Free chapter · Read without an account
Page5
Kowa ya shiga gidan amma ita ta kasa saboda hango Abba da tayi ya coge hannun shi a baya,tunanin ta ya bata cewa dorina ya boye dan wannan lefin nata ya fi karfin bugu da tsintsiyar kwakwa.
Mama ce ta dubi Abba bayan shigowar su bola,ta ce", ka gani ko basu taho da ita ba ,shi yasa nace maka Gara mubisu Zahra bazata iya fidda kanta a wajen yansanda ba tunda bata taba zuwa ba", murmushi ne ya subcewa Abba duk da yadda ranshi yake a bace, yace da mama duba hanyar shigowa gida zaki gano yarki tana lekowa da komawa", da sauri mama ta nufi hanyar zauren gidan tana jin farin cikin da take kokarin boye shi na dawowar zahran, Abba ya ci gaba da fadin lallai bilkisu na fahimci har yanzu baki gama sanin halin autarki ba,ita dai mama bata kula shi ba har sai da ta shammaci zahra wadda sam bata ankara da tahowarta ba,sai cafkar hannunta da taji maman ta yi tana cewa zonan dan ƙaniyarki,dukan da kike gudu bayan kin aikata laifin ki yau shi zaki sha idan yaso kafin kiyi laifin kya fara tuna dukan.
Tirjewa Zahra ta fara yi idanunta na fara zubar da hawayen da baza a kira su na nadama ba,magiya ta fara yiwa mama akan su yi hakuri bazata sake ba", mama bata kulata ba ta cigaba da janta har gaban Abba.
Ai ganinta gaban Abba yasa ta kuma kecewa da kuka tana cewa dan Allah masoyina Abbana me kaunata kayi hakuri wlh bazan sake ba,na tuba nabika nabi Allah da ma aiki,dan Allah masoyi kaya hakuri", kara tsuke fuska Abba yayi duk da yadda Zahran take karya zuciyarshi da tausayinta da kuma kaunarta dake dankare a ranshi ga kuma dariyar da take son kwace masa,wai masoyi Ni ba masoyinki ba ne da masoyinki ne da baki dinga jawo min magana ba", ya fada yana warware wayar cajar dake hannun shi,ganin da gaske yake fa bugunnata zaiyi yasa ta kuma zunduma ihu tare da kankame mama tana cewa mama Abba ya daina sona amma nasan ke kina so na dan Allah kar ki bari ya bugan min fata wlh fashewa zata yi fatata kinji abar kauna mamana",
A'a fa Zahra bakya jin magana idan aka kyaleki gobe ma zaki kuma,dan haka bazan hana Abbanki ya bugeki ba tunda bakyason zaman lafiya", kuka ta kuma sawa kamar zata shiɗe wanda har sai da Abba ya aje wayar hannunshi ya kamo hannunta sannan cikin hade fuska ya ce", Zahra na am Abbana ta fada cikin Muryar tausayi ya kuma kiran sunanta har sau uku sannan yaja kunnenta da dan karfi ya murda yana cewa wlh duk ranar da kika kuma maimaita barna makamanciyat ta yau to bazan kyaleki ba duk kuka da magiyarki kinji ko? Naji Abbana bazan sake ba", to Allah yasa a wannan karon har zuciya kika fada ya kare maganar tare sakin kunnenta da har yayi jawur saboda rikon da yasha gurin Abba,tana jinta a sake ta mike da gudu ta fada dakinsu tana sakin ajiyar zuciyar tsira daga bugun Abbanta.
Ganin ba a bugeta ba yasa yan tsegumi suka dinga gunguni daga inda suke labe a jikin kyauren dakunansu,jiki a sanyaye suka koma ciki ba dan ransu yaso kin dukan Zahra da a kayi ba.
Femi kam tafi Zahra jin zafin abinda akayi mata amma akan Zahra domin duk wani alwashinta akan Zahra ne,dan zuciyarta bata da kwarin gwiwar jin zafin ABM dan wani irin so take masa me shiga farad daya.
Washe gari da safe,Zahra bata fito ba sai wajen karfe goma, tana sane taki fitowa dan tasan yau zata koma aiki, tana jin lokacin da su hafsa suka biyo mata mama tayi ta tashinta amma tayi luf tamkar me bacci,haka suka hakura suka tafi suna jin fargabar kar ta makara a yi mata me gaba daya wato kora.
Mika tayi tana mai rarraba manyan idanunta kan tsakar gidan da yake kaca kace komai yana zaman kansa,kofofin su ta fara bi da kallo tana tunanin ta hanyar da za ta saka su yin shara dole a cikin gidan kullum ta Allah dan ita kadaice hanyar da zata bi dan kare kansu daga daukar muguwar cuta,cizon yatsa ta yi tana dan kallon kofar dakinsu,ba komai ne zai hana ta yin wani abu yau ba sai dan kashedin jiya da dukan da taso sha a hannun Abba dan haka dole ta bada iska ko na kwana ɗaya ne kafin ta ɗora daga inda ta tsaya.
Tsuka tayi tana shirin barin wajen dan zuwa yin wanka,har ta kai ruwa banɗaki bayan yasha mugun wanki,ta fara cuɗa jikinta kenan tajiyo hayaniyar lola tana karadi da zagin su bola akan abinda su kayi mata jiya,aiko da gudu Zahra ta janyo zani ta daura tare da yafa dankwalinta tayo waje jikinta duk kunfa,kawai sai ganinta su kayi tsakiyarsu tana faman tuntsurawa lola dariya har da rike ciki,bakin cikin da lola ke ciki yasa ta wawuri bokitin dake kusa da ita a yashe ta yi kan Zahra ,take suka fara zagaye faffadan tsakar gidan wanda ke cike da shirgin su bola,Zahra na sane take bi ta kan bokitocin roba tana markade su da kafafunta yayinda take cilli da duk abinda taci karo da shi wanda ba zai fasu ba,kankace me sun rude da yiwa zahra magiya ta bar fasa musu kaya,hatta kai da lola ta gaji da binta ta samu waje ta tsaya tana maida numfashin wahala, zahla Allah ya chine maka shege ka cuceni wuta balbal tsakanina da kai,lola take fada tana danna hannunta da ta buge a wajen bin Zahra.
Zahra kuwa ba abinda take yiwa lola sai gwalo, su kuwa tuni suka shiga tattare kayansu iyayen san banza har bokitin da suka fashe basu barsu ba,suna yi suna jefawa Zahra Allah ya isa a zuciyoyinsu dan basu da damar magana yanzu ta shiga dakunansu ta jawo musu asarar da tafi wannan,duk bala in yarbawannan sun sallamawa Zahra ta fi su iya shege sai dai su nuna mata hayaniya da daga murya dan Zahra bata da kwarafniyar magana sai iya salon tsokana kala kala.
Da kyar lola ta nufi hanyar dakinta tana dingisa kafarta da har yanzu bata dawo daidai daga azabtarwar Zahra ba,bakinta kuma bai mutu wajen zagin Zahra ba.
Yadda lola ke tafiya ya kuma bawa Zahra dariya hakan yasa ta kuma kwashewa da dariyar tana yi tana gwada tafiyar lola da maganarta, Allah ya chine maka zahla," kayi asala zahla",zahla bazaka gama da iyaye naka lafiya ba," sai da ta kusa isa bandakin ta dakata tana yatsine fuska irin yadda lola take yi tare da cewa kai zahla kai dan ishka ne wallahi kashan takan chiya", sai ta kuma sa dariya ta cigaba da cewa in banda iskanci da rashin hali irin na bayerabe kace baza a taba kayanka ba amma kai kana son na wani , wannan bakin hali da me yayi kama, Allah ya kyauta ta fada tare da yin adduar shiga bandaki ta cigaba da wankanta ranta fes amma duk da haka ta tuna da abm sai taji wani bacin rai wanda har sai ka gane akan fuskarta.
Tsit gidan yayi baka kuma jin motsin kowa ba,koda mama ta shigo gidan bata yi zaton Zahra ta tashi ba,sai dai kuma tana shiga dakin ta ci karo da kamshin turarenta me sanyi wanda duk tsananin rashi mama sai ta siyo mata shi,cikin mamaki mama ta kalli Zahra dake bude gogaggen hijab dinta za ta saka,kafin ta ce", yanzu zahra tun fita ta baki tafi ba sai yanzu ? Lallai naga alama so kike a sallame ki daga aikin gaba daya Allah yasa ba wata fitinar kika tsaya dauka bayan fita ta ba", Amin Zahra ta fada tana gifta maman tare da cewa mama ayi mana addu'a sai na dawo,idan kika fara addu'ar kar ki shiru har sai na fita kinji mama,Tom Allah ya kiyaye abinda mama ta iya fada kenan tana jin jina KURUCIYA irinta ZAHRA azuciyarya tana mai ci gaba da yiwa Zahra addu'ar kariya daga dukkan abin ƙi da fatan rayuwa me albarka.
Zahra tana fita bata saurari yan gulma da suke ta fatan fitar Zahra ba,tasa kai ta bar gidan tana mai fidda murmushin nuni da cewa ta gano su,aiko Zahra na fita suka fara iface ifacensu masu yin Allah ya isah nayi masu zaginta na yi duk da sun san cewa mama na cikin gidan amma basu fasa ba tunda sun san mama ba gayawa dodon tasu zata yi ba.
.................
Tun dawowar abm komai ya canja,duk wanda ya shigo Company a cikin kwana biyunnan zai san cewa an samu canji,gyara ne ake ta yinsa ta ko ina,duk wani ma aikaci ya shiga taitayinsa saboda yadda ake ta binciken manyan ma aikata da kanana dan acikin kwana biyu an sauke wajen mutum uku daga kan kujerarsu wanda aka same su da Handama da baba kere akan dukiyar Company har da masu cin amana ta hanyar fitar da sirrin Company zuwa Company da suke kishi da Company ABM,sai kananun ma'aika da suke da hannu a cikin case ɗin, wannan yasa kowa ya kama kansa don yanzu sun san babu wasa aiki kawai tsakani da Allah,shi yasa ta bangaren makara ma komai ya fara saituwa karfe takwas kowa ya hallara a wajen aikinsa.
Yana tsaye jikin window office dinsa da yake a hawa na shida yana kallon me shiga da me fita duk da dai ba kowa yake rike fuskarsa ba amma dai zai iya gane cewa makara ta ragu sosai akan ranar da ya fara zuwa tunda ya dauki mataki da babbar murya,har zai bar wajen yaga kamar security na magana cikin fada da alama shida wani ne,fasa komawa yayi ya tsaya don son ganin waye haka yazo a wannan lokacin? Kara duban agogon dake daure a tsintsiyar hannunshi yayi yaga har goma ta gota bayan kuma tun bayan kwana biyun aka saka dokar duk wanda ya wuce tara da rabi to ya koma kar security ya barshi ya shigo,kuma tunda aka sa dokar babu wanda ya taba kaiwa ko tara bai karaso gun aiki ba sai yau din da aka samu me taurin kai ga yadda yaga alama.
Jan numfashi yayi tare da fesarwa lokacin da yaga Zahra ta sunkuya ta karkashin security ta shigo da gudu ba tare da ko waiwayen shi tayi ba,tuni ragowar security suka take mata baya dan dakatar da ita daga shiga cikin ma'aikatar.
Fatima y Adam ✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*