Free chapter · Read without an account
BABI NA SHA TAKWAS
**************
Bayan kwana biyu.
Shi komai ya wuce a ɓangarensa amma ni na kasa mantawa.
Ina kwance ina karanta wani littafi.
Muhammad Zaid ya shigo hannunsa da ɗan ƙaramin kwalin mai kyau ajiye shi ya yi a gabana.
Ajiye littafin hannuna na yi na kalle shi na ce.
"Wannan fa?"
Murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce
"Buɗe."
A hankali na buɗe.
Agogo ne mai kyau sosaia ciki.
Ido na ɗaga ina kalle shi.
Murmushi ya yi tare da shafa kansa ya ce.
"Kyauta ce."
Ban san lokacin da na yi murmushi ba na ce.
"Amma gaskiya My Zaid ya yi kyau sosai Allah yasa ka da alkhairi."
"Kin yafe min ba zan sake ba?"
Shiru na yi na ɗan lokaci sannan na yi dariya na ce.
"Da sharadi."
Kafin na ce wani abu ya ce.
"Na yi alkawari ba zan sake barinki a mota ba."
"Shi kenan komai ya wuce na haƙura."
Tun daga ranar ba mu sake faɗa ba.
*****************
Bayan wata uku.
Abubuwan da yawa sun faru, ciki har da auren su Khadijah da Siyama wata biyu kenan da yi.
A ɓangaren Aunty Mansura kuma sai dai muce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Komai ya lalace Mijin da ta aure ɗin ya yi mata shegen duka har da kwanciya a gadon asibiti.
Kowa ya shiga damuwa sosai, ana cikin wannan yanayin ne ciki ya fito a jikinta Ummah ta yi kuka har ta gaji Abba ma sai da ya yi kuka ganin irin masifun da Aunty Mansura take shiga.
Duk muna asibitin zaman jinyarta ashe Mijin nata ya aiko da takardar saki har gida, mun ga rashin mutunci sosai a wajen mutumin nan.
Aunty Mansura ta yi kuka ta yi nadamar abin da ta aikata, sosai muke tausayin halin da take ciki My Zaid ya so ya yi magana da Mijin nata amma Abba ya ce.
"Duk tsutsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka."
Papa ma cewa ya yi a rabu da shi, dole sai haƙura aka yi, zaman gidan dai da Aunty Mansura ba ta so shi ta dawo.
***************
A ɓangarena kuwa yau muke Exam ta ƙarshe a Makaranta, ina cikin farinciki sosai.
Lokacin da muka fito daga Exam a gaban hall na tsaya ina kallon tsakiyar harabar Makaranta na yi shiru.
Shekarun da suka shuɗe suka fara dawo min a zuciya kamar a fim.
Ranar farko da na shigo wannan Makaranta... Ranar da na fara haɗuwa da Prof Muhammad Zaid... Ranar da na fara jin tsoron sa... Ranar da na fara sonsa ba tare da na sani ba... Ranar da na gano shi ne mijina...
Hawayen farin ciki ne suka zubo min.
"Alhamdulillah."
Na furta a hankali.
Samiha ce ta rungume ni ta ce.
"Maryama mun yi nasara."
Murmushi na yi kafin na yi magana
Hafsat ta yi dariya tana cewa.
"Yanzu fa Madam Professor Muhammad Zaid ta gama karatu."
Dariya duk muka yi muna ɗaukar hotunan tare kowa yana ta murna.
Na san wannan ranar ba za ta taɓa gogewa daga ƙwaƙwalwata ba.
Muhammad Zaid na hango a tsaye yana kallon fuskata.Yana jingine da motarsa.
hannunsa kuma yana ɗauke da Zayyan.
Yana hango ni sai ya ɗaga Zayyan sama ya ce.
"Ga Mummy."
Da gudu Zayyan ya miƙo hannayensa gare ni na karɓe shi ina sumbatar goshinsa.
Muhammad Zaid ne ya matso kusa da ni cikin wata sansanyar murya ya ce.
"Congratulations Mrs. Muhammad Zaid."
Murmushi na yi tare da cewa.
"Thank you My Zaid."
Hannunsa ya saka a aljihunsa ya ciro wani farin envelope ya miƙo min yana murmushi.
Na buɗewa na yi na fara karatawa.
"Ina alfahari da ke Noor. Kin zama matar kirki, uwa ta gari kuma ɗaliba mai jajircewa. Allah Ya ƙara ɗaukaka ki a duniya da lahira."
Kafin na ɗago kaina...
Na ji ya riƙe hannuna.
"Na gode da komai."
Kai na girgiza
"A'a... Ni ce zan gode maka."
Lumshe idonuwansa ya yi yana cewa.
"Saboda?"
" Da ba ka riƙe hannuna ba... Da ban kai nan ba."
"Mun riƙe hannun juna ne."
*****************
Da yamma aka shirya ƙaramin taro a cikin wani hall na makarantar.
Abba... Ummah... Mama... Papa... Ammyy... Siyama... Khadijah... Samiha... Hafsat... Prof Ahmad Zayyan... Sauban...
Har wasu daga cikin daliban kowa yana cikin farinciki.
Abba ne ya ɗaga hannu sama ya ce.
"Alhamdulillah! Allah ya nuna mana wannan rana Uwata ta gama karatu."
Ummah kuwa kuka fashe da shi tana rungume ni cikin kuka ta ce
"Uwar masu gida... Allah Ya saka miki da aljannah saboda irin haƙurin da kika yi da biyayyar da kike wa iyayenki."
Aunty Mansura ce ta zauna a gabana tana kallon fuskata idanuwanta cike da nadama ta ce.
"Maryama."
"Na'am Aunty Mansura."
"Ki yafe min."
Hannayenta na kama ina hawaye na ce.
"Aunty... Tun tuni na yafe miki."
Ta fashe da kuka tana cewa.
"Na rasa komai saboda son zuciya."
Rungume ta na yi ina cewa.
"A'a kin dawo wajen iyalanki Allah yana karɓar tuban bayinsa na san Abba ya jima da yafe miki."
Abba ne ya buɗe baki ya ce.
"Na yafe miki Mansura tun ba yau ba,
Ni ma na yi kuskure da na kasa gane abin da kike so, na yi nadamar abin da na yi ki yi haƙuri ki yafe min na shiga hakkinki ba haka ya kamata mahaifin ya kasance ba......."
Hannun Abba na kama ina cewa.
"Abba komai ya wuce Aunty Mansura ta yi laifi, kuma kai ma ka taka rawar gani wajen laifin nata sai dai mu ce Allah ya shirya yan baya komai ya wuce Allah yasa iyaye su gane abin da ya'yansu suke buƙata."
"Amin ya Allah Uwata."
Muhammad Zaid na kalla ina yin murmushi na ce.
"My Zaid..."
"Na'am Noor."
"Ka san wani abu?"
"A'a."
Ido na lumshe na ce.
"Shekaru da suka wuce... ni matar aure ce, amma kai ba ka sani ba."
Dariya ya yi yana riƙe hannuna ya ce.
"Haka ne na kamu da sonki ashe ke Matata ce."
Na jingina da ƙirjinsa.
"Haka Allah yake tsara rayuwa."
Ya ce,
"Da na san ke ɗin Matata ce tun farko, da ban wahalar da zuciyata da neman inda kike ba."
Dariya na yi na ce.
"Da na san kai Mijina ne tun farko, da ban fara gudun soyayyarka ba."
Rungume ni ya yi tare da kallon Zayyan da ke wasa a gabanmu.
"Yau na fahimci cewa..."
"Matar aure ce... amma ita ce matar zuciyata, matar rayuwata, kuma uwar 'ya'yana."
Na lumshe ido ina cewa,
"Alhamdulillah."
Dariyar Zayyan ce ta cika hall ɗin taron
ya zo da gudu ya rungume ƙafafunmu.
"Mommy... Daddy..."
Ɗaga shi sama muka yi muna dariya.
Rayuwa ba koyaushe take tafiya yadda mutum yake so ba.
Wani lokaci abin da kake ɗauka jarabawa ne...
Shi ne Allah Ya tanadar domin ya zama alherinka.
Da farko na yi tunanin jarabawa ce auren da Abba ya ɗaura min sai yanzu na gane komai nufi ne na Allah.
Na ji daɗi sosai da Aunty Mansura ta koyi darasin rayuwa ta hanyar nadama.
Kuma kowa ya fahimci cewa...
Haƙuri, yana tafiya ne da dogaro ga Allah.
"Ni Maryama Ahmad Usman ni ce da kaina na bada labarina a rubuta domin wasu su koyi darasi, ban yarda wata marubuciya ta rubuta min labari ba.
Labarin ban ƙare ba na tsaya ne a nan saboda da wasu dalilai.
Story
By
Maryama Ahmad Usman.
Writer
Maryam Usman Mamyy writer FULANIN JAJIRTATTU ✍️
ALHAMDULILLAH!✍️✍️✍️
📚 KU SHIRYA... SABON LABARI NA NAN TAFE📚
Bayan kammala MATAR AURE CE, kada ku yi nisa...
Maryam Usman Mamyy Writer (FULANIN JAJIRTATTU) ta sake taho muku da wani labari mai cike da tausayi, sirri, ƙauna, hawaye da darussa.
🌹📖 FANSAR RAI 📖🌹
Shin me mutum zai iya sadaukarwa domin ceton rayuwar wani?
Ta taso cikin wahala da ƙunci, rayuwarta cike da baƙin ciki da ƙalubale.
Lokacin da ta yi tunanin komai ya ƙare, ƙaddara ta jefa ta cikin wata rayuwa da ba ta taɓa tsammani ba.
A can ne ta tsinci kanta a cikin masarauta mai cike da sirruka, inda aka ɗora mata nauyin da ya fi ƙarfinta.
Akwai wani siri tsakaninta da Yariman masarautar wanda ƙaddarori suka yi masa ƙawanya.
Shin za ta iya zama fansar rayuwar yariman? Ko kuwa ita ce za ta rasa nata rayuwar a wannan tafiya?
🔥 FANSAR RAI 🔥 Labarin da ya haɗa ƙaddara, juriya, sirri, sarauta da soyayya mai cike da jarabawa.
Ku kasance tare da mu domin shaida yadda rayuwa ke canzawa cikin lokaci kaɗan... 👑❤️📚
By Maryam Usman (Mamyy Writer) ✍️✨