba ni maganin aka ba ni da allura, tana yi min allurar, na fara hajijiya, zan faɗa.
Likinta ce ta tambaye shi na ci abincin kuwa, kallon fuskata ya yi yana taɓa kumatuna ya ce.
"Noor ba ki abincin ba ko?"
Kaina kawai na iya ɗagawa domin allurar juya ni take, likitan ya kalla ya ce.
"Ba ta ci abinci ba,amma yanzu zan ba ta."
Ina jikinsa muka fito a mota ya saka ni, sannan ya shiga muka fita daga asibitin, ɗan tsayawa ya yi ya siya min abinci, sannan muka koma Makaranta.
Lokacin da muka isa ai na yi nisa ba na iya tsayawa da ƙafata, dole abincin ya fara shiga da shi, ya zo ya ɗauke ni cak.
Da yawwan ɗaliban da suke wajen da kallo suka bi shi, har ya shi da ni, a cikin office ɗinn nasa akwai wani ɗaki har da gado, a ciki ya kwantar da ni, sannan ya rufe ƙofar office ɗin.
Zama ya yi a kusa da ni yana cewa.
"Noor tashi ki ci abincin sai ki kwanta."
Shiru ya ji yasa ya duba fuskata ga har na yi bacci, ajiye zuciya ya sauke sannan ya dawo cikin office ɗin. Yana zaune a office ɗin har sha ɗaya ta yi, sannan ya rufe ni a ciki ya shiga wani class ɗin.
*******************
A ɓangaren su Hafsat kuwa tun bayan tafiyarmu suke faɗa da su Zainab Usman akan su Zainab Usman ɗin sun ce ni karuwa ce.
Faɗa sosai suke har Faisal sai da ya shiga jin
Ana cewa ni karuwa ce. Sai da Prof Kamis ya shiga maganar sannan ta mutu office ɗin Prof Muhammad Zaid ya zo yana ta knocking.
Shiru da ya ji ne yasa ransa ɓace kuma bayan su Zainab Usman sun ba shi tabbacin muna cin office ɗinn.
Juyawa ya yi zan koma sai ya ga Prof Muhammad Zaid ɗin a bayansa, murmushi ƙarfin halin ya yi tare da cewa.
"Ai na yi tunanin kana ciki."
"Na shiga class ne."
Juyawa Prof Kamis ya yi ba tare da ya sake magana ba.
**********
Ban jima da fita ba, na farka, kuma zazzaɓi ya saka abinci na ci, sai na kwanta ina tunani, zafi na ji yasa na shiga toilet na yi wanka na ɗaura ɗan kwalina.
Ina zaune daga ni sai ɗan kwalina a jikina ya shigo, murmushi ya yi tare da zama a gefen gadon yana shafa jikina ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
"Sannu Noor zazzaɓi ya tafi ko?"
Murmushi na yi ina riƙe hannunsa na ce.
"Eh na ji sauƙi sosai, ni tun ranar ban taɓa jin daɗi jikina ba irin yau."
Saman gadon ya hau yana kwantar da kansa a kafaɗata ya ce.
"Ni kuma, ban taɓa jin rashin jin daɗi ba irin yau, Noor jiya kasa bacci na yi, yau da safe na yi tunanin na zo gidan sai na makara dole na haƙura na taho Makaranta."
Hannunsa na riƙe da yake ƙoƙarin cire min ɗan kwalin jikina na ce.
"To kai me zan hana ka bacci."
Hannunsa ya maida yana cire min ɗan kwalin na yi saurin cewa.
"A'a wallahi a Makarantar ma ni gaskiya ban yarda."
Murmushi ya yi muryarsa ƙasa ƙasa ya ce.
"Ai ke mai tsada ce Noor kin fi ƙarfin wannan gadon, ba zan iya mu'amala da ke a irin wannan wajen ba, kawai dai nutsuwa nake so ki sama min."
Ajiyar zuciya na sauke jin abin da ya ce, kallon fuskarsa na yi na ga duk ya shagwaɓe fuska na ce.
"To ai sai ka daina kallona ko?"
Murmushi ya yi yana rufe idanuwansa ya ce.
"Dole ne tun da za'a yi min abin da nake so."
Shiru na yi ina tunani irin abubuwan da ya koya min a Kano ban tsaya ɓata wa kaina lokaci ba, na yi masa abin da ya buƙata ɗin sosai kuma ya yi farinciki, ni ma na ji daɗi ganin na sa shi farinciki.
Bayan kammalar komai, ni ce na fara fitowa cikin office ɗin, sallah na yi sannan na zauna ina shan tea ɗin da Mama ta dafa min.
Fitowa ya yi yana murmushi ya ce.
"Noor ko wani abincin zan nemo miki?"
Shafa fuskarsa na yi na ce.
"A'a My Zaid, ina so zan shiga class ne, ka ga har biyu ta yi."
"Okay muje sai na raka ki ko?"
Hijabinna na saka ina cewa.
"Don Allah ka rufa min asiri ni zan tafi da kaina."
Murmushi ya yi yana cewa.
"To waye yake muku lecture ɗin."
"Prof Ahmad Zayyan ne, kuma shi ma halinka ne da shi na san zai hana ni shiga."
Hijabi ya gyara min ya ce.
"To yau dai dole ne ya yi haƙuri ki shiga, zan kira shi tun da bakya so na raka ki."
Hanyar fita na nufa ina murmushi, babu wasu ɗalibai da yawa a gaban office ɗin shi yasa na wuce cikin kwanciyar hankali har na je baƙin ƙofa class ɗin ban haɗu da wanda ya san ni ba.
Ina fita ya kira Prof Ahmad Zayyan.
"Ahmad Zayyan ga Noor nan."
Dariya Ahmad Zayyan ɗin ya yi tare da cewa.
"Kamar ya Noor nan bayan na zo ina knocking baka buɗe ba kai mai Mata ko? Wai a Makarantar ma ba za ka haƙura ba?"
Dariya ya yi tare da cewa.
"Eh, ai Matata ce ko? Malam ka yi abin da na saka ka kawai."
Lokacin da isa babu mutane sosai su uku na samu sai ni ta huɗu, na ɗan tsaya sai na ga message ɗinsa.
"Ki shiga na yi masa magana."
A hankali na shiga Ahmad Zayyan ɗin ne ya ɗago idanunsa ya kallona murmushi na ga ya ɗan yi, sannan ya amsa gaisuwar da nake masa.
Nuna min wajan zama ya yi yana cigaba da abin da yake yi. Taɓa ni na ji an yi na yi saurin juyawa domin na tsorata.
Dariya Hafsat ta yi tana cewa.
"Wai Maryama lafiya kike daga taɓa ki sai ki tsoranta?"
Ajiyar zuciya na sauke na ce.
"To ke ɗin me na taɓa ni ɗin."
Shiru muka yi ganin Ahmad Zayyan yana kallonmu.
Uku na yi ya fita, zama muka yi ni da su Hafsat muna magana.
Zainab Usman ce ta zo gabana tana cewa.
"Lailai Maryama Ahmad Usman ashe karuwancin nake yafi ƙarfin hankalina."
"Ai Zainab Usman lamarin Maryama Ahmad Usman ya yi girmama, yanzu ke da aurenki ki ke bin Maza."
Murmushi na yi ina kallonsu Samiha na ce.
"Ciwon kai fa nake, kuma na ga mahaukata za su ƙara min wani zo mu fita."
Maganar da na yi ce ta yi zafi yasa Zainab Usman ɗaga hannu za ta mare ni na riƙe hannun na ce.
"Wallahi Zainab Usman ki fita harkarta ba ni da mutunci ki bar ganin ina raga miki."
"Ke har kina da bakin magana, bayan kowa yasan ke karuwa ce."
Dariya na yi ina kallon Ƙawar Zainab Usman ɗin na ce.
"Eh ai karuwancin ma iya wa ne, ni shi na ga ya fi min, indai kin da wani ki yi magana ya zo akwai kayan..."
Buge min baƙi Hafsat ta yi tana cewa.
"Ke Zainab Usman kin san wacce Maryama Ahmad Usman kuwa.."
Hana Hafsat magana na yi ina cewa.
"Wai Zainab Usman jikinki ne ko nawa? To babu ruwanki da duk wanda zan sakarwa jikina ke ma in dan za ki yi wa hanya to ya zo."
Ko damar magana ban wa Zainab Usman ba, na kama hannun Hafsat muka fita.
Dariya Samiha ta yi tana cewa.
"Wai Ke Maryama bakya tsoran magana, da mutane fa a class ɗin kika yi irin wannan maganar wani zan yi tunanin da gaske ne."
Ita ma ban kalleta ba, Hafsat ce ta ce.
"Ni wallahi tsoron na ji, yanzu maganar ta fita ai mun shiga uku ɗazu fa da Prof Muhammad Zaid ya ɗaukeki sai da muka yi faɗa da su."
Samiha na kalla na ce.
"Samiha help me."
Dariya ta yi tana cewa.
"Ina ji."
Kwantar da murya na yi na ce.
"Don Allah ki karɓo min ɗan kwalina da jakata a office ɗin Prof Muhammad Zaid."
Dariya ta yi tana kallon fuska Hafsat ta ce.
"Amma Maryama baki da mutumci ni za ki aika."
"Ba na so na zauna ne shi kuma na san ina zuwa zan ce na jira shi, don Allah ki rufa min asiri zan yi masa message ba sai kin yi magana ba."
Hannunta Hafsat ta kama suka tafi, su na tafiya Prof Kamis ya zo inda nake, jikina na rawa na ce.
"Lafiya Prof Kamis?"
Zama ya yi kusa da ni, har jikinsa yana taɓa nawa, da sauri na tashi ina cewa.
"Subbahallahi! Prof Kamis lafiya."
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Zauna Maryama kar ki tara min mutane mana, ko office za mu shiga?"
Kaina na girgiza ina cewa.
"Subbahallahi! Prof Kamis ni fa MATAR AURE CE don Allah ka rufa min asiri."
Gudu zan yi ya riƙe hijabina yana murmushi ya ce.
"Ai na ji labarin kina da aure, to amma ai auraki ba zai hana ki yi min abin da kike yi wa sauran ba ko."
Hawaye ne suka zubo min na ce.
"Ni fa ba Yar iska ba ce, ni MATAR AURE CE ko ba ka ji ba?"
Ban bari ya yi magana ba, na gudu ina ɓuya a bayan wata mota, ban san ya biyo bayana ba sai hannuna da na ji ya riƙe hannunsa ɗayan yasa zan rufe min baki aka riƙe hannuna da ƙarfi.
Ƙara ya yi yana sake min hanuna gudu zan sake yi na ji, an rungume ni, ajiyar zuciya na yi da jikina ya haɗu da nasa, ko mafarki nake zan gane shi.
Idona na ɗago ina kallon fuskarsa ashe shi da Ahmad Zayyan ne sai Samiha da Hafsat da suke baya.
Ahmad Zayyan ne ya sake riƙe hannun Prof Kamis har sai da ya sake yin ƙara, saki na Prof Muhammad Zaid ya yi, yana shaƙe wuyan Prof Kamis.
Sosai ya shaƙe wuyan Prof Kamis idanunsa duk suka fito waje, tsoron ne ya kama ni kar ya mutu mu shiga uku, na yi saurin cewa.
"Don Allah ka sake shi ka da ya mutu."
Abin da na faɗa ne yasa Ahmad Zayyan ya riƙa hannunsa ya ce.
"Muhammad Zaid sake shi ka yi haƙuri ai bai mata komai ba."
Sakin wuyan nasa ya yi tare da cewa.
"Kamis dama kai ɗan akuya ne? Matar aure ka ke bi? To duk akuyancinka ya tsaya haka wannan Matata ce."
"Ai ka yi kuskure Kamis tun ba yau ba, na faɗa maka Maryama Ahmad Usman MATAR AURE CE."
Hanuna Prof Muhammad Zaid na kama ina cewa.
"My Zaid bai min komai don Allah ka yi haƙuri ka da maganar nan ta fita bana so mutuncin ya zubai don Allah."
Hannuna ya kama yana nuna Prof Kamis da yatsa ya ce.
"Ka kiyaye babu ruwanka da Matata, ko kallon fuskata ba na so na yi maka kara sosai, ka kiyaye kafin hukumar Makaranta ta san halin da muke ciki."
Fita ya yi da ni, daga bayan motar, mutane na ga kamar suna kallon wajen na kalleshi na ce.
"Don Allah mu sauke su Samiha a gida."
Hannuna ya saki yana yin gaba baya na dawo ina kallon fuskarsu na ce.
"Ku zo mu tafi gida."
Babu musu muka bin bayansa lokacin da muka isa har ya shiga motar, ni ce na fara shiga sannan duk suka shigo.
A hankali yake jan motar kamar baya so, tun da muka shiga babu wanda ya yi magana har muka yi nisa gyara murya ya yi min.
Ɗago kaina na yi ina kallon fuskarsa, ruwan dake kusa da shi ya nuna min alamar yana son sha. A hankali na ɗauki ruwan ina ba shi a baki kamar yadda yake so.
Sosai ya sha ruwan sannan na ji yana sauke ajiyar zuciya, a hankali na ce.
"Ka yi haƙuri ban san zai zo inda nake ba."
Kallon fuskata ya yi da idanuwansa da suka yi ja rai a ɓace ya nuna min na yi masa shiru.
Shiru na yi ina kawar da kaina gefe, har muka sauke su Samiha ban yi magana ba, maimakon ya kai ni gida sai na ga ya nufi wata hanya.
Dole na yi shiru ganin yana fushi da ni.