Free chapter · Read without an account
Pg 2
To idan beyerabe ne ya za kiyi?cewar Hafsah da sai yanzu ta saka musu baki a hirartasu," tabe baki zahra ta yi sannan cike da nuna kyama ta ce", daina zuwa zanyi Dan wlh bazan zauna a Karƙashin beyerabe ba", nadiya tayi caraf ta ce", amma ai kinsan Abbanki ba zai barki ba ko? Shiru ta yi kafin ta kuma cewa to ma Allah kar yasa ace beyerabe ne,ke Bama shi bane tunda dai kina jin irin yadda ake fadar taimakonsa kuma beyerabe ba zai yi haka ba dan su yarbawa ba wanda yafi rowa da son abun duniya", waike zahra me kika dauki yarbawa ne? Me suka yi miki haka da ba ki yi musu ko kyakkyawan zato? Kafin Hafsah ta rufe bakinta zahra ta kai mata bugu a labbanta tana cewa bakinki baya jin magana tunda har ba zai dinga kiyaye abinda Banaso ba", to zahra me tayi Miki daga tambaya,"kallon da ta watsawa nadiya ne yasa ta rufe bakinta,daga haka basu kuma yin wata hira ba har suka kai kamfanin, dake ba wani nisa ne dashi sosai ba.
Ga mamakinsu suna zuwa katafaren kamfanin na ABM suka tarar ana ta haɗa guri da kimtse kimtse kamar dai za ayi wani babban taro na musamman,tsayawa zahra ta Yi tana karewa katon farfajiyar companin kallo tare da mutanen da suke ta hada_hada kowa da abinda yake yi,rike kugu tayi tamkar me shirin dambe tana kara ware manyan idanunta a hadadden companin da ba tayi zaton haka yake ba,dawowa gefanta su kayi suna cewa zahra kinga cimpanin me kyau ko? Muma farkon shigowarmu haka muka sha kauyanci sai ma kin shiga cikinsa Zaki tabbatar da cewa an kashe uwar nera",harara zahra ta zabgawa Nadiya tare da cewa to Ni an gaya miki kauyanci na tsaya Yi? Allah ya baki hakuri Nadiya ta fada a sanyaye ,da hakurin ta mutu sadakar nawa kika bani? Kafin wata Ta Kuma magana suka ji wasu ywrbawa dake tsaye jikin katuwar bishiyar gwaiba daga gefansu suna cewa lallai ABM ya cancanci fiye da wannan karramawar daga staff dinsa kuma talakawansa dan haka duk abinda aka yi masa dan shirin tarbarsa ba a fadi ba", dayan ta ce", kin san ance kusan shekaru takwas baya kasarnan yana can katar tare da mahaifiyarsa yanzu kuma mahaifinsa ya bukaci da su dawo gaba daya har mahaifiyartasa shi yasa ya dawo,jiya da daddare jirginsu ya sauka,ance tun yau zai fara zaga kamfanoninsa dan yana so ya duba wanda ya kamata ya yi aiki a ciki",
Wani uban tsaki zahra taja tana cewa ashe ma ba aikin za ayi ba. yau ranar neman sunace", kamar ya neman suna budurwar da suke magana akan dalilin dawowar ABM ta tambayi zahra cike da mamakin furucin zahran,murguda baki zahra ta yi tana cewa ai ba dake nake ba shishshiganatu beyerabiyar bayelsa " take budurwar nan ta harzuka ta fara kumfar baki saboda irin yanmatannan ne marasa hakuri da jan girma kuma gata beyerabiya da babu hakuri,
Hakuri su Hafsah suka fara bawa budurwar amma kamar turata ake yi se hankoro take zata bugi zahra wai ta mata rashin kunya,ita ko zahra ko a jikinta abinda ta sani ne baza ta taɓa bari wata banza ta bugeta ba,banzarma kuma beyerabiya wadda take kyamar su ,dan haka bazata bari jikinsu ya hadu ba.sannan dai ita zahra fa bata danbe acewarta dambe na matsoraci ne kuma na ballagazar mace ne 😀
Ita kuma ta girma ta wuce dambe a titi,shekara sha biyar ba karya ba zahra .
Haka beyerabiyar nan ta fara tara musu jama'a dake zahra tana son taga ABM kodan tasan yaren da zata yiwa aiki, shi yasa ta janye kawayenta suka bar gurin tana cewa Ku zo mu bar gurin nan kunsan su 'yanmatan yarbawannan ba kai suka cika ba", har beyerabiyar ta kuma yunkurowa sai kawarta ta rikota saboda sanarwar da aka fara yi ta zuwan ABM din cikin Companyn.
Cikin kankanin lokaci kowa ya kama kansa duk inda ka duba jami ai ne da masu tsaron lafiyarsa kamar basu da wani aiki a duniya sena bautawa rayuwar ABM.
Dankareriyar motar da yake ciki ce tayi pakin daidai saitin dogon Capet din dake shimfide har zuwa inda aka tanada masa don zama,take gurin ya kuma ɗaukar shiru saboda tsayuwar motar da bude masa da wani basamuden mutum yayi cikin tsananin biyayya da kan da kai.
Sai da yaja mintuna kusan biyu kafin ya zuro doguwar ƙafarsa dake sanye cikin wani arnan coversue baki me tsananin sheki,nan ma sai da ya kuma jan sakanni sannan ya zuro gangar jikinsa waje inda mutanensa ke dakon jiran fitowarsa. wanda suka taba ganinsa da wanda basu taba ganinsa ba suna raba ido dan kare masa kallo,a hakikanin gaskiya wadanda basu taba ganinsa ba sune mafi rinjaye a gurinnan suma saidai dattijai wadanda basu fi sa annin fafinsa ba.
Take gurin ya kaure da wani irin daddadan kamshi, wanda duk tsananin kwarewarka a gulma baka isa tantance kalar kamshin turaren dake jikinsa ba,duk yadda mutane suka ci burin kare masa kallo sai hakan ya gagara saboda tsananin kwarjininsa da kamewa wadda ya cakude da wata irin nutsuwa,taku yake kamar wani dawisu,fuskarshin nan dai babu yabo babu fallasa,idanunshi saye suke da fari ƙal din sun glass wanda be hana kyawawan idanunshi masu dan girma bayyana ba,fuskarshi ta kawatu da dan saje irin na gayunnan kai kana ganinshi kasan ya haɗa alaka da larabawa,bakar cot ce ajikinshi wanda ta hadu da ginannan jikinshi ta bada wani kyau na musamman.
Baka jin motsin komai a gurin sai na nutsatstsan takunsa dake hade da wani Dan zafin nama,Wanda hakanne ya karawa takunnasa armashi da fidda sautin takun cikakkun maza.
A sirrince kowa ke satar kallonsa saboda kwarjini da kamalarsa,da haka ya karasa inda aka tanada dominsa.
Yanmatan yarbawa kuwa kuwa ji suke tamkar su hadiyeshi ko wacce a ranta tana fatan ace wannan hadadden sadauki ya zama rabonta,sai dai ina sun San cewa wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa.
A hankali zahra ta saki wani Dan siririn tsaki tare da ballawa wajen da ABM ya zauna harara,kafin cikin yin kasa da murya tace da kawayenta,ku wannan fa mutumin inaga aljani ne dan kyawunsa yayi yawa", hafsa ta CE", haba zahra wane irin aljani Kuma?idan aljani ne ai da yanzu duk mun mutu tunda ance duk Wanda yaga aljani a gaske to zai mutu ko ya haukace",Jim zahra ta Yi kafin ta daga kanta sama ta CE", ey kuma fa haka ne to mutumne kenan shi yasa ya fiye girman kai saboda yaga yana da kyau? Nadiya ta CE bazamu Yankee masa hukunci ba tukun har sai munga halayyarshi ta zahiri" idan a nan zaiyi aiki ba hafsa ta tuna musu.
Daga nan shuru su kayi saboda tsinkayar daddar sautin muryarsa me Dan kauri da zurfi wacce ke fita cikin wani irin salo saboda rashin daidaituwar hausa a kan harshensa.
Sosai muryarsa ta Kuma tafiya da yanmata da zawarawan da suke karkashinsa.
Yawan mata a Company zai iya daidaita dana maza koma su fi masana yawa,kasancewar al'adar BEYERABE ne zaman gida mata su fita nema,shi yasa yawancin mazan sune hausawa da wasu yarukan yarbawa kuwa duka mata ne idan ka cire tsirarun zuwaw irinsu ZAHRA.
Magana yayi kadan amma me muhimmanci da Kuma tarin ma'anoni,tafi gurin ya dauka cikin burgewa da tsari,daga nan aka umarci ko wane ma aikaci ya nufi gurbinsa saboda me girma ABM zai zaga maaikatar yaga yadda suke tafi da aiyukansu.
Cikin kankanin lokaci duk yawan mutanen da sukayi dafifi a gurin suka watse kowa ya nufi wajen aikinsa.
Su zahra dama a bangaren zuba gyararriyar shinkafa a buhu suke,bayan sun zuba a kwai bangaren masu dinke buhu,Dan haka suka nufi bangarensu zahra na faman leke leke Ana kauyanci tunda ita sai yaune zata Fara aikin,amma babu dama su hafsa suce tayi kauyanci duk da cewa kauyencin take zubawa kamar tazo daga kauyenne.
Suna zuwa saboda zuwan ABM yasa aka bawa zahra aikinta da wuri,take kuwa su hafsa suka zage suka fara aikinsu,murmushi zahra tayi ganin Ashe ma aikin ba me wuya ba ne tunda a bakin injin dake tace shinkafar zasu tara buhun har sai ya cika daga nan akwai mata majiya karfin da zasu janje buhun su matsar dashi gurin dinki Wanda shima ba wani wahala ba ne sai dai shi ya danfi durin shinkafa tunda da hannu za a dinke.
Zahra ki fara aikin mana ga injinki nan a gabanki kunnawa kawai Zaki,kinga yadda Zaki kunna,"Nadiya ta shiga nuna mata,harara zahra ta watsa mata tamkar idanunta zasu Fado kana ta CE", nifa Nadiya bana son shishshigi ce miki nayi ban rike yadda aka nuna min kunnawarba? Hafsa daketa aikinta cikin kwarewa tace nifa zahra dadina dake abin fada baya miki wuya Dan Allah ki koyi hakuri", zahra na shirin balbale hafsa da masifa taji an shako wuyanta ta baya kafin ta Ankara taji mari akan kyakykyawar fuskarta da take matukar ji da ita.femi CE buduewar da suka Yi fada da zahra ta shiga nuna zahra da yatsa tana cewa daga yau ko kallon inda nake ba Zaki kara Yi ba bare kimin rashin kunya", Aiko zahra Bata San sanda tayi wani kukan Kura ta shako wuyan femi ba,saboda yadda taji zafin marin da shakar da akayi mata,kankace me tuni fada ya runcabe tsakanin femi da zahra sosai zahra ta zage karfinta na kuruciya tana jimgar femi harda cizo da yakushi,rabasu ake kokarinyi amma hakan ya gagara gashi da alama dai zahra karfi NE da ita.haba autar mama ya da fada haka kin manta kin girma kin dena fada cewar Nadiya cikin son rarrashin zahra da tuna mata alkawarin da tayi na ta daina dambe.
Ana cikin wannan danbarwar Oga kwata_kwata ya karaso shida mukarrabansa Dan duba sashen kananun maaikata.
Da sauri manager ya karaso Yana daka musu tsawa,cikin hanzari suka rabu da juna amma fa femi Tasha suburbudar masu kwarin jini,zahra sai faman cika da batsewa take Yi tana faman hura dogon hancinta,kuzo sir ABM na kiranka cewar manager dake ta zafga musu harara yana kwafa.jiki a sanyaye femi taja kafafunta da sukayi tsamin dukan zahra ga kuma tashin hankalin ganinsu da abm yayi suna danbe a company dinsa tasan babu bata lokaci zai koresu daga aiki dan tun kafin su ganshi sun san ko waye baya daukar nonses ga manyan ma aikata ma bare kuma su.
Zahra kam ko a jikinta haka ta karaso tana faman tura Karamin bakinta tana ci gaba da harara WA femi.
Durkusawa femi tayi, ita ko zahra gefe ta samu ta coge tana cewa aranta kaji shegiya me ladabin mage wallahi babu wani Kato da zan durkusawa idan ba abbana ba"shuru gurin ya dauka na wasu yan mintuna da basu wuce biyu ba,kafin a hankali cikin kamewarsa da ajinsa dake cikin jininsa ya fara magana da hausarshi dake fita tamkar turancin ingila,me yasa kuke mana fada? Dama nan gurin fada NE? To Ni ban San shirme da rashin kamun kai kuje Gida duka kubar aikin sai an neme ku tunda Baku da manner", daga haka yayi gaba cikin takunshi me zurfi irin na mazaje,
Kuka femi ta saka duk da cewa taji salama da ba korarsu akayi duka ba.
Itako zahra harara ta rakashi da ita zuciyarta najin wani irin zafinsa saboda maganganun da ya fada musu,Bata taba jin tsanar abu lokaci daya ba kamar yadda taji tsanar ABM ba,wallahi baka ci bulus ba,idan har na barka kasha kenan ba sunana zahra Yar gidan yarbawa ba,idan na bar companin nan ban dasa Maka abinda zaka dinga tunawa bani da tarbiya ba Ashe ban cika Yar mamana ba,Zan ci gaba da zuwa aiki bayan ka GA dama ka nememu daga nan zaka tabbatar da cewa zahra bata da tarbiya da kamun kan da ka ambata,daga haka taja kafafunta cikin wata iriyar fusata da ita kanta take mamakinta ta wani bangaren,amma idan ta tuna da maganganunsa sai taga cewa lallai tsanarshi da fusatarta tana dalili. Da wannan kuncin ran ta isa gida.
Koda mama ta ganta bata ce mata komai ba Dan tasan Halin abarta.
Sai da Abbanta ya dawo mama take jin abinda ya faru a bakinsa Wanda zahra tayi mamakin inda ya sani,abin bai Kuma daure mata kai ba sai da ta ji Abban ya ce ance jibi ta koma aiki wato dai hutun na kwana daya NE.
Maimakon taji haushi sai taji farinciki saboda kawai zata koma ta dauki fansar abinda ABM yayii mata.
..............✍🏽
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: YAR GIDAN YARBAWA