Free chapter · Read without an account

Pg15

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

........ sosai hankalin Zahra ya tashi amma duk da haka taki ta nuna hakan a fuska.

Malam ku sauke Ni na tafi gida ban son reni", idan ke da kike karatu kin tanka to sun tanka mata,bare kuma Ab da yayi tamkar baya cikin motar,yadda taga sun manna mata hauka yasa dole ta yi shuru tana faman zare manyan idanunta da suka kara haske saboda bata fuskarta da ta yi.

Sosai su kayi tafiya me nisa kamar zasu bar garin,kafin lokaci daya taji josuwa ya taka burki,jafar kuma ya fito fuskar nan kamar an aiko masa uwarsa ta mutu.

Bude bangaren da Zahra take ya yi tare da yi mata nuni da ta fito, zaro idanunta ta yi kafin cikin ƙunkuni ta ce", wannan ai wulakanci ne ya za ai ku kawoni inda tunda uwata ta haifeni ban taba zuwa ba kuma kuce na fito, ina zanje? Ta ina zan koma gida a wannan dajin Allah da ko bera banga alama da akwai ba? Koma yaya ne ke kika sani ki ma godewa Allah da hukuncinki ya tsaya iya nan", ta bude baki zata kuma yin magana kenan taji tsayayyar muryarsa ta daki kunnenta,cikin salon maganarsa na me kamar yana koyan hausar ya ce", get out before counting five", da sauri ta dube shi sai dai kuma tamkar bashi yay maganar ba dan har yanzu idanunsa na akan tab dinsa da yake dakilarta tamkar dole.

Fuuu ta fita daga motar tare da buga kofar da karfi idanunta na cika da hawayen da take ta dannewa bata son su gani bare su ce ta karaya har su samu abin yi mata dariya.

Wata irin figa josuwa ya yiwa motar cikin sakanni suka bar gurin ko kurarsu ba a hangowa.

Kure sawayen motar da kallo Zahra ta yi, zuciyarta na yi mata wani irin tururi tamkar ana babbaka kara,wai shin me zata yiwa wannan bawan Allah ta huce irin bakincikin da yake sata a ciki?

Cikin kunar zuciya ta kawar da idanunta daga kan hanyar da suka bi,tare da cije lips dinta har sai da taji alamun gishiri_gishiri dake nuna cewa ta hudashi, wallahi BAZAN Barka ba, wannan abun duka bashinsu kaci kuma sai ka biya,domin BAZAN taba bar maka wannan bashin gabar ba,mugu kawai dan gidan masu jajayen kunnuwa(ke kuma yar gidan masu bakaken kunnuwa ba).

Zahraddin ne ya faka motarsa a gabanta cikin fatan ta amince ta shiga ya maida ita gida.

Fitowa yayi daga motar ya tsaya a gabanta cikin dan karkatar da kai na neman a tausaya masa,ya ce", pls kizo na maidaki gida gurin nan bashi da kyau a kwai yan fashi da makami sosai zamu iya shiga matsala idan bamu yi gaggawar barin gurin ba", dubansa ta yi cikin son sauke fushinta akansa ta ce", wai kai wane irin maye ne,to Ni dai wallahi kurwata kur,idan banda rashin zuciya ya za ai nasa a yi maka irin wannan duka amma ka cigaba da bibiyana kai gaskiya ina da shakku akanka", ta karasa maganar tana mis mis da baki daga dukkan alamu addu'ar neman tsari da Mayu take yi.

Duk da haka bai karaya ba ya cigaba da yi mata magiya, amma Zahra ko kallo bai isheta ba dan yanzu ta kanta take sosai take addu'ar kubuta daga sharrin Mayu dan da gaske ta fara shakka a kan zahraddin ɗin,sai dai kuma Acan kasan ranta cike take da tsoron hanyar da ma tunanin idan ta bari ya tafi ya za tai ta koma gida,hakan yasa ta yanke shawarar shiga motar,ba tare da yayi tsammani ba ya ji ta bude motar a fusace ta shiga tana ƙunƙuni tare da cigaba da addu'ar ta a fili har da tofawa a kusurwar motar hadi da shafawa a jikinta, duk zahraddin yana kallonta amma bai ce komai ba,hasalima bai bawa abinda take muhimmancin da zaisa ya damu ba.

Da gudu shima yaja motar, zuciyarsa fes gashin ga rabin ransa,yau kwana uku da haduwarsu da Zahra amma ji yake kamar ya shekara goma da sonta a ransa shi yasa baya wasa da dukkan abinda ya shafeta,ko da zata sa a kuma zanesa.

Zahra bata saida addu'a ba har sai da taga sun shigo layin anguwarsu ta yarabawa Sannan ta sauke ajiyar zuciya,duk da cewa ta yi mamakin ganin yadda yasan gidansu amma bata tsaya tambaya ko bi kadi ba,ta fita daga motar ba tare da ko waiwayensa ta yi ba.

A soron gidansu ta ci karo da su nadiya zasu fito daga gidan,kallo su ta yi sannan ta yi kwafa ta bi gefensu ta shige ba tare da ta kula ko waccensu ba.

Da kallo suka bita jikinsu na yin sanyi haka nan Allah ya sa musu kaunar Zahra shi yasa basa son abinda zai shiga tsakaninsu,yanzun ma zuwa su kayi dan suga ko ta dawo gida amma sai suka samu ana nemanta an kawo labarin wai wasu sun saceta,tun dazu mama da Abba suke bin layi layi gida gida nemanta,kaka tana gidan sun kasa gaya mata saboda suna tsoron tashin hankalinta.

Kasa fita su kayi suka bita cikin gidan.

Zahra na shiga mama dake kuma yafa mayafi cikin dabara tana son kuma fita duba Zahran ba tare da kaka ta ankara ba,ta tsaida idanunta akan Zahra kafin ta bude baki ta ce", Zahra daga ina kike? Aka ce wasu mutane sun sace ki? A'a ma Ni ba wanda ya sace Ni ,wani maye na hadu dashi kwana biyu da suka wuce shine fa yake ta damuna,yanzu ma nacinsa ne yasa na shigo ya dawo da Ni gida", ajiyar zuciya mama ta sauke tare da zare mayafin jikinta tana cewa ki shiga kaka tun dazu take jiran dawowarki,kuma nadiya ku shiga ciki bara na karasa girkinnan",Tom mama suka fada suna bin Zahra dako kallo basu isheta ba.

..........daga inda suka ajiye Zahra gidansa dake can bamfaya estate suka wuce dan ya dan samu hutu.

BAZAN iya bayyana muku irin haduwar da gidan ga yayi ba, tabbas masu kuɗi suna hutawa,idan kaga rayuwar da suke yi ba zaka taba cewa suna da wata damuwa ba, luxerys House kenan,sunan da ya dace dashi kenan.

Kai tsaye hadaddiyar room dinsa ya shige,ya Wada bath ya sakarwa kansa shaya idanunsa a rufe ,yana son kawar da takaicin Zahra da duk abinda ya shafeta.

........wani irin kara me hade da kuka Zahra ta saki tare da burgima kamar wadda ake cirar ranta,da gudu matan gidan suka shigo dakin har da mama da jiyo karar kawai ta yi kamar saukar aradu,lafiya de Zahla cewar yarbawan gidansu.

Kaka da su nadiya da suke dakin kuma suka san abinda ya faru tsuru_tsuru su kayi suna kallon Zahra.

Mama ce ta kuma tambaya,wai me yake faruwa kike mana irin wannan tabara haka?nadiya ce ta yi karfin halin bata amsa da cewa mama wai daga kaka tace mata amarya yau dai anyi Kandy kuma ta zama amarya yanzu ba da jimawa ba masu kawo kudin aurenta suka fita,shine kawai muka ga tasa ihu ".

Kaka ta ce", wai dama bata sani ba?

Me hakan ke nufi?

Auren dole zaku yiwa jikkata?

To wallahi baku isa ba babu wanda zai yiwa batula auren da bata so,ai ba neman kai muke da ita ba,idan kun gaji da ita Ni ina so dama dan kunyi min finkarfi ne yasa na hakura na baku",

Su lola Najin haka suka yi sum sum suka bar dakin zuciyarsu fes dan sun kusa rabuwa da jaraba.

Abba ne ya shigo daga neman Zahran ya tarar da abinda ke faruwa,tsawa ya dakata mata yana cewa tashi ki bamu guri maras kunyar yarinyar kawai", su Hafsah ne suka dagata su kayi waje ba tare da ta daina zubar hawayen da take yi ba.

Sosai Abba ya fahimtar da kaka tare da kawo mata manyan hujjojin da suka shi aurar da Zahran a wannan shekarunnata na KURUCIYA ,ya kuma tabbatar mata yayi bincike akan yaron da zata aura bashi da wata matsala kuma yana sonta zai iya hakuri da ita,ita nata rashin son duk me sauki ne sabida akwai yarinta a tare da ita.

Ba dan ranta ya so ba ta hakura,amma da sharafin sai dai ta tafi da Zahran ko kwana uku ne ta yi dan ta samu ta rarrasheta da kyau,to Abban ya amince,dan haka ta tashi ta hadawa Zahra abinda babu a gidanta wanda zata iya bukata.

A can gidan su nadiya kaka ta samu Zahran suka wuce.

Sosai fa Zahra take cikin tashin hankalin aurennan,dan tunda take babu abinda ya taba gigitata kamar batun auren,har wani shuru_shuru ta zama a kwana biyun,wanda hakan yasa kaka ta kuma dagewa wajen kwantar mata da hankali ga kuma su nadiya suna zuwa duk suka dawo daga wajen aiki,dan duk su ɗebe mata kewa.

A hankali ta fara warwarewa tana mantawa da batun auren da take gani kamar ba yi za ayi ba,kwananta hudu gidan kaka taki komawa gida karshe ma su nadiya suka lallabata ta cigaba da zuwa Company...

Yau satinta biyu a gidan kaka, tuni ta ware ta koma zahranta yar GIDAN YARBAWA,kaka bata gajiya da karbar karar Zahra kullum ita ake kawo kara,amma duk ranar da wani ya taba Zahran ta shigo tana kukan tabararta to ranar babu zaman lafiya a anguwarnan dake dama tun can sun san Zahra dan haka halinta va sabo ne a wajensu ba.

Ta bangaren Abba kuwa sosai hankalinsa yake kwance shirin auren Zahra kawai suke yi,hatta da yan uwansu kowa shiri yake ba tare da Zahra ta sani ba.

Wata guda kawai Abba yasa auren Zahra saboda tun Zahra bata kai haka ba yake tarin aurenta duk neman da yake saboda ita ne,ga kuma dan uwanta duk da cewa karatu yake shima yana turo kudi duk dan Zahran.

A bangaren zahraddin ma shirinsa yake cike da doki,dan ma yana dauriyar rashin Zahra,sabida Abba dakansa ya nemi alfarma akan zahraddin din ya hakura da zuwa gurin Zahra saboda fitinarta a samu ayi komai hankali kwance,shi yasa ma Abban ya kyaleta gidan kaka bai ce ta dawo ba.

Su lola kuwa duniya sabuwa ce ta samu a gurinsu,rayuwarsu suke yi cikin sakewa da farinciki ji suke kamar anyi musu sharar masifa saboda rashin Zahra a gidan.

Sai yanzu mama taga amfanin Zahra a gidan, sai yanzu ta gane cewa ashe saboda Zahra ne basu shiga takurar zama da YARBAWAN GIDAN ba,kusan halin mama na kyama shi Zahra ta dauka dan haka mama take zaman takura sabida tsananin kazantar da take fuskanta da fadacen_fadacen su da kullum sai sunyi ko bacci me kyau basa bari su mama su yi,ashe Zahra ce maganinsu shi yasa ko sararin yin fadan basa samu...

Take mama kewar Zahra ya isheta,gashi ta rasa ta yadda za ta yi ta sanar da Abba a dawo mata da Zahran.....

Yau Zahra dai ta bari an tashi daga aiki gaba daya saboda tana son binsu nadiya zata je gida taga mama da itama take cike da kewarta.

Yamma liss ta ƙaraso gidan a lokacin duk YARBAWAN GIDAN sun dawo,baka jin komai sai hayaniyarsu da zage_zage,gidan yayi kaca_kaca kamar gidan mahaukata, wannan na wanki wannan na markade wannan na kitso amma bakunansu sunki rufuwa baka isa kuma ka tantance da wa ake fadan ba kowa ya shiga yayi uwa yayi makarbiya.

Daga farkon layin zaka jiyo hayaniyar gidan,Zahra bata kawo a gidannasu ba ne,saboda kusan ko wane gida da YARBAWAN.

Sai da tazo kofar gidan sannan ta fahimci daga ina hayaniyar ke fitowa.

Murmushi ta yi tana cewa su Zahra abin nema ya samu yau farar yamma ce a gareni zanci uban yarbawa, yau duk sai na biya bashin kwanakin da nayi", ta fada tana cire mayafin abayar dake jikinta tare da yin damara dashi.....✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol