Free chapter · Read without an account

Pg22

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

*SUBY COLLECTIONS &* *MORE....*

*Ina kuke? Nace ina kuke?*

*Ey *nace* *kowa ya zo* *kusa* *mata maza iyaye** *yayyaye da duk* *me son fita kunya,*

*Ina iyayen da suke shirin* *aurarwa?*

*Ina matan da suke shirin* *yin tariya?*

*Ina mijin da yake son* *burge matarsa?*

*Ina dan da yake son* *farantawa Mahaifiyarsa* *ko* *kanwarsa?*

*To duk ku matso nan dan* *kuwa sauki ya zo* *muku ta hanyar* *shahararriyar yar* **kasuwar nan SUBy* *COLLECTIONS & MORE* *tana saida kayan* *daki na kece raini* *kuma na fita* *kunya,ga kayan kiching* *na kere sa a duk* *abinda kuke bukata* *a har kar gida* *tana da shi,kuma masu* *son burge mazajenku ko* *masu son burge* *yanmatansu ta bangaren* *kayan sawa* *zaku iya samunta, tana* *hada lefe na kece raini* *da fita kunya, kun dai san* *in aka ce lefe to ana* *nufin komai da* *komai ko?*

*Haka a bangaren kayan* *yara nan ma ba* *abarta a baya ba kai na* *takaice muku labari dai* *takenta shine komai da* *ruwanka dan haka kawai* *ku taho ku* *tuntube mu dan faranta* *ranku,*

*A bangaren kayan yaji* *ma duk ba abarta baya* *ba, yajin daddawa yajin* *tafarnuwa farin yaji da* *kuma kayan kamshi* *masu *kankaro martabar* *mace wajen* *miji dan babu* *ke babu** *kunyar zuwan* *abokan miji cin* *abinci...ku dai ku* *nememu kawai mu kuma* *zamu fidda ku* *kunya*

*Zaku iya neman ta ta* *wannan lambar kamar* *haka*

**** ko* *****

*Muna nan muna jiranku* *mutanen* *amana.*

*Kar ku manta da sunan* *fa*

*SUBY COLLECTIONS &* *MORE........*

......... cikin damuwa mama ta dubi Abba ta ce ", sai hakuri wata rana wlh zata daina mu godewa Allah ma da ba wani mugun halin take yi ba", tsaki Abba ya yi tare da cewa au kina nufin wannan addabar mutanen da ta yi shi ba mugun hali ba ne? Ke da kanki fa kika sanar dani abinda tayiwa mutanen nan ana i gobe bikinta razana musulmi ba tare da wani dalili ba,kuma kin san hakan babu kyau ko itama nasan ta sani tunda ba jahila ba ce ba,to bari kiji na gaya miki wlh na gaji da wannan halin na Zahra kullum fa sai an kawo min kararta ina dawowa da abinda ake fara tarata kenan dan haka bazan bari ta dade a gidannan ba Gara ta tafi can dangin mijinta su gyara mata zama ", tashi yayi yana cewa zuwa zanyi Companyn na samu shi AB din na gaya masa komai dan kar suce na yaudaresu dan halin Zahra tsaf zai yi sanadin mutuwar aure ,daga haka ya fice yana kabe babbar rigarsa.

Zahra kuwa tuni ai ta tsufa a Company dan ko su nadiya bata biyawa ba,duk da cewa bata da tabbacin basu tafi ba.

Tana shiga sai ga motocin AB sun jero kamar yadda suka saba,rakubewa ta yi a gefe tana kallon yadda ake ta wani tattalin hanyar da zai taka sai kace wani sarki",tsaki ta yi cike da jin haushinsa tama cewa wannan mutum duk wadda ta auresa ta shiga uku dan wlh babu ita ba farinciki yo kullum fuska kamar ana gasa masara babu annuri ko na gamin gafara,sai fa a lokacin ta fara tunanin aikin da zata yi tunda dai ga yadda suka kare da Oga kwata kwata,wata zuciyar ta ce da ita Kema dai da kin tsaya Sunyi magana da Abba duk da ba haka ba,yanzu kin san wane aiki zaki tunkara ne? Ta tambayi kanta rashin amsar da zata bawa kanta yasa ta samu waje daga can nesa ta zauna bisa kujerun hutawa na wajen tana ci gaba da tunanin mafita.

A can bangaren su Ab kuwa cikin sababben yanayinsa ya fara taku zuwa mahayarsa, jafar yana bayansa,daga kan da jafar zai yi sai ko ya hango mutuniyar tasu tana ta zabga masa harara har dasu murguda dan tamilon bakinta.

Dariya kawai ya yi tare da yin salut dinta a ransa yana cewa ina Ni ina fada da matar oga sai ban girma", Zahra kuwa harara ta kuma wurga masa kana ta ce", ji wani rainin hankali dan yasan abinda suka shirya min shi yasa yake yin salut dina munafiki dan Kore kawai", daga haka ta ci gaba da zaman rashin madafa ...

AB bai dade da shiga ba jafar ya shigo da Abban Zahra cikin sabuwar girmamawa.dan a ka ida ba dan matsayinsa ba ba zai samu damar ganin Ab a wannan lokacin ba.

Shima AB din duk da baisan Abba ba cikin girmamawa suka gaisa duk da dai fuskar tana nan a yadda take a kame ma..

Abba bai damu ba dan yasan waye Ab din shi din mutum ne me karamci da kyautatawa amma bashi da fara a,mutane basu da mu da fara'arsa ba tunda hannunsa na alheri ne.

Zamansa ya dan gyara sannan ya fara rattabo masa da bayanin da sam baya fahimtar inda suka dosa bare tushensu,abu daya ya rike shine sunan Zahra da dabi un da yake zanowa irin na yarinyar da ya bata sunan ciwonkai, sai kuma hakuri da ya bashi akan dawowar dai wannan ciwonkan da suka yi baran baran da ita baya haka bai fahimci komai ba.

Dan haka dan ya takaita zancen sai kawai ya ce", cikin kamammiyar Muryarsa baba ba damuwa ta dawo, daga haka ya yi shiru yana ci gaba da taba tap din dake gabansa", jafar da ya fahimci komai da kuma abinda Abba yake nufi da son fahimtar dasu ya ce", shi kenan baba kaje baka da damuwa in sha Allah zamu rike amana kamar yadda ka bamu tunda kaga abin ya zama biyu gata matar oga kuma gata ma aikaciyarmu",

A hankali Ab ya dan kalli sashen da jafar ke tsaye tun dazun a karo na farko jin ya ce matar oga,shi dai a iya saninsa babu wani da suke kira da Oga sai shi,to me hakan ke nufi?

Ya tambayi kansa, kansa yana dan sarawa da tuna auren da dady ya ambata masa duk da cewa bai dauke shi da wani abu ba bare har ya dame shi.

Shi ko jafar kawar da kansa ya yi yana jin dadin yadda sakonsa ya yi saurin zuwa inda ya turasa,yauwa baba muje na taka maka", a'a na hutar da kai Abba ya fada yana ƙoƙarin fita,amma duk da haka jafar saida ya rakashi kofar main office na sectarea siyam da bakinciki ya hanata fitowa. Sannan ya bashi sakon da Ab ya umarta da ya bashi,daga nan su kayi sallama Abba yana ta godiya da saka albarka Duk da yaso kin karba jafar din bai basa dama.

Koda ya dawo office din AB yana nan a yanda yake banbanci kawai yanzu ya cigaba da aikinsa.

Zama jafar ya yi yana dan sunkuyar da kansa dan ko Ab bai yi magana ba yana gane shurunsa da kallonsa,dan haka tun kallon da ya yi masa ya fahimci ma anarsa,cikin nutsuwa kamar yadda yasan Ab din ya fi fahimtar zance idan ka yi matukar nutsuwa.

A hankali ya warware masa zare da abawa kuma yayi masa fashin baki akan dalilin zuwan Abba, ma ana dai yana so Ab din yasan halin Zahra kuma ya dau aniyar yin hakuri da ita tare da kawo kyakkyawan gyara cikin rayuwarta...

Tunda jafar ya fara magana AB ya zuba masa ido,bashi ya dauke idanunsa daga kansa ba har sai da yaji ya yi shiru kansa kuma har yanzu a sunkuye alamun dai ya gama,sosai idanun Ab suke da wani irin tasiri akan duk wanda ya kalla. Shi yasa gaba daya jafar ya kasa sukuni sai mutsumustu yake yi fatansa Ab ya dauke wannan shuuman idanunsa daga kansa tunda bashi ya kar zomon ba hasalima ko ratayar ba a bashi ba.

A hankali Ab ya dauke idanunsa tare da furzar da wani zazzafan huci ta bakinsa,bai ce komai ba ya juya ya cigaba da aikinsa.

Jafar Yana samun Ab ya dauke idanunsa daga kansa yayi wuf ya mike bai saurari komai daga bakinsa ba ya fita,dama bai yi tsammanin zai ce din ba kuma bai fahimci komai a kan fuskarsa ba,kai gaskiya Oga karshe ne a wajen rikita mutum", jafar ya fada bayan ya ganshi a ofishinsa,yasan dai Ab din ya fahimci abinda ake nufi wato Zahra dai matarsa ce ita ce wadda dady yayi kundumbalar karba masa aurenta....

Dan dakatawa ya yi da taba tap din bayan fitar jafar,dan jim yayi kafin ya mike ya shiga bathroom,fuskarsa ya watsawa ruwa har zuwa kwantacciyar sumarsa ta larabawa me tsananin sheki baƙa sidik,towel ya dauka ya fito yana goge fuskar tasa yana dan jin sauƙin zafin da kansa ya dauka..

Cire towel din da yayi yayi daidai da shigowar Zahra office din bakinta dauke da sallama wadda zai ce bai taba ji ta yi ba.

Kallo daya ya yi mata ya dauke kansa dan idan ba tsananin nutuswa kayi ba baka taba fahimtar ya yi kallon,a kujerar hutu ya zauna yana daukar wayarsa da tayi haske alamun kira,karasawa ta yi gabansa ta yi zaman dirshan dan yau maslaha ce ta kawota ba fada ba,tunda tana so ya barta ya kuma canja mata aiki dan kawai ta nemo mijin da aka liƙa mata.

Bai dube ta ba ya ci gaba da wayarsa da duk yadda take kusa dashi bata wani jin sautin muryarsa, sai da ya dauki kusan mintuna goma yana magana a wayar kafin ya ajiyeta alamar ya gama,Zahra na ganin haka ta yi saurin yin durkuso kana ta ce", yallabai ina kwana ya aiki? Banza ya yi mata kamar ma bai san da mutum a gun ba,tura baki tayi kafin cikin ƙunkuni ta ce", shi mutum bai so a zo masa da arziki bayan ma ka samu yau ban kullo wata rashin jin a zanina ba shine zaka wani ci min magani da kin amsa gaisuwata,nata saurari abinda zai ce ba dan dama bata sa ran zai ce din ba,ta ci haba da cewa.

Ni kam dan Allah ka canja min wannan aikin dan nasan Abba na yazo tunda naga fitarsa nasan kuma baiyi maka maganar canja aikin ba,Tom shi yasa nazo da kaina, zan ci gaba da aiki ne ba wai dan wani abu ba kawai ji nayi ance wahalallan mijin da aka liƙa mun a nan yake aiki shi yasa zan cigaba da aikin dan kawai na nemo shi na gurza rayuwarsa a cikin Companyn nan ba tare da anje ko ina ba ya saki auren", har ta kai aya Ab yana jingine da kujerar idanunsa a lumshe,sai dai abinda Zahra bata sani ba yana jinta kuma yana kallon karamin bakinta ta can ƙasan ido yadda baka taba fahimtar idanunsa a bude suke ma bare a kai ga tunanin kallo.

Kallonsa ta yi tare da zaro manyan idanunta baki bude ta ce", lallai ma wannan mutumin wato ma bacci yake yi duk wannan zubar da nake yi,yanzu duk wannan bayanin da nayi sai na sake? To idan kuma na manta wani abu fa? Wallahi bazata samu ba ta fada cikin son fashewa da kuka tare da mikewa tsaye, cikin sanda ta kuma yin taku daya zuwa uku sannan ta dakata,leka fuskarsa ta shiga yi dan son tabbatar da baccin yake yi,har da sa hannunta tana dan fifitasa sai dai ko motsi bai yi ba,rike kugu ta yi tare da furzar da iskar bakinta sannan ta ce", wallahi babu inda zani har sai ka tashi ka bani aiki na san makomata,dama ai dole yanzu kayi min abinda ranka yake so tunda na shiga hannunka Ni nake nema", daga haka ta wuce ta zauna akan kujerar office dinsa, sai kuma ta saki murmushi tare da janyo tap dinsa ta sauki glass dinsa ta saka take ta shiga juyi a cikin kujerar ta kuma hade kyakkyawar fuskarta wai ita a dole zata kwaikwayi abinda yake yi....

Duk abinda take yi yana kallonta ta kasan ido,sosai ya shiga mamakin yarinyar da rigimarta lallai dole Abba ya shiga damuwa akanta dan bata jin magana sam....

Maganar da ta shiga yi a hankali fuskar nan a cushe ita ta dawo da shi ɗan tunanin da ya fada,yadda yake magana da jafar ta ke kwaikwaya harda yadda yake taba tap din,dan tsuka ya yi yana dan rufe idanun gaba daya,karfa ta je ta yi masa wata barnar ,to amma kawai sai ya samu kansa da kasa kwabarta ci gaba ya yi da kallon dramatic girl din da aka kira da matarsa...

Zahra kuwa sosai ta shagala da abinda take yi dan kuwa abun yana bata nishadi, sai da yaga abin nata ba na karewa ba ne sannan ya yi gyaran murya tare da bude idanunsa sosai akanta,zabura ta yi ta mike ta shiga sosa gefen fuskarta alamun dai rashin gaskiya,jikinta ne ya bata kallonta yake duk da cewa tun dazun take jin wannan yanayin na kamar akwai idanu masu kaifi akanta,tura mitsitsin bakinta na rashin barin takwana ta yi tare da dan hararan gefensa ba dai ta ce komai ba har yanzu dan haka nan yau dinma kwarjinin idanunsa suka hanata sakat.

Shima bai ce da ita komai ba ya mike tare da nufar inda take kai tsaye,da sauri ta jiyo saboda jin ƙamshinsa na dada karuwa a hancinta aiko sai karaf suka haɗe idanu gashi a dab da ita,kafin ta samu damar yin magana yakai hannunsa saman fuskarta wanda yasa ta wani zaro idanun baki bude zata yi magana sai kuma taji ashe glass dinsa da ta manta yana fuskarta ya zare, ajiyar zuciya ta sauke tana ci gaba da yi masa hararar kasan ido da haka kawai ta kasa baiyanata,

Ba abinda kike so ba ne Ni ba dan iska ba ne", taki saukar tattausar muryarsa kamar daga sama cikin kunnuwanta,aiko take ta yi wani dan ƙaramin tsalle tare da yarfa hannu kamar wadda wuta ta taɓa,cikin murguda baki ta ce", Ni kam ba yar iska ba ne eh, kuma mutum ya daina taba Ni dan yanzu na kuma zama haramun ga yan is...buf ta ji ya bige bakinta kafin ta karasa kalmar iskancin,duk kika kuma kiran wannan kalmar a gabana sai na nuna miki karshen iskanci wuce ki bani waje kuma aikin shi zaki yi," wuce ta yayi yana dan sakin karamin tsaki tare da cewa Allah ya dubawa wannan bawan Allah da aka lika masa ke ,fitinanniya kawai",

Karar buga kofa kawai yaji ta fice a matukar zuciye,lumshe idanunsa ya yi( a idona Ni dai sai naga kamar murmushin gefen baki ya yi to amma nayi nan kar ace min yar tsurku).........✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol