Free chapter · Read without an account

BABI NA SHA ƊAYA

by Maryam Usman · MATAR AURE CE

*********

Babu ɓata lokacin muka isa gida, ta wata hanya muke bi, yanzu ba ma shiga ta cikin falon su Ammyy ta ƙofar baya muke shiga ɓangarenmu.

Ko a falo ba mu tsaya ba, Direct bedroom muka shiga ba zan iya faɗa muku irin ƙaunar da muka nuna juna a lokacin ba, amma mun ji daɗin kasancewa sosai, ni da kaina na san babu ranar da muka shayar da juna zumar ƙauna irin ta wannan lokacin.

Ranar dai kowa ya san muna cikin nishaɗi, ko a wajen cin abincin dare ma, su Ammyy sai rufe idanunsu suka yi, dan mun manta da zancen su a wajen, daga ƙarshe ma su ne suka tashi.

Washegari da sassafe ya kai ni gidan A'isha, a can na yini sai dare ya zo ya ɗauke ni, kullum a can nake yini ko ranar suna bai yarda na kwana ba.

Washegarin suna Aunty Fati ta haihu sosai na yi farinciki.

Ana gobe suna na tafi, sai da na yi kwana biyu, sunana aka sakawa yarinyar da aka haifa na yi farinciki my Zaid ma ya yi ƙoƙari sosai dan kayan da ya yi wa yarinyar da Aunty Fati ba sa su faɗi ba.

*************

Yau sati biyu da hutu, tun bayan hutun Makarantar da aka yi My Zaid bai fi ya zama a gida ba kullum yana Makaranta yau ne kwai ya samu hutu.

Zaune muke a falo ina amfani da wayarsa shi kuma yana duba Exam murmushi ya yi tare da cewa.

"Noor."

Ban ɗago kaina ba na ce.

"Na'am."

"Don Allah zo ki ga wani hauka."

Ajiyar wayar na yi ina dawowa gefensa na zauna ina duba abin da yake nuna min.

Ido na zaro na ce.

"Baby waye kuwa ya rubuta wannan exam ɗin yana da hankali kuwa?"

Murmushi ya yi tare da nuna min wata exam ɗin tare da cewa.

"To haka fa suke yanzu don Allah ko ki ba za ki ba wa wannan Corry over ba?"

"Taɓ ai da ana bayarwa sau biyu to sai na ba shi wannan ai hauka ne. A yi maka tambaya ka rubutawa Malami don Allah ka yi haƙuri Malam ban yi karatu ba."

Tsaki ya yi yana ajiye exam ɗin tare da jana jikinsa ya ce.

"Ni fa Noor na gaji wai babu wani abu da zan samu ne?"

Dariya na yi ina kama hannunsa da yake ƙoƙarin saka min a riga na ce.

"Allah my Zaid baka son zaman lafiya, ana maganar arziki sai ka..."

Shiru na yi sakamakon ɗaga ni da ya yi cak zuwa bedroom, yana sauke ni na fito ina dariya bayana ya biyo tare da cewa.

"Noor ka da fa ki bari na kama ki, Allah rainki zai ɓace."

Zama na yi a kujerar ina turo baki na ce.

"To na tsaya amma me ka ce jiya?"

Murmushi ya yi yana kwanciya a cinyata ya ce.

"To ai jiya ta wuce maganar yau ake yi."

Shafa kansa na yi ina wasa da yatsun hannunsa na ce.

"To ka yi haƙuri sai zuwa dare ko yamma yanzu fa wani abu nake yi a wayarka."

Shiru ya yi jin ya ina wasa da gashin kansa ganin ya yi shiru ne yasa na yi masa kitso a sumar kansa.

Ban san na yi ba domin bacci ya fara yi har na gama ba farka ba, ni ma bacci ne ya kama ni, kaina na ɗara a saman ƙirjinsa.

Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali muke bacci, sallama na ji kamar a mafarki na yi saurin buɗe idona Aunty Mansura ce tsaye a falon da alama ta jima da shigowa, sai na ji murya Khadijah da Samiha da sauri na motsa zan tashi ya riƙe ni.

A hankali na kwantar da murya na ce.

"Baƙi fa na yi don Allah ka tashi kasan ba wasu kayan arziki ne a jikina ba."

Tashi ya yi da ɗan zafi yana ɗaga ni cak bedroom ya shiga tare da rufe ƙofar da ƙarfi.

Akan ido su Hafsat ya shiga da ni ɗaki, zama suka yi a falon Khadijah ta kawo musu ruwa.

Kallon fuskarsa na yi ina cewa.

"Ka yi baccin ni zan fita wajen su."

Kwanciya ya yi tare da rufe jikinsa kiss na yi wa fuskarsa ya kama hannuna ya ce.

"Amma ki saka hijabi kafin ki fita."

Dariya na yi ina sauya kayan jikina na ce.

"Na sauya kayan jikina ma."

********

Zaune suke a falon Samiha na hotuna Khadijah kuma tana waya Aunty Mansura ce zaune a kujerar da muka tashi tana duba takardun wajen.

Murmushi na yi ina cewa.

"Assalamu alaikum."

Duk kallona suka yi na zauna ina gyara takardu da ya bari.

Dariya Samiha ta yi tana cewa.

"Yau dai ƙarshen ƙarya ya ƙare."

Murmushi na yi ina cewa.

"To wa nake jin tsoron a cikinku?"

Khadijah ce ta yi dariya tana cewa.

"Ni dai Aunty Maryama abinci zan ci, su Aunty Hafsat ne suka hanani cin abincin wai sai na rakosu."

Ajiyar takardun hannuna na yi ina cewa.

"Ni kuma ban yi abinci ba, sai dai ki kira Siyama ta zo sai ku dafa mana ni ma na fara jin yunwa."

Dariya Hafsat ta yi tana kallon fuskata ta ce.

"Dama ta ya za ki yi wani abinci kun manne da juna ana shan ƙauna."

Dariya na yi ina harararta zan yi magana Aunty Mansura ta ce.

"Maryama wannan exam ɗin wannan semester ce?"

Kallon exam ɗin da ya ajiye na yi ina cewa.

"Eh."

Ido Samiha ta zaro tare da cewa.

"Don Allah nuna min tawa na ga ko wannan semester ma ya ƙara min Corry over."

Murmushi na yi ina cewa.

"To ba ta mu ba ce ta yan level one ce."

"Ina ta yan level 3 nuna min na duba tawa"

Kallon Aunty Mansura da ta yi magana na yi na ce.

"Tana bedroom kuma bacci yake yi ba zan koma ba."

Ina faɗar haka na dawo kusa da Samiha da Hafsat muna magana, ina kallon Aunty Mansura tana duna exam ɗin ban kula ta ba.

Khadijah ce da Siyama suka shigo sai Ƙawayen Siyama da suke bayansu. Siyama ce ta zauna kusa da ni tana cewa.

"Ina kwana Aunty Maryama tun ɗazu nake son shigowa amma na ga Yayanmu ban fita ba."

Harararta na yi ina cewa.

"Amma ai na kira wayarki ba ki ɗaga ba."

"Wai dama ke ce kika kira ni da wayar Yayanmu wallahi na yi tunanin shi ne ba na so ya yi min faɗa shi ne naƙi ɗagawa."

Kallon Ƙawayen nata na yi ina amsa gaisuwar da suke min zama suka yi suna kallon falon.

Kitchen Siyama da Khadijah suka shiga abincin suka yi mana muna hira ni da su Hafsat, daga ƙarshe Aunty Mansura wani bedroom ɗin ta shiga har suka gama abincin sannan ta fito.

Sosai na yi farinciki ganin mutane a ɓangarenmu, dan tun da na tare babu wanda ya shigo iya Siyama ce ita ma ba kullum ba.

Abincin ya ji kifi da naman rago sai ƙamshin yake zubarwa, a tsakiyar falon muka zauna ni da su muna ci har Aunty Mansura kowa yana farinciki.

A hankali na ji muryarshi yana cewa.

"Noor! Noor! Noor!

Tashi na yi duk suka bi ni da kallo, ɗan murmushi na yi ina cewa.

"Ina zuwa ku ci abincin..."

"Noor! Noor!

A hankali na ce.

"Na'am Baby irin wannan kir..."

Tsaye na same shi daga shi towel yana kallon ƙofar falon.

Hannunsa na kama ina cewa.

"Ka tashi? To zo na shirya ka ka tafi masallaci."

Zame hannunsa ya yi tare da zama a gefen gado yana marerece murya ya ce.

"Tea nake buƙata sannan sai wayata da sauran kayana duk suna falo."

Tashi na yi ina cewa.

"Okay yawwa yanzu my Zaid da ban zo ba a haka zaka fita Falon?"

Ɗaga min kansa ya yi tare da cewa.

"Na manta da baƙi har na fita sai na ji muryar mutane na tsaya."

Fita na yi ba tare da na sake magana ba, a tsaye na samu Siyama da Ƙawayenta na ce.

"Siyama lafiya na ga za ku fita?"

Ido ta zaro tana nufar hanyar fita ta ce.

"Taɓ so kike ya fito ya same ni a falonsa yau na shiga uku, a'a yana fita dai zan dawo."

Hanyar kitchen na nufa ba tare da na yi mata magana ba tea ɗin na haɗa masa sannan na fito.

Kallon fuskata Aunty Mansura take tun fitowa ta, ban kula ta ba na shiga bedroom ɗin, wayarsa na dawo na ɗauka da takardunsa.

Duk shigar da zan yi akan idon Aunty Mansura ta zuba min ido sai kallon shiga da fita ta take.

Ina zaune a kusa da shi ya sha tea ɗin sannan ya yi alwala, tare muka fito da shi hannunnsa cikin nawa.

Shiru duk suka yi suna gaida shi, amsawa ya yi tare da fita har baƙin ƙofar falon mu na raka shi, sannan na dawo.

Zama na yi ina cigaba da cin abincin.

Tare muka zauna da su har la'asar sannan suka tafi, Allah ya taimake ni a lokacin yana gida Sauban ya saka ya maida su gida sannan ya bawa kowa dubu biyar -biyar.

A daren ranar kasa bacci na yi domin wannan abinci da na ci amai ya saka da ciwon ciki, sai da na amayar da shi, sannan muka huta kafin safiya na yi zuru-zuru.

Kuma har lokacin ban danna yin aman ba, asibiti ya ce za mu tafi na ce bana so dole sai haƙura a ka yi.

Sai wajen yamma na ji sauƙi sosai tun daga lokacin ban sake yin aman ba, a lokacin shi ma kansa ya rame kamar tare muke yin aman, sosai ya yi wa Siyama faɗa wai sun zuba wani abu ya ɓata min ciki.

Dole sai Ammyy ce ta ba shi haƙuri, sannan ta ba shi wani magani ta ce na sha zan ji sauƙin cikin nawa.

Cikin nufin Allah kuma na ji daɗinsa sosai.

**********

Tun daga ranar ya hana ni cin abincin kowa iya na Ammyy ya yarda na ci.

Ana cikin haka muka koma Makaranta satin da aka koma ban koma ba, saboda bana jin daɗin jikina tun daga ranar da na ci abincin nan shi kenan na fara jinya daga zazzaɓin dare sai mura mai saka ciwon kai.

Saboda murar da nake fama da ita yanzu ko AC ba ya kunawa babu abin da ake sha na sanyin wai duk dan na ji sauƙi amma kamar ƙara min murar ake yi.

Yau ma kamar kullum na tashi da ciwon kai sosai, amma duk da hakan na shirya za mu tafi Makaranta ina kwance a kujera ya fito.

Tsayawa ya yi yana kallon fuskata cike da tausayi ya ce.

"Noor ki haƙura da zuwa Makarantar nan, kin ga idanunwanki kuwa?"

Ɓata fuska na yi ina cewa.

"Ni fa gaskiya sai na je ba gidanmu zan wuce bayan na gama ba?"

Shiru ya yi da alamar tausayi akan fuskarsa ya kama hannuna muka fito, Ammyy ma sai da ta yi magana akan na haƙura da zuwa Makarantar amma na nuna ina so.

Tun fitowar mu daga gidan nake kallon titi idona ne ya sauka akan mai saida ɗata da layo, da sauri na kama hannunsa ina cewa.

"Don Allah ka tsaya My Zaid."

Kallon fuskata ya yi tare da tsayar da motar ya ce.

"Lafiya Noor?"

Baki na turo gaba na ce.

"Wancan zan ci."

Kallon inda nake nuna masa ya yi tare da juyowa yana cewa.

"Noor me za ki yi da shi?"

Karkatar da kaina na yi ina cewa.

"Ci fa zan yi my Zaid."

Murmushi ya yi kaɗan, sannan ya sake kallon mai saida ɗata da layo ɗin.

"Da gaske Noor? Wannan kike so cin ke da kike fama da ciwon ciki shi ne za ki ƙara masa da wannan abun?"

Kai na girgiza masa cikin shagwaɓa na ce.

"Eh mana, tun da na gan shi nake jin kamar idan ban ci ba zan yi kuka."

Ɗan dariya ya yi amma akwai damuwa a idanunsa, ya ce.

"To ina zuwa."

Ya buɗe ƙofar motar ya fita. Kallon sa nake yi har ya isa wajen mai sayarwar.

Bai daɗe ba ya dawo da leda a hannu.

Murna na yi sosai ina karɓa na ce.

"Nagode My Zaid."

"Ki ci kaɗan don Allah Noor bana so ki sake yin aman nan, ko cikinki ya ƙara ciwo."

Kai na ɗaga masa, sannan ya wanke min na fara ci.

Muna tafi a hanya yana kallona lokaci-lokaci. Ni kuma hankali na yana kan ɗata da layo.

Muna isa Makaranta kuwa, fitowa na yi da layona da ɗata ta a hannuna.

Murmushi ya yi tare da cewa.

"Idan kin gama lecture ki kira ni."

Shafa fuskarsa na yi ina cewa

"To."

"Idan kuma kin ji ba daɗi ko kaɗan, ki kira ni nan take."

Murmushi na sake yi ina turo baki na ce

"To Prof."

Sai da ya tabbatar na shiga cikin class ɗin sannan ya tafi.

A class ma hankalina bai kwanta ba. Ciwon kan ne yana dawo min amma duk da haka ban daina cin layo da ɗata ɗin ba.

Samiha da Hafsat sai kallona suke yi tun da na shigo babu wacce ta yi min magana akan layon da nake ci.

Sai bayan an gama lectures ne muna zaune a ƙarƙashin bishiya na ga wani yaro yana sai da alawar madara da iloka na tsyar da shi.

Kallon fuska Hafsat na yi ina cewa.

"Siya min."

Samiha ce ta siya min ta ɗari biyar tun kafin yaron ya tafi na cinyeta.

Kallon fuskata Hafsat ta yi tana cewa.

"Amma Maryama ba ki da mutunci yanzu a siya mana abun shi ne za ki shanye ko?"

"Ta shenya kuma?"

Shiru na yi ina kallon su, mai alawar madara ne zan tafi na yi saurin cewa.

" Tsaya mai alawar madara."

"Ai babu wanda ya ce yana so, na yi tunanin tawa ce ni ɗaya"

Na faɗa ina kallonsu.

"Yanzu waye zai sake siya to wallahi yau ban zo da kuɗi ba, Samiha ce mai kuɗi kuma ta siya kin shanye."

Jakata na ɗauka ina cewa.

"Kai zo muje a siya min dan wallahi ba ta ishe ni ba."

Hanya na nufa zan tafi Hafsat ta ce.

"Wai office ɗin Prof Muhammad Zaid za ki je?"

Idanuwana na juya mata tare da cewa.

"Eh ko da magana?"

Tafiya ta na yi ba tare da sun yi magana ba, ina tafe mai alawar madara yana bayana, har cikin office ɗinsa da baya rabo da mutane.

Sallama na yi da muryata wacce mura ta gaba cinyewa.

Ɗaliban ne su biyar sai Prof Kamis a zaune ni tun ranar da abun nan ya faru ban sake kallonsa ba sai yau ko class ɗinmu ya daina shiga.

A hankali ya ɗago kansa yana lumshe ido ya tsaya yana kallona. Sai kuma ya zaro ido ganin mai lalle a office ɗin nasa.

A hankali na ƙarasa shigowa na yi ƙasa da murya na ce.

"Wannan zaka siya min."

Tashi tsaye ya yi tare da saka hannunsa a aljihu yana zaro kuɗi masu yawa, da sauri na karɓa ina cewa.

"Na gode sosai."

Hannuna ya riƙe tare da kallon mai alawar madara ya ce.

"Don Allah ki rufa min asiri Noor kar ki sha wannan kayan zaƙin wai kin manta ciwon ciki kike yi ne?"

Hannuna na ƙwace ina turo baki na ce.

"Ai na cinye layon kuma bana son na zauna bana cin wani abu, bakina ne babu daɗi."

Kafin ya yi magana na siya mana alawar madara dubu ilokar dubu, ko sallama ban yi masa ba na fita da farinciki na koma wajen su Hafsat, tare muka shaye.

Zamana a wajen duk abun da na gani sai na siya mana, kafin wani lokaci muku kashe kuɗin da na karɓa a hannunsa.

Karfe biyu muka koma class lokacin na siya mana gyɗa da ayya, kaɗan na basu na riƙe masu yawan.

Shi ne ya shigo mana domin yanzu da muke level 3 sai yamma yake mana lecture, ban san ya shigo ba.

Ashe tun shigowarsa yake kallona, ina ɗago ido na yi masa murmushi, shi ma ya yi min. A hankali yake koyarwa, ina jin abin yake ina cin gyaɗata.

Ban san ya fahimci ina cin wani abu ba, sai da na ji muryasa yana cewa.

"Noor me ki ke ci?"

Shiru class ɗin ya yi ana kallon inda yake kallo wato ni, da sauri na cinye ta bakina ina yin ƙasa da kaina.

"Me kike ci?"

Jin murya shi a ɗan ɓace ne yasa na ce.

"Gyaɗa ce."

Kallona kowa yake yi wasu suna mamakin jin irin sunan da ya kirani.

A hankali ya ce.

"Ba ni sauran."

Taɓa ni Samiha ta yi tana nuna min hannunsa da ya miƙo, a hankali na tashi ina zuwa inda yake na zuba masa gyaɗar hannuna, na juya zan koma na zauna ya riƙe hannuna.

Rai a ɓace ya kalla Hafsat ya ce.

"Hafsat ki ba ni sauran da ta ajiye."

Hannunna na ƙwace ina hawaye na kalli Hafsat na ce.

"Allah sai kin biya ni."

Dariya ta yi tana ba shi duk abubuwan da na siyo, mamaki ne ya kama shi ganin irin abubuwan da na siya nake ci, komawa na yi na zauna ina kuka sosai.

A aljihunsa ya zuba sannan ya cigaba da abin da yake yi, sosai nake kukan a hankali ya juyo cikin sanyin murya ya ce.

"Noor zo ki fita ba na son rigima."

Shiru na yi da kukan ina kwantar da kaina bai sake yi min magana ba, ƴan class ɗinmu kuwa sai kallona suke.

️

Bacci na fara yi ban sani ba, sai da ya gama aikinsa zan fita ya kalli ƴan class ɗinmu ya ce.

"Maryama Ahmad Usman Matata ce, na ga kuna kallana bana so ƙananun maganganun da fatan ku fahimta."

Shiru Ajin ya yi ana kallon kallo, babu mai bakin magana, a hankali ya zuwa inda nake, matsawa ɗaliban suka yi ya kamo hannuna zai ɗaga ni na tashi tare da matsawa gefe.

Ganin na tashi ne yasa ya ɗauka min jakata da sauran kayana ya kama hanyar fita, a hankali na bi bayansa ina turo baki.

Bayanmu duk ƴan class ɗin suka bi, har muka shiga mota, suna kallonmu.

Zainab Usman ce ta fashe da kuka tana zama a bakin baranda taruwa aka yi akan ta. Sosai take kuka sai Ƙawayenta ne suka kamata zuwa gida.

************

Ni kuwa muna shiga mota na fara kuka har muka isa ƙofar gidanmu, a hankali yake kallon fuskata ya kasa magana.

Mun jima a haka sannan ya yi murmushi tare da cewa.

"Sorry Noor ni ne ko ba zan ƙara ba."

Tsayawa na yi da kukan ina kallon yadda ya riƙe kunnuwansa, alamar na yi haƙuri.

Goge fuskata na yi ina cewa.

"To ba ni kayana."

Kwantar da murya ya yi tare da cewa.

"A'a Noor Allah bana so kina cin irin wannan kayayyaki ranar fa kin tsorata ni da irin yadda kika yi ciwon ciki nan ni bana so na sake ganin kin yi irinsa."

Fita na yi daga motar ina shiga gida girgiza kai ya yi sannan ya biyo bayana da sallama a bakinsa ya shigo ina zaune kusa da Mama ina hawaye.

Gaisawa ya yi da Mama, Ummah ta yi saurin cewa.

"Allah yasa dai ba wani abun Uwar masu gida ta yi ba ka korota."

Kallon fuskar Ummah Mama ta yi tana girgiza kanta.

Murmushi ya yi tare da cewa.

"Noor don Allah ki yi haƙuri da wannan rigimar sai mun koma gida kin ga ciwon kai kike yi ko?"

Kallon fuskata Mama ta yi tana cewa.

"Wani abun aka yi mata ne?"

Sosai kansa ya yi tare da cewa.

"Uhm uhm Mama kawai dai rigima ce irin ta Noor tun da safe take fama Mama ko abincin ba ta ci ba."

Kallon fuskata ta yi tana girgiza kanta ta ce.

"Ko ba ta da lafiya ne?"

Kafin wani ya yi magana a cikinsu na ce.

"Ni wallahi ƙalu nake ai ya san abun da ya yi min gyaɗa fa na siya a Makarantar ya ƙwace min kum..."

Hannun Mama ta ɗaga zata buge min baki ya yi saurin kama hannun Mama tare da cewa.

"Don Allah Mama ki yi haƙuri ke da za ki rararsheta."

Tashi na yi daga kusa da Mama na dawo kusa da shi har jikinmu yana haɗu.

Khadijah ce ta kawo masa ruwa, bayan ya gama shan ruwa ne na kalle Khadijah na ce.

"Khadijah me aka dafa yunwa nake ji?"

Dariya Khadijah ta yi tana cewa.

"Tuwo ne da miyar kifi."

Kallon fuskata Muhammad Zaid ya yi kamar zan yi magana sai kuma ya fama.

Mama ce ta ce.

"Khadijah kawo musu abincin mana."

Kafin kowa ya yi magana na ce.

"Ni wallahi ba zan ci tuwo ba, sai dai a dafa min wani abu."

Shigowar Abba ce tasa babu wanda ya yi min magana, gaisawa muka yi da shi sannan na fara hawaye, kallon fuskata ya yi tare da cewa.

"Uwata lafiya kike kuka da yamman nan?"

Ummah ce ta yi saurin cewa.

"Tun shigowarsu take kuka ina ga fa yarinyar nan bata jin daɗin zaman gidan Mijin ne..."

Hannu Abba ya ɗaga mata yana kallon fuskar Muhammad Zaid ya ce.

"Lafiya take kuka?"

Sosai kansa ya fara yana kasa magana, kallon Abba na yi ina cewa.

"Wai tuwo aka dafa shi ne na ce su dafa min wani abu na ci yunwa nake ji shi ne babu wanda ya yi min magana."

Murmushi ya yi tare da kallon Aunty Mansura ya ce.

"Haba Mansura ai baƙonka annabinka ita fa baƙuwa ce yanzu."

Hannuna Muhammad Zaid ya kama tare da kwantar da murya ya ce.

"Noor tashi mu tafi gida ni zan dafa miki duk abin da kike so."

Da sauri na goge hawayena ina kallonsa na ce.

"Da gaske?"

Murmushi ya yi ya ce.

"Eh mana, me kike so?"

Baki na turo gaba ina cewa.

"Indomie da kwai da naman kaza."

Dariya ce ta kwace masa ya girgiza kansa ya ce.

"Duk wannan rigimar akan wannan ne to yanzu zan yi miki taso mu tafi."

Abba ne ya girgiza kai yana cewa.

"Ai ba sai kun tafi ba Khadijah ko Mansura sai su dafa mata ko Uwata?"

Hannunsa na rungume ina girgiza kaina na ce.

"Mu tafi gida my Zaid Mama gobe da sassafe Khadijah ta kawo min kunun tsamiya."

Muhammad Zaid ne ya miƙe tsaye bayan ya yi sallama da su Mama da Abba muka kama hanyar gida.

Da kallon mamaki duk suka bi ni Ummah tana son magana amma babu dama har ƙofar gida Abba ya rako mu.

Tun muna mota nake yi masa bayanin irin yadda nake son a yi min Indomie ɗin.

Shi kuwa lokaci-lokaci sai ya kalle ni yana dariya.

"Noor kamar ba ki taɓa cin Indomie ba?"

Shiru na yi sannan na turo baki na ce.

"Ai yunwa nake ji kuma ba kai ne ka hana ni cin gyaɗata."

Kai kawai ya girgiza yana murmushi har muka isa gida.

Muna shiga kai tsaye kitchen ya shiga.

Ni kuma na bi bayansa kamar ƙaramar yarinya a hankali ya yi dariya ya ce.

"Fita ki zauna mana."

Kai na girgiza.

"A'a zan tsaya ina kallo."

"To idan kayan miya ya taɓa ki fa?"

"Ba zai taɓa ni ba."

Na faɗa ina zama akan kujerar kitchen ɗin.

Dole sai haƙura ya yi yana cigaba da girki.

Tun ina kallonsa muna hira da shi, wani irin jiri ya fara ɗibana.

A hankali na dafa kujera.

Ya lura da ni da sauri ya ce.

"Noor lafiya?"

Murmushin ƙarfi na yi.

"Lafiya lau."

Amma kafin ya sake magana sai na ji cikina ya juya.

Da sauri na tashi na nufi toilet.

Amai na fara yi sosai.

Cikin tashin hankali ya biyo bayana.

"Noor! Noor! Noor!

Ya kama ni saboda har ƙafafuna rawa suke yi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol