Free chapter · Read without an account

BABI NA SHA BIYAR

by Maryam Usman · MATAR AURE CE

~~~~~~~~~~~~~~~~~

A ɓangaren Muhammad Zaid kuwa...

Kai tsaye ya nufi inda mutanensa suka ce an gano wayar.

A wani ƙaramin gari ne da ke bayan gari kaɗan.

Yana isa ya tarar da wani saurayi da aka kama.

Saurayin yana ta rawar jiki

Muhammad Zaid ne ya zauna yana kallonsa cikin nutsuwa ya ce.

"Ka faɗa min gaskiya."

Saurayin ya sunkuyar da kai ya ce.

"Wallahi ni ban san komai ba."

Haɗe fuska Muhammad Zaid ya yi tare da cewa

"To ta yaya wayarta ta kasance a hannunka?"

Shiru ya yi tare da fashewa da kuka ya ce.

"Ni direba ne wata mata ce ta bani wayar ta ce idan wani ya kira kada na ɗaga."

Da sauri Muhammad Zaid ya miƙe tsaye ya ce.

"Wannan mata ce?"

Hoton Mansura aka nuna masa.

Da sauri saurayin ya ce.

"Ita ce."

Muhammad Zaid ya ce.

"Ina ta sauka?"

Saurayin ya nuna masa wata hanyar ya ce.

"Nan na sauke ta."

A ɓangarenmu kuwa

Muna gida zaune cikin tashin hankali.

Wayar Muhammad Zaid na kira amma bai ɗaga ba.

Hakan ya ƙara tada min hankali.

A hankali na dafa cikina.

Na ce.

"Ya Allah ka tsare min my Zaid."

Sai kawai na ji motsin jaririn cikina.

Murmushi ne ya ɗan suɓuce min duk da damuwar da nake ciki.

Har yamma muna zaune shiru

Wayar Abba ce ta yi ƙara da sauri ya ɗaga.

Fuskarsa muka ga ta sauya yana cewa.

"Me ka ce?"

Ya tambaya cikin sauri sai ya yi shiru yana sauraro can kuma ya ce.

"To muna zuwa yanzu."

Wayar ya kashe yana kallonmu .

Ummah ce ta ce.

"Me ya faru?"

Yawu ya haɗiye sannan ya ce

"An same ta."

"Alhamdulillah!"

Muka faɗa gabaɗaya muna murmushi.

Sai dai...

Abba bai yi murmushin ba sai ma damuwa ƙarara a fuskarsa.

Hakan ya sa zuciyata ta ɗan buga a hankali na ce.

"Abba lafiya dai?"

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon fuskata ya ce.

"Eh tana lafiya."

"To me ya sa baka yi farinciki ba?"

Na faɗa ina dafa cikina da yake juya min.

Shiru ya yi yana sake gyara zaman shi.

Kawu Haruna ne ya ce.

"Faɗa mana abin da yake faruwa Ahmad."

A hankali Abba ya ce.

"Ba ita kaɗai aka samu ba..."

Kowa ya tsayawa cak ya yi muna kallon fuskar Abba.

Rufe idanunsa Abba ya yi sannan ya ce.

"An same ta tare da wani mutum."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"

Ummah ta faɗi tana riƙe ƙirjinta.

Mama kuwa a ƙasa ta zauna tana hawaye Khadijah ma kuka ta fara.

Maganar Abba na ji kamar tsawa sake maimaitawa na yi

"An same ta tare da wani mutum."

Shiru muka yi na wasu daƙiƙu kowa yana jiran jin cikakken bayani.

A hankali ƙofar falon ta buɗe.

Prof Muhammad Zaid ne ya shigo

Fuskarsa sun nuna alamar akwai wani babban al'amari.

Da sauri Ummah ta miƙe tsaye tana cewa.

"Muhammad! Ina Mansura?"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.

"Tana lafiya Alhamdulillah."

Numfashi muka sauke gabaɗaya.

Sai dai bai yi kama da wanda yake son ƙara magana ba.

Abba ne cikin ƙarfi ya ce.

"Muhammad Zaid ka faɗa mana abin da yake faruwa."

Shiru ya yi na ɗan lokaci.

Sannan ya ce.

"Mansura ta yi aure."

Kamar an jefa bam a cikin falon haka muka ji.

"Meye?!"

Mama, Ummah da Khadijah suka faɗa lokaci guda.

Hawaye ne suka cika idanun Ummah ta ce

"Aure? Mansura ta yi aure?"

Muhammad Zaid ya girgiza kansa yana cewa.

"Eh."

Abba ne ya miƙe tsaye cikin firgici da damuwa ya ce

"Ta yi aure ban da masaniya ina mahaifinta?"

Nan take fuskarsa ta sake sauyawa numfashinsa ya fara yin nauyi.

Kawu Haruna ne ya yi saurin riƙe shi tare da cewa

"Ahmad lafiya?"

Hannunsa Abba ya kai ƙirjinsa.

Cikin wata irin murya ya ce.

"Ta... ta yi aure fa....."

Kafin ya ƙarasa maganar kawai ya faɗi ƙasa.

"Abba Abba Abba bba!!!"

Ni da Khadijah muke kiransa.

**************

Asibiti aka garzaya da shi.

Likitoci suka tabbatar cewa tashin hankalin da ya shiga ne ya tayar masa da hawan jini.

Ummah sai kuka take yi kamar ranta zai fita, Mama ma idanunta sun kumbura.

Ni kuwa ina zaune ina jin jikina yana ƙara nauyi kaina na ƙara ciwo kamar zai faɗi.

Muhammad Zaid bai bar gefena ba duk halin da ake ciki.

A hankali ya ce.

"Noor don Allah ki daina kukan nan ba'a so mace mai ciki ta shiga damuwa irin haka fa."

Kaina na kwantar a kafaɗasa ina sake ajiyar zuciya zuwan su Papa ne yasa na tashi zaune.

*********

Kwana uku Abba yana kwance a asibiti.

A rana ta huɗu aka dawo da shi gida.

Ba ya magana da kowa ba ko sunan Mansura idan aka ambata sai ya juya kansa.

A wannan lokacin ne aka muka samu labarin cewa Mansura tana son zuwa ta ga jikin Abba.

Amma Abba ya hana da an yi maganar zan ce.

"Kar ta zo."

Kalmar da yake faɗa kenan.

Ummah ta yi kuka sosai kowa yana tausaya mata sosai.

Mansura ma ta yi kuka a waya.

Amma Abba ya ƙi yafe mata ya ƙi sauraranta.

*************

A wannan daren ne muna kwance

Na farka cikin matsanancin ciwo.

"My Zaid..."

Na kira a raunane.

Da sauri ya tashi.

"Noor lafiya?"

Hawaye ne suka zubo min ina ciza baki na ce.

"Ciwon mara..."

Riga ya saka min shi ma ya shirya ya fita da sauri ya kira Ammyy da sauri aka tafi da ni asibiti.

Tun da daren da ke fama har safiya, wai jinina ne ya hau, kuma ga na fara naƙuda lokacin haihuwar bai yi ba.

Tun da asuba Siyama ta kira Khadijah, kafin ƙarfe bakwai su Mama da Ummah da Khadijah sun zo asibitin.

Muhammad Zaid kuwa tun bayan dawowarsa daga masallaci yake addu'a.

A ɗakin haihuwa kuwa

Ciwo ya yi tsanani sosai na rasa ƙarfin jikina Likitoci suna ta ƙoƙarin taimaka min.

Muhammad Zaid kuwa yana waje yana kai kawo bai taɓa shiga irin wannan tashin hankali ba.

Mama tana karanta Al-Qur'ani da duk wata addu'ar da ta zo bakinta.

Ummah kuwa addu'a kawai take yi. Haka ma Ammyy.

Bayan sa'o'i masu tsawo,

Na ji kukan jariri alama kenan na haihuwa.

Gyara shi suka yi tare da fita da shi zuwa wajen su Mama duk tashi suka yi ganin jaririn.

"Allahu Akbar!"

Mama ta faɗa tana kuka.

An haifi kyakkyawan yaro.

Likitoci suka faɗa suna murmushi

Muhammad Zaid ne ya karɓe shi hannunsa na rawa.

Hawaye ne suka gangaro masa.

Ya kalli ɗansa sannan ya ce.

"Alhamdulillah! Wannan nawa Allah na gode maka.."

Ahmad Zayyan ne ya karɓi yaro yana dariya ya ce.

"Alhamdulillah! Me aka samu?"

Likitan ce ta ce.

"Namiji ne."

Dariya duk suka yi sannan Muhammad Zaid ya ce.

"Ina mahaifiyar yaron da fatan tana lafiya?"

Likitar ce ta ya yi shiru sannan ta ce.

"Mun samu nasarar ceton jaririn..."

Fuskarsa cike da damuwa Muhammad Zaid ya ce.

"Lafiya dai? To ita fa?"

Likitar ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

"Ita tana cikin mawuyacin hali yanzu. Ku yi mata addu'a jininta ne ya hawan sosai"

Kamar an zuba masa ruwan sanyi a kai haka Prof Muhammad Zaid ya tsaya cak yana kallon likitar.

"Kamar ya?" Ya sake tambaya cikin rawar murya.

Likitar ta girgiza kai a hankali ta ce.

"Muna iya bakin ƙoƙarinmu. Amma yanayin nata ya yi tsanani sosai. Ku dage da addu'a."

Nan take murmushin da ke fuskarsa ya ɓace.

Yaron da yake riƙe da shi ya miƙa wa Ahmad Zayyan, sannan ya juya ya nufi ƙofar ɗakin da aka kwantar da ni.

Mama ta fara kuka tana cewa.

"Ya Allah ka ceci yarinyar nan ya Allah kada ka raba yaron nan da mahaifiyarsa."

Ummah ma ta fashe da kuka tana cewa.

"Ya Allah ka ba ta lafiya."

Ammyy kuwa ta zauna tana jan tasbihi.

Muhammad Zaid ne a tsaye jikin ƙofar ɗakin da nake kwance.

Ya jingina goshinsa da bango yana runtse idanunsa.

A rayuwarsa bai taɓa jin tsoro irin wannan ba.

A hankali ya ɗaga hannayensa sama ya ce.

"Ya Allah..."

Muryarsa ta karye cikin rauni ya sake cewa

"Ya Allah idan akwai wani kuskure da na yi ka yafe min ka bar min Noor ya Allah."

Hawayen da ya daɗe bai yi ba suka gangaro masa.

"Ya Allah ba zan iya rayuwa babu ita ba."

A cikin ɗakin da nake kwance kuwa...

Numfashina yana fita da ƙyar.

Na ji kamar ina cikin wani duhu mai zurfi.

Sai dai can nesa nake jin wasu muryoyi kamar ta Mama kuma kamar ta

Ummah.

Sai kuma muryar Muhammad Zaid da nake ji kamar sarewa a hankali na buɗe idanuna.

Abu na farko da na gani shi ne farin hasken ɗakin.

Likita ce ta lura na motsa.

Da sauri ta ce

"Doctor! Ta fara dawowa!"

Likitocin ne suka yi saurin taruwa a kaina

Na yi ƙoƙarin yin magana amma ban iya ba.

A hankali na lumshe idanuna sannan na sake buɗewa.

"Ina abin da na haifa ?..."

Na faɗa da ƙyar.

Likitar ta yi murmushi tana cewa

"Yaronki yana lafiya."

Hawaye ne suka zubo min a zuciyata na ce

"Alhamdulillah..."

A ɓangarensu Mama kuwa

Likita na fitowa

Duk suka miƙe tsaye lokaci guda.

Muhammad Zaid ne ya yi saurin cewa

"Doctor?"

Likitan ya yi murmushi tare da dafa kafaɗarsa ya ce.

"Alhamdulillah."

Shiru ya ne mamaye wajen suna kallon juna

Murmushi ya sake yi sannan ya ce.

"Ta fara farfaɗowa."

"Allahu Akbar!"

Mama ta faɗa cikin kuka.

Ummah ma ta durƙusa tana godiya ga Allah.

Muhammad Zaid kuwa ya rufe idanunsa.

Wani irin nauyi ne ya sauka daga zuciyarsa.

Ya yi sujadar godiya ga Allah.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol