Free chapter · Read without an account
Pg30
........a hankali ta zura harshenta cikin karamin pinkinsh lips dinsa,kai tsaye ta shiga juyashi a cikin bakinsa,ido ta dan ware saboda jin zakin da take son tabbatarwa,dagowa ta yi da niyar zare bakinta ,amma sai me,ji ta yi gaba daya ya janyota ta fado jikinsa,a lokaci daya yana mai ware gaba daya girman idanunsa a kanta.
Ita ma ware nata idon ta yi cike da mamakin dama idonsa biyu ya yi mata shiru ko kuma dai farkawa ya yi? Tab idan ko haka ne lalle wannan kurma ya cika dan gidan yarbawa na gaske, buɗe baki ta yi zata yi magana ya riga ta da cewa, idan kina bukatar yin iskanci da mijinki ai ba sai kin saci hanya ba, ko fada min kika yi zan iya temakawa na miki", bai bata damar masifeshi da ta kuma bude baki zata yi ba,ya haɗe bakinsu guri daya ya shiga yi mata kyakkyawar sumba me aji ba irin tata ta neman magana ba😄.
Babu irin masifar da Zahra ba ta yi a ranta ba tunda an rufe bakin tsiwar,tuttureshi ta shiga yi amma maimakon ta samu nasarar kwacewar ai saima wata dama da ta kuma bawa dan gidan yarbawa, ga rigar da take jikinta itama ta bada gudummawa saboda yadda take da santsi,sosai yake son rabuwa da ita amma hakan ya gagara duk da ya sawa ransa abinda yake yi din a matsayin hukunci yake yinsa.
Zahra bata samu kanta ba sai da yaga tana kuka da hawaye saboda yadda bakinta ya sha tsotsa wajen dan gidan yarbawa Oga AB,jikinta kuwa ko ina ciwo yake duk dai ba wani abu ya yi mata ba kawai dai tasha zazzafan romance ne me aji irin na maza masu aji.
Wani dan muskilin murmushi ne ya subce masa lokacin da ya tuna abinda ya kawota dakin,kuma riketa ya yi a cikin jikinsa sannan ya hade fuskarsa da Tata da take ta zubar hawaye ,can ƙasan maƙoshinsa kuma cikin dakakkiyar muryarsa ya ce", yanzu kin tantance abinda kike son tantancewa? Da karfi ta kai masa bugu a kirji saboda ta rasa ta yadda zata yi ta huce fushinta,sai dai ko gezau baiyi ba baya ga lumshe idanunsa da ya yi tare da kara yi mata kyakkyawan riko saboda yadda take ta son kwace kanta,abinka da jiki ya mutu yasa nan da nan ta sare ta hakura da son kwacewar ta yi luf kamar yar bage a cikin faffadan kirjinsa,ganin ta dan nutsu sai ya kuma kai bakinsa saitin kunnenta ya ce", yanzu waye dan is ... Ɗin mijin ko matar uhmm?
Kuka ta kuma fashewa dashi tana harbinsa da hannu da kafa irin dai borin da ta saba yiwa su mama a tsakar gidan yarbawa yau kuma a jikin Oga AB ya kare,rufe idanunsa ya yi tare da rike hannayenta da suke ta kai masa wasu yan kananun bugu a kirjinsa wanda hakan ke haifar masa da wani irin yanayi me wuyar fasaltawa.
Ita kuma sai lokacin ta samu bakinta ya bude ta shiga gunguni da kananun maganganu akan abinda ya fada mata,cikin fidda huci da iskar dake bakinta da kuma yanayin maganarta da ta koma sanyi sanyi da shawaga,ta ce", Ni ba yar iska ba ce kuma kar ka kara yi min abinda kayi min yau, kuma Ni ba dan inyi iskanci na sha maka baki ba," to saboda meye? Ya Samu kansa da yi mata tambayar duk da yanayin yadda ya yi maganar baka taba cewa shi din ya yi ba, ga kuma hucin bakinta dake sauka kan fatar kirjinsa da fuskarta ke fuskanta bakinta kuma ke dab da taba fatar gurin da ke dauke da wani kwantaccen gashi dan idan ta bude bakinta labbanta suna gugar wajen. zazzafan huci ya furzar yana jin sautin muryarta da ke fita da dan zafi zafin yanayin sangartarta ta ce" to ai Ni ba wani abu zanyi ba kawai ji zanyi ko zuma kasha ko madara shine kai kuma dan cin zali ka kama Ni kana min...sai kuma ta yi shuru tare da maida idanhnta ta rufe a karon farko ta ji kunyar fadin wata kalma ga Ab din ...
Daga haka bata kuma sanin me ya faru ba dan bacci ne me shegen dadi ya yi awan gaba da ita, duk kuwa da cewa tana faman kuncin rai da takaicin ogannata,wajen mintuna uku yana kallon fuskarta da ta yi wani fes sai glowin take kamar zaka ga taka fuskar a cikin Tata, daga karshe ya lumahe idanunsa tare da jan dogon karan hancinta yana cewa queen danger...daga haka shima bai san baccin ya yi awon gaba da shi ba.
Yau dai Ab yaso ya makara sallah, sai da yazo fita ya tashi Zahra da har yanzu baccinta take hankali kwance ,dake bata da nauyin bacci kuma ta saba da tashin sai bata yi jinkirin tashi ba,alwala ta dauro tazo ta yi raka atanal fijr daga nan ta yi sallah ta ɗora da karatunta,sai da gari ya dan fara haske kana ta ajiye Alkur'ani ta kwanta akan dardubar ta ci gaba da baccinta,shima sai a lokacin ya shigo idanunsa a kanta, daukarta ya yi ya maida kan gadon sannan ya wuce bathroom...
Karfe takwas ta fara shaƙar sassaanyan ƙamshinsa da tuni ta gaddacesa a hancinta ,a hankali ta fara bude idanunta har ta bude su gaba daya ta sauke su akansa da yake tsaye a shirye tsaf ,ya yi wani irin kyau me daukar hankali waya ce a kunnensa yana magana cikin wani irin nutsuwa yanda idan ba nutsuwa ka yi sosai ba bazaka fahimci magana yake yi ba,ganin yana takowa zuwa bakin gadon yasa ta dauke kanta tana tura ƙaramin bakinta da har yanzu jawur yake bai canja ba,tsayawa ya yi a kanta yana ci gaba da wayar idanunsa nayi mata kallon kai tsaye,tashi ta yi zaune tana cewa Ni kam a daina kallo na ban so,dan kallonsa ta yi ta kawar da kai tana ci gaba da cewa ka barni na koma kasa duka kayana suna can, Ni kam bazan kuma aron daki da kayan wata ba ehe",juyawa ya yi yana cewa zaki iya fita amma ki tabbata kin shirya duka kayan dakin da dakin naki ne",
Tsalle ta yi ta duro daga gadon ta bi bayansa tana cewa da gaske kake ko mai nawa ne? Dan wani tsallen murna tare da juya mazaunanta tana cewa ahayye Zahra ta zama yar gayu idan na koma gida da gayu na haduwa yanmatanci me lasisi Zahra me sa a ko mai nata na dabanne", yana jinta bai tanka mata ba sai dai kalmar yanmatancin da ta ambata ne bai gama fahimta ba dake yasan halin shirmenta sai bai damu da hakan ba,sai da yazo zai fita ya kuma dakatawa ya juyo yana kallonta tana ta juyinta cikin kamilalliyar muryarsa ya ce", pls banda sa magana idan kin sauka,daga haka ya fice yana fatan kar ta tara masa wasu magana da ciwon kan kafin ya dawo.
Dariya ta yi tare da cewa ai kai ma kasan mafarki ne Zahra ta tashi bata yi abin magana ba,yanzu ina shiryawa zanje na gaida Ammi da daddy sai kuma na duba jikin wannan yan renin hankalin.
Cikin sauri ta gama shiryawa, ta yi kyau kuwa kamar me,su Zahra anga banza wannan kyan na yau na Musammanne,ta fadawa kanta tana ci gaba da bulbule jikinta da turaruka har da humras masu ƙamshi da kyau da suke jere a wata showglass kai Zahra fa ta yi barin turare, bangaren takalma ta koma ta zaba masu ɗan tudu wanda idan ta yi tafiya Zaka ji yace, kwass,sai da ta fara gwada tafiya a dakin hannu makale da wuya, sai da ta tabbatar komai ya yi sannan ta fita daga dakin....
Karar takalminta da ƙamshinta da ya kuma cika falon bayan na Ab da ke wajen ne ya jawo hankalinsu kanta,kurman ashe bai tafi ba ya tsaya tsegumi ta fada ƙasa ƙasa tana ci gaba da saukowa.
Masha Allah my Zahra ta samu lafiya", cewar Ammi fuskarta cike da fara'a da ɗokin ganin zahran,ɗan kallonsa Zahra ta yi a ranta ta ce", ji karya wato ce musu yayi bani da lafiya bayan kuma shi ne ya kulleni.daidai nan ta karaso dinning din ta durkusa har kasa ta gaida Ammi haka daddy ma ta gaidasa,juyawa ta yi inda mama da siyam suke ta ce mama ina kwana fatan kun tashi lfy? Da har zata ki amsawa sai kuma ta amsa fuska babu yabo babu fallasa,duban siyam ta yi ta ce", sis Barka da safiya,bata saurari me siyam din zata ce ba dan babu ma alamar zata kulatan juyawa ta yi suka hada hannu da Amira dake ta faman washe bakin ganin Zahra lafiya kalau,matar yaya AB Barka da safiya ya jikinnaki? Alhamdulillah Zahra ta fada tana mikewa saboda gurin zaman da Ammi ta ke nuna mata kusa da Ab da har yanzu idanunsa na kan tab dinsa lokaci lokaci yana spin din tea dake gabansa.
Zama ta yi tana dan hararar gefen da yake,Ammi ta ce", maza Amira hada mata abinda take bukata,matar yaya me kike so ? Komai ma Zahra ta fada cikin nutsuwa,ashe idan ta ga dama tana nutsuwa,ya fada a ransa tare da janye idanunsa daga kanta wanda sam babu wanda ya kula da kallonnasa akanta sai ita da da take jin kaifin idanunnasa akanta.
Chips da kwai ta fara zuba mata sai farfesun kan ragon ruwa sai ta haɗa mata tea, dubanta Zahra ta yi ta ce", ke kam Amira amma tare zamu ci duk wannan ko? A'a matar yaya naki ne harma da kari so muke ki fi haka girma dan a tabbatar mun iya kiwo", murmushi kawai Zahra ta yi sannan ta fara cin abincin cikin nutsuwar da Ni kaina ban san Zahra tana da ita ba,nata dade da fara ci ba siyam da take ji kamar ta shake zahran ta dago ta dubi daddy cikin marairaita ta ce", pls daddy zamu tafi tare da ya AB yau bala baya jin dadi gashi Ni kuma bana jin dadi jikina bare nayi tuki", daddy ya ce", ashsha ai na yi tunanin yau bazaki fita ba saboda yanayin jikinnaki? Zan iya zuwa daddy amma dai su yi dropin dina " Zahra ce ta kalli siyam din cikin nuna tausayawa ta ce,ayya sorry sis ban san baki da lafiya ba shi yasa banyi maki sannu ba", wata muguwar Harara siyam ta ballawa Zahra tare da jan tsaki ba tare da ta tanka mata ba,fakar idanunsu Zahra ta yi ta yiwa siyam gwalo karaf kuwa sai akan idanun AB da yake mikewa,kallon gargadi ya yi mata sannan ya nufi barin dinning room ɗin,itama siyam mikewa ta yi tare da daukar Bag dinta ta bi bayan Ab din tana yi musu sallamar sai sun dawo.
Da sauri Zahra da taji wani abu ya caki kirjinta itama ta mike ta bi bayan su,a tunanin su Ammi rakiya ta tafi yiwa mijinta.
Daidai tana fita jafar na kokarin bude masa mota ,hangota da ya yi yasa shi dakatawa tare da maida hankalinsa kanta, da yaga dai da gaske nufosu take yi gashi ko mayafi babu ajikinta ga jikinta Masha Allah me nuna baiwar da Allah ya yi mata ne,sai yaji duk ranshi ya ɓaci da sauri ya tare ta tare da yi mata rumfa da jikinsa idanunsa a kanta muryarsa a ba ce ya ce, me kika fito yi me zaki yi a waje? Samun kanta ta yi da sakin hawaye tana cewa Nima zuwa zanyi ta fada hawayen na karasa zubowa,ware idonsa ya yi a kanta kafin da idon ya yi mata tambayar ina? Company mana Nima ai aikin nake a can kuma ba cewa nayi na daina ba, ya ilahil alamina ya fada yana dafe kansa,yanzu fa ta yi kamar ba ita ba ashe abin yana nan shi kam ya zaiyi,dake fatansa ta bar gurin a daina kallonta sai kawai yace je ki dauko mayafi amma kato ko kisa hijab,aiko sai ga wani kyakkyawan murmushi ya subce mata har kumatunta suna lobawa can ciki saboda murna bata san lokacin da ta ɗora lips dinta akan nasa ba ta sumbace shi tana cewa yauwa dan gidan YARBAWA, kafin ta zare daga tsakiyarsa da ya yi mata rumfa ta yi ciki da dan gudunta tana yi tana waiwaye da yi masa kashedin kar fa ya tafi yanzu zata dawo,jinjina mata kai kawai ya yi, sai da yaga ta kule sannan ya juya da hanzari ya shige motarsa,siyam da take ji kamar ta fasa tafiya saboda bakinciki ta biyo shi sai dai kafin tazo jafar ya rufe kofar tare da nuna mata motar gead din AB yana cewa shiga wannan daga haka ya shige gaba kusa da josuwa suka fita daga gate ɗin,babu yadda ta iya haka ta shiga motar tana tsinewa Zahra dan a tunaninta ita ta hana Ab ya shiga mota daya da ita...
Ko su Ammi bata kula ba ta haye sama da gudu, bata tsaya wata wata ba ta kuma fitowa da gudun ta Nufo falon kasa inda su daddy suke zaune yanzu duka a maimakon cikin dinning room ɗin........✍🏼
Haba Zahra ki dinga yin abun tunani mana ina kika taba ganin amaryar kwana ɗaya ta fita aiki🤣
Kai kuma Ab babu ruwanmu kuma babu wanda zai kawo maka maganin ciwon kai ehe dan kai ma kasan ka taro mach....🤣
Soyayyar Ab da yar GIDAN YARBAWA fa ta musammance dan zahramu ta musamman ce .
Rayuwar Zahra da su maman siyam ma ta musamman ce🤣
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*