Free chapter · Read without an account

BABI NA SHA UKU

by Maryam Usman · MATAR AURE CE

*********

A ɓangaren su Aunty Mansura kuwa tun shigar mu ɗakin suka saki baki suna mamaki.

Mama kuwa kunun tsamiyar ta fara yi min amma ita ma ta yi mamakin shiga ɗakin da muka yi har da rufe ƙofa.

Aunty Mansura kuwa hawaye ta fara tana kuka sosai cikin kukan take cewa.

"Ummah kin cuceni ni ma na cuce kaina Allah da gaske ina son prof Muhammad Zaid har zuciyata Ummah kin hana ni na yi wa Abbana biyayya ga shi na kamu da ciwon son shi, bana jin daɗin ganinsu da nake yi shi da Maryama.."

Rufe mata baki Ummah ta yi tana hawaye ita ma ta ce.

"Mansura na yi nadama sosai ban san haka Muhammad ɗin yake da kuɗi ba, na yi tunanin cuta ta Maman Fati zan ta yi a lokacin..."

Zame jikinta Aunty Mansura ta yi daga na Ummah tana sake fashewa da kuka,

Tun fara maganar Abba da Mama suke tsaye a kansu sai Khadijah da take hawaye ita ma.

A hankali Mama ta kama Aunty Mansura tana goge mata hawayen fuskata ta ce.

"Mansura ki yi haƙuri haka Allah ya tsara ke ba matar Muhammad Zaid ba ce ko da Saratu ta amince a lokacin..."

"A'a Mama na yi imani cewa da Ummah ta amince da tuni ni ce matarsa ina son shi fa, don Allah Mama ki duba lamarin na san ke mai adalci ce.."

Hawaye Mama ta fara tana cewa.

"Ki yi haƙuri Mansura babu wani abu da za mu iya yi yanzu, sai dai ki yi haƙuri Allah ya kawo miki wanda ya fi shi..."

"A'a Mama babu wanda ya fi Prof Muhammad Zaid babu shi a duniya."

Gyaran murya Abba ya yi tare da cewa.

"Ya isa bana son wannan kukan wai ba motar Muhammad Zaid na ga a ƙofar gida ba?"

Shiru duk suka yi babu mai bakin magana. Cikin ɓacin rai Abba ya ce.

"Wai ba tambayarku nake ba."

A hankali Khadijah ta ce.

"Eh Abba yana cikin ɗakin Aunty Maryama."

Kallon Ummah da Aunty Mansura ya yi yana cewa.

"Kuma shi ne kuke yi mana hauka a gida?"

********************

A ɓangarenmu kuwa cikin aminci muka sha soyayyarmu lokacin da muka fito Abba ya fita iya kunun tsamiyar na karɓa muka tafi gida babu wanda ya yi mana magana.

Kwana biyu a tsakani aka kafe Result wane lokaci ban samu zuwa ba domin bana jin daɗi, My Zaid ne da kansa ya duba min kuma Alhamdulillah! Result ya yi kyau sosai.

Sai bayan sati biyu da kafe Result ɗin na shiga Makarantar ranar Prof Kamis ne zai mana lecture, My Zaid ne ya kai ni har cikin hall ɗin, yanzu kowa ya san ni matarsa ce kuma da yawan mutane suna girmamani.

Har ya gama lecturesa bai kalleni ba,sai bayan ya fita ne Ahmad Zayyan ya shigo a lokacin na gama gajiya na kwantar da kaina, yana cikin koyarwar na ji ya kira sunana da ɗan sauri na tashi tsaye.

Cike da kulawa yake kallona cikin sanyin murya ya ce.

"Me yake faruwa Maryama? Ko kin gaji? Kina buƙata wani abu ne?"

Girgiza kaina na yi ina cewa.

"Uhm Sir dama ina so na fita ne?"

Hanyar fita ya nuna min, a hankali na fita daga hall ɗin ina sake ajiyar zuciya office ɗin My Zaid na shiga.

Ban same shi ba sai wasu ɗalibai zama na yi a kujerar da yake zama lumshe idanuwana na yi ina jin wata nutsuwa tana shigata.

A hankali bacci ya ɗauke ni, ban san ya shigo ba, kawai farkawa na yi na ganni a kwance a gado alwala na yi sannan na yi sallah.

A hankali na ji muryarsa suna magana shi da Ahmad Zayyan. Yana cewa.

"Allah Ahmad Zayyan ina tausayin Noor sosai ka ga bata da cikakkiyar lafiya ga karatunsu ya ɗauki zafi bana so ta sami matsala a wannan semester."

Dariyar Ahmad Zayyan na ji yana cewa.

"Ni ma tausayi ta ba ni ɗazu na ce ta fito amma ni a tawa shawarar kawai ta haƙura da wannan semester sai.."

"A'a Ahmad Zayyan haka ma ba za ta faru ba, in sha Allahu ka ba ni dai wata shawarar."

Dariya Ahmad Zayyan ɗin ya sake yi tare da cewa.

"Muhammad Zaid ni ban san abin da zan faɗa maka ba bayan wannan shi ne kawai mafita ta huta bayan ta haihuwa sai ta cigaba shi ne magana."

"Ai da Noor ta haƙura da wannan semester gwara ni na haƙura da nawa aikin har sai ta haihu ɗi domin na yi mata alƙawarin za ta yi karatu cikin jikinta ba zai hana ta karatu ba."

Tausayinsa ne ya kama ni, na san ina shan wahala a cikin nan amma wahalar da yake sha har tana so ta fi tawa, wani irin ƙaunarsa ce ta sake shiga zuciyata.

Shafa cikin jikina na yi wanda ya fito domin lokacin watanninsa biyar. Ina shafawa tare da cewa.

"Ina sonka sosai kuma mahaifinka ma yana ƙaunarka Allah ya albarkaceka."

Ban ji buɗe kofa ba sai maganarsa na ji yana cewa.

"Amin ya Allah Noor."

Dariya na yi ina ɓoye fuskata almar na ji kunya.

A hankali ya shigo yana zama kusa da ni ya ce.

"Yau dai na kama ki."

Hannunsa na buge daga jikina ina dariya na ce.

"To ai addu'a nake yi masa ba wani abin ba ne."

Murmushi ya yi yana tattara min kayana, tun daga ranar nake tsananta jikina, bana sakin jiki hakan da na yi ya ƙasa masa garkuwar jiki domin yanzu yafi sakewa ya yi aikinsa.

Ni ma yanzun na fi jin daɗin jikina, ko a Makaranta bana kwanciya kuma Alhamdulillah! ina cin abinci sosai.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol