Free chapter · Read without an account
Page32
.....cikin sauri ta ja blanket ta rufe jikinta kullum sai a dinga kallewa mutum jiki", ta fada tana rufe jikinta gaba ɗaya,saboda rawar sanyin da ta fara yi dan sosai zazzaɓin ya kuma rufeta,janyewa ya yi daga gurin yana dan furzar da hucin bakinsa, bathroom ya shiga ya yi wanka dan Ab haka yake kamar wani dan ruwa.daure da towel a kugunsa ya fito,da kukanta ya fara cin karo ga rawar sanyinta da ya karu dan yana hango yadda jikinta yake ta rawa,cikin dan takunshi me dauke da alamar hanzari ya karasa bakin gadon tare da bude ta yana kallon fuskarta da ta yi jage jage da hawaye, sorry ya fada can ƙasan maƙoshinsa tare da gyara mata dogon bakin gashinta da ya rufe kusan rabin fuskartata,janyo blanket din ta yi tana kuma rufa,matsawa ya yi gaban can wata drower wanda sai an budeta zaka fuskanci meye a ciki.
Kayan asibiti ne da allurai kala kala dan wannan ya wuce a kirata da akwatin temakon gaggawa dan akwai abubuwa da yawa da suka danganci asibiti a cikinta( kar ku manta AB cikakken likita ne da yayi karatunsa a kasar waje).
Allura ya fara hadawa sannan ya nufota kai tsaye yana mai yaye bangon da ta cukyikyiye kanta a ciki,da kyar ta bude idanunta da suka sauya daga na Zahra yar gidan yarbawa zuwa na mara lafiya kana kallonta kasan tana jin jiki,amma saboda karfin hali irin na Zahra sai da ta harareshi tare da cewa Ni kam ba zaka rabu dani naji da ciwona ba? Naga dai bani nace ka kawoni dakinka ba idan ma rowar bargon kake min tunda gashi sai bude Ni kake yi bayan kasan sanyi nake ji ko? Ta karasa fada tana cuno bakin hawaye na gangarowa kan kuncinta,bai tanka mata ba sai allurar da ya daga tare da kallonta yana mata alamar da ta gyara ya yi mata,ai sai a lokacin Zahra ta lura da allurar.
Wani tsalle tayi ta wuntsilo daga kan gadon har towel din da ke daure har yanzu a jikinta ya fara kokarin zamewa amma saboda bala'in tsoron allura da take yi bata bi takansa ba kakarin da take yi kawai na taga ta tashi ta gudu ne,shima cikin zafin naman ya kai dogon hannunsa ya dankota dai dai lokacin towel din ke karasa zubewa.
Kara ta saka tare da mannewa ajikinsa a kokarinta na kare kirjinta da suka bayyana a fili.
Da karfi ya wani irin runtse idanunsa kansa na wani irin sarawa saboda jin abinda tunda Ammi ta kawosa duniya bai taba jin irinsa ba,cikin karfin hali ya fara ƙoƙarin rabata da jikinsa,amma ina tuni ta kuma shigewa jikinnasa da shima babu riga daga shi sai towel tana kuma manne masa kamar zata huda cikinsa ta shige,duk ka sake ka kalleni sai na fadawa Ammi ta fada bakinta a akan kirjinsa take hucin zazzabinta ya bugeshi sai kawai yaji yana neman rasa nutsuwarsa,dakyar ya iya bude baki maganar na fita dai dai ya ce", baki son alluran?
Ey bana so kuma kar ka kallemin jiki idan ba haka ba sai munyi Shari'a da kai ta fada cikin zubda hawayen takaici da tabara,bai san ya a kayi ya saki wani makalallen murmushin gefen baki ba,a kallo kawai zaki Shari a dani? Ey ta fada tana kuma cusa fuskarta a kirjinsa lumshe idanunsa ya yi kafin a hankali ya ce", idan nayi abinda ya fi kallo fa? Kamar ya? ta fada tana dago kanta,kamar wanda yake jiran hakan sai kawai ya hade mitsitsin bakinsa da nata ba tare da ya bata amsar baka ba ya shiga nuna mata a aikace cikin wani irin salo me taba zuciya,shi kansa Ab din ji yake kamar ba shi ba,bai taba sanin yadda ake kiss ba ma balle a kai ga wagga zazzafan romance da yake neman juya masa lissafi.domin shi a rayuwarsa ko hannun mace bai taba kamawa ba bare ya kai ga yin wani romance da ita.
Iya durzuwa Zahra ta yi a hannun ab, kiran sallar magriba da aka rangada shi ya kwaceta, duk da dama bai yi niyyar yi mata wani abu ba kodan rashin lafiyanta,a hankali ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ce", mutum ko bashi da lafiya bakinsa ba zai mutu ba,ya fada yana hade bakinsa da nata saboda tunawa da ya yi baiyi mata allurar ba,sai da ya gama ya saki bakin tare da cewa dadina da iskanci bai san na gida ba,har masu fadarsa yinsa suke yi yanzu gashi duk kin tsotseni saboda is.....kuka tasa tana kai masa bugu a kirji.
Rike hannun ya yi yana mai tsirawa idanunta da suke rufe ido,gashin idon sun kwanta saboda ruwan hawayen da ya jikansu.sai kuma ya ɗan yi ajiyar numfashi yana rabata da jikinsa cikin nutsuwa.kai tsaye ya shige bathroom ya bar Zahra da ciwon takaicin maganganunsa da kuma abinda ya yi da jikinta.
Sosai ta ji zazzaɓin ya sauka dan haka ta fara ƙoƙarin tashi dan samun tsira daga hannun Ab da yake neman maida ita yar iskar karfi da yaji,saboda tsamin da jikinta ya yi ga kuma rashin kuzarin da zazzabin ya sa ta sai take yin komai a hankali,sai alokacin ta tuna a yadda take, laluben towel din ta shiga yi tana ci gaba da zubda ruwan hawayen da ita kanta bata ce ga dalilinsu ba...
Tana cikin haka Ab ya fito wannan karon sanye yake da rigar wanka,ganinsa yasa ta zabura ta koma cikin blanket din tana tabe baki da shirin karfafa kukanta,hannu ya ɗora saman goshinta yana jin yanayin zafin jikinnata,jin babu zafi zazzabin ya sauka yasa shi dan sakin numfashi tare da nufar mirror dinsa cikin yaukinsa kamar wata mace ya gama shiryawa duk da cewa cikin gaggawa yake yi amma baza ka fahimta ba, closed dinsa ya shiga ya sako kayan sallah jallabiya sky blue wadda ta yi matukar amsar jikinsa har kwanciya take saboda sulbinta.
Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta mike tana gungunin takura mata da ya soma yi,dakinta ta wuce itama dai wanka ta yi ta daura alwala tazo ta yi sallar laziminta ta zauna ta yi har akayi isha'i. tashi ta yi, daga nan ta dauko wata tsadaddiyar atampa me gold kalar baki da ja,ta saka tana cewa ai dole na ɗana ku kafin na tafi dan nasan kiris ya rage na karya waccan siyam din da mamanta kuma ina karyasu nasan cewa daddy da wannan kurman zasu yi na yi lungu wato gidan yarbawa namu na asali,dan haka dole na saka kayan da raina ya biya,tana gamawa ta fesa turarukanta na fama take ko ina suka bude da ƙamshi kamar shagon turare, daure gashinta ta yi ta can kasa tare da yin daurin ture kaga tsiya,kallon kanta ta yi tare da yin juyi kafin ta ce", Allah ya yi halitta Zahra yarinya yar duma duma,sai da ta gama juye juyenta sannan ta zura takalmanta suma masu ɗan tudu ta fito daga dakin, ko kallon dakinsa ba tayi ba ta fice dan karma ta je ko yana nan ya hanata sauka.
Ammi dake kokarin kiran Amira ta kaiwa Zahra abinci sai kawai suka ji takun zahran ga ƙamshinta da ya cika hancinansu har shi uban gayyar da yake zaune cikin main falon bai karasa dinning din ba,tap ce a hannunsa yana latse latsensa na fama.
Cikin farinciki Ammi ta taro Zahra tana mata sannu da jiki, har kasa Zahra ta zame zata gaida ammi amma sai Ammin ta yi saurin taro ta jikinta tana cewa a'a dougter ke da baki da lafiya muje kici abinci yanzu dama nake cewa Amira tazo ta kai miki saman ashe ma kina tafe",
Murmushi Zahra ta yi tare da cewa naji sauki Ammi daddy bai dawo ba ne? Ta tambayi Ammin ganin bata ga daddy din ba,yana ciki yau ba zai fito ba akwai aikin da yake yi ne", ayya ta fada tana satar kallon ogannata.
Ammi bari naje na duba mama da jikinta", Tom yar albarka ki fito sai ki ci abinci dan yau duk baki sa wani abu me nauyi a cikinki ba,Tom Ammi ta fada tana wucewa ta gefansa, sarai ya san me zata yi dakin mama hakan yasa tana zuwa zata giftasa yasa mata kafa aiko nata yi wata wata ba wajen fadawa jikinsa,kebe baki ta yi tana kallonsa idanunta har sun cika da kwalla sai kuma juya ta gurin ammi cikin shagwababbiyar Muryarta ta ce", Ammi kin ganshi ko, ƙarasowa falon Ammi ta yi tana cewa ya haka Abrahab ya zaka sa mata kafarka kuma da ta fadi fa? kasan dai ai ba lafiya gare ta ba ko? Bai ce komai ba sai ci gaba da ya yi da taba tap dinsa hankali kwance,yayin da har yanzu Zahra ke zaune dare dare kan cinyarsa ya ki bata damar tashi kuma ya fuske kamar bashi ya yi hakan ba,idanunta cike da hawayen takaicin AB din ta kuma kallon Ammi ta ce", ammi kice ya rabu dani na tashi.
Dakatawa ta yi daga jera abincin da suke ita da dije me aiki tana duban AB din ta ce", Me yasa kake haka ne dubiyarce baka yarda ta je ba shine ka biyo tanan? Bai tanka ba sai kallon kasan ido da yayiwa Zahran da duk ƙamshinta ya bi ya takurasa can ƙasan maƙoshinsa ya ce", tashi kije idan naji wani abu ba daidai ba umm," harara ta dan watsa masa cikin tura baki kana ta mike ta yi hanyar corridor da zai kaita dakin maman siyam.
Siyam kuwa na can ta tsare Amira ta tayar mata da hankali, cikin kosawa Amira ta ce", wai dan Allah siyam me kike so nayi miki ne? Kin kira Ni kuma kin sani gaba da hawayen da bansan dalilinsu ba,cikin yar fusata siyam ta ce", ey mana dole kice haka tunda kun kawo jaraba cikin gida yarinya ta asirce ku bakwa ganin tsiyar da take shukawa duk idanunku sun rufe,kamar baku san halin da nake ciki ba,ke Amira kin fi kowa sanin irin son da nake yiwa broth AB amma gaba daya yi kike yi kamar baki sani ba,shi kansa yadda yake yi sam abin bai da xe ba.
To meye ya dace siyam idan bamu kula da matar yaya AB ba da wa zamu kula? Wani banzan kallo ta watsawa Amiran kafin cikin mugun jin zafi ta ce", Tom shike nan indai ba zaku yi mata magana da ta daina abinda take.yi ba wlh wata rana sai na sumar da ita shegiyar yarinya muguwa kuna fa ganin dukan da ta yi min ranar Ni da mama ta fake da jinnu wai kuma saboda rashin son gaskiya aka bi bayanta, ga yau ma yadda ta maida min da hanci kamar ba nawa ba," to kiyi hakuri in dai wannan ne zata daina.
Sakin baki kawai siyam ta yi tana kallon Amiran da ta kama hanyar fita daga dakin tana kuma cewa ai ke ma kin san KURUCIYA ke damun matar yaya dole ne kuwa muyi hakuri da ita daga haka ta karasa barin dakin,tabar siyam cikin wani mugun takaici da daukar alwashin salwatar da rayuwar Zahra.
Mama na kwance tana fama da kugunta kwanciya ma ta kasa yi me kyau, har yanzu bata daina jawa Zahra Allah ya isa ba, dan ko itama ta tabbatar ita ce ta sa mata bawon ayaba ta yi faduwar da har yanzu bata da tabbacin cewa bata karye ba,tana cikin damuwar wannan halin sai kawai ganin Zahra ta yi a kanta tana cewa mama tunanin me kike haka ina ta sallama baki amsa ba.
Wata irin yar dungure mama ta yi har sai da ta fadi daga saman gadon ta kuma buguwa da kugunta take ta saka kuka tana yiwa Zahra Allah ya isa,da ci mata alwashin sai ta rama fiye da abinda ta yi musu muguwa yar gidan mugaye,dariya Zahra ta yi kana ta yi juyi tana turawa maman mazaunanta tana yi mata gwalo me cin ran wanda ke cikin halin takaici, waka ta fara yi mata tana cewa maman siyama me karkataccen kugu siyama me lauyayyan hanci,ihu maman siyam tasa tana zagin Zahra, Ammi ce ta shigo tana cewa lafiya mama?
Da sauri Zahra ta durkusa gaban maman tana mata sannu tare da kokarin dagota daga wadowar da ta yi tun shigowar Zahran.
Ammi ce ta shiga temaka mata suna dagata aiko Zahra tasa hannu ta kuma galla mata mintsini sai ga mama na sakin fitsari kamar wata yarinya saboda zafin mintsinin da Zahra ta yi mata.
AB ne ya shigo dakin fuskar nan kamar bai taba sanin meye dariya ba,dama abinda ya guda kenan shi yasa yaso hana ta zuwa amma sai mama ta daure mata shi kuma miskilanci ba zai barshi ya bude baki ya yi maganar da mama zata fahimcesa ba ya gwammace ya rabu da zahran ta je neman tsokanar da yasan shi zai kaita.
Amira da siyama ma shigowa su kayi hankali tashe suna tambayar meke faruwa,kai tsaye Zahra ta ce ", ina shigowa Nima naga ta razana har ta kaita ga faduwa ta bugu akan kugunta,hankalinta kwance take basu bayanin yadda akayi,siyama ce tayi kanta tana cewa shegiya muguwa wani abun kika yi mata kamar yadda kikayi mata dazu Wallahi kika kashe min mama bazan barki ba Nima da hannuna zan kasheki,"
Bayan AB ta yi duk da yadda yake ta faman watsa mata mugun kallo,ta rike shi ta bayan tana cewa Oga dan kurma kaga me lauyayyan hanci zata duke Ni,ai Amira bata san lokacin da ta fashe da wata muguwar dariya ba,sai da AB din ya watsa mata kallon gargadi sannan ta yi saurin nutsuwa tana mai kunshe bakinta dan sosai dariya ke cinta gashi babu halin yi..
Dole ammi ta shiga kiran masu aiki dan su gyara maman.
Zahra kuwa ganin babu fuska wajen Ab sai kawai ta nufi komawa bangaren Ammi, ta yi taku na daya a na biyu ta ji ya danƙi hannunta kamar zai ɓallasa biyu ya janye ta sunyi waje,ganin sama yake shirin wucewa da ita yasa ta fashe da kuka tana cewa Ni yunwa nake ji,ƙin saurareta ya yi ya cigaba da janta ransa ga dukkan alamu a bace yake da ita,sai da suka haye saman sannan ya juyo ya ce da Amira da itama ta fito daga dakin fuskarnan a kame ya ce" ki biyota da shi", to amira ta ce tana mai nufar dinning room ɗin.
Suna shiga ya saki hannunta tare da nunata da yatsa ransa a ba ce duk da cewa fuskarsa bata nuna hakan ba, cikin kaushin murya ya ce", duk randa kika yi abinda zai kai ki ga hukuma Ni kam babu ruwana ita wannan din da kika raina baki san yadda nake da ita ba ne? Daga yau ba ki kara fita ko hanyar kofa ne wuce na daina ganinki anan.
Hawaye na zuba kamar famfo jikinta a sanyaye kamar sabuwar marainiya ta wuce dakinta tare da rufe kofar da key ta fada kan gadon ta shiga rera kukanta, wallahi siyam sai na rama fadan nan da aka min akanki kuma dama naci alwashin idan Allah ya kaimu ba zaki bi shi office ba duk sai nayi sanadin zamanki a gida tunda Ni banje dan haka Kema ba zaki je ba,duk cikin kukanta take wannan surutan yayin da laifin ab ya kara hauhawa akan na baya.
Koda Amira ta kawo abincin da kansa ya karba ya zuba mata ya taho kawo mata,amma sai me Zahra ta rufe kofa ta ki budewa gashi shi kansa ya tabbatar tana jin yunwa tunda yau bata ci wani abin kirki ba saboda zazzabin rigimar da ta nemowa kanta.
Dafe kansa ya yi ya murza goshinsa saboda ciwon da yake masa, shi da sai a kwana a wuni bai yi magana sama da kalma ashirin ba amma yau shine bayan magana har da hauka Zahra ke neman sashi.
Komawa ya yi dakinsa ya dauko safaya key ya bude dakin, yana shiga ya sameta kwance akasa ta kame jikinta guri daya idanunta har kumburi su kayi saboda fitina da kukan da tasha,tashi kici abincin ya fada cikin dakiya irin ta mazan da suke son iya sarrafa matansu duk irin son da suke musu,amma shi ab sai yaji kamar ba zai iya zama wannan jarumin ba saboda yanayin da yake fuskanta wanda bai tantance ko meye ba akan Zahra.yadda ya yi mata magana cikin calm sai bata yi musu ba ta tashi zaune sai dai ta ki kallon inda yake bare abincin da ya shigo dashi a cikin wani hadaddiyar karamar kula me guda uku wanda idan ba budeta kayi ba sai ka dauka daya ce a hade.
Tausasa murya ta kuma yi yana cewa ba kina jin yunwa ba? Tunzura bakinta ta yi sannan cikin kukan da bashi da sauti ta ce ", ina ji amma na gidanmu zanci bana cin wannan tunda baka so naci saboda na gidanku ne,to Nima Allah yasa duk rashinmu Abbana bai taba barinmu da yunwa ba dan haka ka ɗauke abincinku ko zan mutu da yunwa ba zanci ba sai na gidanmu.
Allah sarki sai ga Ab da zama dirshan gaban Zahra idanunsa a kanta yana kallon karamin masifaffaffen bakinta da yake ta zaro magana babu sauki irin haka...✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*