Free chapter · Read without an account
Pg18
*.......maman Jo na kwance a cikin falonta sai munshari take saki baki bude ga daurin kirjin da ta yi yana neman kama gabansa,da alama dai ba karamin jin dadin baccin take yi ba.
Kai tsaye Zahra ta shiga ciki dan har sai da ta tsallake maman jo din saboda tana daga bakin kofa ne.tsayawa ta yi akanta tare da sunkuyowa har gashinta yana taba fuskar maman Jo din.a hankali ta fara juya fuskarta ta yadda gashinnata zai cigaba da goguwa a kan fuskar maman jo,hannu maman Jo tasa ta fara yarfar da gashin duk atunaninta sauro ne,to amma me tana kaiwa sauran danka cikin zafin rai dan ta.kasheshi sai taji ta rike abu me laushi .da sauri ta bude idanunta, aiko basu sauka a ko'ina ba sai akan fuskar aljana Zahra,take maman jo ta zunduma ihu wanda ya tashi kusan rabin mutanen GIDAN,da gudu ta fita tana nuna musu Zahra da ta biyota tana wani irin abu da dogon gashinta da ya rufe fuskarta sosai dan haka babu wanda zai ganeta.
Sai da kowa ya fara gudun ceton rai dan kuwa Zahra ta koma aljana sak da duk wanda ya kalleta a daren sai ya tsorata.
Abin gwanin dariya gwanin tausayi, dan kuwa da bakin da YARBAWAN GIDAN guri suka samu suka haɗe kamar ya'yan mage jikinsu banda rawa babu abinda yake yi.
Wata yar uwar mama da suke cewa hajjo ta ce", ke kuwa baiwar Allah me mu kayi miki zaki mana haka cikin daren da ya zama mahutarmu? Wata irin dariya Zahra ta kyalkyale da ita kafin cikin Muryar da ta sauya ta ce", ba gurin ku NAZO ba dan haka kar ki kara magana", too too too bazan kuma ba", hajjo ta fada cikin rawar baki.
Juyawa ta yi inda su lola suke a makure jikinsu tamkar ana kada mazari,ta nunasu tana cewa ku kuma zaku gane kurenku yanzu dan kune sanadin zuwana saboda kuna yi mana kazanta a gurin zamanmu wato banɗaki kuna taka mu yadda ranku yaso dan haka dole mu dau fansa.hehehehe ta kwashe da wata muguwar dariya,kaya kuri zamu dena in sha Allah ba zamu kuma ba pls for d sake of Allah karki kara tsoratamu",
....ai walle baku isa ba yau sai naci kaniyar yan iska sai na gyara muku zama , Zahra ta fada a ranta tana kokarin kumshe dariyar dake cinta saboda yadda su ke yi din,bulalar da ta daure kugunta da ita ta zaro tana gyarata.
Tuni fitsari ya kece a tsakaninsu dan baka tantance wanda suke yin fitsarin,yemi ta fara shinfidawa bulalar take ta gantsare tare da sa ihu ta yi hanyar kofar dakinta da gudu ta shige tare da saka sakata.
Saboda tsananin tsoro da rudewa suna kallo yemi ta samu damar guduwa amma su sun kasa dan haka Zahra ta kuma samun damar tsulawa maman Jo aiko take ta mike tana tsallen kwado itama ta nufi wata hanya daban har tana kifawa dakyar ta mike sai gata a dakin lola ba tare da ta gane ba,itama rufe kofar ta yi tare sakin ragowar fitsarin da bai gama fita ba.
Hajjo da suke kallon duk abinda yake faruwa jikinsu har yanzu bai daina rawa ba,ta radawa ta kusa da ita tana cewa Ni kam tsautsayi ne ya kawo Ni bikin Zahra wallahi da ba dan kar na tafi yanzu na kuma haduwa da ita a hanya ba to da a tasha zankwana gobe sai jalingo",
Su mama da kaka zainab da kaka kuwa basu san meke faruwa ba saboda baccin da suke sakamakon maganin bacci da Zahra ta bade musu a furar da ta kawo musu da dare,shiko dama Abba saboda bikin can gidan kaka suka koma da baƙin jalingo maza,su kuma mazajen yarbawa dama ba mazauna ba ne dan basa yin cikakken sati biyu a gida yawanci duk suna legos a can suke neman kuɗinsu,Ade ne kawai yake gida shi kuma yana fursun sanadin Zahra, shi yasa yau Zahra ke cin karenta babu babbaka take wajiga yarbawa da bakin bakinta san ranta.
Lola kuwa kasa motsawa ta yi tana daga tsaye tun bulalar da Zahra ta yi mata ta kasa motsawa saboda tsananin tsoro saiga zawayi dan ita fitsarinta ma ya kare dan tun farkon lamarin ta fara yinsa.
Yaransu kuwa masu wayon da suka samu farkawa babu abinda suke sai zagaye tsakar gida hannu a saman ka suna surutai saboda razana.
Maman dady kuwa da aka bata nata bulalar wata yar dungure ta yi sai Gata a kofar banɗaki tana faman waige da sosa bayanta bakinta dauke da addu'ar neman tsari da jinnu,karshe dai bandakinne ya zama wajen buyarta,Zahra na ganin haka ta saki dariya tare da jufar bandakin ta tsaya a bakin kofa tana konkosawa.
Tsuru maman dady ta yi zuciyarta na kadawa da tsoro,Zahra ta kuma buga kofar tana cewa ke wai nan kina nufin tsira kika yi? To ai kin yi ta banza dan kuwa Sarkin garinmu da shine ya turoni gurinku nayi muku kashedi yana ciki tare da tawagarsa ta muggan aljannu marasa imani",
Ji kake zuuuuuuu ƙuuuuu uuuuuuu,karar zawayin maman dady wannan shi ake kira gaba kura baya siyaki,idan ta fito aljana a ciki kuma tawaga guda, to amma Gara wajen guda dayace dan su wannan bata san me zasu yi mata ba tunda suna da yawa dan haka ta gwammace fitowa,tana faman zazzare ido jikinta duk ya ɓaci da zawo,Zahra tana ganinta ta kwashe da dariya wadda ta yi sanadin sasu tseren gudu su da yaransu da ragowar yan bikin da suke makure a guri daya,kowa kokari yake yaga ya tsira dan haka gaba dayansu dakin maman dady suka shige tare da rufe kofar suka saka sakata ba tare da basu da tabbacin zata iya keto kofar ta shigo ba.
Dariya Zahra ta yi sannan ta yi saurin shigewa dakin mama ta dauko kayanta ta saka ta cire bakar abayar tare da goge fuskarta, cikin kankanin lokaci ta dawo tsaf da ita kamar ba Zahra sunbuka me razana muten gida da baki ba,hatta da bulalar da ta yi duka sai da ta boye sannan ta samu can kurya ta yi kwanciyarta kankace me baccin gajiya ya sureta ranta fes ko ba komai ta rage radadin auren dole da za ayi mata.
Yayin da Zahra ke bacci su kuwa gaba dayansu babu me ko gyangyadi,sai da aka fara kirayen sallah sannan suka fara sakin ajiyar zuciya dan a lokacin sun tabbatar aljanar ta tafi,sai a sannan suka fara jin warin zawayin da su maman dady da lola su kayi sai kuma zarnin fitsarin manya,take kowa ya fara toshe hanci,ganin zasu kashe kansu ta hanyar shakar warin yasa su ka yi kundumbalar zare sakatar suka fara fitowa cikin tsoro tsoro,sai da suka tabbatar babu kowa sannan suka saki jikinsu har da masu yin a mai saboda tsananin warin kashin su lola.
Daidai nan kaka da mama da suka fara tashi suka fito tsakar gidan,dan su duk nauyin baccin da suke baya hanasu jin kiran Sallah,cike da mamaki suke bin tsakar gidan da kallo saboda yadda ya rikice ko ina a hargitse ga shimfidu duk sunyi nasu waje,kafin kaka ta kai ga yin magana man dady da lola sun fito da gudu dan shiga bandaki su kimtsa jikinsu duk da cewa kuwa a matukar tsorace suke,take kaka ta toshe hancinta tana cewa wai Ni me yake faruwa a gidannan kamar bamu kwana a cikinsa ba? Hajjo ce da ta gama daura alwala ta matso kusa da kaka ta ce", ku kuwa dan Allah wane irin bacci kuka yi jiya da har aka yi yakin Badar na karshen duniya baku sani ba?Mami zainab da ta fito tana dan kutstsuke idamunta alamar tashinta kenan ta bata amsa da cewa Wallahi hajjo Ni kaina mamakin nauyin baccin da nayi yau nake yi ashe ma bani kadai bace hadda innarmu da mama Zahra", Hajara wadda take itama kusan ya ga mama ta ce", ina ga gajiya ce kawai amma tabbatas jiya Allah ne yayi da tsawon rayuwarmu a gaba",
Zahra dake jin duk abinda suke fada ta kwashe da dariya sai kuma tayi saurin toshe bakinta dan kar su jita a ranfota.
Hajjo ce ta yi karfin halin yi musu bayani yadda zasu fahimta a takaice daga karshe ta ɗora da cewa Allah yasa basu ji Ni ba kar su bini har can jalingo su zargo kafafunsa", aiko Zahra me zata yi ba dariya ba,Mami ma da mama sai da su kayi dariyar maganar hajjo ta karshe,daga nan suka jajanta musu, duk da cewa mama da kaka sun dora a yar tambaya akan Zahra duk da cewar bata kwana gidan ba.
Ganin Zahra ta fito daga dakin mama yasa suka gaskata tunaninsu,Mami ce ta ce", a'a amarya wai anan kika kwana dama? Yatsina fuska ta yi tare da cewa a'a Mami ba anan na kwana ba yanzu na shigo ganin hankalinku yana kan jin sukiburutsu yasa ban yi muku magana ba na shige", Harara hajjo ta watsa mata tana cewa ey kyace shirme mana tunda babu ke a takin karshen duniyar", dariya zahra ta yi tana xewa kai hajjo mu tumda muke a gidannan bamu taba ganin aljani ko na bera ba bare na mutum", to ya mutan g danku nan komai da ya faru tare da su ya faru",
Duban maman dady Zahra tayi sai dai kuma dariyar dake cinta idan ta tuna karonsu da ita yasa ta waske ta dauki buta ta yi banɗaki tana cewa to ku hajjo tunda ba gunku a ka zo ba meye na damuwa ku saki ranku ku cigaba da bikinku babu wani abu ", ey kuma fa kinyi gaskiya yar nan dan su da bakinsu suka ce ba gurinmu suka zo ba,dan haka ba na cigaba da sabgata",
Shigewa banɗaki tayi tana murmusawa,mama da kaka suka hada ido tare da jinjina kai,kowacce zuciyarta cike da tunanin shakiyanci irin na Zahra amma dole su ja bakinsu su yi shiru tunda lallabata suke ba damar yin fada gashi kuma yau take ranar daurin aurenta, Allah ya shirya mana ke Zahra abinda suka iya fada cikin zukatansu kenan
Sai a lokacin yemi da maman Jo suka iya fitowa suma jikinsu jagab da fitsari nan fa baƙin biki suka shiga maida magana ana tuntsura dariya dan sai yanzu dramar da akayi take dawo musu dalla dalla sai kuma abin yake basu dariya barinma abinda su maman dady da lola su kayi.
*...........*karfe 10:35 babban masallacin dake cikin anguwar yarbawa daga can gabas ya fara daukar mutane, su Abba tuni sun hallara cikin masallacin,kasancewar zahra ta mutane ce duk da halinta kuwa ga kuma Abbanta da yake mutumin kirki da kyakkyawar mu'amala,sai gurin ya kuma cika ga kuma mutane su zahraddin da abokan mahaifinsa na kusa kowa ta hallara,karfe 11:00pm za a daura auren shi yasa har yanzu mutane suke da damar hallara.
A bangaren su zahraddin kuwa a safiyar yau din ya tashi da jin bakon labari na aurensa da yar yakunbonsa farira sosai ya tashi hankalinsa to dake anyi masa barazana da idan bai hakura ba sai dai ya hakura da su gaba daya dan haka ya koma yayi lakwas zuciyarsa na ci da wutar fusata.
Rigima ta tayar akan sai an fara daura auren farira sannan su tafi a daura na Zahra ,cikin dabara ta kwashe wayoyinsu ba tare da sun kula ba,duk dan ya zamana an bata lokaci yasa Abban ya yarda suka fara daura auren farira.wannan ne ya bata damar zare jiki ta fita daga gidan ba tare da kowa yasan inda ta tafi ba.
A can wajen daurin aure kuwa tuni lokaci yayi har Abba ya fara kokarin kiran Abban zahraddin sai dai wayar a kashe, haka ta zahraddin ɗin,mutane har sun fara kosawa,wani abokin Abban zahraddin da suke da kusanci sosai shi ya tausayawa Abban Zahra shima ya fara taya shi neman duk wata nomber da yasan abban zahraddin yana amfani da ita sai duka a kashe.
Ana cikin wannan taraddadin daga can wajen Masallaci suka jiyo hayaniya na tashi, da sauri suka fita dan ganin abinda ke faruwa,wata beyerabiyar mata su ka gani tana ta zanga tujara daga yanayin maganganunta ne su Abba suka farga cewa maman zahraddin ce,ina uban yarinyar ta fada tana kuma kurdawa cikin maza babu abinda ya dameta, shigar abokin abban zahraddin da ta fi nuna kudi da arziki kwance ita tasa tayi zaton shine uban amaryar dan haka ta nufosu kai tsaye tana cewa, tun wuri ka nemi mijin yarka amma ba nawa dan ba zahraddin ya fasa auren yarka babu ku babu mu me ye hadin fillo da beyerabe wannan ai shi ake kira hadin gambiza.
Ganin irin cin mutuncin da take yiwa abokin mijinta ba tare da ta sani ba a tunanin Abban Zahra yasa shi nuna kansa da cewa bashi ne uban yarinya ba nine dan haka ki yi min duk abinda zaki min kar ya shafi wanda yazo taya mu murna", wani kallo ta watsawa Abban Zahra tana cewa au ashe yar gidan matsiyata ya kwaso mana dama, dan da gani wannan baka gama koshi ba to ina mai tabbatar maka da cewa mun fasa baka danmu sai abu wani sarkin", daga haka ta juya ta bar gurin ranta fes dan tasan ko su zahraddin sunzo aure ba zai dauru ba in dai suna da zuciya.
Zufa ce kawai ke ketowa Abba ta ko ina yan uwansa ma ransu ya ɓaci hatta da mutane da komai ya faru akan idanunsu sun tausayawa Abba,abokin Abban zahraddin ne ya riko hannun Abba da yaji kaunarsa ta shige shi lokaci daya ga kuma tausayinsa da ya mamaye shi ya ce", bawan Allah idan baza ka damu ba zan karbawa data auren yarka yanzu nan ba tare da An matsa ko ina ba..........✍🏼
Kut.... Bari dai na kama bakina.
Aure ya tashi daga kan zahraddin to kan waye zai fada?
Mu dai Allah yasa zahranmu ta yi gamon alkhairi.......😄😄
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*