Free chapter · Read without an account

Pg23

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

.........tana fita da har zata tafi gida sai kuma ta fasa ta nufi hanyar room dinsu,anan ta samu su nadiya suna ta aikinsu cikin kwanciyar hankali,waje ta samu ta zauna ba tare da ta ce musu komai ba.

Zaro ido nadiya ta yi sai kuma ta kalli hafsa suna so su yi magana suna tsoro,dubansu Zahran ta yi sannan ta dan tabe baki ta ce ", ku yi maganarku ku daina wani kwana kwana Ni ban san munafunci", Hafsah ta ce", Zahra ya a kai kika dawo kuma? Dawowa nayi saboda dalilin da bai shafeku ba,ta fada tana tsaresu da idanunta kamar wata boss,yi hakuri maida wukar nadiya ta fada tana ci gaba da aikinta

itama bata kuma cewa komai ba shiru tayi tana kulla me yiwuwa.

Gab da zasu bar Company,jafar ya samu wayar dady,dagawa ya yi cikin girmamawa tare da gaishesa,daga can bangaren dady ya ce,jafar lallai idan kun tashi yanzu ka wuce da Ab gidan surukansa ya gaidasu idan da halima ya gana da matarsa dan bana so muja lokacin bikin", Tom shike nan dady in sha Allah zamu je dama yanzu muke shirin tafiya dan fitowarsa ma nake jira", yauwa to Allah yayi muku albarka", amin ya Allah jafar ya amsa yana kashe wayar.

Zahra yau dai kin jira mu antashi kafin ki kuma baudewa", nadiya ta fada tana hada kayansu zasu tafi.

Ni bana son gulma idan kungama ku same Ni a waje zanje bandaki", cewar Zahra tana yin gaba ba tare da ta saurari abinda zasu ce ba. Da kallo suka bita kafin Hafsah ta ce", kai Zahra ta cika neman rigima tsaya fa kiga ba bandakin zata je ba wata tsokanar zata yo.

Zahra kuwa da gasken hanyar bandakunan nasu ta nufa, duk da cewa bata taɓa shiga ba dan ita tsentseninta baya barinta shiga banɗakin makaranta da na Company,amma yau saboda tana son gani ko zata iya aikinsa idan har Ab bai canja mata wani aikin ba yasa ta zuwa.

Sai dai kuma tun kafin ta bude banɗakin ta fara jiyo wani nishi da maganganu ƙasa ƙasa daga ta can bayan bandakunan,tauru ta yi tana tunanin ko dai aljanun wajenne suke wani Shagalin, har zata komawa saboda ta danji tsoro sai kuma ta fasa kawai ta nufi inda take jiyo nishin dan haka nan taji zuciyarta ta dake.

Na shiga uku me zan gani kwartanci a Companyn Ab ", Zahra ta fada cike da tashin hankalin yanayin da ta kama su femi ita da wani saurayi da bata tantance fuskarsa ba,( femi budurwar da suka fara fada da Zahra a Company farkon zuwanta har ab ya Koresu daga baya aka dawo dasu).

Da sauri suka saki juna suna faman raba ido, ita ko Zahra tuni ta saka kuruwa,jama a kuzo na kama kwartaye eho jama a ana iskanci a bayan bandakunan Company,kan kace me har Zahra ta tara musu jama a.tana ganin mutane sun rutsasu ta ce", bari na kirawo ogannin su zo su gani da idonsu babu sharri", daga haka ta baza da gudu sai hawan Oga AB,na samu hanyar da za a canja min aiki ko ba komai na ceto Companynsa daga shiga wuta ", ta fada tana haurawa ba tare da ta bi lipter ba.

Dai_dai lokacin Ab ya fito dan tafiya, shima bai bi ta mahaya ba kai tsaye doun step ya biyo hannunsa rike da waya daya saboda jafar ya fita da komai.

Zahra kuwa da gudu_gudu take hayewa saman jikinta har rawa yake yi yau za ayi tashin hankali.

Siyam da ta hango zahra itama fitowarta kenan dan tafiya dan yanzu ta daina bari Ab ya fara tafiya saboda abinda ya faru,ta gwammace ta yi gaba dan karma taga tafiyarsa bakinciki ya kusa kasheta.da sauri ta koma office ta dauko bawan ayabar da ta ci a cikin dusbin tana fitowa ta jefawa Zahra a hanyar step na ukun karshe,ita ko Zahra Sam bata kula ba mita kawai take akan da ta sani ta biyo mahaya wannan jarabar tsayin matakalar ai dole a saukaka ta hanyar yin lipter,bata ankara ba sai jinta ta yi ta zame lokaci daya kuma ta yi baya zata gangara.

Salati ta saka, tana cewa shike yau Zahra zata mutu a hanyar Allah Allah na tuba Allah ka dubi niyata ta zuwa wajennan ka kara min tsawon rayuwa, Allah ga Zahra yar mama Allah ka karka kasheni banga danbalaja U shafaffe da man da aka likamin a matsayin miji ba," a shirmen Zahra duk shirmen maganganun da take yi wai bata fara gangarawa ba Allah ya bata dama ta gama wasiyyar da rokon tsawon rayuwar tukuna, jin har ta gama surutunta bata jita a kasa ba yasa ta fara bude idanunta a hankali sai me caraf idanunta suka sauka kan Ab da shine ya tareta da dogayen hannayensa ta fado jikinsa,da sauri ta dubi jikinta taganta Male Male jikin oga,sai a lokacin ta tuna yadda taji wani taushi me dadi wanda yafi laushin katifar mama a lokacin da ta zame,cikin sauri ta yunkura tana kokarin barin jikinsa tana cewa wayyo kwarto naso kawo karar kwarto na hadu da dan is......kafin ta karasa ya wani irin fincikota ta dawo jikinsa bai yi wata wata ba ya hade mitsitsin bakin da ya kware da fadin dan iska da kwarto cikin nashi karamin bakin da yake wani irin ƙamshin sweet mint na strawberry.

Zaro manyan idanunta ta yi jikinta yana daukar rawa, shiko Ab da mugunta yake tsotse harshe da miyan bakinta tare da karamin labbanta,duk yadda taso kwatar kanta ta kasa.

Siyam da komai ya faru a gabanta tuni ta ɗora hannu aka ta ware baki zata fasa ihu da gangan,sai ji ta yi an fizgota tare da rufe bakinta an janye ta daga wajen gaba daya,sai da ya shiga lipter da ita sannan ya sakar mata baki tare da dage mata gira,jafar wannan wane irin salon wulakanci ne? Dariya yayi yana cewa ramin mugunta na haka sai kuma na fada dan haka dole nayi hakuri na yi zamana a cikinsa tunda Ni na haka a bina", wani mugun kallo ta yi masa tare da yin kwafa tana matukar jin haushin abinda ya hanata yi,taso tara musu jama a ta bawa ab kunya fiye da kunyar da ya bata,to amma idan yau bata samu dama ba wata rana zata samu.

Kamar jafar yasan abinda take tunani ya ce", ki daina tunanin zaki kunyata Ab da Zahra dan kuwa su din hadin Allah ne", daga haka ya fice daga mahayar ya barta sake da baki.

A can kuwa tun Zahra na mutsumutsun kwatar kanta har ta gaji ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido, wannan shi ake kira kayi nayi, ita tazo kawo karar wasu ita ma gashi tana samun tabonta,zare bakinsa ya yi daga nata tare da sakinta yana Binta da wani shu'umin kallo, goge bakinta ta shiga yi tana cewa nazo na gaya maka ana aikata haram a Company ka sai ka kama matar aure ai in haka ne kai naka ya fi nasu dan jefe k....kallon da ya watsa mata yana matsowa kusa da ita yasa ta yi shiru.

Tura bakin ta yi tana gunguni,juyawa yayi ya koma zai bi ta mahaya da sauri tabi bayansa tana cewa ina zaka kazo muje kayi musu hukunci kai kuma hukuncinka yana hannun lusarin mijin da aka liƙamin, dan dole kafin ya sake Ni sai na gaya masa abinda kayi min saboda fita hakkin Allah ", daidai lokacin suka iso mahayar shiga ya yi tabi bayansa bata ko tsoron ya kuma yi mata abin dazun,dafe kanta ta yi tana cewa wai Allah da yanzu Zahra na lahira ko gadon asibiti,ko da ike addu'ar da nayi ce Allah ya karba ta hanyar turo min ɗan.....sai kuma ta waske da ci gaba da goge bakinta da har yanzu radadi yake mata gashi yayi jawur alamun yaji maza.

Suna fitowa daga mahayar suka tarar an kawo su femi bakin wajen inda Ab ba zai sha wahalar tafiya ba,jafar na wajen dashi da manager da sauran manyan Company,su femi kuwa suna durkushe daga dukkan alamu duka suka sha a hannun kananun ma aikata.

Zara ce ta yi zaraf ta ce", oh su femi ashe a taba harka, duban AB ta yi tana cewa Wallahi da ina da waya sai nayi musu video dan baka ga yadda ya kwakumeta yana cinye bakinta ba kamar wani halalinsa,dariya kafar ya yi dan yasan wannan maganar tata ba da kowa take ba sai da Oga,shi dinma yasan dashi take sai dai ko kallon inda take baiyi ba.

Kallon su femi ya yi sai dai ya kasa cewa komai, sai ya bude baki zai yi magana sai kuma ya yi shiru,cike da mamaki Zahra ta kallesa ta ce", Oga ya dai ko ciwo bakin yake maka ne? Bai ce komai ba ya dubi jafar wanda tuni ya fahimci abinda ogannasa yake nufi,da sauri jafar din ya ce da su femi ku tashi ku.tafi an sallameku daga aiki za kuji alert ɗin aikinku na kwanaki", daga haka yabi bayan Ab da tuni ya shige motar da josuwa ya bude masa.

Harara Zahra ta bisu dashi ranta be so aka tsaya a iya wannan hukuncin ba,ita ce farkon wadda ta fara yiwa su femi ihu da yi musu dan kira aiko masu jiran kiris suma suka fara a haka suka raka femi da saurayinta har waje,daga nan suka dau hanyar gida.

Hafsah ta ce", Zahra kin kula da kallon da saurayin femi yake miki kuwa? Nadiya ta ce", tabbas Nima na kula akwai wani abu da ya kulle a ransa game da Zahra dan tabbas sunji zafin abinda kika yi musu", yarfa hannu Zahra tayi tana cewa oho musu duk ma abinda suka kulle Allah ba zai basu dama ba in dai nice dan kuwa Zahra kafin Allah ce", amma dai da kin sani baki tara musu jama a ba", cewar nadiya tana tsoron abin da hakan zai janyo,a karo na farko Zahra ta yi murmushi sannan ta ce", ku kwantar da hankalinku kawayena babu abinda zai faru in sha Allah", to Allah yasa daga haka suka ci gaba da tafiya suna mai canja wata hirar....

Bash saurayin femi da yake bahaushe ya dubi femi bayan sun bar ereal Company gaba daya suka samu waje suka tsaya,ya ce", a wannan karon ba zan bar yarinyar nan ba,tabbas ta daukowa kanta ruwan dafa kanta ,femi da duk ta shiga damuwa akan rasa aikinta da ta yi ta ce",bash shi yasa ban so ka ce yau mu yi a cikin Companyn ba wlh"

Kar ki damu femi zan je nayi shirin daukar fansa zan yi nisa da nan sai na tabbatar ta sakankance zan yiwa rayuwarta dirar mikiya", Ni kam bash zan bika duk inda zaka tunda idan ma na zauna bani da kowa idan ba kaiba,in yaso sai muyi aurenmu", a'a femi idan zaki bini ki bini amma babu batun aure domin kudi zamu nema dan lokacin yinsu ya yi ko ta wane hali", ya fada yana kunna wiwinsa tare da watsa wasu kwayoyi a bakinsa,shike nan na amince,kin amince duk sana ar da zanyi zaki yi? Ey na amince,daga haka su kayi deal tare da aje lokacin da zasu tafi....

A fusace siyam ta shiga falon,sai dai ganin mamanta da ta yi yasa ta yi wani irin ihun murna ta rungumeta sai kuma ta saki kuka kamar wata karamar yarinya,Ammi ce ta kama baki cikin mamaki ta ce", oh siyam duk kukan murnar ganin mamanki ne wannan?dariya maman tayi tana bubbuga bayan siyam din ba tare da ta ce komai ba dan dai ita tasan dalilin kukan yartata,tashi Ammi ta yi tana cewa siyam aike ba yarinya ba ce ya kamata ki daina abin yara",

Harara suka raka ammin da ita daga nan siyam ta janye maman suka kule a daki.

Zahra na zuwa kofar gida ta ci karo da motocin AB ,dafe kirji ta yi tana cewa na shiga uku ba dai mutumin nan karata ya kawowa Abba ba? Tab aiko da kwai yar tone_tone dan wallahi Nima sai na gayawa Abba ya sha min baki", tana fada tana shigewa gidan da shirin ko ta kwana.......✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: **YAR GIDAN YARBAWA*.......😍

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol