Free chapter · Read without an account

Pg28

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

......kallon Amira ta ci gaba da yi kamar zata hadiyeta idanunta kuwa tamkar zasu fado kasa saboda furgincin da ta shiga,lafiya dai naga kin shiga shock din maganata? amira ta fada cike da mamakin yanayin zahran.

Girgiza kai Zahra ta yi sannan ta ce", Asiya kike ko Amira ko ma dai wa kike yanzu ki matsa daga kusa dani", saboda me? Amira ta kuma tambaya adan razane,kai tsaye Zahra ta bata amsa da cewa saboda aljanuna zasu tashi, dan yau ina cikin bakincikin da ban taba shiga irinsa ba,kuma bakinciki ne yakesa aljanuna su tashi,Kema dalilin da yasa nace ki matsa shine saboda idan suka tashi babu wanda suke ragawa dan hatta da wancan kurman yayannaki bazasu kyaleshi ba,ke kuma ina ganin dan mutuncinki shi yasa nace ki matsa dan wlh yaki za ayi a gidannan ehe,tab yarbawa GIDAN YARBAWA na kuma dawowa tashin hankali ta karasa fada tana rushewa da kukan da ta gama shirya yinsa dan fara yakin sunkuru a gidan sabbin yarbawanta.

Da sauri Amira ta matsa ganin Zahra ta fara aljanun da ta fada, dan atunaninta kukan da Zahra tasa ba ita ba ce aljanun ne.

Ab kuwa koda ya fito kai tsaye ya nufi hanyar da zata sadashi da katafaren falon Ammi,yana dab da shiga saiga Amira da gudu hannunta dafe da kirjinta sai faman nishi take kamar wadda ta yi gudun kwanaki bata tsaya ba,ganin yadda ya watsa mata razanannen kallonsa me cike da gargadi yasa ta dan nutsuwa dan tasan yayan nata ko mutuwa ta gani bai yadda da rashin nutsuwa ba.cikin jan numfashi take nuna masa inda Zahra take tsaye tana ta rusa ihu,ita ko zahra ganin yadda Amira ta rude ne yasa ta juya al'amarinnata zuwa aljanun da ta ambata dan haka sai kawai ta yo kansu da gudu a ranta tana cewa Wallahi yau sai na rama duk wata azaba da ka taba yi min mugu kawai.

Ai da gudu Amira ta fada falon tana kiran Ammi da daddy ,a bakin kofa suka ci karo dasu gaba daya suna fitowa saboda jin ihun da suka yi,ganinsu yasa Amira ta boye a bayan daddy tana karanta masa abinda yake faruwa tana kukan tausayin Zahra da duk ta fita hayyacinta.ita ko Zahra na ganin siyam sai kawai ta canja akalar shirinta akan siyam,dan haka kai tsaye ta nufi siyam din tare da kai mata wata muguwar cakuma ta shiga bugun ta baji ba gani,ganin haka yasa maman siyam rudewa itama ta shiga jan Zahra da kai mata bugu dan ta samu ta sakar mata diya.

Ai sai kawai Zahra ta kuma haɗasu ita da siyam din ta hade tana kai musu bugu tare da cewa, baza mu yarda ba tunda aka yaudari godiyarmu aka kuma kawota cikin yarbawa dan haka sai mun dauki fansa ba zamu kyale ba hhhhhh ta karasa da dariyar da ta sa hanjin cikin siyam juyawa,Ammi da daddy ne suke ta kokarin kama Zahra amma ina abin yaki yuwuwa sai kace me aljanun gaske sosai Zahra tafi karfinsu,maman siyam cewa take shike nan Bukhari ka auro mana mahaukasi saboda toseyinka, ka aurewa yaro abinda ze kessi,gashi nan ze fara takan yarona da nake so da kauna.dariya Zahra ta yi aranta tana cewa shegiya Gara na fara ta kanku na wuce abinda akayi min kanku,dan dama naga wani gani gani kuke min yarbawa masu kwalokwalo kawai,"

Dan matsawa jafar ya yi kusa da ab da ya dafe kansa yana jin hayaniyar Zahra da ta su siyam har cikin kanshi,ga tunanin yadda zai yi da wannan sakaryar Zahra dan ya tabbata wannan abidlnda take yi na karya ne,a dan zaman da ya yi da ita ya karanci halayyarta tsaf sai dan abinda ba a rasa ba.maganar jafar ce ta katseshi inda yake ce masa yallabai yarinyar nan fa idan ba a rabata da siyam ba zata iya ji mata ciwo ina ga a samu mafita kawai,"ya karasa maganar da dan murmushin da bai bari ya fito duka ba,bai iya cewa komai ba dama kafar yasan ba tankawar zai yi ba sai ma mikawa jafar din ragowar wayarsa dake hannunsa ya yi tare da nufar inda ake tafka gumurzu tsakanin aljanun Zahra da su siyam.basu ji takunsa ba sai kawai jin ƙamshinsa da ya kuma cika hancinsu,da ganin dogon hannunsa da su kayi ya janyo Zahra kamar wanda ya janyo cup kafin su yi wani tunani ya sabata a kafadarsa kamar wata yar tsana ya yi ciki da ita, duk yadda take buge bugen kwatar kanta kuwa ko ajikinsa.

Jafar ne ya dubesu ya ce ", ku koma ciki ammi case closed,mama ayiwa siyam ruwan zafi ko ta ji dadin jikinta dan gaskiya ta bugu,daga haka ya wucewarsa yana dariyar siyam ɗin.Ammi ce ta taimakawa mama da ita ma jikinta yayi matukar tsami dan sosai ta samu nata rabon suka kama siyam da take fidda numfashin wuya idanunta babu abinda suke sai ruwan hawaye da tururin daukar fansa.

Sai da ta tabbatar sun gama hayewa saman da taji alamar suna hawa sannan ta fara kokarin sauka tana cewa Ni ka rabu dani malam ba dama mutum ya yi abu sai ka fara daukarsa kana wayon tabawa mutum jiki, kuma wlh ka sani kai ma ba hakura nayi ba, haka kawai dan mugunta kasan kai BEYERABE ne amma ka bari aka daura mana aure wannan ai yaudara ce, to ka ma sani Ammi da daddy ne kawai zasu sha ruwa a gidannan amma kowa ya ga takansa ehe," ta karasa maganar hawaye na sauko mata na gaske dan har ga Allah taji bakincikin kasancewar Ab BEYERABE wanda ita kanta bata san meye dalili ba,yana jin duk abinda take fada tare da dumin hawayenta da ya sauka a kan kafadarsa, bai direta a ko ina ba sai dakinsa akan gadonshi da babu wanda ya taba hawa idan ba shi ba,yana direta ya koma kofa ya rufe ya zare key ɗin,yana jinta tana ta gunguni da hawayen da suka ki tsayawa wanda zamu iya kiransu na shagwaba,ya yi wucewarsa ya shige bathroom ya sakarwa kansa shaya.

Kofar ta je ta murda ta ji ta a rufe hakan yasa dole ta koma ta haye kan gadon tana shafawa tana ci gaba da hawayenta, can idanunsa suka kyalla suka hango mata wayarsa da ya ajiye kan bedside drowa,da sauri ta miƙa hannu ta ɗauka.tayi ko sa a babu password dan haka cikin hanzari ta shiga loda lambar maminta.bugu biyu Mami ta daga tana rangada sallama sai dai kuma me makon taji an amsa mata sallamar sai kawai taji kukan Zahra cikin kunnuwanta.ya subhanallah my love wa ya taba min ke me aka yi miki kike kuka haka maza sanar dani damuwarki kinji baby? Cikin jan majina Zahra ta ce " Mami ashe wannan mutumin shima BEYERABE ne amma kuka yi min aure dashi?zama mami ta gyara daga bangarenta tana cewa babbar magana kenan, yanzu Zahra akan wannan kike bata ranki? Haba my friend ke yanzu baki ga mutunci da sanin Yakamata wajen iyayen mijinki ba? Baki ga sabanin halayyar da kike tunani duka yarbawa na da ita a wajen mahaifinsa ba? Haba Zahra kowa ce kabila fa da kike gani akwai na kirki a kwai Baragurbi duk inda kika shiga yanzu a duniyarnan sai kin samu mutanen kirki da na banza,yanzu wane hali daddy ya nuna miki daga jiya zuwa yau tel me idan saurarenki? Hawayen da suka zubo mata ta share sannan ta ce", Mami daddy Yana da kirki da tausayi Tun ranar da ya fidda Abbana kunya nake sonsa da ganin girmansa ba tare da nasan shidin wane yare bane,aiko shima wannan kurman saboda Daddy nake daga masa kafa tunda nasan shine babansa,ita kuwa Ammi dama ina ganinta Naji ina sonta saboda ta nuna min kauna dan haka ina sonsu kuma bazanyi duk wani abu da zai shafesu ba," yauwa to kin gani dan haka dan Allah Zahra ki sasautawa yarbawa ki gane cewa kowane yare suna da side,sannan wannan halin naki ki yi hakuri ki aje shi tunda yanzu kin girma.

Tura ƙaramin bakinta ta yi sannan ta ce", Ni kam Mami sai dai su daddy susha amma WLh banda wannan siyam din da mamanta da na ga suna min wani kallo tun jiya da muka zo,shi ma kuma kurman ba zai sha ba", waye kuma kurma? mami ta tambaya tana mai nemawa Zahra shiriya a ranta,gashi nan wanda kika ce wai mijina ne", dariya mami ta yi kamar cikinta zai yi ciwo,haba zahra wato wai ne ma kuma shine kurma ko,? To ki bini bashi akwai ranar da zan tsokane ki da wannan kalmomin naki,amma dai yanzu ki yi hakuri ki manta da komai ki zauna lafiya da mijinki kinji...jin an zare wayar daga kunnenta yasa ta dago fuskarta tana kallon me yi mata wannan gangancin...

Wata irin zabura ta yi tare da dukunkune kanta cikin tattausan blanket dinsa tana cewa,wayyo Allah nayi gamo,ta fada tana kokarin dan leko da kanta dan san tabbatar da abinda ta gani ɗin,aiko shi din ne yake tsaye jikin mirror jikinsa daure da karamin towel Wanda ko cinyarsa bai gama rufewa ba, hankalinsa kwance yake goga hadaddiyar turarukansa da sai yana shafawa zaka fahimci dalilin da yasa ake kasa tantance kamshinsa.da sauri ta kuma maida kanta tana rufe idonta ga wata kunya da bata taba sanin da irinta a duniya ba,ji tayi numfashinta yana sama saboda tsananin yadda ta kunshe kanta.

Tashi ta yi tana hararar gefen da yake tare da jan numfashinta,cikin ƙunkuni ta ce", mutum babu kunya ya dinga abun yan is.....da sauri ta rufe bakinta saboda tunawa da karonsu na Company da ta yi sai kawai ta karasa a ciki tana mai kin kallon inda take tsammanin yana nan.

Ko kwakkwaran motsi Ab ba ya yi komai cikin nutsuwa da rashin hayaniya yake yinsa,yana gamawa ta karasa clothing dinsa ya saka jallabiyarsa ta sabo a irin wannan lokacin da ba fita zai yi ba,dama duk ya dawo daga tafiya bai cika kara fita ba saboda bawa kansa damar hutu.sai da ya kama kofar zai fita sannan cikin kamewarsan nan ya ce", ki yi sallah zuhur,daga haka ya fice daga dakin ya barta sake da bakin yadda ya manna mata hauka duk abin nan da take yi,kwafa ta yi tare da mikewa tana cewa to an gaya maka zama zanyi har kake wani bani umarni wai shi miji, kiyi sallar zuhur ta maimaita abinda ya fada harda kwatanta yadda ya yin sai dai ita maimakon kofar ta bude sai taji ta gam da alama dai rufe ta ya kuma yi ta waje,cike da jin haushi ta wuce bathroom dinsa tana cewa Wallahi duk kaci bashi.

Sauri ta yi ta daura alwalar tana cewa bari nayi sauri na yi sallar ma dawo nayi kallo tab wannan wane irin banɗaki ne, ta fada tana fita bayan ta gama alwalar.

Doguwar riga ce ajikinta dan haka ta warware mayafin dake kanta ta yi sallar,Zahra rigima yau ko doguwar addu'a bata tsaya yi ba tana Allah Allah taje tayi kallon aljannar duniya a banɗaki.

Kai tsaye jakuzin da tun dazun shi ya tafi da imaninta ta nufa, bayan ta cire rigarta ta ta watsar da ita a toilet din,cikin sa a ta iya budewa tana shiga ya koma ya rufe bata damu ba tunda taga ta iya budewa a ganinta fita bazata gagareta ba,wani abu ta danna take kuwa ruwa ya fara zuba da farko abin ya dan bata tsoro sai kuma daga baya ta shiga wanka tana murmushi, wanka ganin ruwan yana ta taruwa sai ta fara kokarin kashewa,wayyo Allah na kasa kashewa gashi ruwan karuwa yake baya tafiya ta fada cikin yanayin tsoron da.ya fara kamata ganin ruwan sai yawa yake yana ƙoƙarin kai mata har wuyanta,kuka ta saka tana buga kofar jakuzin ko zata iya budewa shima A banza dan ya ki budewa...

Tunda ya shigo dakin yake dan binsa da kallo a nutse neman ta inda zata bullo yake yi,amma har tsawon mintuna biyar babu ita, matsawa ya yi ta wajen bakin toilet ɗin ya dan kasa kunnensa da farko shiru ya ji, sai kuma har zai bar wajen ko me ya tuna sai kawai ya bude toilet din ya shige yana raba idanunsa loko da sakon bath ɗin.

Zahra kuwa tuni ta sume a cikin jakuzin dan ruwan har ya cimmata,dan rantse idanunsa ya yi kafin cikin dan hanzari ya taka zuwa wajen ya bude jakuzin yana saurin kashe ruwan dan ya samu hanyar tafiya, ruwan yana yin kasa Zahra ta fado jikinsa a sume........✍🏼

Allah ya tashi kafadun zahranmu🤪🤣

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol