Free chapter · Read without an account

BABI NA SHA HUƊU

by Maryam Usman · MATAR AURE CE

~~~~~~~~~~~~~~~~

Bayan wata biyu.

A cikin wata biyun nan abubuwan da yawa sun faru, a cikin har da saka ranar auren Khadijah da Sauban, Siyama da Nasir yaro ne ga Abokin Papa.

Aunty Mansura ta so ita ma Abba ya yi mata aure amma ya ce sai ta gama karatu, ta yi kuka har ta gaji daga ƙarshe ma har gida ta zo ta same ni.

A lokacin My Zaid ya fita, tun shigowarta na fahimci tana cikin damuwa sosai, a hankali na ce.

"Aunty Mansura don Allah ki faɗa min abin da yake damunki na san kina cikin damuwa."

Hawayen fuskata ta goge tare da kama hannuna ta ce.

"Maryama ina cikin masifa Abba ya kasa gane halin da nake ciki aure nake so shi kuma ya ce dole sai na gama karatu ni kuma gaskiya ba karatun ne a gabana ba."

Shiru na yi tsawon lokaci sannan na yi ƙarfin halin cewa.

"To amma Aunty Mansura ni a tunanina ba za ki yi haƙurin har ki gama karatun da yake so ki gama ɗin ba?"

Murmushi mai ciwo ta yi tana cewa.

"Eh za ki faɗi haka mana, ke yanzu ba Miji ne da ke ba? Yawwa ba na wannan ba me ye haka a jikinki ba ciki ba ne? To ba na fito miki a mutum ina buƙatar Namiji.."

A ɗan firgice na rufe mata baki ina cewa.

"Haba Aunty Mansura! Wannan wace irin magana ce? Don Allah kar ki sake faɗa har wani ya ji."

Shiru ta yi na ɗan lokaci sannan ta sauke ajiyar zuciya.

"Ki yi haƙuri Maryama. Wallahi ban san abin da nake faɗa ba. Damuwa ce ta yi min yawa......."

Kafin ta ƙarasa maganar ta fashe da kuka

Cikin tausayi na matso kusa da ita na rungumeta ina cewa.

"Aunty Mansura, ki kwantar da hankalinki komai yana da lokacinsa kin ga ni ma ban taɓa tsammanin rayuwata za ta koma haka ba."

Share hawayenta ta yi tana kallona cikin sanyin murya ta ce.

"Amma ke kin yi sa'a Maryama dama ni ce."

Murmushi na yi ina cewa.

"Ba sa'a ba ce Aunty. Jarabawa ce da Allah ya sauƙaƙa min. Ke ma Allah zai sauƙaƙa miki."

Mun daɗe muna hira ina ƙoƙarin kwantar mata da hankali har ta fara sakin jiki.

A dai-dai lokacin ne aka buɗe ƙofa.

My Zaid ne ya shigo.

Da ganin Aunty Mansura ya ɗan tsaya sannan ta gaishe shi cikin mutunci.

Yana kallon fuskata ya ce.

"Lafiya lau Mansura?"

Sannan ya kalli idanunta da suka yi ja saboda kuka amma bai ce komai ba.

A hankali ya ce.

"Noor kin ci abinci kuwa?"

Murmushi Aunty Mansura ta yi mai ɗaci ta ce.

"Wallahi Prof, kai dai duk duniyar nan babu abin da ya dame ka sai Maryama."

Ni kuwa kunya ce ta kama ni.

Murmushi ya yi tare da zama kusa da ni yana cewa.

"To ai ita ɗin amanata ce."

Wani irin bugawar zuciyata na ji.

Aunty Mansura kuwa ta sunkuyar da kanta.

Na fahimci maganar ta sake tayar mata da damuwar da take ciki.

Da yamma ta tafi gida bayan na rararsheta.

A ranar na kira Abba a waya na yi masa bayanin halin da Aunty Mansura take ciki, amma bai nuna damuwarsa ba sai ma tabbatar min da ya yi dole sai ta gama karatu sannan zai yi mata aure alƙawari ya yi wa kansa.

Mama na kira muka yi magana ita ma ta nuna damuwarta akan rashin amincewa da Abba ya yi a kan auren da Aunty Mansura take so.

Washegari na shiga Makaranta bayan mun gama lecture ne na kira Khadijah domin jin abubuwan da suke faruwa a gida ina son sirri ne ko My Zaid bana so ya san halin da gidanmu yake ciki shi yasa na kira Khadijah gefe inda babu mutane sosai daga ni sai ita.

A hankali na kalle Khadijah ina kama hannunta na ce.

"Khadijah wai me yake faruwa a gida ne da safe Aunty Mansura ta kira ni wai ta yi tafiya ka da na faɗawa kowa kuma ni ma bata faɗa min ina ta tafi ba...."

Khadijah tana hawaye ta ce.

"Aunty Maryama muna cikin masifa Aunty Mansura ta gudu daga gida babu wanda ya san inda take..."

Katse ta na yi ina cewa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Khadijah wacce masifa ce wannan ta gudu fa? Wayyo! Allah mun shiga uku abin da nake gudu kenan."

"Aunty Maryama wallahi tun jiya Ummah take kuka Abba kuwa bai nuna komai ba, har yanzu bai ce komai Mama har Kawu Haruna ta kira shi ma ya zo yanzu haka yana gidan."

Hawayen fuskata ta goge tare da cewa.

"Khadijah a gaskiya ni laifin Abba na ke gani a wannan lamarin tun ba yanzu ba kowa ya san Aunty Mansura aure take so shi kuma ya dage dole sai ta yi karatu..."

"A'a Aunty Maryama da laifin Aunty Mansura har na Ummah komai fa Ummah ce sanadi da a ce a lokacin da Abba ya ba da umarnin zai yi wa Aunty Mansura aure Ummah ba ta ƙi amincewa ba da duk haka ba ta faru ba."

Shiru na yi ina tunanin maganar Khadijah sannan na ce.

"Khadijah zo mu je gidan ina so yin magana da Abba."

Goge fuskata na yi ina gogewa Khadijah hawayen fuskarta sannan na kama hannunta, office ɗin Prof Muhammad Zaid muka fara zuwa bayanan office ɗin a rufe wayarsa na kira bai ɗaga ba.

Mun ɗan jima a tsaye sannan muka fara leƙa hall ɗin da suke kusa, hall uku muka leƙa a na huɗu muka same shi a ciki.

A hankali na shiga bakin da sallama, kallona aka fara yi idonuwansa ya zubo min yana kallona sannan a nufo inda nake tsaye.

Hannuna ya kama a hankali ya ce.

"Lafiya Noor kuka kika yi wane abu ya faru ne?"

Hannunsa na cire daga nawa ina fita daga hall ɗin, bayana ya biyo yana cewa.

"Wai lafiya Noor ko wani abu yana yi miki ciwo ne?"

Kwatar da murya na yi na ce.

"My Zaid gidanmu nake so zuwa za mu tafi da Khadijah in ka gama sai mu haɗu a can?"

Murmushi ya yi yana kallon fuskata ya ce.

"Noor lafiya kike son zuwa gida yanzu? Kuma na ga fuskarki ta sauya almar kin yi kuka ko Abba ne ba shi da lafiya?"

Dole ce tasa ni yin murmushi na ce.

"My Zaid irin wannan tambayar ni kawai son zuwa gidan nake yi don Allah ka da ka ce a'a."

Agogon hannunsa ya duba sannan ya ce.

"Shi kenan Noor sai na zo ɗin."

Hannunsa na kama ina yi masa kiss sannan na ɗan rungumeshi ina raɗa masa magana.

Murmushi ya yi yana koma wa hall ɗin hannun Khadijah na kama muka tafi.

*******************

Lokacin da muka shiga gidan kamar an yi mutuwa Mama da Ummah ne zaune sai Abba da Kawu Haruna da suke tsaye.

Duk wanda ka kalla a cikinsu kasan suna cikin damuwa sosai a hankali na ƙarasa ina zama kusa da su Mama na ce.

"Abba Kawu Haruna wai me yake faruwa ne? Aunty Mansura ta kira tana..."

Ɗaga min hannun Abba ya yi tare da nuna min hanyar fita, Kawu Haruna ne ya ce.

"Uwata ba ma son maganar Mansura a cikin gidan nan."

Fashewa da kuka Ummah ta yi tana cewa.

"Uwar masu gida kin ji abin da suka ce wai kada na sake maganar Mansura don Allah ki ta ya ni basu haƙuri...."

"Ya isa Saratu duk waye ya ja mana wannan matsalar, tun da ta zaɓi bin duniya to ga duniyar nan wanda bai zo ba ma zai sameta balle wanda yake ciki."

Kallon Kawu Haruna na yi jin irin abin da ya fara hawaye ne ya zubo min rasa abin da zan ce, da sauri na ɗaga wayata na kira number da Aunty Mansura ta kira ni.

Kiran duniya bata tafiya,

Cikin tashin hankali na sake danna lambar Aunty Mansura amma har yanzu ba ta shiga.

Wayar na sauke a hankali zuciyata na bugawa da ƙarfi a hankali na ce.

"Abba don Allah ku yi haƙuri. Aunty Mansura ta yi laifi amma don Allah a madadinta ina mai baku haƙuri."

Kafin Abba ya yi magana sai muka ji ƙarar mota a waje.Khadijah ce ta miƙe tana leƙawa domin ganin waye.

Jiki a sanyaye ta dawo ta ce.

"Prof Muhammad Zaid ne zai shigo."

Shiru ne ya mamaye falon, ba jimawa kuwa ya shigo cikin nutsuwarsa ya gaishe da su Abba.

Amsawa duk suka yi amma babu walwala a tare da su.

Ya zauna a kusa da ni yana kallon fuskata da ɗan firgice ya ce.

"Noor lafiya? Wai me yake faruwa ne kike kuka tun ɗazu?"

Ban iya magana ba sai girgiza kaina da na yi.

Ummah ce ta share hawayen fuskata ta ce.

"Mansura ce ta bar gida."

Idanuwansa ya ɗan buɗe cikin mamaki ya ce.

"Ta bar gida kuma?"

Kawu Haruna ne ya amsa da cewa.

"Eh. Tun jiya babu wanda ya san inda take."

Shiru Prof Muhammad Zaid ya yi na ɗan lokaci sannan ya ce.

"An kira wayarta?"

"Ba ta shiga." Abba ya amsa a taƙaice.

Duk kallon fuskar Abba muka yi tun fara maganar bai ce komai sai yanzu.

Muhammad Zaid ne ya ɗan gyara zamansa yana kallon fuskar Abba ya ce.

"In sha Allah za a same ta. Amma ya kamata mu fara bincike cikin hankali ba cikin fushi ba.Ina so a bani number Ƙawayenta da number wayarta zan saka wani ya bincika mana ita."

Abba bai ce komai ba.

Amma na lura maganar ta shige shi, Ummah da Mama ma sun ji daɗi Kawu Haruna kuwa har da godiya yake yi masa.

Har muka tafi gida Kawu Haruna yana yi wa Muhammad Zaid godiya.

~~~~~~~~~~~~~~

Tun dawowarmu nake hawaye abinci ma kaɗan na ci.

Da da dare kuwa ban samu bacci ba.

Ina kwance a ɗaki ina ta tunanin Aunty Mansura hawaye na zubo min.

A hankali My Zaid ya kamo hannuna tare da kwantar da murya ya ce

"Noor."

"Na'am."

Na amsa da muryata wacce ba ta fita sosai.

Hannuna yake shafawa tare da cewa

"Ki daina kuka haka Noor har zuciyata nake jin wannan kukan naki."

A hankali na goge hawayen fuskata ina cewa.

"My Zaid ina tsoron kada wani abu ya same ta."

Kaina ya shafa cikin lallashi ya ce.

"Allah na tare da ita."

Sai da ya sama min natsuwa sannan bacci ya ɗaukemu.

Washegari da sassafe muje gidanmu.

A zaune muka samu Mama da Ummah wacce idanunta suka kumbura saboda kuka kowa ya ga Ummah sai ta bashi tausayi.

My Zaid ne ya gaida su sannan ya sake kwantar musu da hankali Abba ne ya fito daga ɗakinsa suka gaisa da shi.

Shiru duk muka yi kowa yana tunanin wani abu.

Kwatsam sai wayar Mama ta yi ƙara, tana dubawa jikinta ya fara rawa tana cewa.

"Mansura ce Allah Mansura ce."

Karɓar wayar Abba ya yi zai ɗagawa my Zaid ya yi saurin cewa" A'a Abba ka da ka yi magana da ita."

Mama ce ta karɓi wayar tana cewa.

"Mansura!"

Kowa ya miƙe tsaye lokaci guda muna kallon fuskar Mama.

"Ki ina ne? Mansura kina ina? Mansura ki faɗa min zan zo na same ki."

Mama ta tambayar cikin kuka, mu kuwa mun yi shiru muna sauraro.

Bayan wasu daƙiƙu Mama ta fashe da kuka, tana sauke wayar.

Da sauri na kama hannunta na ce.

"Mama me ta ce?"

Mama tana kuka ta ce.

"Ta ce tana lafiya... amma kada mu neme ta."

"Innalillahi!"

Ummah ta faɗi tana riƙe ƙirjinta.

Abba kuwa miƙewa tsaye ya yi da sauri yana cewa

"Ta faɗi inda take ne?"

"A'a."

Mama ta amsa tana kuka.

"Ta ce idan lokaci ya yi za ta dawo."

Falon ne ya sake yin shiru, wayar My Zaid ce ta katse mana shirun.

Da ɗan sauri ya ɗaga yana cewa.

"Assalamu alaikum Yakubu ka samu daga inda ta yi wayar?"

Kallon fuskarsa duk muka yi domin jin abin da yake faɗa.

Murmushi ya yi tare da cewa.

"Okay good ya yi kyau zan zo yanzu amma a kama shi."

Wayar ya kashe yana kallon fuskar Abba ya ce.

"Abba na sa an bibiyi SIM card ɗin ta yanzu haka an sami inda take."

Kukan farinciki ne ya kama Ummah ni ma kaina kukan nake, a hankali ya tashi zai fita na yi saurin cewa.

"My Zaid zan bika."

Murmushi ya yi min yana shafa fuskata ya ce.

"Yanzu Noor a haka za ki fita, cikinki fa ya yi gimman da za ki haƙura da fita."

Wayarsa aka sake kira ya yi saurin fita

Prof Muhammad Zaid yana fita daga falon, kowa ya bi shi da kallo.

Zuciyata kuwa ta kasa nutsuwa a hankali na ce.

"Abba don Allah ku bar ni na je tare da shi."

Da sauri Abba ya girgiza kai ya ce.

"A'a Uwata ba inda za ki je da wannan cikin."

Ummah ce ta goge hawayan fuskarta ta ce.

"Haba Uwar masu gida! Kina son kashe mana kanki ne?"

Hawaye ne suka cika min idanuna ban san dalili ba amma zuciyata ta kasa samun nutsuwa sai bugawa take kamar za ta fito.

Ina jin kamar Aunty Mansura tana cikin wata matsala.Khadijah ma kuka take yi.

Mama kuwa addu'a take yi tana cewa

"Ya Allah ka dawo mana da Mansura lafiya."

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol