Free chapter · Read without an account

Pg19

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

*.............zuba masa ido Abba yayi jikinsa har rawa yake wajen damke hannun mutumin da bai taba gani ba,ya ce ", yallabai me kake nufi? Abinda kaji shi nake nufi ba kuma komai yasa nayi wannan tunanin ba sai irin yadda naga anci maka mutunci a bainar jama a kuma Nima yarona saurayi ne bai taba aure ba hasalima bashi da niyar yin auren shi yasa nayi wannan tunanin kaga kenan zan jefi tsuntsaye biyu da dutse daya ne na fidda ka kunya kuma Nima nayi abinda zai faranta min ta hanyar samawa yarona suruki na gari dan ina kyautata zato akanka",

Kasa cewa komai Abban Zahra ya yi sai kawai ya rungume mutumin tare da fashewa da kuka yana cewa na gode na gode Allah ya faranta maka fiye da yadda ka faranta min Allah ya saka da alkhairi ya raya zuri'a ", Amin kar ka damu mu koma ciki muyi abinda ya da ce",

Kafin mutane su fara yunkurin watsewa sun tsinkayo Muryar maroki yana shelanta auren Zahra da MUHAMMAD ABRAHAB BAKARE AKAN SADAKI NAIRA DUBU DARI BIYAR LAKADAN BA AJALAN BA",take kowa sai ya fara washe baki ana taya Abba murna dan kuwa wannan sunan ba bako ne a kunnen mutane ba.

Har gida dady ya rako Abba saboda ya ga gidan kuma ya gaisa da iyayen Zahra mata.

Dake tuni labari yazo musu ta wajen yan bani na iya abinka da zamani na social media tuni har da masu yin video su dora a tiktok da su facebook da dai sauransu,shi yasa ko da suka shigo gidan su mama suka yi masa kyakkyawan tarba wadda dady ya kuma shaida cewa ya kawo dansa gidan tarbiyya.

Daga nan dady ya nemi alfarma idan sun gama biki amarya ta zauna a gida zuwa lokacin da zasu gama shirin nasu bikin da tariya gaba daya,Abba ya ce babu komai ai abin suma yazo musu babu shiri ne dan haka dole a samu lokacin shiryawa da kuma sanarwa mutanen da ya kamata su sani,a haka suka rabu cikin girmama juna.

Dady yana tafiya mutanen gidan suka cigaba da sabgar biki zuciyarsu tas basu ji kunyar sauke tunkunya ba.

Kaka kuwa guda take tana cewa wani hanin ga Allah baiwa ne, yanzu ba gashi zahranta ta yi goshi ba,dan haka ita ranta fes tunda dama Zahran ba son zahraddin take yi ba.

Duk wannan abun dake faruwa Zahra basu sani ba suna can gidansu nadiya,har sai da Mami zainab tazo tasa ta ta yi wanka ta shirya tana faman cin magani,Mami zainab na fita wata kawarsu nadiya da take da waya tazo tana nuna musu abinda ya faru a wajen daurin aure.

Wata zabura Zahra ta yi tana fusge wayar daga hannun safiya tana cewa kumbura U.....kan ta karasa nadiya ta rufe bakinta dole ta hadiye zagin da ta aro za ta yi dan dama ba yin take yi ba, ta ce nadiya Hafsah ku ga min tsinannniyar mata waya ce mata ubana matsiyaci ne? To wlh kuwa taci bashi dan bazata karasa bikin yartata da kafa ba ku tashi muje", ta fada tana kokarin saukowa daga kan katifar da take zaune, da sauri nadiya ta tare ta tana cewa haba Zahra ki dinga bin abu a hankali mana karfa ki manta bikinki fa ake yi yau, kuma ai ke gaba ta kaiki kina ji fa alhajin da ya karbi auren naki babban mutum ne kuma da alama irin wanda kike so ne wato bahaushe.

Sufa basu tsaya sun kalli fuskar kowa ba daga kan maman tunde suka tsaya shi yasa babu wanda yasan waye mijin da aka bata,a fusace Zahra ta ce", Ni kinga babu ruwana da wani aure yanzu can ta matse musu danni bani da damuwa nasan idan nayi musu wata barnar da gudu zasu koroni da takarda ta dan haka yanzu wannan shegiyar ce a gabana wlh sai na karkatar mata da kugu",

Hajjo dake shigowa ce ta ce", kin yi min dai dai Zahra zo muje nayi miki jagora ungonan ta mika mata liƙaf dinta tana cewa ke nadiya bata tsofaffin kaya ta saka ta rufe fuskarta babu wanda zai ganeta har mu dawo", yauwa hajjo shi yasa nake sonki dan kin san abinda ya da ce", daga haka ta mike ta cire kayan jikinta ta saka wata atamfar nadiya da hijab sannan ta saka nikaf din ta ce", hajjo muje na gama", hajjo ta ce", to yanzu me kike ganin za ki mata wanda zatasan cewa ta tabo uban Zahra? Murmushin mugunta Zahra ta yi tana cewa hajjo muje koma me ye zaki gani Zahra ce fa ai Ni bana rasa salon daukar fansa kullum ina tare da makamaina a hannu saboda shirin katsaham kamar dai wannan", Tom shike nan muje.

Su nadiya suna kallo suka fice basu da damar hanawa yanzu fadan ya dawo kansu.

Suna fita Zahra bata tsaya a ko ina ba sai kofar gidan maman Sadik,kamar wancan lokacin kira ta shiga kwada mata,da gudu maman Sadik ta fito tana cewa amarya me kina so yau kuma? Dage gira Zahra ta yi tare da cewa maman Sadik yau ma aiki ne ya taso kamar waccen ranar sai dai akwai banbanci da na waccan ranar saboda yau karnukanki zasu ci agara idan da hali su hada yatsu duk babu wani abu asarar ba tawa bace,an gama amerya",a'a fa mana Sadik amaryar nan ta fita a bakinki idan ba haka ba zamu bata wlh", da sauri maman Sadik ta rufe bakinta tana cewa shike nan Zahla bani karawa sorrio kaji",

Kafin maman Sadik ta fito tuni Zahra ta tare okada, hajjo ta ce", to wai Ni Zahra kin san gidan kuwa? Shiru Zahra ta yi tana dan tunani kafin ta ce", ey zahraddin ya taba min kwatance shi wai dole yana gabatar min da kansa dan haka ina ga zamu gane tunda ba biyayye ba ne", haka ne"hajjo ta fada tana satar kallon kofar gidan su Zahran dan kar wani ya fito ya gane Zahra duk danta rufe fuskarta,dai_dai nan maman Sadik ta fito da karnukanta,Zahra ta dubeta ta ce", maman Sadik gaskiya bazan shiga nafef da kare ba sakan ya cije Ni yadda karnukannan baki basu da hakuri da sabo,dan haka bari na tsayar da wani sai ku shigo ku biyo bayanmu", to ba masala hakan yayi dai dai cewar mana Sadik kenan.

Dake ba wahala abun hawan suke musu ba, cikin kankanin lokaci suka samu wani suka hau, ita kuma maman Sadik ta hau wanda suka tare da farko nan dai suka dau hanyar gidansu zahraddin........

Lokacin da aka gama daurin auren farira da zahraddin karfe sha daya da rabi da mintuna bakwai, cikin sauri sauri zahraddin da Abbansa suka fito dan tafiya daurin auren Zahra, alokacin maman tunde tuni ta dawo gida kuma ta maida musu wayoyinsu ba tare da sun ankara dama basa jikinsu ba.

Suna shiga Mota Abba ya ce", da zahraddin maza kira min Abban Zahra mu bashi hakuri dan gaskiya munyi musu laifi gashi babu wanda yayi musu waya ya sanar dasu wani abu wlh bamu kyauta musu ba," zaro waya zahraddin yayi ya shiga kiran wayar Abba Zahra sai dai ina yaki dagawa sai da yayi masa kira wajen goma sannan ya daga ba tare da ya ce", komai ba, Abban zahraddin ne ya yi magana, kayi hakuri abban Zahra wlh Wani uzurine ya shigo kuma na nemi wayoyina duka na rasa da zan kiraka amma yanzu gamu nan mun taho ayi mana afuwa dan Allah.....

Abban Zahra ya dan aje numfashi sannan ya ce ", kar ka damu sakonka tuni ya iso,dan haka ba sai kayi wani kame_kame ba Ni tuni na daurawa yata aure da wanda suka san darajanta, ka daina yi kamar baka san abinda ke faruwa ba", take Abban zahraddin ya shiga yiwa abban Zahra rantsuwa akan bai san kome dake faruwa ba,dan haka kai tsaye ya ce dashi ya shiga facebook zai gani idan ma bai sani ba,daga haka ya kashe wayar gaba daya dan baya bukatar wata magana daga baya tunda aikin gama ya riga ya gama.

Sosai hankalin zahraddin ya tashi ganin video abinda ya faru ,Abba kuwa wata irin kunya ce ta kama shi tare da tausayin baban Zahra,sai dai ta wani bangaren yayi farincikin ganin wanda ya karbi auren da wanda aka bawa Zahra a matsayin miji, take shima ya kuma tabbatar da cewa lallai wani hanin ga Allah baiwane kuma rabonka duk inda yake bai wuceka dan haka shi sai dai yayi masu fatan alkhairi,kuma in sha Allah zai je har gida yayiwa baban Zahra bayanin komai cikin nutsuwa dan baya so ya rike shi a zuciyarsa kamar yadda yaga alama daga gareshi yanzu.

Yana can yana wannan tunanin sai juyowa ya yi yaga zahraddin ya sume masa,babu shiri yasa drevan ya juya da motar suka koma gida.

Ko a gidan ma tuni labari ya watsu tunda abu ne na social media,kankace me an rufu akan zahraddin da kyar aka samu ya farfaɗo sai dai yana farfadowa ya ce", ya saki farira saki uku wlh sai dai kowa ya rasa kuma barin garin zaiyi yanzu tunda ya rasa Zahra..

Ihu farira da aka sha ado ta saka haka maman tunde,tuni ta soma kukan anci mata mutunci,amma babu wanda yabi ta kanta dan sosai ta ɓatawa mutane rai da abinda ta yin,zubewa farira ta yi babu alamun numfashi a tare da ita, hakan yasa maman tunde ta fita waje da gudu tana neman daukin mutane dan duk yan bikin sunyi biris da ita sai ma hada kaya da suke zasu tafi inda suka fito.

Dai-dai lokacin nafe din su Zahra ya shigo layin, tun daga nesa Zahra ta gane maman tunde dan sai da ta kalleta sosai a dazun dan haka ta saki murmushi tana cewa Zahra duk inda take me sa a ce, tunda na shiga nafef dinnan nake tunanin hanyar da zanga matarnan ita kadai kuma a sararin da zan saka ta gudun ceton rai sai gashi Allah ya kawo dauki alhamdulillah ", dariya hajjo ta yi tana cewa ey wlh ko Ni na shaida Zahran kaka me sa a ce tunda ga yanayin aurenki ma", tura bakin da Zahra ta yi cikin ƙunkuni da shagwaba shi ya ankarar da hajjo katobarar da ta yi nayi mata zancen auren,dan haka cikin sauri ta rufe bakinta tana cewa na tuba Zahran kaka", dariya su kayi gaba dayansu sannan Zahra ta ce", me nefe tsaya anan bana so muyi gab da gab da ita na fiso su bita dw uban gudu dan naga alamar bata da kafa me kwari.

Haka kuwa akayi suka tsaya maman tunde ta saki karnuka ta lafe a cikin nafef tunda yau an bawa karnukanta damar cin agarar tsohuwar banza kuma tasan ko ta tafi tsaf zasu kai kansu gida dan kuwa ba karamin horo suka samu ba.

Maman tunde nacan na ihun neman taimako kawai sai jin haushin karnuka ta yi ta bayanta ,tuni mutane da yara suka fara yin takansu hatta da masu dauriyar rashin tsoro sai da suka sa gudu dan karnukan maman Sadik babu maganar wanda suke ji sai ta ubayen gidansu wato ita da mijinta sai ko karanta.

Zaro kwala_kwalan idanunta ta yi tana cewa wayyo wannan karnukan daga in....kafin ta karasa tambayarta ta rashin hankali tuni sunyo kanta aiko ta wani irin kwasa da gudu,gashi taci uban zanin farin leshinta da Goggoron bikin da har yanzu yana kanta, tuni zanin ya fara hardeta gwaggoron kuwa ya zamo saman fuskarta ya rufe mata ido ta yadda bata iya ganin gabanta,take taci uban tuntube ta kifa kanta da hancinta da bakinta lokaci daya hakorin gaba guda biyu suka cire, ga azaba ga karnukan na gab da cimmata haka ta daure ta mike tare da zare zanin gaba daya daga ita sai under din ciki ta wasa da gudu tana ihun temako fyskarta duk ta ɓaci da jini.

Zahra kuwa suna daga cikin nafef suna kallon abinda ke faruwa ga hajjo na yin video cikinsu tamkar zai yi ciwo saboda dariya .....

Cikin dariya Zahra ta ce ", kai wlh tsohuwar nan akwai karfin hali, karfinta fa bai kai na tayi wannan gudun ba amma duba yadda ta zage take zagaye anguwa daga ita sai dan kamfai,gashi ta kasa yin dabarar shigewa gidan dan ta ceci kanta,cewar hajjo da take goge hawayen dariya, da ke ba a daya a dangi itama kusan halinta Zahra ta dauko dan haka ko ajikinta........✍🏼

Zahra ki yi hakuri haka mana ke da Allah ya kashe ya bawa dan gidan yarbawa🤣🤣🤣

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol