Free chapter · Read without an account
Pg 12
.........bai jima da shiga office ba, duk da dama yau din bai shiga Company da wuri ba saboda hospital da ya fara ziyara.
Turo kofar office din tare da sallama baisa shi dakatawa daga taba tap din dake gabansa ba,a can ƙasan maƙoshinsa ya amsa tare da fadin welcome dad", zama dad din ya yi yana amsawa cikin annuri kafin ya dora da cewa Tom dad son gani Ni na biyoka harma da guzurin sectarea", uffan bai ce ba, shima dad din bai matsa ba dan dama bai yi magana dan yana da tabbacin zai tanka masa din ba,ci gaba yay da cewa dole ne zamanka sai da sectarea duk da dai kai kana ganin bata da wani muhimmanci a gurinka saboda kana da jafar amma.....dagowar da Ab yayi yasa dad yin shuru dan yasan meye ma anar kallonnasa maganarce ta yi masa yawa,a hankali ya dan lumshe idanunsa kafin ya kuma bude su a kan dad din yana cewa is ok tunda hakan ya maka",
Mikewa dad din ya yi yana cewa na wuce sai ka shigo amma kayi kokarin zuwa ganin filin nan a yanzu dan bamu jima da yin waya da hamis ba", ok kawai ya ce yana mai ci gaba da abinda yake yi,fita dad din yayi.
Inda ya ce", siyam ta zauna a nan ya sameta, tana ganin dad din ya fito ta mike ta tare shi da cewa dad ya amince kuwa? Dariya dad yayi yana cewa siyam ta zama sectarea din Ab daga yau zaki fara aikinki dama na gaya miki komai zai tafi daidai", cike da farinciki siyam ta rungume dad tana cewa thanks dad I'm happy",bubbuga bayanta yayi cike da so, daga nan ya umarceta da ta zauna idan ta dawo gida zai nuna mata duk abinda ya dace ko yasa jafar ya nuna mata,ok dad se na dawo daga haka ya fita daga ofishin yana fatan siyam din ta dinga samun ko kallon arziki ne daga AB din.
Ko cikkaken minti ashirin dad baiyi da fita ba,jafar yazo ya shige shima bai jima ba sai ga shi ya fito, AB dinne a bayanshi tsayawa yayi ya gama fitowa fuskar nan babu alamar fara a a tsuke tamkar bai taba sanin meye murmushi ba, sannan jafar ya rufo kofar yana mai saurin bin bayansa dan har ya fice daga main falon office din cikin takunsa dake cike da nutsuwa amma akwai karsashi a cikinsa.yadda ogansa bai nuna yasan da wata halitta a gun ba shi dinma hakan ya yi.da kallon takaici ta bisu kafin tayi kwafa tana aiyana yadda zata juya AB muddin mammanta ta je wajen me sasuba,ajiyar zuciya ta sauke tare da janyo takardun da ta gani bisa teburin ta fara dubawa.
Da sauri jafar ya bude masa mota ya shiga,jasuwa yaja motar bayan jafar ya zauna a gefansa take suka fice daga cikin Company gaerd dinsa na biye dasu a baya.
............gudu Zahra take tana waiwaye har dai karfinta ya fara karewa lokaci daya suka cimmata,kokawa su kafara da ita har da su cizo amma ko ajikinsu burinsu kawai su cika aikinsu tunda an biyasu,cak suka dagata daya daga ciki ya dorata a kafada,duka da yakushi kuwa babu wanda basu sha ba,sosai ta jigatasu dan dakyar suka samu damar daure fuskarta da kyalle,daga nan suka Kaita can karshen bayan gari wajen sabbin filaye da gonaki inda Ade ya umarcesu su Kaita.
.....a nan suka samu Ade cike da kaguwa,bakinsa a washe ya nufosu, baiyi magana ba dan kar Zahra taji muryarsa,sai sune suka ce oga sai fa ka kara mana canji dan wannan yarinyar ta wahalar damu gaba daya jikinmu taban cizo da yakushinta ne",nuni yayi musu da kar su damu zai kara musu,nuna musu yayi dasu daure masa ita a jikin bishiyar dake gurin ,aiko wajen daure tan ma sai da suka sha artabu,daga karshe dai sun samu nasarar daureta,daga nan suka tafi sukasa a gun.
Lashe baki ya fara yi yana kallonta zuciyarsa cike da mugun nufi,nufarta yayi ba tare da tunanin komai ba ya fara kokarin afka mata.
..........a hankali lafiyayyun motocin suka fara danno hancinansu zuwa cikin hanyar da zata sada su da bangaren manyan filayen da zasu je dan yin cinikinsu.a nutse jafar ya fara nunawa jasuwa hanyar da zasu bi daga nan din,yana yi yana waya da dillalan da suke kwatanta masa hanyar.
.........garin kokawa Zahra ta zame kyallan dake fuskarta sai ga fuskar Ade tar akan tata fuskar,waro manyan idanunta ta yi cike da mamaki kafin ta ce", Ade kai ne? Idanu ya fara zazzarowa dan har ga Allah bai so Zahra ta gane shi ba,dan shi dinma fa yana tsoronta dan yasan tana da hanyoyin gasawa mutum aya a hannu,dan haka cikin borin kunya ya fara hargagi Ni ba Ni ne ba Ni da na temakek....kafin ya rufe baki Zahra ta kurma wani uban ihu saboda ganin motocin da.suke wucewa shimfida shimfida,da sauri Ade ya fara kokarin kwance Zahra ya gudu, a maimakon ya gudu amma saboda rudewa da shiga firgici sai ya kama kwanceta ita ko take ta kuma samun dama ta kanainaye shi kamar irin suna kokawa tana son kwatar kanta...shi ko Ade bai fahimci komai ba hasali ma bai kula da motocin da suke shigewa ba......
.........sosai ihun da Zahra ta yi ya shiga kunnensa, suma sunji sai dai basu bawa abin hankali ba,sai kuma suna gab da shigewa wajen suka kuma jin ihun harda neman temako,jasuwa ya ce", jafar baka ji kamar ihun mace ba? Naji wlh ina ga da akwai abinda ke faruwa", basu yi kokarin tsayawa ba saboda ogan bai bada dama ba,har sun cigaba da tafiya can kuma kamar me rada can ƙasan makoshi ya ce", ku dakata", wani irin burki josuwa ya taka saboda saurin bin umarnin oga,ganin sun tsaya sai sauran ma suka tsaya, jafar da josuwa ne suka fita dan duba abinda ke faruwa.
Da sauri suka karasa gun da Zahran take Ade har ya gama kunceta,josuwa yayi ihu yana cewa oh kidnapper ku rike shi kar ya tsira,"tuni jikin Ade ya fara karkarwa har da sakin fitsari a wando,tuni josuwa ya cafke shi ya dankawa gerd din shi,jafar kuwa sarai ya gane Zahra dan haka bai ce da ita komai ba dan yasan kadan daga cikin halinta,tashi ta yi tana kuka tare da cewa ba kidnappin dina yayi ba fyade zai yi min," kai tsaye suka tasa ƙeyarsa ita kuma jafar ya dubeta tare da cewa sai ki dinga sanin irin mutanen da zaki taba,da har zata murguda masa baki sai kuma ta fasa ta marairaice fuska dan Allah kar ka ku barni anan ku taimaka ku fita dani ko bakin hanya ne wlh bansan hanya ba,banza ya yi mata sai ma shigewarsa da yayi yana cewa mun yi miki iya temakon da zamu iya miki,"
Binsa ta yi da kallo me dauke da hararar kasan ido ba tare da ta bari ya gani ba.
Jafar ya bude zai shiga Mota kenan kamar daga sama yaji nutsatstsan sautin muryarsa a can ƙasan maƙoshinsa tamkar wanda akayiwa dolen yin maganar ya ce", ku taho da ita nan",ware idanu jafar ya yi amma dake bashi da damar musawa ko nuna masa baiji abinda ya fada din ba yasa shi komawa in da Zahra take tsaye idanunta kamar zasu fado saboda hararar da take antayawa su jafar din kamar ba wadda tasha da kyar ba.Zahra ko a bakin kura take ai sai ta yi halin 😄.
Tana ganin jafar din ya nufota ta yi saurin daidaita tsukakken bakinta da take ta faman murgudashi ta maida kanta kalar tausayi saboda yanzu temakon take bukata dan haka dole ta sauke kai,kizo muje", jafar ya fada yana juyawa, bin bayansa ta yi tana cewa ayya na gode ai dama nasan duk me imani baya tafi ya barni a gurin nan ba", daidai sun ƙaraso bakin motar bude mata kusa da Ab yayi ya yi mata alamar ta shiga,ran jafar cike da mamakin Ab din da ya bada umarnin ta shigo motarsu,ba tare da ta duba wanda ke hakimce cikin motar ba ta shiga tana mai lumshe idanunta tare da bude kofofin hancinta tana shakar daddan kamshin da take ji kamar ta sanshi.
Sai da jafar ya rufe motar shima ya shiga suka fara tafiya, sannan ta bude idanunta da suke rufe tana emagin ita ce me motar nan.
Dan zabura ta yi ganin wanda ke gefanta cikin tsare gida kamar yadda kowa yasanshi,hannunsa akan tap dinsa da yake kan cinyarsa yana faman latsawa cike da kwarewa,tamkar ma bai san da wanzuwarta a gefansa ba.
Kai anya kuwa ba shiryawa kuka yi kai da Ade ba? Anya ko ba kai ka dauki nauyin shirinnan ba?
To idan ba haka ba ya a kayi kasan Ade ya sace Ni yana so yayi min fyade saboda kararan da na zuba masa a ruwan wanka?
Tamkar da kurma take magana dan babu wata alama da yayi wadda zata shaida yana jin duk abinda take fada ɗin.
Bata saurara ba ta cigaba da cewa Wallahi to duk dinku nafi karfinku daga kai har shi ɗan beyerabiyar me karyar musulunci kuma ana fita wajen gari ku sauke Ni na tafi gida.
Wato shi zai yi min fyade kai kuma Allah masani", ta fada tana murguda bakinta tare da kai masa hararar gefen ido.
Jafar ne ya kasa daurewa a dan fusace ya juyo ya nunata da yatsa yana cewa ke anya ko ba daga turu kika fito ba?
Kan balastin Ni kake cewa mahaukaciya?
Kallon da Ab yayi masa ta ƙasan ido ne yasa shi hadiye sauran abinda ke bakinsa ya juya yana kallon hanya zuciyarsa cike da haushin Zahra ,shi ya rasa abinda yasa oga yaki bari a sallami yarinyar nan daga aiki yarinya sai shegen raini da tabara.
Babu wanda ya kulata har ta gaji ta sawa bakinta gum sai yan harare harare da murguda baki da ta kasa dainawa.
Tana cikin motar suka kulleta suka fita su kayi abinda ya kawo su,ko da suka dawo kasa cewa komai ta yi dan tuni ta fahimci so suke su maida ta mahaukaciyar da suka ambata.
Suna fitowa cikin gari kuwa josuwa ya taka burki tare da cewa to Madam zaki iya tafiya Allah ya kiyaye gaba",Amin idan da gaske kake ta fada tana mai ficewa daga motar,ƙasa ƙasa ya bita da kallon da babu wanda zai fuskanta kafin ya maida idanunsa ya rufe ruf tamkar me bacci.
Wata kakkarfar ajiyar zuciya ta sauke tare da shafa fuskarta tana cewa oh Ni Zahra yar balaja U yau naga rayuwa ,ko ina suka kai Ade kuma oho Allah yasa ma yana hannun yansanda da wallahi sai ya gane kurensa dan sai na sa yayi zaman kaso.
A kofar gida ta ci karo da iyoka, tana fama Safa da marwa ta kasa shiga gidan bare ta fada abinda e faruwa ,tana cikin tsaka me wuya Allah ya kawo mata dauki ta hanyar dawowar Zahra.
Da sauri ta nufeta tare da rungumeta tana cewa sannu Zahra ina fata basu yi maka komi ba ko?
Kar ki damu iyoka babu abinda ya same ni amma kinsan wani abin mamaki ?
Girgiza kai iyoka ta yi, Zahra ta rike baki cikin nuna mamakinta ta ce ", Ade ne fa yasa a dauko Ni zai min fyade", waw Ade Zahla? Iyoka ta tambaya cike da tsoro me hade da mamaki,jinjina kai Zahra ta yi tare da cewa iyoka muje idan na samu kaina zan baki labarin abinda ya faru", daga nan suka shige gidan kowa ta nufi hanyar dakinsu
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*