Free chapter · Read without an account

BABI NA SHA BIYU

by Maryam Usman · MATAR AURE CE

Bayan na gama aman ne ya taimaka min na zauna.

Fuskarsa cike da damuwa ya ce.

"Yanzu za mu je asibiti."

Kai na girgiza, na ce.

"A'a na ji sauƙi."

"Noor!"

Ya kira sunana cikin murya mai nuna ba zai yarda ba.

Duk yadda yaso mu tafi asibiti ƙin yarda na yi dole sai haƙura ya yi.

**************

Washegari da safe kuwa yana shirin fita Makaranta, ni kuma ina kwance.

Yana kallona da fuska tausayi duk na rame yau kam ko tashi kasawa na yi, ya lura ban tashi ba kamar yadda na saba.

Ya taɓa goshina.

Da sauri ya janye hannunsa ya ce.

"Noor wannan zazzaɓi ba sauka zai yi ba kawai mu tafi asibiti."

A hankali na buɗe ido ina kama hannunsa na ce.

"Ka bar ni kawai."

Haushi ne ya kama shi tun jiya yake bina mu je asibiti amma na ƙi yarda, wayarsa ya ɗauka ya kira Ammyy.

Fita ya yi suka yi magana sannan ya dawo yana ɗaukata falo ya fito da ni tare da kwantar da ni a kujera.

Cikin lokaci kaɗan Ammyy ta iso tare da wata likita. Sannu da jiki Ammyy ta yi min sannan likitar ta duba ni sosai.

Kallon Muhammad Zaid ta yi sannan ta ce.

"Ina ganin akwai labari mai daɗi."

Fuskarsa a ɗaure ya ce.

"Wane labari?"

Likitar ce ta sake murmushi.

Ammyy kuwa tun kafin ta yi magana ta fara murna.

Ni kuwa cikin mamaki nake kallonsu.

Likitar ta ce.

"Da alama matarka tana ɗauke da ciki."

"Alhamdulillah!"

Ammyy ta faɗa cikin farinciki.

Muhammad Zaid kuwa ya tsaya cak yana kallona ya kasa motsi.

Ni kuwa baki kawai na buɗe cikin mamaki.

Na kalli likitar, na kalli Ammyy, sannan na kalli Muhammad Zaid wanda har lokacin ya kasa cewa komai.

A hankali na ce.

"Ni?"

Likitar ta yi murmushi tare da cewa.

"Eh ke."

Kaina na girgiza da sauri na ce.

"A'a ba ni ba."

Dariya Ammyy ta yi tana cewa.

"To wa kuma Maryama ai ni ma tun ba yanzu nake zargin hakan ba?"

Bakina na ɗan turo ina cewa

"Ban sani ba, amma ni dai ban yarda ba"

Muhammad Zaid kuwa har lokacin kallona kawai yake yi.

Idanunsa sun canza, kamar zai yi kuka ko kuma ya yi dariya.

A hankali ya zauna kusa da ni ya ce.

"Da gaske?"

Likitar ce ta gyara zama tana cewa.

"Za a yi wasu gwaje-gwaje domin tabbatarwa gabaɗaya amma alamun suna nuna haka."

Shiru duk muka yi ya

Ni kuwa zuciyata bugawa take da ƙarfi.

Ban san dalili ba amma sai na ji tsoro ya kama ni.

Na kama hannun Muhammad Zaid.

Da sauri ya matso kusa da ni yana cewa.

"Lafiya Noor?"

A hankali na ce.

"Tsoro nake ji."

Nan take ya riƙe hannuna cikin nasa, ya ce.

"Babu abin da zai faru da ke in sha Allah."

Bayan sun tafi ne muka rage ni da shi a falon.Shiru ya yi na ɗan lokaci.

Sai kuma na lura yana kallona yana murmushi shi kaɗai.

Harararsa na yi masa ina cewa.

"Me aka yi?"

Kai ya girgiza tare da cewa.

"Babu komai."

"To me yasa kake murmushi?"

Sai ya kamo hannuna, yana dariya ya ce.

"Noor kin san kuwa irin farincikin da kika ba ni?"

Na ɗan sunkuyar da kai na ce.

"Ai ba ni na yi ba."

Dariya ya yi yana matsa hannuna ya ce.

"To wa ya yi?"

Na yi saurin cewa.

"Allah ne."

Kai ya ɗaga.

"Haka ne."

️

Sannan ya sumbaci goshina cikin kulawa a ranar babu inda ya fita muna tare.

************

Da yamma kuwa labari ya bazu wai ina da ciki. Sai yamma ya fita yana fita

Siyama ta shigo da gudu tana cewa.

"Aunty Maryama! Da gaske ne?"

Kallon ta na yi ina cewa

"Ban sani ba."

Rungume ni ta yi tana dariya.

"Wallahi ni na sani."

Shigowa Khadijah ce ta Siyama yin shiru.

Daga baya kuma Aunty Mansura ta shigo, kallon fuskar Khadijah na yi ina cewa.

"Ina kuma kunun tsamiyar da na ce ki kawo min?"

Dariya ta yi tana cewa.

"Ai dole mu kawo kunun tsamiya tun da yaron mu yana so ko Siyama?"

Murmushi Siyama ta yi tare da zuba min kunun tsamiyar kuma Alhamdulillah! Na ji daɗinsa sosai sai da na sha cup uku sannan na ji na ƙoshi.

Aunty Mansura ce bayan na gama shan kunun tsamiyar ta ce.

"Wai da gaske ciki ne da ke?"

Kwanciyata na gyara ina cewa.

"Ni ma ban sani ba, kawai dai likitar ta ce wai ciki ne da ni."

Rai a ɓace ta ce.

"Amma ke mahaukaciya ce, wai dama lokacin da kika yi miscarriage babu wani planing da kika yi? To yanzu da kika yi ciki ya za ki yi da karatunki?"

Shiru na yi ina tunani maganar ta gaskiya ina son karatuna sosai, kuma ga abin da Aunty Mansura take ce min yanzu, kenan tun da ina da ciki ba zan yi karatu ba.

Kamar ta san abin da nake tunani a zuciyata ta ce.

"Samun ciki a wajenki babbar matsala ne shi kenan ba ki da damar yin karatu wahalar ciki ma ta ishe ki."

Khadijah ce ta yi saurin cewa.

"Amma Aunty Mansura ina ruwank.."

Buge mata baki Aunty Mansura ta yi tana cigaba da tsorata ni, sosai kuma na tsorata, sai bayan sallar magriba suka tafi gida a lokacin jikina ya yi sanyi sosai.

******************

Da dare muna zaune a falo.

Kaina yana kan cinyarsa.

Shi kuma yana shafa gashina.

A hankali ya ce.

"Noor."

"Na'am."

"Kin san wani abu?"

Kai na ɗaga ina cewa.

"A'a."

Ya yi murmushi sannan ya ce.

"Tun da kika ce za ki cin ɗata da layo da iloka da alawar madarar nan na fara zargin wani abu."

Da sauri na tashi zaune na ce.

"Kuma shi ne ka ƙwace min gyaɗata?"

Dariya ya yi tare da cewa.

"A'a kawai dai na ji tsoro ne ka da ta ɓata miki ciki."

Na turo baki.

"Ban yarda ba kuma sai ka biya ni kayana."

"To me zan yi ki yarda?"

A hankali na ɗan yi tunani.

Sai na ce.

"Ice cream."

Da sauri ya ce.

"A'a."

"Me ya sa?"

Na faɗa ina turo baki.

"Saboda ba na son ki sake yin mura."

Hararar sa na yi.Shi kuma ya fashe da dariya.

Bayan kwana biyu haka muka je asibiti domin sake gwaji.

Zuciyata cike take da fargaba.

Muhammad Zaid ma ya fi ni shiga tashin hankali.

Har likita tana masa dariya.

Bayan an gama komai ne Likitar ta dawo da sakamakon.

Ta yi murmushi tana kallonmu.

Sannan ta ce.

"Masha Allah an tabbatar."

Na ji gabana ya faɗi.

Muhammad Zaid kuwa lumshe ido ya yi yana faɗin.

"Alhamdulillah."

Likitar ta ce.

"Za ku fara kula sosai daga yanzu."

Ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba.

Wani irin farinciki ne da tsoro a lokaci guda suka shiga min zuciya.

Muhammad Zaid ne ya kamo hannuna.

A hankali ya ce.

"Noor..."

Na kalle shi.

Sai ya ce.

"Kin ba ni kyauta mafi girma a rayuwata."

Nan take na fara kuka sosai.

Shi kuma ya rungume ni cikin kulawa.

Bai san cewa a wannan lokacin ba farincikin cikin ne kawai yake sa ni kuka ba...

Kukan tsoro nake da rashin sanin matsayin karatuna.

A hankali ya ɗago fuskata daga ƙirjinsa yana goge min hawayen da suka cika idanuwana ya ce.

"Me ya sa kike kuka haka Noor?"

Kai na girgiza masa ina ƙoƙarin hana sabon kukan fitowa na ce.

"Ban sani ba."

"Kin sani."

Ya faɗa cikin nutsuwa yana shafa kuncina.

Na ɗan yi shiru kafin na ce.

"My Zaid..."

"Na'am Noor."

"Idan na haihu fa?"

Murmushi ya yi tare da cewa.

"To me zai faru idan kin haihu?"

A hankali na ce.

"Karatuna fa?"

Shiru ya yi na ɗan lokaci.

Sai kuma ya ɗauki hannuna ya manna a ƙirjinsa ya ce.

"Noor ki kalle ni."

A hankali na ɗaga kai na kalle shi ina hawaye.

"Wa ya ce miki za ki bar karatu?"

Cikin rawar murya na ce.

"Aunty Mansura ce ta ce ba zan iya ba tun da ina da ciki."

Ɗan numfashi ya sauke yana girgiza kansa ya ce.

"Noor, kin san wani abu?"

Kaina na girgiza ina kallon fuskarsa.

"Ba kowa ne ya san abin da Allah ya shirya ba."

Shiru na yi ina saurar sa.

Ya cigaba da cewa.

"Kin yi wahala kafin ki kai wannan matakin na karatu. Kuma ni ne mutum na farko da ya san yadda kike son makaranta."

Shiru ya yi na ɗan lokaci sannan cikin tausasawa ya ce.

"Ko da duniya gabaɗaya za ta ce ba za ki yi karatu ba, ni zan tsaya a gefenki har sai kin gama."

"Na san mahimmancin karatu kuma ina da burin Matata ta yi karatu mai zurfi."

Kallon fuskarsa na yi babu komai sai zallar gaskiya babu wasa a maganarsa.

Hannunsa ya ɗora a cikina yana murmushi tare da cewa.

"Wannan ƙaramin baƙon da yake zuwa ba zai hana mahaifiyarsa karatu ba."

Dariya ce ta kuɓuce min duk da hawayen da nake yi, shi ma dariya ya yi tare da cewa.

"Kin ji ko?"

Kai na ɗaga masa ina kwantar da murya na ce.

"Na ji."

"Good girl."

Kaina na kwantar a kafaɗarsa.

A karo na farko tun da aka tabbatar min da cikin nan na ji wani irin kwanciyar hankali ya sauka a zuciyata.

Tun daga ranar kuwa Muhammad Zaid ya canza gabaɗaya.

Da safe idan zai fita sai ya tabbatar na ci wani abu.

Da rana sai ya kira ni fiye da sau goma.

Da dare kuma babu abin da yake yi sai tambayar lafiyata.

Tun a ranar na kira A'isha na faɗa mata ina da ciki, sannan na kira Aunty Fati sosai ta yi murnar jin ina da ciki kasa faɗawa Mama na yi.

Sai Siyama ce ta faɗawa Khadijah, ku san halin Khadijah da yaɗa zance a lokacin ta faɗawa Ummu da Mama har Abba da yake kasuwa sai da aka kira.

Aunty Mansura kuwa hauka ne ba ta yi ba domin rasa inda zata saka kanta ta yi.

Sai da na yi sati guda sannan na koma Makaranta, ranar na ga kallo kowa kallona yake.

Tun shiga ta harabar Makaranta na ji ni tamkar sabuwar ɗaliba domin irin kallona da ake yi, wasu suna murmushi, wasu kuma suna raɗaɗi a tsakaninsu.

A hankali na ja numfashi ina ƙoƙarin nuna kamar ban damu ba.

Har a class ɗin ma sai kallona ake yi babu wanda na kula ko Samiha da take min dariya ban kula ta ba.

Sai bayan mun samu hutu ne muna zaune a ƙarƙashin bishiya, duk na gaji ga bakina babu daɗi.

Tsaki na yi ina cewa.

"Ni wallahi abu mai ɗin daɗi nake son ci."

Dariya Hafsat ta yi tana cewa.

"To me kike son ci Maman biyu?"

Ido na zaro bakina na rawa na ce.

"Ke! Waye ya faɗa miki ina da ciki?"

Dafa kafaɗata Samiha ta yi tana dariya ta ce.

"Ke! Dai ina ruwanki ciki dai mun san kina da shi, kuma muna addu'ar Allah ya sauke ki lafiya."

Murmushi na yi ina cewa.

"Ko ma wane munafukin ne ya faɗa muku ban yafe ba."

Dariya duk suka yi, ni kuma ina tashi ko kallon su ban yi ba na kama hanyar tafiya.

"Na zo na raka ki?"

Juyawa na yi jin abin da Hafsat ta ce, murmushi na yi ina cewa.

"Zo mu je mana."

Tasowa suka yi ita da Samiha muka tafi muna tafiya muna hira, tare muka shiga office ɗin.

Prof Ahmad Zayyan ne ya tashi ganin shigowarmu yana murmushi ya ce.

"Maryama ya jiki ashe baby ta kusa zuwa duniya?"

Kunya ce ta kama ni na kasa magana sai fuskata da na rufe, kusa da ni Muhammad Zaid ya zo tare da riƙe hannuna ya ce.

"To kai Ahmad Zayyan ina ruwanka?"

Dariya Ahmad Zayyan ɗin ya yi tare da cewa.

"Dole na tambayi lafiyar Babyna."

Yana gama faɗar haka ya fita yana dariya, yana fita su Hafsat suka fita suma.

Shafa fuskata ya yi tare da cewa.

"Noor ya jikin kina buƙatar wani abu?"

Zama na fara yi sannan na ce.

"Ni Allah bakina ne babu daɗi kuma na gaji."

Murmushi ya yi tare da cewa.

"Sannu yanzu ki fara kwanciya ki huta sannan ki faɗa min abin da kike so ko?"

Hijabin jikina na cire ina hamma sannan na kalle fuskarsa na ce.

"My Zaid ka raka ni gidanmu na sa Mama ta yi min kunun tsamiya na sha da zafinsa."

Hannunsa ya ɗora akan cikina yana murmushi ya ce.

"Yanzu kai Ahmad Zayyan haka za mu yi da kai? Ba zaka bar Mamanka ta huta ba?"

Dariya na yi ina ɗaga hannunsa daga jikina na ce.

"Ni fa gaskiya sunan Yarinyata A'isha."

Murmushi ya yi kawai ba tare da ya yi min magana ba, a office ɗin na yi bacci kafin lokacin salla.

bayan na tashi kasa zuwa lecture na yi dole sai haƙura na yi na kwanta shi kuma yana aikinsa.

Sai bayan ya gama ne muka tafi, hanyar gidanmu ya nufa farinciki ya kama ni sosai, murmushi ya yi ganin ina farinciki.

Yana tsayawa a ƙofar gidanmu na fita da gudu ina shiga gida.

"Mama! Mama! Mama!

Shin abin da nake faɗa har na ƙaraso tsakar gidanmu, Mama na ga a tsaye tana kallon hanya murmushi na yi ina cewa.

"Assalamu alaikum Mama."

Ummah ce ta fara magana tana cewa.

"Amma dai Uwar masu gida sai addu'a yanzu haka ake shigowa gida?"

Baki na turo na ce.

"To ai na yi sallamar ko babu wanda ya ji ne?"

Tsaki Aunty Mansura ta yi tana cewa.

"Ai ke ba ki da hankali."

Cike da rashin mutunci na ce.

"Wallahi sai dai ke ce marar hankali amma n...."

Baki ta buge min tana cewa.

"Ni sa'ar ki ce?"

Ko kallon fuskata ban yi ba na ce.

"Allah ya isa ai ni ma ba sa'arki ba ce tun da ina da ciki kuma ina haihuwa na zama Uwa.."

Mama ce ta ɗaga hannu na yi saurin ɓuya ina cewa.

"Ai gaskiya na faɗa kuma wallahi kika sake ce min marar hankali sai na ram.."

Da gudu na fira waje ganin Mama ta biyo ni yana tsaye a jikin motarsa yana waya na fito da gudu, wayar ya kashe yana cewa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Noor wai ke bakya tsoron wani abu ya samu cikin nan?"

Baki na turo gaba ina cewa.

"Ba Mama ce za ta dake ni ba."

Magana zan yi ya fara sakamakon ɗaya motarsa da ya ga ta tsaya a ƙofar gidanmu, tsayawa ya yi yana kallon motar ni ma na yi mamakin ganin ta.

Khadijah ce ta fito ita da Sauban suna murmushi mamaki ne ya kama ni sosai ganin yadda suke kallon juna.

A hankali na taɓa Muhammad Zaid ina yi ƙasa da murya na ce.

"Baby kana ganin abin da nake gani soyayya suke kenan?"

Shiru ya yi ba tare da ya yi magana ba, a hankali Sauban ya ɗago kansa Muhammad Zaid da ga a tsaye ne yasa ya yi sauri zai koma motar Muhammad Zaid ya tsayar da shi.

Sosa kai Sauban ya fara yana kasa motsi, a hankali na kama hannun Muhammad Zaid na yi ƙasa da murya na ce.

"My Zaid kasa Sauban ya ji kunya, gaskiya ka rabu da shi ya tafi gida in dai ka koma gida sai ka yi masa duk abin da za ka yi masa."

Shiru ya yi bai sake magana ba, a hankali Sauban ya shiga motar yana fita daga layin, Khadijah kuwa tun ɗazu ta shige gida.

Tare da shi muka koma cikin gidan, tun shigowar mu Ummah take zaune a tsakar gidan domin jin abin da zan faɗa.

A hankali na ce.

"Mama kunun tsamiya zan sha".

Tsaki Aunty Mansura ta yi tana cewa.

"Ƙaryar banza."

Ban kula ta ba, domin maganar da my Zaid yake min a kunne murmushi na yi ina kallon fuskarsa sannan na kalli Mama na ce.

"Mama my Zaid zai ta ya ni duba wani littafi a cikin ɗakina kafin mu gama don Allah kin yi min kunun tsamiyar."

Babu wanda na bawa damar magana na tashi ina kama hannunsa, bayana ya bi kamar jela har cikin ɗakina wanda yanzu ya zama na Aunty Mansura.

Ajiyar zuciya duk muka yi lokacin da muka kwanta akan gadon murmushi Muhammad Zaid ya yi tare da cewa.

"Gaskiya na yi farinciki sosai yau dai ganin ga Noor a ɗakinta da take korata."

Dariya na yi ina cewa.

"To ai yanzu ban koreka ba ko?"

Lumshe idonuwansa ya yi tare da cewa.

"Noor ɗan rufe mana ɗakin mana."

Harararsa na yi ina tashi rufe ƙofar na yi kamar yadda ya buƙata sannan na kwanta kusa da shi na ce.

"Na rufe me zaka yi ne? Ni fa dama ban gama yarda da kai ba tun da ka ce mu shigo ɗakin nan."

Rungumeni ya yi sosai yana faɗa min kalamai masu sanyaya zuciya.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol