Free chapter · Read without an account
Pg17
..........jafar kamar yasa me take shirin yi yayi saurin bin bayanta,dan shi kam yanzu kallon me aljanu yake yiwa Zahra dan neman fitunarta yayi yawa.
Sai dai kafin ya cimmata tuni ta shige mahayar ta direta a hawa na shida,ba tayi wata wata ba ta fada office ɗin..
Ba tare da ta kula da sabuwar sectarea siyam ba ta nufi kofar da zata Kaita ainihin office din.
Tana dora hannunta dan murda handle din kofar taji an rike wani hannun ya shima ya riƙe kofar ,a fusace ta waiga dan a tunaninta jafar ne,sai dai kuma taci karo da sabanin tunaninta.
Tsaf ta shiga karewa siyam kallo ba tare da ta tanka ko ta cire hannunta daga kan handle din kofar ba kamar yadda itama siyam bata cire ba.
Sai da Zahra ta tabbatar da cewa itama wannan din beyerabiyar ce sannan ta yi saurin janye hannunta tana cewa wash Nifa bana son ko wane hannu yana taba Ni saboda gudun daukar ciwo ma ana ciwon da yake samuwa ta hanyar kazata",
Siyam da bata fahimci abinda Zahra take nufi ba,tunda ba Hausa taki sosai ba, ta ce", me ye kike kokarin yi ? Ke din wacece?
Kuma haka ake shiga gurin Oga kai tsaye babu neman iso ko baki ganni a gurin ba eye?
Cuna baki Zahra ta yi sannan cikin rashin ji ta ce", idan tambaya kike je ki nemi malami danni ba Malama ba ce,sannan kuma ni bana neman iso ko dakin mata da miji ne fadawa nake bata tare da sallama ba,
Cikin harzuƙa siyam ta kai hannu zata buge bakin Zahra,aiko zaraf Zahra ta rike hannun tare da yar far dashi tana cewa kul kar ki soma wanda suka fi ki ma sun yi basu ci riba ba, dan haka kar ki soma shiga gonata Ni din ba sakarya ba ce wahala zaki sha wlh",
Ta kai karshen maganar da zabga mata harara da murguda baki irin na mara sa kunyar da suka kuna basu sha yi ga duk wanda ya tabo su.
Bude kofar office din da akayi shi yasa su kallon kofar a tare,kafin ya gama kirkiro abin fada tuni Zahra ta sunkuya ta karkashinsa ta shige office din tana cewa idan kina da karfi kizo ki fiddani daga office dinnan", ta fada tare da cogewa ta bayan Ab da har yanzu ya kasa cewa komai tun fitowarsa da ya ji hayaniyarsu sama sama.
Kasa magana siyam ta yi dan ita duk Abb zai kasance a guri ji take ko mai nata ya tsaya kwarjininsa kan hanata sukuni,shi yasa yanzu mamakin Zahra ya kasheta a tsaye ganin yadda babu shakkar ab cikin idanunta.
Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya koma cikin office ɗin,shiru siyam ta yi tana mai zurawa kofar idanu tare da tunanin ganin Zahra Ab ya wurgota waje.
Sai dai me shiru kake ji har tsawon mintuna biyar bata ga wata alama da ke nuna Zahra zata fito ba,kai babu alamar ma ab ya yi wa Zahran wani abu da zai sa ta ji haushi ta fito duk da cewa bata san me ya kawo Zahran ba,ba kuma tasan tsakaninta da ab ba,kawai dai kyawun Zahra ne ya bata tsoro tun farko har tayi kokarin hanata shiga office ɗin.
Samun guri ta yi ta zauna ba tare da ta dauke idanunta daga kan kofar ba ,dan a ko da wane lokaci tana tsammanin fitowar Zahra.
Lokacin da jafar ya biyo Zahra , daidai lokacin yaga fitowar AB dan haka kawai ya zare jikinsa ya bar gurin ba tare da ya yi wani motsin da zaisa su gane yazo gun ba.
.......me kike da bukata ,Ab ya fada yana zama cikin kujerarsa tare da jingina yana mai lumshe idanunsa,yadda yayi maganar ba karamin kara kular da Zahra ya yi ba.
Hakan yasa ta fara gunguni da ficincina ido tana son ta yi rashin ta ido amma wani bangare na zuciyarta na shakka,
Bude idanunsa ya yi akanta, daidai ta dago zata yi magana a tunaninta tunda ba kallonta yake ba gara ta yi saurin fadar abinda ke bakinta,sai dai kuma cak idanunta suka sarke da nashi da suke yi mata wani irin kallon ƙasan ido,wanda ita Zahra kai tsaye ta kira kallon da kallon yan iska,dan haka tayi saurin kawar da nata idanun tana tura ƙaramin bakinta ,ciki ciki ta ce", Ni kam a daina kure min kallo haka dan salan mutum ya gano haram", tsaf yaji abinda ta fada sai dai bai ce komai ba sai kallonnata da ya cigaba da yi.
Juyawa ta yi zata bar office din tana cewa wlh BAZAN yi wannan kaskantaccen aikin ba,sai dai na hakura da zuwa,dan ma an raina min hankali ya za a yi kamata na bige da share sharen Company har da su wankin banɗaki to wlh BAZAN yi ba,idan ma kun yi haka ne dan ku kuntata min to kunyi a banza tunda sai nazo nayi ne zaku ji dadin da kuke son kujin." Bude kofar ta yi ta fice ba tare da ta juyo ta kalleshi ba bare ta fuskanci yanayin da ya karbi maganarta,duk da cewa shi din ba wani fahimtar aimahinsa a ke yi ba.
Tana fita idanunta suka fada kan siyam da har yanzu take jiran fitowar Zahran,dariya Zahra ta yi tana cewa kai yau naga jaraba ke kam anya ba a gidan su zahraddin kike ba dan irin nacin ku daya? To na fito kuma ki kwantar da hankalinki ba abinda kike zato ne ya kawo Ni ba,dan naga wawta a idanunki,wucewa ta yi tana ci gaba da cewa yo wawta mana idan ba wawta ba waye zai so wannan cinnakan fuska kamar an aiko sakon mutuwar uwa da uba",
Harara siyam ta bita dashi tana jin hankalinta yana dan kwanciya, da abinda Zahran ta fada.
Zahra na fitowa gidan kaka ta nufa tana ta fasifa ita kadai saboda abin ya mata ci,wai share share da wankin kazamin banɗaki ma kananun ma aikata.
Kaka ce ta tareta tana cewa me ya faru yar gidan kaka kike ta fada ke daya?
Zama ta yi a gefan kakan dake zaune kan tabarma a tsakar gida,tana cewa ke dai kaka bari wani rainin hankali a kayi min wlh", nan ta kwashe Abinda ya faru ta sanar da kaka har da labarin abinda ya haɗa su a baya.
Rike haba kaka ta yi sannan ta ce", kin min dai-dai jikalle. da baki dau mataki ba da yanzu wani abu ya sameki kuma aiki kin barshi tunda ba yanke talauci zasu baki ba,duk da cewa ba fin karfin aikin ki ka yi ba,to amma manufar ita ta rusa komai dan haka ba za ki yi ba", ke da za ki tafi gidan mijinki ma ina ke ina ci gaba da zuwa aiki.....abincin da ta dauko ta ture tare fasa kuka kafin wani lokaci ta tuje tabarmar da suke kai saboda burgima.
Salati kaka ta saka tana cewa wannan wane irin shashashanci ne ashe duk baki ji abinda na gaya miki ba? Ina nasihar da nayi miki kika nuna min kamar kin hakura ashe lumbu lumbu ki kayi min,to wallahi zuwa zaki mu tafi na maida ke gida na daina rarrashinki gara ayi miki auren kowa ya huta haba wannan wace irin masifa ce,yarinya kina girma kina ci gaba da cin kasa(😄kakama ta gaji da iskaranbarancin Zahra)
Zahra na nan tana share hawaye da sheshsheka sai ga kaka ta fito da mayafinta a hannu tana cewa maza ta shi yau baki kwana min a gida kina min iya shege", Zahra bata Musa mata ba ta mike dan dama sun saba irin haka ko da can,idan su kayi fada maida ita gida take yi ta duddugure mata kai sai an kwana biyu kuma ta dawo biko da kanta.
Kwana biyu da Zahra ta yi a gida babu abinda ya faru saboda damuwar auren sosai ta dawo mata,dan dawowar Tata ta fahimci da gaske Abba ya ke yi dan gashi nan sai shiri suke yi, hankalin ta bai kuma tashi ba sai da taga mama ta hado kayan gyaran jiki ta saka ta gaba kullum ta Allah sai ta yi mata,ga wasu kayayyaki da ake yawan bata wanda bata da damar ki saboda babu fuska.
.........a bangaren gidansu zahraddin ma sosai a ke hidima da duk wasu al'adu na yarbawa,bidi a kala kala a ka shiryawa bikin dan gata.
A hankali lokaci ya cigaba da matsowa har dai Allah ya kawo lokacin bikin Zahra yar gidan yarbawa.
Yau Alhamis ta kama za ayi kamu.
Kememe Zahra ta ki shiryawa a yi mata kamu sai da taci dundu a wajen mama,duk da kaka na hanawa ita da Mami zainab,dan dole ta bari Mami zainab ta shuryata tana faman sauke hawaye.
Kawayenta kansu yanzu tausayin Zahran suke ji ,saboda yadda duk ta canja,dan yanzu ko magana bata yi sai dai kuka da hawaye,kawayenta yarbawa kuwa sosai suke hidima dan su kam farinciki suke Zahra zata yi aure su huta su samu sakewa a gidansu.duk da Zahra na cikin damuwa sai da ta fahimci hakan dan haka ta sha alwashin sai ta yi musu na karshe koda zata bar gidan sai ta bar musu tabonta da zasu dinga tunawa da ita koda bata nan.....
...........a can ɓangare su zahraddin kuwa gida ya cika dam da yan uwa da abokan arziki kowa yazo za a fara Shagali,maman tunde yaya ce ga Abban zahraddin ita ma zuwanta ke nan daga can inugu, dan bata san da maganar auren ba sai a na saura sati daya.tunda tazo take kuka tana fyatar majina tambaya kuwa har sun gaji da yi mata ita sun zuba mata ido.
Sai da ta yi me isarta sannan ta saurara tana cewa yanzu kamarni BAZAN san auren zahraddin ba sai a kusan biki?duk ba ma wannan ba ai ina ji kunsan cewa farira ke sonsa har ma da alkawarin aure a tsakaninsu da kai da kanka kayi mata, wai dan an shirya munafunci sai naji zance daga sama,wato Ni za a nunawa ban haifi zahraddin ba farira na haifa ko?
Tuni Abban zahraddin ya dabarbarce dan shi wallahi sam ya manta da wannan alkawarin,dan haka ya shiga bata hakuri,Nifa babu batun hakuri a wannan lamari dan yanzu haka farira bata da lafiya saboda tashin hankalin da ta shiga," to yanzu aunty me kike so a yi", Abba ya fada yana kallonta cikin saurare.
Zamanta ta gyara tare da yin gyaran murya sannan ta karkace dankwalinta yayi gaba sosai tare da tsaida idanunta akansa ta ce", so nake a fasa da waccen a daura da farira," eye me kika ce? Abinda kaji shi na fada",
Zufa ce ta fara tsoyayo masa saboda tuna irin son da zahraddin ya ke yiwa Zahra. Kafin cikin tattaro nutsuwarsa ya ce", ai ba a yi haka ba kiyi hakuri in yaso sai a hada su a aura masa ai ba zai gagara ba", wani banzan kallo ta yi masa tare da yin kwafa amma bata ce komai ba,ita kadai ta san abinda ta shirya dan sam baza ta bari farira ta yi zaman boranci ana son kishiyarta ita ba a sonta ba.
Haka aka cigaba da Shagalin auren mutum biyu ba tare da sun san abinda maman tunde ke shiryawa ba.
A can bangaren su Zahra ma an yi kamu irin na al'adarsu kowa ka kallah fuskarsa da farinciki irin na wanda suke taron biki,amma banda Zahra da take kallon kowa a matsayin makiyinta,dan hatta yan wajen aikinsu sai da su nadiya suka gaiyatosu, duk da ita Zahra ba mutunci take da kowa ba idan ka cire manyan wajen hausawa dan idan tana gaidasu cikin mutunci sai ka dauka ba ita ba ce,to amma ga mamakinta duk sunzo,tsaki ta yi a ranta tana cewa mugaye dan sun san ba auren so za a min ba shi yasa suka zo(haba Zahra ke ba a miki gwaninta ne😄)
Misalin ƙarfe daya da arba'in na dare kowa ya saka hakarkarinsa ya kwanta dan ya huta ,bayan an gama hada miyar daurin aure.
Da yawan baƙin jalingo dangin su Zahra a makeken tsakar gidansu suka baje da shimfidu kasancewar zafi ne sai hakan yayi musu dadi,dan haka suma YARBAWAN GIDAN basu kulle kofofin su ba wasu suna daga bakin kofar dakinsu wasu kuma suna ciki ,sai ya zamana kofar waje kawai aka rufe.
Babu wanda yasan Zahra bata bi su nadiya gidansu da suke kwanan amare ba,dan bata shigo gidan ba sai wajen sha daya da rabi dan haka babu wanda ya lura da ita.
......a hankali ta bude idanunta tare da fara kallon kowa da yake cikin tsakar gidan dan tabbatar da cewa kowa yayi bacci,sosai ta duba ta tabbatar kowa baccin sa ya yi nisa. alokacin karfe biyu ta buga,dan haka ta mike cikin sanda ta bude ledar dake hannunta ta dauko doguwar bakar riga ta saka tana daga zaune kuma cikin takatsantsan,sannan ta kuma bude wata farar leda sai ga farar hoda harda kwalli baki ,nan take ta shafe fuskarta har zuwa wuyanta tayi fari fat baka isa gane ainahin kalarta ba,ta saka kwalli ta yi zane zane.
Cikin kankanin lokaci ta koma aljana sunbuka sak🤣dogon gashin ta da yake har gadon bayanta ta warware duk gyaran da Mami zainab tayi masa haka ta hargitsashi ya sauko har gaban fuskarta ya rufe wani bangare daga fuskartata.
Murmushin mugunta saki tana kara haska karamin budubin dake hannunta a dan haske farin watan da ya haska tsakar gida tana cewa ba ku kunzo biki ba duk zaku gane kurenku babu wacce zata iya tuka tuwon daurin aure bare ta yi kwalliya saboda tsoro,ku kuma yarbawa zaku ci ubanku daku da murnar san bar gidan da kuke yi,daga haka ta mike tsaye cikin sanda ta nufi bakin kofar dakin maman Jo........✍🏼
Tofa Zahra yau kuma me zaki aikatawa YARBAWAN naki?
🤣🤣🤣🤣Zahra ki musu a hankali koma meye kar a yi yadda za a zo ana nadama🤣🤣
Ke kuma maman tunde kike kowa wai me zaki yi ne me ye shirinki akan auren zahranmu ehe?
Walle idan bakwa yin com akwai matsala wasan fa yanzu ya fara ,zamu zo inda idan ban baku ba ko bacci Zahra bata garinku kuyi dan haka abini a hankali ehe😉...
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*