Free chapter · Read without an account

Pg3

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

.....ABM ya zabi yin aiki a company shinkafa na cikin anguwar YARABAWA ,Wanda mahaifinsa yayi mamakin hakan Harma da mutanen da suke kusa dashi Wanda suka San zaiyi aiki a company.papa dai yasan ABRAHAB bashi da ra ayin yin aiki a company tunda shi din cikakken Dan boko ne,Dan tuni aka kammala ginin shahararren asibitinsa me suna BAKARE'S special hospital,amma lokaci daya ya sauya ra a Yi ba wai kwata_kwata ba zai zauna a asibitin ba ne,a'a zai dinga zuwa duk Monday 8to10 daga nan ya wuce company,hatta Ummu ABRAHAB sai da ta shiga mamaki ta yadda ya sauya ra'ayi,to amma ta wani fuskar ba abin mamaki ba ne ga ABM me aikin sa kai da ra'ayi.

Babu Wanda yayi mishi tambaya akan dalilin da yasa ya sauya ra'ayi,duk da sun so hakan Dan sun San dole akwai wani boyyayyan dalilin Dan ABRAHAB baya abu ba tare d wani Dan dalilin ba ko yaya yake.

So basu bi ba asin yin hakan ba sun San zurfin cikinsa ba zai CE musu komai ba sai dai ya barsu da tarin haushin fuskewarsa.

...........

BAKARE'S FAMILY...wani Dan takaitaccen family NE Wanda yake cike da arzikin dukiya....

Abubakar (BAKARE) wani bayeraben attajiri NE Wanda tun a samartakarsa yayi suna.Shi din cikakken beyeraben bayelsa NE,kasuwanci ne ya Kaishi kasar 'katar har ya auro balarabiya ummu sulaim,iyayenta basu hanashi aurenta ba saboda mahaifinta ABRAHAB shahararren malamine masanin littafan addini shi yasa be yi amfani da bambancin kabila ba,yayi amfani da fadin Allah.

(Allah bai haramta aure tsakanin ko wane jinsi da jinsi ba kabila da kabila in dai har dukansu sun yarda Allah daya NE Kuma annabi ma aikinsa ne).

Bayan auren a nan katar suka ci gaba da zama saboda dama kasuwanci Yake a nan.

Sai bayan haihuwar ABRAHAB da shekara biyar sannan ya tattara ya dawo Gida bayelsa tare da matarsa, ABRAHAB kuwa Yana tare da kakanninsa saboda karatunsa karya zama Yana wasa.

Bayan dawowarsu ne ummu ta Kuma haifar zainab wadda suke kira Amira,daga nan basu Kuma haihuwa ba.

BAKARE MUHAMMED Yana da yan uwa amma duka iyayenshi sun mutu,su hudu NE a dakinsu shine auta,Adebayo da opeyemi,suna CE mata yemi,sai femi da Kuma BAKARE da yake auta,ke nan yana da yaya namiji daya sai mata biyu,duka kowa da zuriarshi.

Tunda suka bar ABRAHAB acan sai dai yazo hutu hakanne yasa ya San yan uwa da dama.

ABRAHAB BAKARE MUHAMMED (ABM) bai dauko kamannin kowa ba sai na mahaifiyarshi wadda ta dauko kamannin kakanshi,hakanne yasa baza ka taba cewa ABRAHAB bayerabene ba Indai ba fada Maka akayi ba,ko an fada din da sunan mahaifin kawai ake yadda,domin sam bai Yi kama da su ba,sabanin kanwarshi Amira da ta dauko kamannin mahaifinta.

Idan nace Zan zauna fasalta muku waye ABRAHAB to zamu dauki dogon lokaci,abu daya zuwa biyar Zan iya fada shine ABRAHAB kyakkyawane miskiline me aji ne sannan me taimako NE Kuma me addini NE.bazaka taba cewa bayerabene ba saboda sabanin hali,sam bai dauko halinsu na yarabawa ba kodan ba cikinsu yayi rayuwa ba,yana da da taimako ainun wamda haka ne yasa ya tara masoya wamda suka sanshi da wanda basu sanshi sai a wannan dawowar tasa,amma sunanshi tamkar su suka rada masa, wannan kenan.

Zahra *YAR GIDAN* *YARABAWA........*

Malam Yusuf shine asalin kakanta.

asalinsu Fulanin membilane,matarshi daya da yara biyu Ali da zainab,tun kafin zuwanshi cikin garin garin bayelsa aka yiwa zainab aure tana can cikin babban birnin jalingo saboda mijinta babu laifie me haline yaranta uku duka maza,sai Ali da baiyi aure ba har sai bayan dawowarsu bayelsa da kusan shekara uku sannan aka daura masa aure da yar uwarsa bilkisu 'yar yayar innarsu,sun haifi yara biyu Al'amin da sahara daga haka suma haihuwar ta tsaya,

Zahra na da shekara biyar a duniya Allah yayiwa malam Yusuf rasuwa,daga nanne rikon zahra ya dawo hannun kaka,shi kuma Al'amin a lokacin ya koma can membila tare da Adda zainab saboda shakuwa da amintar dake tsakaninsa da dan farinta Habib,hakan yasa mijinta Dr asadullah ya dauki nauyin karatunsu gaba daya dan a halin yanzu ma basa kasar.

Zahra yarinya CE me shiga rai kasancewarta kyakykyawar bafulatanar mambila inda asalin kyau yake,wadda ta biyo kakarta sak da sak,shi yasa kaka ke matukar ji da ita, wannanne yasa zahra ta taso da rashin ji da sakalci da tabara iri_iri,

Zaman zahra hannun kaka ya dada bada gudun mawa wajen sakalcinta da tsiwa,amma duk da haka ba zamu kira zahra mara tarbiya ba dan a hakan kaka na kokarin koya mata tarbiya ta bangarori da dama, takance zahrere bari ba don bana sonki ba,ita dai barta da tsiwa da tsokana da rashin barin takwana,Sam bata daukar reni,idan ka nuna mata yatsa kafin ka maida ta karya shi,duk abinda tayi kaka takance ai kuruciya ce idan watarana akace tayi duk wannan karyatawa za ayi.

Ganin yadda zahran ke dada sakalcewa yasa abbanta yiwa kaka dabara ya dauko abarsa,to duk da haka dai ance Hali zanan dutse,da alama dai ba a iya kuruciyar wannan hali zai tsaya ba,dan babu abinda zahra ta Bari daga halinta saima abinda ya karu,sai dai a maimakon gidan kaka da ake daure mata kugu,gidan mama sai dai tasha tsintsiyar kwakwa gurin mama da Abba,a kullum idan ba a kawo kararta sau goma ba to a kawo sau bakwai.

Malam Ali Bashi da karfi sai dai akwai rufin asirin Allah kayan gumama Yake saidawa,babu laifi Yana samun na ci da iyalansa da mahaifiyarsa,dan ma sau tari Yana samun sauki daga gurin kaka dan idan Adda zainab ta turo mata kudi har shi Bashi take Yi. shi yasa nauyin baiyi masa yawa ba suke zaune cikin rufin asiri,gidan Kansa NE dai har yanzu Allah bai bashi ikon samu ba,dan da Farko kaka taso su dawo gidanta su ci gaba da zama amma sai ya nuna mata cewa zasu takura gaba daya tunda gidan bashi da girma daki daya ne sai kichin da bandaki,haka ta hakura dan yafi ta gaskiya.

Zahra tun yarintarta ta taso da wani irin tsana a zuciyarta na wannan yare,dalilin da ya assasa haka kuwa ya samo asali da yadda suka zauna makwabtaka da yarbawa ta fahimci mugun halinsu wanda take yasa mata tsanarsu,abinda ya fara jawo musu tsana a zuciyar Zahra kuwa shine yadda zata rungume juna tsakanin mace da namiji wanda a iya kuruciyar ta tasan babu kyau saboda hudubar da take sha gurin kaka da mama,sai kuma shegiyar rowarsu,wanda Zahra ta tsani rowa dan ita yarinyace me son kyauta sam Zahra bata da rowa, shi yasa ta kuma kullatarsu akan wannan hali,abu na karshe wayon da ta fara yi yasa ta san cewa suna haihuwa ba tare da aure ba acewarsu dole sai an gwada saboda kar mutum ya auri juya ko mace ta haifi juya,sai su haifi yara uku biyar ba tare da aure ba,sai daga baya azo ayi auren,azamanta dasu ta fukanci wadannan mugayen halayyar tasu wadda babu musulmi babu kafiri duk haka suke gudanar da rayuwarsu,baka taba banbance musulmi acikinsu sai idan kaga yana Sallah,kai abubuwan da Zahra ta tsana a tare da su masu yawa ne dan kullum kara bata mamaki suke tare da sabon darasin tsanarsu.

Duk anguwar da zasu zauna sai Zahra tayi dalilin da zasu barta in dai har sunyi makwabtaka da yarbawa,shine dalilin da yasa suke ta yawan haya,daga karshe dai suka yada zango a anguwar Hausawa duk da cewa suma da kwai yarbawan a ciki sai dai basu da yawa kamar hausawa da Fulani da suka yo hijira ko yawan fatauci.anan dai sun daɗe dan anan Zahra ta gama frimary har ta shiga secondry,tana zana jarabawar shiga ss ne me gidan da suke ciki ya bukaci gidansa saboda buƙata da taso masa akan gidan, wannan shine dalilin komawarsu anguwar yarbawa.

Kunji dai irin tashin hankalin da ta shiga da danbarwar da akayi da ita kafin su dawo anguwar yarbawa.

..............

Yau tunda ta tashi take ciwon rai da neman rigima saboda ta huce haushin jiya na ABM,yadda take jin tsanar ABM ko wadda suka Yi fadan da ita Bata jin haushinta kai hasalima tuni ta manta da ita,fitowa tayi ta tsaya bakin dakinsu tana karewa tafkeken tsakar gidannasu na yarbawa kallo cike da kyama tana faman Harare harare,komawa ta Yi daki ta dauko tsintsiyar kwakwa ta Fara shara,yadda zahra ke yin sharar kawai zakasan cewa taso tsokano rigima ne dan duk abinda taci karo dashi hadawa take dashi hatta da gawayinsu na girki haka take bi tana sharewa,saboda tsabar neman tsokana ko girman tsakar gidan Bata gani, Lola ce ta fara fitowa jin yadda ake hargitsa gidan kamar ana yaki,idanunta basu sauka a ko ina ba sai kan kayan sana arta na fanke wanda ta kwaba tun asuba ta saka shi a hantsi dan ya tashi ga kuma gawayinta da 'kullun kosai duk ta fito dasu.komawa d'aki tayi dan shiryowa ta fita wajen sana arta,sai gashi zahra ta watsa mata shara kan 'kullum kosanta, fanke da yake a rufe ta wancakalar dashi gefe ya kife a kasa gawayi kuwa ko wanne yayi nashi guri.

Wani irin ihu Lola tayi kana tayi kan zahra da bata ko daga kai ta kalleta ba,sai da ta tabbatar Lola taba ta take da nufin Yi sannan ta watsar da tsintsiyar tayi tsalle gefe daya daidai lokacin da Lola ta iso dan fizgo zahra, kaucewar da zahra tayi yasa Lola ta bugi Iska ta fad'i da baka, sai ga baki ya fashe.dariya zahra tasa harda ri'ke ciki dama abinda take bukata kenan ko ba komai ta rage rad'ad'in ba'kin cikin ABM,ihun da Lola tasa yasa duka matan gidan suka fito. anan kowa yayi arba da irin barnar da zahra tayi masa,kule ce ta kada baki ta ce", keko zahre me Lola tayi miki kika mata wanna dukan haka gashi muma duk kin mana barna garin danbe", zahra ta CE", me zata kuma yi ba dariya ba,cikin rike ciki ta ce", amma dai wallahi ku yarabawannan kun cika shirme da wawanci kuna kallon mace 'kasa tana shure shure amma kuce duka tasha,to ba duka tasha ba kasa tasha",ta'kare maganar da saurin gimtse bakinta saboda fitowar mama.maman farkawarta ke nan daga baccin da ya dan kwansheta saman sallaya tajiyo haniya,gadonsu ta fara dubawa taga babu zahra hakan yasa tayi azamar fitowa tana cewa yau da rigimar zahra zan fara kalaci Allah ka shirya min zahra.

A hankali zahra taja da baya dan tasan tsaf mama zata kawo mata bugu,dubanta maman tayi cike da takaici ta CE", zahra me kikayiwa Lola harda fashewar baki? Tura 'Karamin bakinta ta Yi tana cewa mama ba abinda nayi mata dubeta fa katuwa da ita ya zanyi na iya dukan Lola,rigimarta ce kawai daga ji ina shara ta fito ta fara masifa har tana shirin kaimin bugu shine na matsa ta bugi Iska ta fadi bakinta ya fashe abinka da bakin da ba ya samun burushi"dakuwa mama tayi mata har tana kasa cewa komai saboda takaicin zahran.tashi Lola tayi tana cewa maman zahra 'barna ta yimin duba kayan sana a ta kiga yadda ta min asara wallahi sai na daki kudina ko me zata yi yau bazanyi hakuri ba", anan kowacce ta fara duba yan kayanta dan ganin tata 'barnar. take kuwa kowacce ta ce" sai ta daki kudinta ,duk da kaunar da suke ma zahra a ransu yau sunsha alwashin dukanta kodan su yi maganinta.

Harara mama ta ballawa zahra tana cewa to sai ki tsaya su daki asarar daki kayi musu babu ruwana gaki gasunan", daga haka mama ta wucewarta daki tana jin tashin hankalin dukan da za ayiwa zahran ina zahra zata shanye dukan wadannan girka_girkan yarbawan? To amma ai ita ta kawa kanta dole ta rufe idanunta daga kallon hukuncin da za ayiwa zahran.

Zahra kuwa kugu ta ri'ke tana jijjiga jikinta tare da kallonsu daya bayan daya tana jiran ta inda zasu fara,dan tsaf ta riga ta shirya muguntar da zata yiwa kowaccensu.

Kuzo ku begen mana ya kuka tsaya kamar wasu zakaru", ta fada tana cije labbanta na kasa,Lola da abin yafi karewa akanta bata daddara ba ta kuma yin kukan kura tayi kan zahra tana tattara duk wani haushin zahra dake ranta dan tafi jin karsashin zane Yar banza,ganin haka su bola da kule da ragowar matan su biyar su kayi kan zahra,sai dai kafin su karasa sun kuma jin ihun lola kafin su akara da abinda ya kuma sa lola ihu a karo na biyu suma sunji idanunsu ya rufe saboda watsin yajin da zahra tayi musu,take kowacce ta fara nan hanyar dakinta tana tsinewa zahra iface_iface.

Zahra dan dariya har kwanciya tayi a gurin,Lola da tafi kowa shan wahala kuwa burgima ta shiga Yi tana jerawa zahra tsinuwa da Allah ya isa,ta gabanta zahra ta wuce ta dauki kullun kosai ta yad'e 'kurar kai shima 'kullun fanken kwashewa ta Yi ta gyara ta had'a komai tsaf ta d'ora aka tana cewa bari naje na saida dama yau kwadayin tsiren audu me nama nake Allah ya kashe ya bani🤣

Ihu Lola ta Kuma sawa tana kokarin riko zahra,kunsan dai beyerabe da shegen son kudi,shi yasa hankalinta ya Kuma tashi dan tasan tsaf zahra zata sayar ta cinye kudin.....

Idan typing na Yi muku dadi to Naga ruwan comment......

Fatima Y adam ✍🏽

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: YAR GIDAN YARBAWA

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol