Free chapter · Read without an account
Pg26
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*****
*****
.......jiki a sanyaye amina ta fito, sai dai me Zahra ta gani ta tare hanyar.bata tanka ba sai kawai ta zagaye Zahran zata wuce,aiko Zahra ta yi mata wata figa ba tare da ta tsaya komai ba ta bata kyakkyawan mari a fuskarta tana cewa,Ni zakiwa munafunci? Wato kin manta wace Zahra ko ? To tunda kin manta bari na tuna miki,kafin Amina ta samu damar kwatar kanta tuni Zahra ta zare hijab din jikinta tana cewa a kanki zan fara cajen yanzu haka ma kin sace wani abun shi yasa kika je kika gayawa mama saboda kitsira", me haka Zahra ki rabu dani cewar amina tana kokarin kwace kanta.
Kwace hijabinta Zahra ta yi bayan ta gama yi mata cajen yan makaranta, sannan ta kirawo yaran gidansu da suke kofar gidan suna wasa ta ce", maza ku raka min ita gida a haka ku hada da watsa mata kasa kuna yi mata wakar munafuka me bakin angulu",aiko yara sun samu nayi take suka fara abinda Zahra ta saka su,da sauri amina ta bar gurin su kuma suna binta a baya da wakar da Zahra ta koya musu,kuka Amina tasa saboda yadda mutane suke binta da kallo kuma duk wanda ya tambaya ko ya hana yaran da anji sunan Zahra ake matsawa tare da jan bakinsu su tsuke.
Hegiya munafuka Zahra ta fada tana maida kallonta kan maman Sadik da ita ce ta ukun fitowa.
Washe baki maman Sadik ta yi tana cewa amarya zahla ka tako arziki me kyau Allah ye baka zaman lafiya kaji yaron kilki", Harara Zahra ta zabga mata tana cewa kinga babu ruwana da wannan maganganun naki dan kuwa yau babu sani ba sabo caje ki zanyi tsaf ciki da waje babu kara bare alkunya.
Take kirjin maman Sadik ya fara dukan tara tara,mayafinta ta kuma gyarawa tana kame kame, haba zahla kar muyi haka da kai", ke Malama nasan fa halinki da rashin daukar ƙaddara dan haka wlh sai na caje ki zaki bar wajennan",
Bata saurari abinda maman Sadik din take shirin fada ba,ta fige mayafinta da take ta cukyikyiyewa a hammata,tana figewa saiko ga wasu kayayyaki sun fado doguwar rigar me shegen kyau wadda kudinta zai tasamma dubu dari da ashirin sai kuma karamar jaka wadda itama zata kai kusan dubu hamsin", da sauri su nadiya da suke gefe suka matso suna kwashe kayan da suka tarwatse akasa fuskokinsu dauke da tsantsar mamaki, kallon mamaki Zahra ta ke wa maman Sadik sannan ta ce", nasan za ayi haka saboda kuɗin wainar ki da basu wuce dubu biyar ba shine zaki kwashe min kayan daruruwa,lallai maman Sadik kin taro mach kin taro yakin basasa na karshen duniya, dan haka yau Kema zaki dandana irin hukuncin Zahra yau zaki san waye Zahra ai dama ke mutunci na kika sani ba kisan halina akanki ba dan haka ki shirya",
Tsugunawa maman Sadik ta yi tare da rike kafafun Zahra hawaye na bin fuskarta ta ce", kayi hakuli Zahla ka rufe min asili na tuba na bika na bi Allah nabi Manzo", ture ta Zahra ta yi tana duban su nadiya tare da cewa yanzu kun gane abinda nake nufi da yin caje? Yanzu na tabbata akwai irinsu suna nan a ciki waka Allah idan suka ga hukuncin da zan yiwa maman Sadik su koma su ajiye, gaskiya maman Sadik kin raina min hankali yanzu wannan kayan da kika dauka ai kin kassarani bakincikin yanmatancin da zanyi kike min tun yanzu,baki son kiga nafi ko wacce budurwa a anguwarnan idan na tashi yammatancina bayan na dawo,to Allah karyarki tasha karya kuma kin kwana da yunwa,bari yarannan su dawo kigani",
Nadiya ce ta shiga gidan ta sanar da mama abinda ke faruwa, lokaci daya mutanen da suka cika gidan dan ganin lefe suka rude,sai ga shi kowacce barauniya tana maida kayan da ta diba. saboda rudewa ma a gaban mutane suke ciro kayan daga inda suke boyewa suna maidawa.
Mamaki ya kama mama da su kaka,su duk suna ina akayi wannan ta'a'sar? Kaka ce ta rafka salati tana cewa ashe Zahra tafi mu gaskiya yarinya me hikima da wayo,to Allah ya toni asirinku kuma kar ku dauka kun tsira wlh sai na fadawa Zahran nadiya maza kirge munsu ki gane su,ku kuma sauran ku tashi ku tafi amma babu wadda zata fita sai mun cajeta",
A can kofar gida kuwa yaran da zahra ta aika suka raka Amina ne suka dawo, kallonsu ta yi ta ce, yauwa aikinku na kyau maza ga wata ku yi mata fiye da abinda kuka yiwa Amina ", dubanta ta dawo dashi kan maman Sadik tana cewa ba fa iya shike nan ba , akwai hukuncin Zahra me zafi wanda zaki karbe shi kafin Zahra ta tafi", daga haka ta basu dama.nan kuwa suka ture maman Sadik suna mata wakar barauniya har da abinda ta sata,kuka take tana rokonsu su kyaleta amma ina sun zagayeta sun hanata matsawa ko ina tunda ita babu damar rakata tunda a kusa da gida take.
Cikin gidan suka shiga ita da Hafsah. nan fa suka samu kaka na caje ita da nadiya,mama kuwa ta kasa cewa komai dan lamarin Zahra da kaka azumunne ,yanzu kuma bata da damar hanawa tunda kaka ta shiga lamarin .
Yauwa kakata ta kaina ina sauran barayin da kika kama? Gasu nan yar albarka,dubansu Zahra ta yi tana cewa kowacce tazo na cajeta ta bar mana gida,aiko cikin rawar jiki suka fara tasowa, duk wadda Zahra ta caje sai ta hankadata hanyar waje tana cewa fita barauniyar wofi,da haka suka gama cajen,sai gidan yayi shiru dan tun farkon lamarin YARBAWAN GIDAN suka gudu dan shafawa kansu lafiya,duk da basu da tabbacin sun tsira daga tijarar zahra...
Maman Sadik kuwa da rarrafe ta shiga gida tana ihu da tsinewa zuciyar da ta bata wannan gurguwar shawarar,gashi yanzu bata san ta inda Zahra zata kuma biyo mata ba.
(Zahra cinnaka bata san na gida ba🤣)
........tsaf ya gama shirinsa ya fito cikin takunsannan me daukar hankali.ga ƙamshinsa da ya sanar da zuwansa tun kafin ƙarasowarsa,fuskar nan a sahale babu yabo babu fallasa,jafar da daddy suke falon suka dan dubeshi, sunkuyar da kai jafar yayi a ranshi tana cewa Allah ya kashe ya bawa wannan fitinanniyar Allah dai yasa kar ta sa masa hawan jini duk da cewa yasan halin AB ba ko maine yake dada shi da kasa ba ,amma duk da haka sai anyi masa addu'a akam wannan fitinanniyar matar tasa.
Maganar daddy ce ta katse masa tunani,dan Allah jafar tun da Allah yasa tafiyar taku ta matso kusa kayi kokari ku dawo zuwa ranar bikin kunga a ranar zai tare da matarsa babu dadi ta tare baya nan", in sha Allah daddy ai tafiyar bata jimawa ba ce,a kwana uku ma zamu iya gama abinda ya kaimu", cewar jafar yana kawar da kansa daga kaucewa kallon da Ab yake watsa masa.shike nan Allah ya bada sa a,ya dawo daku lafiya.
Ab na kokarin wucewa part din Ammi sai gata ta fito tana cewa yarona zai tafi Allah Ubangiji ya kareka daga dukkan abin ƙi ya dawo min da kai lafiya dan alfarmar shugaba Annabi Muhammad s.a.w,gaba daya suka hada baki suka karasa s.a.w, ɗin daga nan suka wuce har bakin mota suka raka su inda josuwa ke jiransu dan wucewa dasu filin jirgi.
Duk abinda suke maman siyam da siyam din na daki suna lekensu da jin duk abinda suke fada,kwafa mama ta yi tana cewa zaku ci kaniyarku gaba dayanku,Ni wlh har na matsu yarinyar ta tare dan da ita zamu yi amfani mu kama shi Ab din a hannu dan ta hanyarta zamu yi amfani da duk maganin da nazo dasu", rungumeta siyam ta yi tana cewa yauwa mamana ta kaina shi yasa nake jin alfahari dake,daga haka suka ci gaba da tattauna yadda zasu ci uban Zahra da wahalar da ita a gidan.
........yau saura kwana biyu Zahra ta tare, Zahra bata taɓa shiga takura irin ta wannan lokacin ba,saboda yadda mama ta matseta duk dabararta a wannan karon ta rasa hanyar fita ta kaddamar da rashin jinta na karshe,mama ta toshe duk wata hanyar fitarta kuka duk bagiya da kukan tabarar da zata yi bazata barta ba,babu abinda take mata sai Banka mata magungunan da bata san na meye ba, ga wani hakin na turare da kullum sai anyi da gyaran jiki.
Sosai mama ta tara kudi da gudummawar da ta samu ta yiwa Zahran gata ta hanyar hado mata magungunan sanyi a shahararren islamic dinnan me suna alkutubiyya islamin, wanda suka kware wajen gyara mace ciki da waje sanyi ko na meye idan kaje wajensu ka gama da izinin Allah.(Zaku iya samun nomber su a saman pg din)
Ana i gobe za a kai Zahra,Mami zainab ta karaso daga jalingo,duk Abba ya hanata yace ta yi zamanta saboda abin ze yi yawa, amma sai taki karshe ma fushi ta yi saboda abinda ya fada ɗin...
Saukarta kenan ta tarar da Zahra na rigima da yiwa mama magiyar ta barta taje ta dawo bazata jima ba,da sauri Mami zainab ta aje jakarta tare da kamo Zahra jikinta tana cewa haba Adda bilki me kuma yarinyata ta yi ake sa ta kuka?
Uhmm,zainab ba zaku gane ba tunda ku kullum ba ganin lefin Zahra kuke ba keda kaka,Zahra bata ji so take na barta ta fita ta dauko magana kafin a Kaita,tunda Allah ya kawoki ma yi sauri ki kira min yayanta na gaya masa tunda Ni taki jin maganata,ko jiya sai da ta jawo Abbanta ya bubbgeta a banza,saboda wannan banzar rigimartata kullum girma ake ba a san an girma ba",
Duban Zahra Mami zainab ta yi wadda ta lafe ajikinta tana jan ajiyar zuciya,ta ce", wai haka ne my love? Au tambayarta ma kike wato Ni nayi karya ita ce zata fada miki gaskiya ko? A'a Adda bilki ba haka nake nufi ba,cewar mami zainab tana dariya, kwafa mama ta yi ta bar su a gurin, itama mamin janye Zahra ta yi suka shige daki tana faman rarrashinta, dole Zahra ta hakura ba dan ta hakuran har cikin ranta ba,sai dan ganin yadda Mami take ta lallabata ga uwar tsaraba da ta kawo mata kamar dai yadda ta saba duk lokacin da tazo.
Washe gari suka tashi da hada haɗar tafiyar Zahra.
A can bangaren su Ab ma sosai Ammi suke biki na kece raini danginta larabawa da dangin Abba yarbawa duk sunzo gida ya cika,tun daga farkon layin zaka shaida cewa ana bikin dan dangi, anci ansha anyi al'adu kala biyu na larabawa da na yarbawa sosai abin ya kayatar ,kan kace me social media ta dauka duniya ma ta shaida ana bikin ABRAHAB MAKARE MUHAMMAD.....
Karfe hudu za azo daukar amarya,Zahra na jin haka ta fito daga daki jiki a sanyaye, sai dai tana lura mama bata falon ta yi wuf ta fice ko waiwaye ba ta yi ba,cikin ikon Allah ta samu ta bar gidan ba tare da kowa ya ganta ba,bata tsaya ko ina ba sai shagon maman Sadik .
Maman Sadik bata nan sai yaronta Sadik da ta barwa jira taje ta dawo,hakan yayiwa Zahra dadi dan haka ta koma ta kira yara su kayi layi ta shiga jidar kayan maman Sadik tana raba musu har dasu biredi yara kuwa sai murna suke,bata hakura ba sai da ta tabbatar ta yiwa maman Sadik banna me kyau wadda zata sa ta jinyar kwana biyu, sannan ta fice ta bar yaron yana kuka dan shima yasan abinda Zahra tayi sai yasa mamansa karamin hauka..
Haka ta koma gida babu wanda yasan ta fita bare a san bannar da ta aikata, dai dai lokacin da ta koma daki mami zainab ta shigo nemanta dan su shiryata lokaci ya kusa.
Yadda Zahra ta tsaya aka shiryata lafiya har sai da ya dan bawa Mami mamaki to amma dai bata tanka ba dan kar ta ballo ruwa,idan na ce zan tsaya baku labarin irin kyan da Zahra ta yi to tabbas zamu cinye lokaci me tsayi dan haka na baku dama ku kintata kyau na karshe a ranku.
Karfe hudu masu daukar amarya suka zo,a lokacin Abba ya gama yiwa Zahra nasiha wadda ta sa ta tayi laushi kamar dai abin ya shigeta,sai kuma mama ita ma tayi nata har da su sharar kwallah,dago Kai Zahra ta yi ta ce", mama ki daina kuka bafa dadewa zanyi ba shi yasa Nima kika ga banyi kukan ba, sannan dan Allah mama ki kula min da kayana dan ina dawowa yammatanci zanyi na burgewa kowa a anguwar nan sai yasan Zahra ta zama budurwa",
Salati kaka tasa tana cewa Wallahi yarinyar nan anyi yar kaniya yanmatancin me kuma zaki yi ke da aka daurawa aure da igiyoyi uku cif da gwagwgwaban sadaki? Tura baki ta yi tana kallon mama da ta kasa cewa komai,shima Abba bai iya cewa dinba sai Mami da ya kalla ya ce", zaku iya tafiya,to sai a lokacin mama ta samu bakin magana da cewa fatana Allah ya basu hakurin zama dake Zahra kar su kasa jurewa abinda kika fada ya tabbata", kaka ta yi zaraf ta ce", in sha Allah hakan bazata faru ba bakinta ya sari danyen kashi me doyi", hararar kakan ta yi tana gunguni daga haka Mami ta fice da ita tana kunshe dariyar dake cinta tana addu'ar Allah yasa halin Zahra ya tsaya a KURUCIYA.....✍🏼
Sai ku gyara zama Zahra dai ta tare bari mu bisu a next PG muga wainar da za Toya a gidan Ab yanzu wasan zai fara da zafinsa🤣🤣🤣
Wai ya kuka gano min maman Sadik 🤣🤣
Ya wasan zai kasance tsakanin Zahra da sabbin yarbawanta maman siyam da siyama?🤔🤔
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*