Free chapter · Read without an account

BABI NA SHA SHIDA

by Maryam Usman · MATAR AURE CE

*****************

Bayan wasu sa'o'i...

Aka ba shi damar shiga wajena.

A hankali ya shigo.

Idanunsa sun yi ja saboda kuka da rashin barci kamar tare da shi muka haihuwa.

Da ƙyar na yi murmushi tare da cewa.

"My Zaid..."

Da sauri ya kamo hannuna bakinsa na rawa ya ce.

"Noor..."

Muryarsa ta nuna irin tashin hankalin da ya shiga.

Ɗan gyara kwanciya ta yi ina murmushi na ce.

"Ka ga ɗanmu?"

Dariya ya yi tare da goge hawayen fuskarsa ya ce.

"Na gani."

Lumshe idanuwana na yi ina mai jin farinciki na ce.

"Yana da kyau kamar ka?"

"Kyau ma ya wuce kyau Noor ai da ke yake kama"

Duk da ciwon da nake ji sai da yi murmushi

Bayan hannuna ya sumbata cikin tausayawa ya ce.

"Kin tsorata ni Noor."

A hankali na ce.

"Yi haƙuri."

Kai ya girgiza ya ce.

"Ni ne zan ce ki yi haƙuri."

Yaron Ammyy ta shigo da shi yana kuka, sannu da jiki ta yi min tana nuna min yadda zan shayar da yaron.

Muhammad Zaid ne ya fita su Mama duk suka shigo kowa yana yi min ya jiki.

A'isha ce ƙarshen zuwa ko Aunty Fati da ba a gari take ba ta rigata zuwa, tare muka zauna har dare Abba ma ya zo ganin yaro.

Ahmad Zayyan kuwa har ya fi My Zaid ɗin rawar ƙafa a kan yaron, duk lokacin da ya shigo asibitin to yana hannunsa har ya fita sai dai in kuka ya yi.

Sosai ake ba mu kulawa ni da yaron babu mai cewa lokacin haihuwar bai yi ba aka haifa saboda kulawar da muke samu, washegarin da haihuwa na kira Samiha da Hafsat.

A ranar kuwa suka zo asibitin sun yi wa yaro hotunan sosai ni dai ina gefe ban ce komai ba, a group na Department ɗinmu Hafsat ta ɗora.

Tana ɗora wa aka fara kiranta domin jin labarin ina kwance ita da Samiha sai fama suke da kira, kafin yamma kowa ya san na haihuwa.

Yawo aka fara yin da hotunan jariri tare da sunana da na Prof Muhammad Zaid wanda ban sani ba ma a ranar ya ga abin da na haifa.

****************

Bayan kwana biyu ..

Aka sallame mu daga asibiti domin jikina ya yi sauƙi shi ma yaron haka.

Murna ta cika gida saboda dawowata da jariri lafiya Ammyy ta rasa inda za ta saka ni da yaron.

A ɓangaren ƴan gidanmu kuwa

har yanzu akwai wata damuwa da ke cikin zuciyarmu maganar Mansura.

Tun lokacin da ta gudu ta yi auren nan ba ta sake zuwa gidan ba.

Abba ma bai canza ra'ayinsa ba.

Ko sunanta idan an ambata fuskarsa sai ta sauya.

Wata rana da yamma Mama ta zo duba ni, dama Ummah tare muke kwana.

Ina zaune ina shayar da jariri wayar Ummah ta yi ƙara.

Tana dubawa sai ta fara hawaye.

Mama ce ta kalleta ta ce.

"Waye?"

Ummah tana share hawaye ta ce.

"Mansura ce."

Nan take falon ya yi shiru.

A hankali Ummah ta ɗaga wayar tana cewa.

"Mansura..."

Sai kuma ta yi shiru tana sauraro.

Ba zato ba tsammani fuskarta ta canza.

"Meye kika ce?!"

Ta faɗa cikin firgici duk muka miƙe tsaye.

Hannunta yana rawa ta ce.

"Mansura me ya same ki?"

Wayar ta zame daga hannunta ta faɗi ƙasa.

Mama ta yi saurin kama ta.

"Me ya faru?"

Ummah ta fashe da kuka.

Tana kallonmu ta ce.

"Mansura tana asibiti..."

"Meye ya same ta?"

Na tambaya cikin tashin hankali.

Ummah ta girgiza kai hawaye na zubo wa daga idanunta ta ce.

"Wai bata da lafiya..."

Kwantar wa da Ummah hankali muka yi, sai bayan Khadijah ta dawo daga Makaranta ne aka tura ta domin ta gano Aunty Mansura lokacin da ta je sun koma gida ba ta same su ba.

Yamma na yi duk suka tafi gida har Ummah ni ɗaya aka bari sai Ammyy da ta shigo.

Ana sallar magriba My Zaid ya dawo shi da Ahmad Zayyan lokacin Ammyy ta yi wa yaro wanka ta shirya shi cikin kayan sanyi, ni ma na yi wanka har abinci na ci.

Hijabi na saka ina gaida Ahmad Zayyan da ya ɗauki yaron yana murmushi.

My Zaid na kalla ina lumshe idona a hankali na ce.

"Barka da shigowa My Zaid."

Ban ankara ba na ji ya rungumeni sosai a jikinsa da sauri na zame jikina ina harararsa.

Ahmad Zayyan ya kalla ya ga wasa yake yi da jaririn ya ce.

"Ahmad Zayyan za mu shiga ciki ka yi wa mai sunan naka huɗuba ka ga jibi suna."

Baki na saki ina kallon rashin kunya irin ta My Zaid to in dan mun shiga cikin me za mu yi, ina wannan tunanin na ji ya yi sama da ni, baki na buɗe zan yi ihu ya rufe min da hannunsa ɗaya.

Ni dai na sha kunya iya kunya a ranar ai tun da muka shiga ɗakin ban iya fitowa ba yin sallama da Ahmad Zayyan ɗin ba.

Sai bayan ya tafi ne na samu damar fitowa, Ammyy ce ta shigo a lokacin goma na dare.

Da sauri My Zaid ya tashi domin ya saka riga ina dariya ya shiga ɗakin lokacin da ya dawo muna magana da Ammyy.

Fuskarsa a hade ya zauna yana gaida ita ko kallonsa ba ta yi ba ta ce.

"Kai ba zaka kwana ba ne?"

Sosa kansa ya yi tare da cewa.

"Uhm ai yanzu muke son kwanciyar ko Noor Zayyan ɗin ne ba yi bacci ba sai yanzu."

Rufe fuskata na yi ina dariya na fahimci My Zaid ba san inda maganar Ammyy ta dosa ba.

Tsaki Ammyy ta yi tana cewa.

"Okay ka tafi ka kwanta na zo dama aikin Papa ne ban gama ba."

Baki ya buɗe yana kallo Ammyy alamar tambaya ni kuwa ina gefe sai dariya nake yi na san tun da Ummah ta tafi za'a samu matsala.

Ummah babu ruwanta rabuwa take da mu ta yi kwanciyarta a ɗakinta, babu wanda ya san muna kwana ɗaki ɗaya da My Zaid.

A hankali ya buɗe baki ya ce.

"Ammyy a nan za ki kwana? Wani abu ne ya faru a can ɓangaren naku? Ko..."

Hannun Ammyy ta ɗaga masa ta ce.

"Kai bana son shirme ba Saratu ta tafi ba to ni ce me kula da Maryama."

Murmushi ya yi tare da sosa kansa ya ce.

"To Ammyy ai ga ɗakin Ummah ce a can take kwana.."

"Kai ni ban ce a ɗakinka zan kwana ba, ni da Maryama ɗin zan tafi, Allah ya rufa min asiri na kawana a ɓangarenka."

Ido ya zaro yana zama kusa da ita ya ce.

"Ammyy ban fahimta ba? to akan wane dalili za ki tafi da ita ni kuma da wa zan kwana indan kika ɗauket...."

Tashi Ammyy ta yi tana ɗaukar Ahmad Zayyan ta ce.

"Da Ubanka wai kai har yanzu ba zaka yi hankali ba, ke Maryama tashi mu tafi kafin na mare shi."

Tashi na yi ina kunshi dariyata na saka hijabi ina bin bayanta, har muka saka ƙasa Muhammad Zaid yana tsaye ya kasa magana.

Ban san ta ya aka My Zaid ya yi bacci ba a ranar ni dai kam na yi bacci sosai domin Ammyy take kula da yaron in dan ya tashi, saɓanin lokacin da muke kwana da My Zaid sai dai duk mu tashi muna rasa abin da za mu yi masa.

Tun daga ranar muke kwana a ɗakina Ammyy sosai take kula da mu.

Ranar suna yaro ya ci sunan mahaifinsa wato Ahmad Zayyan, idan na ce zan faɗa muku abin da Ahmad Zayyan ya yi zan ɓata lokacin ne, amma maganar gaskiya ya yi ƙoƙari sosai.

Duk wanda ya zo gidan sunan nan ya san nera ta yi kuka, da yawwan ɗaliban Makarantarmu sun zo wanda na sani da wanda ban sani ba.

Ranar dai na ga gata sosai Papa ya yi ƙoƙari sosai domin kayan da ya yi mana ni da jariri ba za su lissafu ba.

Bayan an gama bikin suna ne yan gidanmu suka ya yaba wa Ahmad Zayyan da irin abin da ya yi.

Muhammad Zaid kuwa tun daga wannan rana ya ƙara manne ɗansa.

Duk da yawan aikinsa a jami'a, da zarar ya dawo gida abin farko da yake nema shi ne Ahmad Zayyan.

Tun Ammyy na korarsa har ta haƙura, shi ma tun yana jin haushin riƙemu da Ammyy ta yi har ya kwantar da murya.

*****************

Bayan wata uku.

Lokacin mun yi kyau sosai ni da Ahmad Zayyan tun bayan arba'in na koma ɗakina amma sai da na zaga dangina.

Ina arba'in aka fara exam, Muhammad Zaid ne ya ke kula da Zayyan ni kuma nake karatu.

Muna zuwa Makaranta kuwa to kulawarsa ta koma hannun Ahmad Zayyan cikin nufin Allah kuwa Zayyan baya kuka indan yana hanuna Ahmad Zayyan.

Har muka gama exam shi ne yake kula da shi, yanzu har ya fara gane shi, da ya ji muryarsa zai fara ɗaga hannu.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol