Free chapter · Read without an account

Pg29

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

.........gaba dayanta ya tare ta a cikin jikinsa wani yanayi da bai taba riskar kansa a ciki ba na dabaibayesa.dan taune lips dinsa ya yi yana kokarin daidaita kansa tunda yake bai taba taɓa ko da hannun macen da ba muharramarsa ba bare akai ga ganin tsiraici,shi yasa yanzun yake jinsa duk a dame da wannan fitinanniyar yarinyar.

Daukarta ya yi ya fita da ita yana ji kamar jijiyar kansa zata tsinke saboda kokarin kawar da idanunsa da yake daga kallon abinda yake ganin kamar bai gama zama tabbaci a gareshi ba,kwantar da ita ya yi akan gadon yana ta son kawar da fuskarsa sai dai ina hakan ya gagara dan sai da idanunsa da zuciyarsa su kayi masa gardama wajen kin bin umarnin kwakwalwarsa,zama ya yi a gefenta yana kallon shafaffen cikinta da kamar ba a taba saka masa kwayar abinci ba,fatarta kuwa wani irin sheki da sulbi take kamar wadda take rayuwa a wani luxury house,a lamar kunburi yaga cikin ya yi wanda ya nuna cewa tasha ruwa.

Wani dogon numfashi yaja tare da fitar da hucinsa ta bakinsa yana mai dafe kansa da tunanin yadda zai yi da ita,hanya daya ce dole sai dai idan ya zuke mata ruwan nan ta baki idan ba haka ba zai iya zama matsala yasan da wannan a matsayinsa na doc,cikin da kawar da abinda yake ji ya sunkuya daf da fuskarta yasa hannunsa ya toshe hancinta tare da dora sopt lips dinsa a saman nata a hankali ya lumshe idanunsa yayin da yaji sanyin bakinta cikin nasa bakin.

Sai da ya dauki kusan mintuna biyu a haka sannan ya dago yayi saurin danna cikinta sai ga ruwa na fitowa ta bakinta, sai da ta gama fitar da ruwan tas sannan taja dogon numfashi tare da bude idanunta, a dan zabure ta fara ƙoƙarin tashi tana kiran sunan maminta,lurar da ya yi bata hayyacinta yasa shi saurin kamata ya riketa a jikinsa amma duk da hakan bata bar kokarin fizgewa ba,fuskarta ya rike da hannunsa guda yana cewa colm doun AM hire.

Jin dakakkiyar muryarsa da ta yi kamar daga sama yasa ta fara dawowa hayyacinta,sai kuma ta yi wata irin zabura lokacin da ta gama dawowa daidai ta kuma tabbatar da inda take, innalillahi me ya faru? Ta tambayesa tana kallon jikinta,tasan ba tanka mata zai yi ba sai kawai ta sa kuka tana cewa dan Allah wa ya dauko Ni daga gidan mutuwa? Me ka gani? Wayyo mamana,ganin duk abinda take yaki tanka mata yasa ta dan nutsu ta matso da fuskarta kusa da shi tana ta fama da zanin gadon da shine ya kare mata jiki ,cikin karamin sauti kamar tana gudun wani yaji ta ce ", dan Allah ka fada min gaskiya ka ganni?

Sannan ina da ina ka gani idan ka ganin?

Zahra bata Ankara ba sai jin Ab ta yi ya burkitata saman gadon ya kuma sauke mata nauyinsa,kafin ta samu abin cewa ya hade bakinta da nasa wani irin zazzafan kis ya shiga antaya mata wanda ya dauki kusan mintuna biyu sannan ya sake bakin kana cikin wata murya da ba dan fuskarsa na daf da tata ba baza ta ji shi ba ya ce" naga nan,a hankali ya gangara da hannunsa ya shafo wuyanta zuwa korjinta idanusa akan kyakkyawar fuskarta da ta yi matukar runtsewa nan ma a hankali cikin taunshin murya ya ce,da nan .

Sai ko ta kara runtse idanunta tana mai jin nadamar tambayar da ta yi masa,bata gama tantance yanayin da yajefata a cikin ba ta kuma ji ya gangara da hannunsa kasan cikinta, Nan ma ya ce", nan ma na gani, tunda Zahra ta taso da kuruciyarta bata taba tsammanin da akwai lokacin da bakinta zai iya mutuwa ba har ta kasa kwatar kanta ba sai yau,tsananin kunya da takaici yasa ta fashewa da kuka, daidai taji Ab na dagata, sauka yayi ya nufi bathroom..

Bude idanunta ta yi tana bankawa kofar bath ɗin Harara tana cewa wuta balbal bazan yafe ba har kabari yana balbal dama akwai abinda ya shirya shi yasa yace na shiga bathroom ɗin,to bazan yafe ba,ta karasa fada tana goge kwallar da ta sauko mata, rashin abinda zata rufa a jikinta yasa ta ci gaba da kwanciyar rashin makama..

A can kasa kuwa sai da akayiwa siyam ruwan zafi daga karshe ma likita aka kirawo ya dubata saboda zazzaɓi da ya rufe ta,tsinuwa kuwa babu wadda Zahra bata sha a bakin maman siyam,Amira kuwa abin dariya ya koma bata duk ta tuna sai dai kawai Ammi taga tana dariya.

Jin shiru har kusan la asar babu Zahra ba labarinta sai kawai Ammi tasa Amira ta shirya abinci ta kai musu can falon Ab, daddy kuwa tuni ya bar gidan shima jafar gida ya tafi dan ya samu hutu.

....tana jin alamun fitowarsa ta yi saurin maida idanunta ta runtse,shi bai ma san tana yi ba closed dinsa ya shige bayan ya gyara jikinsa da Mayun mayuka da turarukansa masu shegiyar tsada as usual wata farar jallabiyar sabuwa kal me kyau da tsada ya kuma dauka ya saka,daga nan ya dauki karamin tasbaharsa,yanzun ma yana dab da fita ya dan tsaya cikin kamewarsa kamar bashi ya gama tsotsewa yar mutane ruwan jiki ba,ya ce", ki fita akwai daki kusa da nan ki shiga akwai kaya ki sa kuma kiyi sallah idan kin kuma maimaitawa jiki magayi,daga hakan yasa kai yayi ficewarsa.

Yan Yan yan ta fada tana gallawa kofar da yabi ya fita harara,shafa shafaffen cikinta tayi tana yatsina fuska wallahi yunwa nake ji kome za kayi sai na sauka naci abinci tunda Ni ba karfe ba ce", tana gama surutunta ta mike tare da katon bedshed din a jikinta duk nauyinsa haka ta dinga jansa har ta fita daga dakinsa, dakin da ya gaya mata ta shiga.

Masu kudi masu duniya ta fada bayan ta gama kalle hadaddiyar bedroom din da bata ma san Tata ba ce, sai da ta rufe dakin sannan ta saki bedshed din akasa ta nufi banɗakin tana cewa,Zahra sai hakuri yau Allah ya kawoki hannun dan is.....sai kuma ta kasa karasawa a karon farko taji kalmar bata da ce dashi ba,dan haka sai ta waske ta karasa da kalmar kurman da ta saka masa..

Yanzu dai bata tsaya kallon komai ba a bathroom ɗin wanka ta yi ba tare da ta kalli bangaren da jakuzi yake ba,tana gamawa ta daura alwala tare da bude wata drower me glass da taga an jera towel kala_kala a ciki,guda ta dauka ta daura kana ta fito.

Dariya ta yi lokacin da ta ci karo da hadaddun mayuka da turaruka a saman mirror dauka ta yi ta fara shafawa tana cewa banza ta fadi yau Zahra ta zama yar gayu, a haka ta gama shafe shafenta ta bulbula turaruka ,sai kuma ta nufi closed kamar yadda taga Ab yana yi,zaro manyan idanunta ta yi tana karewa kayan da suke jere sanka sanka kallo, bangaren kananun kaya daban bangaren dogayen ruguna daban bangaren kayan bacci dana unders kama daga brezia fant fad da dai sauransu kai ko wane kaya akwai su acikin closed dinnan, rike baki ta yi cike da mamaki anya kuwa nasa kayan nan?ban sani ba ko na yar gidan ne,to amma kuma me yasa yace na saka? Wannan tunanin da ta yi yasa ta koma bangaren kananun kaya dan haka nan su kayi wani irin burgeta, wata riga da bata san ya take ba ta zaro.

Ɗaga rigar ta yi tana kare mata kallo doguwa ce sai dai karamin hannune da ita kuma jikinta me irin kwanciyar nan ne,har zata mayar sai dai ko me ta tuna,ko under bata saka ba ta zura rigar.

Sallah ta fara yi kafin ta fara ahiriritarta.

Karasawa ta yi tana kallon kanta a mirror,kai Masha Allah dama haka nake da kyau kamar wannan yar indiyar da su nadiya suke cewa muna kama", ta fada tana wani irin juyi a bakin mirror tamkar wata tarwada,gashi rigar ta fidda surarta ta mace wadda yanzu ne suke kuma bayyana a matakin girmanta.daidai ta yi wani irin juyi wai ita a lallai indiya ,ab na shigowa dakin dan tun dazun ya shigo daga sallah sai dai ya kasa daurewa jiran fitowarta dan a tsammaninsa tana can tana kuma wata barnar.bata lura dashi ba shi kuma bai magana ba tunda ya shigo,ya dai hade hannayensa bayansa jingine da kofar shigowa idanunsa kuma akanta yana kare mata kallon da bai san dalilin yinsa ba.

A garin juyin ta fado jikinsa wanda hakan ya matukar razanata ta bude baki zata kurma ihu ya yi saurin saka tattausan hannunsa ya rufe bakin yana cewa cikin karamin sauti baki jin magana kina sa min ciwon kai da yawa,zare jikinta daga nasa ta yi tana tura ƙaramin bakinta bata ji dadin dawowarsa ba saboda ta shirya sauka kasa cin abinci,fita ya yi tayi saurin bin bayansa tana cewa wai a gidannan ba a cin abincin rana,bayan kuma an san wanda ya yi aljanu yunwa yake farkawa da ita idan ya gama bare kuma Ni da aka hada min da ƙamshin mutuwa, uffan bai ce mata ba sai nuna mata dinning da ke dauke da lafiyayyun kulolin abinci sai wanda ta zaba ya yi,yana mai kaiwa zaune cikin kujerarsa.

Bin wajen da kallo ta yi kafin ta dan saki karamin murmushi tana cewa Masha Allah nasan wannan aikin Ammi ne dan ita kadai take so na a gidannan,karawa dinning ɗin ta yi ta zauna tare da fara bude kulolin abincin, gyara zama ta yi ta yi saven kanta da duk nau in abincin dake gurin,saboda babu a house ko mai dai da ta zuba,sai ga Zahra tun tana cin abincin da marmari har dai ta gaji ta mike tana mika irin wadda ke tabbatar da kishin mutum,falon ta dawo kai tsaye tana nufar kofar fita.

Sai dai me murdawar duniya ta ki buduwa dan dole ta hakura ta dawo ta wuce shi tana gunguni akan ya hanata fita gaba daya.

Ko da ta shiga dakin haka tayi ta tabe tabe kamar wata yar kauye kuma duk abinda ta taɓa sai tayi sharhi akansa cikin salon yarinta, a haka har aka kira sallar magriba, bathroom ɗin ta shige ta dauro sannan tazo ta tayar da Sallah,

Ko da ta idar sai kawai ta dauko Alkur'anin da ta gani tare da kayan sallah a kauwame kamar masallaci ta shiga karatu a ranta tana cewa bari yau muyi karatun magriba na rashin abin kalo magana...bata tashi a gurin ba har sai da ta yi sallar isha'i ta haɗa da shafa,i tana cire abin sallah ta fada saman lafiyayyan gadon da yaji shimfidun alfarma tana cewa bari muji kalar nasa taushin alkur an idan na wancan kurman yafi taushi nan zan koma,jin ta lume cikin tsakiyar katifar yasa ta wani ja ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta.

Da sauri ta bude idanun saboda wani abu da ta tuna kuma ya bata mamaki.tabbas lokacin da Ab yana shanye mata baki taji wani irin zaki kamar na zuma,to abinda ya bata mamakin kuma ya take so ta sani shine tayaya bakin mutum yake zaki? Anya ba wani abu yasha me zaki ba? To me yasa ban ganshi ba? Tashi ta yi tana cewa WLh bazan iya hakuri ba sai na gano meye yake wannan zakin abakinsa Allah yasa yayi bacci dan hakane kawai zaisa na ji kuma na tabbatar tunda dai idan mutum zai kwanta yana brosh,daga haka ta fita daga dakin tana fatan ta sameshi yayi bacci.

Ab kuwa saboda gajiyar dake tare dashi ga kuma wadda Zahra ta kuma haɗa masa yasa bai tsaya wajen su daddy ba duk da dama ba wani tsayawar ya fi ya yi ba,sai da safe kawai ya yi musu ya dawo saman,sai ya zauna a dinning ya dan tsakuri sakwara da miyar egushi wadda ta ji naman rago da bushashshan kifi sannan ya wuce dakin daga nan ma bathroom ya shige yayi wanka tare da brosh kana ya fito ya kimtsa cikin wasu tausasan pijamas masu kalar sararin samaniya, sannan ya fesa turaren baccinsa na musamman wanda bai da karfi sai wani irin sanyin ƙamshi me kashe jikin wanda yake shakarsa,daga nan yabi lafiyar gadonsa sai da ya yi addu'a sannan ya rufe rabin jikinsa da blanket.

Dan tsuka ya yi saboda tunanin duba Zahra da yake son rinjayarsa,haka nan yaji bai yadda da jin shurunnata ba,dan a ɗan zaman da yayi da ita ya fuskanci jinta shiru dayan biyu ne ko bacci ko banna sai kace wata yar yaye trouble danger ya fada can ƙasan ransa da son yakice tunanin zuwa gareta, lumshe idanunsa ya yi fuskarsa na kallon sama.

Daidai lokacin yaji an bude kofar dakin, bai motsa ba haka nan babu wanda zai yi tunanin idanunsa biyu,kallonta yake ta can ƙasan idon ba tare da tasan yana yi ba.

Tsayawa ta yi akansa ta ce bari na tabbatar da baccinnasa, dan haka sai tayi nilin a gabansa tana kallon kyakkyawar fuskarsa me cike da kasumbar da ta yi matukar ƙara ƙawata fuskar da kyau da kwarjini,tabe ƙaramin bakinta ta yi tare da kawar da fuskarta daga kansa,hannu tasa ta bugi bedside drowar dan ta gwada ko zai farka amma sai taga babu wata alama, ga dukkan alamu dai baccin nasa ya yi nisa kamar yadda take bukata,a hankali ta matsa da fuskarta gab da tasa tana cewa yau zan kure karya.mutum zai sha kunya wai banda kakale har da zakin baki a ke karawa kai duniya,ta fada tana da ɗa kusanta bakinta da nasa.......✍🏼

Wai Zahra me zaki yi ne?

Allah wahidin ka shirya mana Zahra 🤣🤣🤣

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA* 😍

*By*

*FATEEMAH y ADAM*( *ZAHRA* )

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol