Free chapter · Read without an account

Pg10

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

.......A hankali ta fito daga inda take labe kamar kadangaruwar dake neman kuda,sadaf sadaf ta fara matsowa dan gab da inda suka faka motocinsu,ta AB ita ce a farko dan haka kai tsaye saitin motar ta nufa ta inda ba za a ganta ba amma tana da tabbacin duk inda ta yi kara guda zasu jiyota har ma su kawo mata dauki,idan kuma shi uban gaiyar be kawo miki temakon ba fa? Tura baki tayi kamar tana kallon zuciyartata ta ce", ai walle duk yadda zanyi yau mugun mutumin nan ba zai sha a hannuna ba", ta karasa maganar hade da sakin guntun murmushin da ya kuma tona sirrin kyawunta, a dai_dai lokacinne AB ya fito daga cikin rantsatstsiyar motarsa kai kana kallon wagga gaye kasan ba duk kai ba,cikin nutsuwar dake tafe da tsantsar kamalarsa ya fara takun dake tafiya da hankalin mutane,ta ko ina yayi staff na gaidashi cikin girmamawa.

Zabura Zahra tayi saboda ganin yana neman bace mata,wayyo Ni Zahra me na tsaya yi ne har yake neman bace min? Kema kallon haduwa da nutsuwa kika tsaya yi, zuciyarta ta bata amsar tambayarta,yamutse fuska ta yi kamar wadda tayi ido biyu da kashi,kafin ta ce", Allah ya kiyaye me wani abin kallo a wannan fuskar kamar danyen kosai", kafin cikin zabura ta bar maboyarta ta fito sarari dai_dai inda ta san zasu jiyota kuma su ganta, sosai ta daddage ta kurma ihu tare da zubewa a kasa ta shiga burgima cikin kankanin lokaci ta bata fuskarta da hawayen da dama ta gama tanadarsu,a ranta kuwa addu'a take tamkar zata sauke Alkur'ani duk dan hakanta ya cimma ruwa.

Take kuwa ta janyo hankalin mutane da dama kanta aka shiga tambayarta me ke faruwa?ganin babu wanda take bukata akanta yasa ta shiga wani irin abu kamar me farfadiya har da yi kamar zata shiɗe.

Yana dab da hayewa mahayarsa ya dan dakata jin hayaniya da kuma salatin da wasu suke yi cikin tashin hankali.

Cikin yanayinsa na rashin fara a ya juyo kadan yana duban gefansa inda jafar ke biye dashi kamar jela,kafin a hankali ya daga labbansa ya ce", meye yake faruwa atacan? Shima jafar din juyawa yayi ya dan kallo inda Zahra ke shimfide tana mateteguwa da wata irin zabura kamar me aljanu,sannan ya dawo da dubanshi kan ubangidannasa bayan ya sauke kanshi kasa yana cewa wata yarinyace ta fadi ina ga ko cutar jinnu ne da ita", dan jim AB ya yi har zai shige sai kuma ya fasa tare daga kafafunsa cikin nutsatstsan takunshi da kamar baya son taka ƙasar dan ko Zahra yafi ta takun natsuwa😄.

Take mutanen da suka yiwa Zahra zobe suka fara darewa dan bashi hanya.

Ita ko Zahra wata ajiyar zuciya ta sauke tana mai kara yin takatsantsan da kararanta dan kar rashe ya juye da mujiya, kallon yadda yake tafiya cikin nutsuwa da kuma dan zafin nama yasa taji kamar ta sheke da dariya saboda tunawa da rawar bonjo din da zai zo yana yi gaban staffs dinsa,da sauri kuma ta yi wata irin zabura ganin ya kusa ƙarasowa ta mike tare da nufarshi kai tsaye tana ihun ya taimaketa gasu nan zasu kamata.

A dai_dai lokacin ta karasa jikin shi ta kwamesa kana cikin Muryar kuka da fitar hankali take fadin astagfurullah zasu kamani Allah na tuba ka taimakeni", yadda take cukyikyisa da hannunta tana kuka sai ka rantse da gasken gamon tayi,aranta kuwa istigfar dinta ba ta komai bace sai ta rungumarsa da tayi,da sauri jafar ya matso dan rabata jikin ogannasa,sai dai kafin ya kai ga yin hakan, tuni Zahra ta nufi Hafsah da shigowarsu wajen kenan,nadiya ce ta rukota bata yadda sunyi mata rikon da kararan zai shafesu ba haka suka kamata su kayi can wani office da dake wajen tare da kwantar da ita suna mata fifita.

Shi kuwa AB tana sakinsa ya juya cikin dan sassarfar takunsa ya haye mahayarsa yana mai jin takaicin Zahra dan ji yake da yasan ita ce babu abinda zai kaishi gurin,shima jafar cikin takaicin Zahran ya bi bayansa da tunanin yasan dole AB din sai ya canja kayan jikinsa tunda dama akwai kaya a office dinsa.......

...........tun fa Ade yana dauriya har abin ya kasa daukar kansa,gashi babu inda yafi takura masa da mugun kaikayi irin matsematsinsa saboda tun kafin ya fara wankan nan ya shiga wankewa wai duk dan ya burge zahra ta ce yana da tsafta,da abin ya fi karfinsa take yayi fatali da kayan wankan ya zabura tare da cukyikyiye jikinsa da zanin da ya shiga dashi yana kwambo wai shi zaiyi wankan burgewa,da gudu ya fito daga bandakin yana ihu kamar wani sabon kamu, yayin da a gefe iyoka ta gama saita wayarta jira kawai take ta cika umarnin Zahra,tana jin ihunsa kuwa ta fara aikinta tana yi tana dariyar da ta kasa rikewa.

Wayyo jema a ku temaka Ade ze yi die pls help me my body, my body is pain oh no my body is hurting and hurts pare,saboda tsananin kaikayi har yana tunanin wuta ne a jikin gaba daya baya tantance kaikayi da zafi,da sauri mama da bacci ya dan fara dibarta ta fito tana zabga salati tare da tambayar abinda ke faruwa? Iyoka ce ta bata bayani akan cewa kawai gani tayi ya fito daga bayi yana ihu,kafin kace me yarbawa da gulma tuni gida ya cika kowa yana kallon Ade da shi da tsirara basu da maraba,shigowar lola yasa kowa ya dare ya bata hanya,kamo shi tayi tana kokarin turashi daki saboda zanin dake daure ajikinshi tuni ya fara kokarin yin takansa hakan yasa dole ta turashi daki ba tare da ta kulawa kowa ba.

........Zahra na kyalla ido ta tabbatar AB ya bar wajen har ma da mutanen da suka dan taru kowa ya fashe ya koma bakin aikinsa,mikewa ta yi tana yamutsa fuska kafin ta karɓe dankwalinta gurin Hafsah tana cewa gida zan tafi", nadiya ta ce dama Zahra dan kawai kina son tafiya gida ne yasa kika yi wannan abun? Duba fa kiga yadda kika yiwa oga AB duk kin bata masa jiki", harara ta watsa mata tare da yin tsuka ta ce", to gulmawiya nayi din ina ruwanku kunga nifa gida zan tafi kuje ku cigaba da aikinku masu tsoron kora kawai,Hafsah bata ce komai ba ta fita daga wajen nadiyar ma Binta tayi dan sun tabbatar suka biyewa Zahra Dukansu zasu iya asarar aikinsu,dan haka salin alin suka rabu da ita suka koma wajen aikinsu.

Sai da ta tabbatar sun bace daga gurin sannan ta fito a hankali cikin sanda,ta dubi gabas kudu arewa yamma taga babu kowa sai jama kadan kadan da suke harkokinsu, dariya tayi tana cewa Wallahi dole sai naga rawar shokin da oga zai debo yadda zan fi tabbatarwa kuma hankali na ya dan kwanta nasan cewa Nima na fara dan ramawa,tana gama fadin haka ta zare Safar hannunta ta yar ta kimtsa kanta tare da aro nutsuwa, sannan kai tsaye ta nufi mahaya.

Ga tsananin sa ar Zahra babu wanda ya hanata nufar bangaren oga AB din securitys kansu basu hanata ba, abinda ya dan so sata taji kamar ta koma kenan amma dai ta daure ta karasa har office dinsa da babu sectary.

Tsayawa ta yi tun bayan shigarta office din farko ta makale a jikin kofar office din tana sauraron ko zata ji ihun Oga AB...

A hankali ya maida idanunsa ya lumshe yana kokarin daure abinda yake ji a ta can wuyansa dai dai kasan keyarsa da yaji Zahra nata mulmulewa a dazun, sai hannunsa da nan ma ta taɓa, kokarin kawarwa yake amma abin ya gagara hakan yasa ya mike cikin nutsuwa,kai idan ba bude baki yayi ya gaya maka yana jin wani abu ba ba zaka taba fahimta ba,idan ya fada din ma zaka iya ƙaryata shi,saboda tsananin yadda yake a kamensa babu wani abu na zautuwa ko firgita a tare dashi.

Kai tsaye toilet ya nufa ya sakarwa kansa shaya wadda ke zuba tun daga saman kansa har zuwa tausasan kafafunsa da kamar ba a taka su a kasa,be ji wani abu ya ragu ba sai ma karuwa da yayi towel ya janyo ya daurashi a kugunsa ya fito fatarsa na digar ruwa tare da azabar radadin dake ratsashi har ƙwaƙwalwa.

Gatsine fuska Zahra dake labe ta yi tana fatan ta ji wani abu da zai bata tabbacin yana cikin wani hali,kai anya kuwa ba sumewa yayi ba sufa irin yan gayunnan jikinsu baya daukar tashin hankali da sun fara ji suke sumewa bari kawai na shiga idan suma yayi sai na zuba masa ruwa ya farfaɗo na kalli yadda zai ta soshe soshe", tana gama sambatunta ta murda marikin kofar cikin sa ar da take da ita a yau din kofar ta bude dan ba a rufe take ta ciki ba,ita kuma tana shiga yanayin yadda ta rufe ta yasa ta rufe gaba daya wanda dole sai an budewa na waje.

Yana zaune a nutsensa sai dai yadda idanunsa suka sauya a yanzu shi zai baka tabbacin cewa yana cikin wani hali,turus tayi tana kallonsa cikin tsoro da danasanin shigowa yanzu haka ma tuni ya sha maganinsu na.masu kudi ya warke Ni kuma gashi na zo zan fallasa kaina wayyo Ni Zahran kaka ya zanyi?

Kin zo kiga ko na mace?

Ya fada can ƙasan maƙoshinsa, yana mai ware manyan idanunsa da suka rine a saman Tata fuskar.

Umm umm dama zuwa nayi umm nayi maka godiya.. s...n....maganar tuni ta kakare ganin yadda ya mike tsaye tare da nufota daga shi sai karamin towel din jikinsa fuskar nan babu alamar rahma bare imani.

Ja da baya ta fara yi idanun nan tuni suka raina fata tsoranta sosai ya bayyana amma duk da haka kokarin danne shi take yi,dan haka cikin TSIWA ta ce", wai me hakan zaka yi? Kar ka sake ka ƙaraso inda nake idan ba haka ba zanyi maka ihun kwar....kan ta karasa fadar abinda zata fada ya cimmata,cikin low voice dinsa ya ce", zaki ji abinda naji ne,a maimakon gani da kika zo yi kinga gara kiji hakan sai ya fi,daga nan sai ki bani magani",

Zaro ido ta kuma yi cikin karfin hali ta ce", wane magani zan baka ?

Tayaya zan baka magani bayan bani nayi maka abu ba,kaji min mutum Ni kam kar ka ƙaraso inda nake..

Ta fada tana kif_kifta manyan idanunta da har yanzu suke cike da jarumta duk da cewa zuciyarta kiris ya rage a ganta a waje saboda tsananin tsoron abinda zai yi mata......✍🏼

Kai AB me kuma kake shirin yiwa zahranmu?

Ade na tausaya maka irin sosai dinnan fa🤣🤣

Up up up ayi comments na cigaba da suburbudo muku taadin Zahra da Ab🤣

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol