Free chapter · Read without an account

BABI NA TAKWAS

by Maryam Usman · MATAR AURE CE

************

A ɓangaren Prof Kamis kuwa, Ahmad Zayyan ne ya yi masa bayanin ni matar Muhammad Zaid ce sosai ya yi nadamar abin ya yi haƙuri ya ba wa Ahmad Zayyan ɗin da alƙawarin ban sake ba.

Sannan ya roƙe shi akan su rufa masa asiri, sai da Ahmad Zayyan ya kafa masa dokokin sannan ya fita daga Makarantar.

Mama ce ta kira ni, ganin har an yi sallar magriba ban dawo gida ba, a lokacin muna gidansu, babu wanda yasa muna ciki dan ta wata hanya ya shiga da ni.

Yana kwance a gadonsa, ni kuma ina bashi haƙuri kamar ni ce na je wajen Prof Kamis ɗin yaƙi yi min magana, har haushi na fara ji.

Tashi ya yi, tare da shiga toilet wanka ya yi ,ya fito jikinsa duk ruwa, wata rigar ya saka sannan ya ce.

"Ki yi wanka mu yi sallah."

Tashi na yi ina cewa.

"Ni wallahi babu wani wanka da zan yi."

Na san bai ji ba, dan ciki ciki na yi maganar.

Alwala kawai na yi muka yi sallah, sannan ya fita cikin gidansu ta ƙofar ciki.

Abincin ya shigo da shi, har da kaje, zama na yi na ci abincina sosai, na sha madarar shanu da na ga, sannan na koma gadon ina hutawa.

Bayan ya gama ne, ya fita da kayan abinci, sannan ya zauna yana aiki, ban ko kalle shi ba, na yi masa shiru ni a tunani ai ya ji lokacin da Mama ta kira ni.

Waya na ji yana da Ahmad Zayyan, sai lokacin na ga ya yi murmushi, sai bayan ya gama ne, na ji yana taɓa ni.

Ko kallonsa ban yi ina ji ya fara shafa min jiki, bai san ina da zuciya ba, na ga alamar raina ni yake son yi. Har ya gama abin da yake so ban ko ce masa uffan ba.

Murmushi ya yi yana kallon fuskata ya ce.

"Noor fushi kike dan na karɓi hakkina?"

Kamar babu ni a wajen, ban ce masa komai sai wankan da na shiga na yi, ko riga ban saka ba, na ɗaura zanin kayana na ce.

"Zan koma gida su Mama suna nemana."

Wanka ya yi shi ma, sannan ya saka wata jallabiya mai kyau, sannan ya kama hannuna muka fita, ta inda muka shigo, babu wanda ya ganmu har muka fita daga gidan.

Ko a motar ban yi masa magana ba, yana zuwa ƙofar gidanmu na fita ko jakata da rigata ban ɗauka ba, ya san haushi nake ji, shi yasa bai shiga gidan ba ya koma gida.

Rai ɓace na shiga cikin gidan iya Abba na gaida na shiga ɗakina tare da rufewa da ƙarfi.

Babu wanda ya kala ni, sosai na yi kukana a ɗaki har na baka kaina haƙuri, wayata yake kira tun shigowata ban ɗaga ba, daga ƙarshe ma da ya dame ni kashe wayar na yi.

*******

Sai da na yi sati biyu bana kula shi ko a Makaranta, ko gidanmu ya zo, sosai ya shiga damuwa duk wata hanya da zai bi ya bi amma ban sauƙo ba, da ya gaji ne ya fara nuna min ƙafin akan hakkinsa.

Ban nuna masa taurin kai ba domin A'isha ta yi faɗa kuma na ɗauka, ranar da ya same ni a gida babu kowa ya nuna min ƙarfi ban hana shi amma ban ji daɗin hakan da ya yi min ba.

Daga baya shi ne ya fara ba ni haƙuri, Mama ce ta fara fahimtar akwai matsala a tsakaninmu, sosai ta yi min faɗa har da duka, na yi kuka sosai a lokacin ga ba ni da lafiya ga duka haka na bashi haƙuri da ya zo da da dare.

Ina ɗakina dan yanzu bana zaman waje tun abin da ya faru, ina kwance ina karatun dan mun kusa fara examination ta wannan semester, ya shigo jikinsa duk a sanyaye.

Yana zama na ce.

"Sannu da zuwa."

Da farinciki ya juyo bakinsa na rawa ya ce.

"Noor ke ce yau kika yi min magana mai daɗi kai Alhamdulillah!"

Gyara kwanciyata na yi ina cewa.

"Ka yi haƙuri da abin da ya faru.."

"A'a Noor ni ne zan baki haƙuri don Allah ki yafe min."

"Na yafe maka."

Na faɗa ina juya masa baya.

A lokacin muka shirya, har ƙarfe goma yana gidan sai sha ɗaya ya tafi.

Yana tafiya Mama ta shigo ta ce.

"Yanzu ashe ke ce kike korar Muhammad Zaid ko."

Baki na turo na ce.

"To ai laifi ya yi min."

Buge min baki ta yi tana cewa.

"Allah ki fita idona."

Hanyar fita ta nufa na ce.

"Mama ba ni da lafiya, ciwon mara nake yi jiya ma kasa bacci na yi."

Dawowa ta yi da baya ta ce.

"Ciwon mara kuma? To ke yaushe kike fara ciwon mara lokacin al'ada."

Hawaye na ji ya zubo min na ce.

"Ni ma ban sani ba, amma fa tun wancan satin ya kamata na yi al'adar amma ban zo ba sai ciwon marar da nake yi."

"To gobe kije asibiti zan faɗawa Abbanku Allah ya baki lafiya."

"Amin ya Allah amma ni gaskiya ba na so ki faɗawa Abba zan wuce daga Makaranta."

Fita ta yi tana yi min addu'a ranar ma haka na kwana tun ranar da Prof Muhammad Zaid ya nuna min ƙarfi nake fama da ciwon marar nan na sha duk wani magani amma ban daina ba.

****Washegari.

Da sauƙi sosai na tashi, na yi wanka na ci abinci ina gama cin abinci ya zo, shi ma abincin ya ci muka tafi.

Tun da na shiga motar na yi shiru, a hankali ya ce.

"Noor ko har yanzu fushi kike yi da ni?"

Murmushi na yi na ce.

"A'a."

Shiru ya yi ba tare da ya yi magana, sai da ya kai ni gaban Department ɗinmu na kama hannunsa ina cewa.

"Ni fa babu komai na ga duk ka ɓata fuska."

"Dole na ɓata fuska Noor na ga duk kin yi shiru kamar wacce ba ta da lafiya ba."

Ɗaga masa kaina na yi ina cewa.

"To ba ni da lafiya ne, ciwon mara da ciki nake yi."

Ya ɗan rikice ya ce.

"Ciwon mara kuma?

Hawaye na fara yi ina kama hannunsa na nuna masa inda yake min ciwon na ce.

"Nan ne yake min ciwo kuma na faɗawa Mama ta ce na je asibiti."

Goge min hawayen fuskata ya yi tare da cewa.

"Tun yaushe yake ciwon?"

Baki na turo na ce.

"Ni ma ban san ba amma na fara jinsa tun ranar da ka yi fyaɗen."

Dariya ya yi tare da cewa.

"Noor har da shiri. To yanzu fito daga lecture sai mu je asibiti ko?

A hankali na fita daga motar ina shiga class ɗin dariya Hafsat ta yi tana cewa.

"Ashe masu faɗa sun shirya, ai wallahi Samiha na faɗa miki yarinyar nan faɗa suke da Prof Muhammad Zaid kuma gashi yanzu mun ga gaskiya."

Zama na yi ina cewa.

"To ina ruwanku mun yi faɗan."

Dariya sosai suka yi su na tsokanata, Malami ɗaya ne ya shigo na ji, kamar zan mutu na tafi gida ko ta san ban bi ba.

Da kuka na shiga gida ina cewa.

"Mama zan mutu wayyoo Allah na."

Da sauri kowa ya fito ana tambayata abin da yake faruwa, kwanciya na yi a ƙasa ina kuka.

Hankalin Mama a tashe take tambayata, hannunta na ɗaga a inda nake jin ciwon na ce.

"Mama zan mutu wayyoo Allah Abba Mama ki kai ni asibiti Mama a kira min Abbana."

Kowa a gidanmu hankalisa ya tashi Khadijah da Asiya kuwa kuka suke duk rashin mutunci da muke da Aunty Mansura yau ita ce ta riƙe ni tana cewa.

"Mama a kira Abba wallahi da gaske ne tun da kika ga Maryama tana kuka."

Wayar Abba Ummah ta kira tana cewa.

"Kana ina to wallahi ga Uwar masu gida za ta mutu sai kuka take wai ciwon mara da ciki."

Mama ce ta kalleta tana cewa.

"Haba Saratu ai sai ki sa hankalisa ya tashi."

Babu wanda ya ji abin da Abba ya ce sai Ummah muka ji tana cewa.

"To za mu zo to ga mu nan."

Wayar ta kashe tana cewa.

"Ya ce mu haɗu a asibiti shima zan zo shi da Alhaji."

Asiya ce ta samu mana abun hawa, duk muka tafi dama Umar yana Makaranta. Lokacin da muka isa ai ban san abin da yake faruwa ba.

Ana shiga da ni wani ɗaki Abba ya zo shi da Papa da Ammyy sai Siyama da take hawaye.

Duk zaman jira suka zauna yi, har wani lokacin sannan Siyama ta kama hannun Khadijah ta ce.

"Khadijah mu kira Yayanmu mu faɗa masa halin da ake ciki."

"Eh haka ne Siyama kira mana shi sai na yi masa magana."

Siyama ce ta kira shi sannan ta bawa Khadijah wayar yana ɗagawa ya ce.

"Lafiya."

A hankali Khadijah ta ce.

"Ni ce Khadijah Aunty Maryama ce ba ta da lafiya muna asibitin sai kuka take wai za ta mutu.."

Da sauri ya tashi tsaye yana cewa.

"What za ta mutu fa, ke gani nan zuwa ya sunan asibitin."

Ahmad Zayyan na ya riƙe shi tare da cewa.

"Haba Muhammad Zaid komai aka faɗa maka ai ba zaka tsoranta haka ba, har gabana ya faɗi."

"Ahmad Zayyan Noor ce fa ba ta da lafiya wai tana asibiti kuma wai za ta mut.."

Kwantar masa da hankali Ahmad Zayyan ya yi a tare suka taho asibitin, sai Ahmad Zayyan ne ya kira Siyama ta faɗa musu inda suke.

Su Abba duk suna zaune kowa da abin da yake tunani wata likita ta fito.

"Yawwa ku ne yan uwan Maryama Ahmad?"

Bakin su Abba na rawa suka amsa shi da Papa, Papa ne ya ce.

"Yarinya mai yake damunta ne?"

Papa ta kalla sannan ta ce.

"Baba ina Mijinta."

"Bayan nan za ki iya faɗa mana komai."

Abba ya faɗa yana kallon fuskarta.

"To dama Baba cikin jikinta ne ya lalace da alama ma ya jima da lalacewar.."

Katse ta Abba ya yi tare da cewa.

"Ciki kuma yarinya wane irin ciki kuma yarinyar da ko tarewa ba ta yi a ɗakin Mijin ba."

"Gaskiyar maganar ta faɗa muku ciki ne da ita na tsawon wata guda kuma ya lalace dole sai an fitar da shi."

Baki sake suke kallon fuskar matar da ta fito daga ɗakin da nake.

Kuka Mama ta fara tana cewa.

"Haba baiwar Allah ciki fa kika ce, don Allah ki sake dubawa Allah yarinyata ba ta da komai."

Khadijah ma kuka ta fara, Ummah ce da ta yi shiru tun fara maganar ta ce.

"A'a Maman Fati ba'a shaidar yaran yanzu kike sani ko a Makarantar wani ya yi mata."

Ammyy ce ta yi magana tana cewa.

"Amma dai Saratu mummunan baki gareki, to wallahi sai dai ya faɗa kanki."

Papa ne ya yi ƙarfin halin cewa.

"Likita ku yi duk abin kuka san za ta samu lafiya."

Amsa wa suka yi suna komawa ciki.

Bayan tafiyar likitan ne Abba ya fashe da kuka yana cewa.

"Alhaji ka ji abin da yake faruwa Allah yasa ba da gaske ba ne, da wane ido zan kalli Muhammad Zaid."

Dafa kafaɗarsa Papa ya yi tare da cewa.

"Haba Ahmad ka yi haƙuri komai zan zo da sauƙi yanzu dai mu yi addu'a ta samu lafiya zan mu ji inda cikin ya fito."

"Allah da sai na kasheta, ba zan iya kallonta da abin ta aikata min ba, ciki fa Alhaji da auren wani a kanta, Subbahallahi! Allah ka yafe min ban sani ba, ko wani laifin na aikata har ka jarabce ni da irin wannan jarabawar."

Papa ne ya zaunar da Abba shi ma yana hawaye, Mama kuwa faɗuwa ta yi a wajen tana kuka sosai, duk familyna da nasa kowa kuka yake, suna cikin wannan yanayin ne Muhammad Zaid ya zo.

Ganin suna kuka sosai ne yasa ya ce.

"Abba, Papa, Noor ta mutu ne?"

Rungumeshi Abba ya yi yana kuka sosai, babu wanda ya bashi amsa sakin Abba ya yi yana kamo hannun Ahmad Zayyan ya ce.

"Ahmad Zayyan ka ga Noor ta mutu innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ta mutu fa shi kenan ni ma na san mutuwa zan yi.."

Riƙe shi Ahmad Zayyan ya yi yana hawaye ya ce.

"Mama da gaske Maryama ta mutu?"

Ummah ce ta goge hawayan fuskarta ta ce.

"Ai Muhammad Zaid har gara a ce Uwar masu gida mutuwa ta yi da irin wannan abun kunyar."

Tsayawa ya yi da kukan ya ce.

"Abba me ya faru ne?"

Aunty Mansura ce ta ce.

"Ciki ta yi."

Bakinsa yana rawa ya ce.

"Ciki! Ciki! wane irin ciki kuma, ai ta ce min cikinta yana ciwo.."

Ummah ce ta yi saurin cewa.

"Oho har ta faɗa maka ma kenan to ba na faɗa maka gaskiyar maganar ciki na haihuwa wani ya yi mata, kuma da muka yi sa'a cikin ma ya lalace babu wanda ya sani har tsawon wat.."

Tsawa Muhammad Zaid ya yi mata tare da cewa.

"Ya isa bana son jin komai daga gareki, Abba don Allah ka faɗa min abin da yake faruwa."

Goge fuskarsa Abba ya yi tare da cewa.

"Haka ne Muhammad Zaid ciki ne a jikin Uwata..."

Kafin Abba ya rufe bakinsa Muhammad Zaid ya rungume shi yana cewa.

"Ma sha Allah ciki fa Abba, Ahmad Zayyan ka ga ni ma na kusa na zama Bab.."

Ammyy ce ta buge masa baki cikin ɓacir rai ta ce.

"Kai yi mana bayani, kana da alaƙa da cikin jikinta ne ko me?"

Bakinsa ya kama sai yanzu ya tuna babu wanda yasa suna keɓewa.

Kusa da Ahmad Zayyan ya dawo yana ƙasa da kaina ya ce.

"Ahmad Zayyan yi musu bayanin."

Rai a ɓace Papa ya ce.

"Uwarka dai ba Ahmad Zayyan ba, za ka yi mana bayani ko sai rainka ya ɓaci."

Shiru Mama ta yi da kukan tana kallonsa.

Ƙasa ya yi da kaisa ya ce.

"Eh Ammyy cikina ne kum."

Duka Ammyy ta kaho masa Mama ta yi saurin tarewa. Rai a ɓace Ammyy ta ce.

"Wai dama kai baka da kunya yanzu sai da ka bi yarinyar nan har gidan iyayenta."

Ajiyar zuciya Abba ya sake yana kallon fuskarsa shi ban san ma abin da zai ce ba.

Tsaki Papa ya yi tare da cewa.

"Wallahi na san Maryama ba za ta aikata abin da kuke tunanin ba, kawai da bani da hujja ne, amma wallahi zuciya Muhammad Zaid ta fara zirgi."

Dariya Ahmad Zayyan ya yi tare da cewa.

"Ai wallahi Papa Muhammad Zaid ba shi da kunya duk yadda Maryama take gudun abun kunyar nan sai da ya ja mata."

"Kai tafi daga nan ba duk bakinku ɗaya ba."

Sosai kai Ahmad Zayyan ya yi yana murmushi. A hankali Muhammad Zaid ya ce.

"Abba ya jikin Noor da fatan babu abin da ya same su ita da cikin ko?"

Papa ya ɗaga hanunsa zai buge shi Abba ya yi murmushi tare da riƙe hannu ya ce.

"Muhammad Zaid ciki dai ya lalace, yanzu ma likita ta ce zubar da shi za su yi."

Da sauri ya kama hannun Abba yana cewa.

"Amma dai ba su ce ni na zubar da ciki ba ko?"

Ahmad Zayyan ne ya kamo shi tare da cewa.

"Kai zaka yi abun kunya. Ka yi subul da baka."

Kama hannun Ahmad Zayyan ɗin ya yi suna ɗan matsowa gefe.

Jikinsu Ummah da Aunty Mansura ne ya yi sanyin tun fara maganar Muhammad Zaid, Mama kuwa ajiyar zuciya ta sauke ta kallon Ammyy ta ce.

"Ni Amina na ga tashi hankali, amma fa yaran nan su ba ni mamaki, ban san yaushe suka fara keɓewa babu wata alama da fahimta ko daga ɓangarenta."

"Uhm ai Amina ni abun yafi bawa mamaki wai fisabililahi, Muhammad Zaid da girmansa ya aikata irin wannan abun kunyar ai wallahi ko Sauban ba na tunanin zan aikata."

Dariya Mama ta yi tana cewa.

"Ni wallahi kunya ma na ji wai mana cikin gidan, amma ba mu san abin da ya faruwa ba."

"Allah ya kyauta, ita kuma Allah ya ba ta lafiya ya kaho wani nan kusa."

"Amin ya Allah Hajiya amma ba'a a gidanmu ba."

Dariya Ammyy ta yi tana kallon Khadijah da Siyama da suke magana ƙasa ƙasa.

Dariya sosai Ahmad Zayyan ke yi, haushi ne ya kama Muhammad Zaid ya ce.

"Wai dariyar me ka ke yi?"

"Dole na yi dariya Muhammad Zaid, bayan abun kunyar da ka aikata shi ne kake ƙoƙarin sake wani, to ta ya ya ka zubar da cikin dole akwai wani abu da ka sani."

Murmushi Muhammad Zaid ya yi tare da cewa.

"Ban san tana ciki ba, kawai dai ɗazu ta ce min tana ciwon mara da ciki, shi ne abin da na sani, amma ban ji daɗin zuɓewar cikin nan ba."

"Sai haƙuri ni ma haka na ji lokacin da Baby ta yi miscarriage ban ji daɗin ga ita ma ta sha wahala sosai."

Kusa da su Abba Muhammad Zaid ya dawo, zama ya yi yana haɗa kai da gwiwa tana cewa.

"Ni fa gaskiya ina so shiga na ga Noor ban san halin da take ciki ba."

Shiru duk suka yi masa babu wanda ya kula shi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol