Free chapter · Read without an account

Pg 14

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

......a can bangaren zahraddin kuwa shima sauri sauri yake yi ya ƙaraso makarantar su Zahra ,dan yana lissafe da ranar candinnasu saboda ita ya bibiyi time tables din exams din, wannan ne yasa yasan ranar da lokacin fitowar su.

Abunka da garin yarbawa babu wanda ya damu da abinda su Zahra suke yi, abu daya ne yasa mutane suka ji haushinsu har suke Allah ya isa su canja hanya shine tsare musu hanya da akayi bayan kuma wannan titin shine Babban titin da zai hadaka da dayawan anguwannin cikin garin.

Oho su basu san ma a nayi ba,dan sosai suke shan shagalinsu,har da masu kida da jarkoki suna yi suna bin wakar da akayi musu ta candy,Zahra kuwa kallo daya zaka yi mata ka kasa rike kanka daga dariya saboda yadda ta bata fuskarta idan ba kyakkyawan sani kayi mata ba walle ba za ka gane ta ba,ita ce oga a oan dukkan wani sha ani na tsokana dan tana sane tasa a rufe hanya.

Nadiya ce ta dan yi mata rada a kunne,Zahra ki bar mutane su wuce haka kar a samu wani mara hakurin azo ana tashin hankali ", a dan fusace Zahra ta wurga mata harara kafin ta dauke kanta tana mai ci gaba da zane fuskarta da koren fenti, sannan ta ce", au wai dama baki san tashin hankalin nake nema ba shi yasa na datse hanyar? To idan baki sani ba yanzu kin sani kar ki kara shiga min hanci da kudundune na gaya miki,"daga haka ta cigaba da tsallenta da wake wakensu na yan candy.

Dole nadiya taja bakinta ta tsuke amma ta tabbata ba za a bar gunnan lafiya ba, ba tare da anyi fada da Zahra ba.

.....a bangaren Abban zahraddin kuwa shima yau din ya gama shiryawa zuwa gidansu Zahra,dan haka shima a daidai wannan lokacin suna tare da Abban zahra,sosai Abba ya karbe su karba ta mutunci wadda tasa Abban zahraddin yaji a ransa zai hada zuri'a da mutanen kirki,shima Abban zahra yaji dadin wagga batu na son aure masa Zahra yar balaja unsu,dan haka take ya bawa zahraddin auren zahra har da karbar kuɗin zance(anya Abba ba kayi mana azarbabi ba😄)....

......tun daga nesa josuwa da jafar suka hango motoci da babura zuwa kan okada sai canja hanya suke suna faman zabga tsaki tare da kananun maganganu.

Me ke faruwa ne? jafar yake tambaya duk da yasan babu wanda zai bashi amsa",josuwa kuwa bai daina tunkarar wajenba har sai da suka zo suka ga abinda ke faruwa,babu wata doguwar tazara tsakaninsu dasu zahra saboda traffic din ya ragu sosai sai wadanda dole nan din ce dai hanyarsu kuma suna jin kyashin yin zagaye saboda takaicinsu ZAHRA..

Suma su Ab nan dince dole hanyarsu idan ba haka ba kuwa sai dai su yi mugun zagaye me nisan gaske,ga kuma Ab din cike yake da gajiyar tafiya dan su shaida ne akan Ab baya son doguwar tafiya amota shi yasa duk rashin nisan tafiya in dai ba acikin gari ba to a jirgi zai tafi,shuru su kayi duka kowa ya kasa cewa komai, idanunsu gaba daya akan titin suna kallon yaran da suke Shagali da kuma tunanin hanyar da zasu bi dan yaran su basu hanyar da zasu wuce.

Shiko uban gayyar ko da alama ba zaka ce yasan wainar da ake toyawa ba,hasalima kwance yake a bayan shimfidediyar motar me kama da jirgin sama(saura kuce nayi kauyanci)idanunsa a lumshe kamar wanda yake bacci me nisa,nan ko idanunsa a bude yake tar, yana kuma kallon komai ta ƙasan mayun idanunsa masu haske da sheki tamkar idanun ashwariya(team Zahra Kar kuji haushina gaskiya na fada)dake motar ba irin motocinmu na yaku bayi ba ne,babu wani abu da take biyewa sai dai na waje ne bai isa ganin na ciki ba,amma kai da kake ciki komai nisan abu zaka iya ganinsa ba tare da ka yi dage ba.

Shima zahraddin tuni ya zama daya daga cikin mutanen dake wajen, duk da cewa shi ɗan Zahra ya zo kuma hanyar magana da ita kawai yake nema,ko da zata maida masa da bakaken maganganunta,fita yayi daga cikin motarsa kai tsaye ya nufi inda su Zahran suke, bakinsa dauke da addu'a dan tunkarar irinsu Zahra sai da komawa ga Allah.

Ganin zahraddin ya nufi wajen su Zahra,hakan yasa shima jafar ya fita ya nufi inda suke dan a tunaninsu shima zahraddin din hanyar yake bukata,sai dai karasawarsa gurin ya gane ba hakan ba ne daga zahraddin dan kuwa zahraddin din yana zuwa ya ambaci sunan Zahra da my love congratulations", ɗif Zahra ta yi daga shagalin da farincikin da take ciki tare da juyowa ga zahraddin wanda jafar ke tsaye kusa da shi yana jira ya gama nasa shima yayi abinda ya kawoshi,shi sam bai gane Zahra ba saboda yadda ta bata farar fuskarta baka ganin komai sai fararen kwayar zagayayyar idanunta masu shep din kwaiduwar kwai sai girmansu ya kara bayyana,sai idan ta yi magana zaka ga fararen jerarrun hakoranta masu dauke da siririyar wushirya sun bayyana.

Wani kallon banza ta watsawa zahraddin kafin ta nunashi da yatsa tana cewa kai wai wane irin mayene?,me yasa kake bibiyata? To ina so kayi gaggawar barin gurin nan idan ba haka ba zaka barshi cikin bakinciki dan Ni kam babu abinda zan bari ya bata min wannan farincikin da nake ciki ehe", ta karashe maganar da wani irin juya fararen idanunta da murguda bakinta,tana mai ci gaba da harkar gabanta.

Ganin haka da jafar ya yi yasa ya fara kokarin barin gurin dan duk da bai gane Zahra ba, tabbas yasan ba zasu karke lafiya ba,dan shima zata iya cewa sonta yake tayi mai rashin ta ido gaban jama a,har ya juya da niyar barin gurin sai kuma ya tuna tare fa da oga AB suke ,gara kawai ya sauke kai ya roka kome a kayi masa zai jure in dai akan oga AB ne,sai yanzu yake kara ganin muhimmancin gerd dinsu da Ab baya son yawo dasu,da wannan tunanin ya koma inda Zahra suke ,har alokacin kuma zahraddin yana tsaye a gun duk da yadda yan candyn keta sha aninsu suna tuttureshi amma ko a jikinsa,shi kansa jafar din dakyar ya karasa gun Zahran saboda yaran da suka kuma cuccushe hanyar.

Pls dan Allah kuyi hakuri ku bamu hanya mu wuce saboda nance kadai hanyar da muke da...kallon da Zahra ta watsa masa da manyan idanunta ne yasa shi kasa karasa abinda yake da niyar fada,(ina gaya muku idanun Zahra duniya ne shi kadai yake sa aji shakkarta sai kace wata babba)tsaf Zahra ta gane shi dan haka ta ji wani dadi a ranta dan tasan ranar ramuwa ce tazo,rike kugunta dake daure da hijab dinta ta yi sannan cikin sanyin murya ta ce", idan anki kana da karfin da zaka ture mu? Kut jafar ya fada ba tare da ya karasa ba,saboda tunawa da yayi shike nema a yanzu,dan haka ya kuma sauke murya ya ce", dan Allah ku bari mu wuce sai ku cigaba da abinda kuke yi uzurine muke dashi me muhimmanci", ka taba ganin inda wanda aka kwanto daga turu yaji lallami ko magiya? take jafar ya gane Zahra amma sai yayi kamar bai ganetan ba ya cigaba da rokonta,amma yarinyar nan fir ta dage ba zasu matsa ba,sai ma bakaken maganganu da take ta yaba masa duk na son rama abinda ya yi mata wanda kuma ogansa ne ya shafa masa.

Da dai taga ba zai rabu da su ba sai kawai ta kurma ihu, tana cewa wayyo jama a korto ku taimake mu", kafin kace me 'yan makaranta sunyi kan jafar da zahraddin da duka kamar Allah ya aikosu..

Komai akan idanunsu ya faru, dan haka cikin sauri josuwa ya kira wayar gerd dinsu,dan su kawo dauki ,dan shi ya kasa fita tsoro yake ji kar a hada dashi dan Sarkin yawa ya fi Sarkin Karfi.

Wani irin taune pinkinsh lips dinsa ya yi tamkar zai hudasu,idanunsa kawai zaka kalla ka fahimci ya kai makurar harzuƙa duk da cewa kuwa babu wata alama da ta nuna ya ma san abinda ke faruwa a tawajen....

Josuwa kuwa kira ya cigaba da yi akan su yi sauri kar yarannan su raunana jafar,bai ankara ba sai ji yayi kawai Ab ya fice daga motar cikin takunsannan me kama da zakin da yake neman abinci.

Cikin nutsuwa yake tunkarar wajen, duk inda yasa ƙafarsa sai kaga ana darewa,wani irin kwarjini da haibarsa ya dinga sawa yaran suna yin kasa da kansu wanda babu su a dukan,a cikin haka ya karasa har inda suke dukan su jafar Zahra na gefe tana share hawayen karya, sai ta faki idanun mutane tayi musu gwalo.

Yana zuwa kamar daukewar nefa haka su ka dakata da dukan su jafar da suka kasa kwatar kansu,wani irin kallo ya watsa musu wanda yasa babu shiri suka fara kokarin guduwa sai dai kuma kafin su yi wani yunkuri,tuni gerd dinsa da karasowarsu kenan suka fara kama duk wanda suka gani a gurin take kowa ya fara kokarin yin takansa.

Su nadiya ma sulalewa su kayi suka gudu tun fara dukan su jafar din dan basa so jafar din ya gansu wata ran ya zukulo su a Company a Koresu,dan haka koda Ab ya karaso basa gurin.

Zahra ma kokarin guduwa take yi,amma kafin ta daga ƙafarta taji anyi wa hannunta wata irin danka tamkar za a karyata,waro manyan idanunta da su kawai ake iya gani ta yi tare da kokarin kwatar hannunta daga rikon tsaurin da yayi masa,sai dai ko gezau baiyi ba.

Janta ya shiga yi ganin tana ciccigewa zata bata masa lokaci sai kawai ya sunkuya ya sunkuceta tamkar wata yar baby bisa kafadarsa....

Watsa ta yayi cikin motar a lokacin jafar ma ya shiga yana faman maida numfashi kamar wanda yayi gudun shekara a kafa.

Wai ina zaka kaini? Ta fada cikin tsawa idanunta na son zubda hawayen fargaba amma tana kokarin janyowa kanta karfin hali dan sam bata son Ab yaga gazawarta bare yayi tunanin ya cinyeta wasa.

Zahraddin kuwa duk da yadda jikinsa ke tsami hakan bai hanshi shiga tashin hankalin ganin an dauke Zahra ba,dan haka ba tare da tunanin komai ba ya figi tasa motar ya bi yabansu jafar da suka yi nisa saboda gudun da josuwa yake fafarawa bisa umarnin uban gida AB.........✍🏼

To Ab me kake nufi?

Ina zaka kai mana ZAHRA ?

Da fatan dai ba wani abu za kayiwa zahranmu ta mutunci ba😄?

Zahra ya haka da sa a doke mana ango so kike yayi angonci da tabo ne?

Muje netx pg dan jin ya zata kaya.

Wai shin ya Zahra Za taji idan tasan an karbi kudin aurenta?

Wane hukunci Ab zai yiwa Zahra akan dukan pa dinsa da su kayi?

Karfa ku manta har yanzu Zahra bata san oganta BEYERABE ne ba🤣

Dan haka kuwa akwai ƙura,

Dan Allah kuyi comments ko na samu kwarin gwiwar yin pg na gaba 🙏

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol