Free chapter · Read without an account
Page35
......kunshe dariya Zahra ta fara yi tana satar kallon Ab da har yanzu bai nuna akamar ma yasan da wamzuwarsu a wajen ba.
Siyam kuwa da gudu ta bar gurin saboda abu biyu da suka haɗe mata wato tsananin kunya da zawayin da take ji kamar ta sake shi a wando.
Kasa daurewa Zahra ta yi ta fashe da dariya tana nuna hanyar da siyam din ta bi ranta fes haka ta ya cimma ruwa,kallon da ta ji a jikinta yana mata ne yasa ta dakata daga dariyar ta dan waiwayo aiko ita din yake watsawa kallon da zamu iya kiransa da na tuhuma, sosai Zahra ta fara fahimtar karatun dan kurmannata dan haka ta dan tunzura baki tana mikewa daga gurin dan karma ya ce zai kawo mata kabila mara riga akan abinda yasan ita ce ta yin.
Daf da zata wuce ya danko hannunta ya dawo da ita suna fuskantar juna bai ce komai ba sai kallon gargadin da ya ci gaba da binta dashi, kafin ya saketa cikin kamammiyar Muryarsa da babu wasa a cikinta ya ce", zanyi maganinki tunda ba zaki canja ba,daga haka ya rabata ya wuce ya bar gidan gaba daya,ko amsa a dawo lafiyar da Amira da ke masa baiyi ba,ita ma Ammi can kasa ya yi mata bankwana ya fice da boyayyan yanayinsa da ba fahimtar damuwarsa ko bacin ransa.
Rau ta yi da ido kamar zata yi kuka har da kebe baki, sai kuma ta fasa ta kuma fashewa da dariya saboda tuna karar tusar da siyam ta yi da yadda ya zura da gudu..karasawa cikin falon ta yi fuskarta dauke da murmushi ta zauna kusa da Ammi tare da dora kanta a kafadarta tana cewa wai Ammi shi baya gajiya da shiru ne ko da yaushe sai dai ya yi ta yiwa mutum yaren kurame?
Murmushin girma Ammi ta yi tana kuma jinjina kuruciyar Zahra wadda tazo mata da salon da bata gundura da ita,ta ce, Zahra ai shi Abrahab tun yana yaro haka yake baya yin magana doguwa duk ranar da ya yi kuwa sai ya kwana da ciwon kai saboda rashin sabo haka Allah ya halicceshi,tabdi jan to yanzu ammi duk wannan yar maganar da na sashi kwana biyu sai da ya yi ciwon kai? Ey hakan zai iya kasancewa in dai ba ya canja ba saboda shiga sabuwar Rayuwa", Ammi ta fada tana dan murmushin tambayar Zahra.
Siyam na shiga dakin mama da yafi mata kusa wani mugun wari ya daki hancinta bata tsaya bin ba asin warin ba ta fada toilet saboda amatsen da take.
Tun daga inda mama take tana jin karar gudawar siyam, sai hakan ya yi matukar bata mamaki dan a halin yanzu itama cikin gudawar take, tunda ta ci abincin cikin ta ya murɗa saboda yanayin ciwon kugunta yasa kafin ta kokarta ta mike tuni har ta sake ta daga inda take a zaunen, tana son tashi ta shiga toilet din sai ga siyam a guje kamar an korota ta fada bathroom ɗin.
Take ta tafi dogon nazari shin me ya kawo musu gudawa a lokaci daya ita da siyam? Ko dai siyam su tasawa maganin ne ba mutanen gidan ba? Wannan tunanin da ta yi yasa cikinta ya kuma murdawa saboda tashin hankalin da taji ta shiga,ga wata zufa da bata san ta ina take zubowa ba duk kuwa da a.c da fankar da suke ta aiki a dakin, tana cikin wannan halin siyam ta fito hannunta dafe da ciki tafiyar ma a durkushe take yinta kamar me nakuda.
Cikin tashin hankali mama ta ce,siyam me kika yi haka,kina nufin mune muka ci abincin da kika zuba maganin ko me hakan ke nufi?girgiza kai ta yi tana shirin bude baki cikin ya kuma juyawa,da gudu juya.
Yayin da mama ma ta samu damar tashi a wannan karon saboda ita kanta warin gudawarta ya isheta sai dai kafin ta kai ga karasawa siyam ta rigata ,a bakin bathroom din ta tsaya tana kiran siyam akan ta fito ta bata guri ta gyara kanta,amma ina siyam bata ma san tana yi ba.
Kaiwa da kawowa mama ta fara yi gaba daya ma ta manta da ciwon kugun da take yi ashe wata masifar na korar wata,tun tana jurewa har ta fara zagin siyam saboda ta ki fitowa daga bathroom ɗin,fitowar siyam dinne ya dakatar da ita, cikin sauri ta ture siyam ta shige duk da dai ita ta riga ta gama ɓaci da gudawar.
Dan Allah mama ki fito na shiga. siyam ta fada tana daga bakin kofar a durkushe dan ji take kamar yana fitowa ga wata irin murdawa da cikin ke yi kamar ana yakin karshen duniya a cikinsa.bazan fitoba dan ubanka yaro mara basira nace ka zubawa mutanen gida magani ka tashi ka zuba mana, to Ni ba zan fito ba ina ciki har sai ya tsaya dan haka ka tafi dakinka kayi naka"haba mama Ni fa ban zuba mana komai ba wlh sai dai idan wannan fitinanniyar yarinyar ce ta zuba mana wani abun tunda ita ta zubo mata abincin daga kichin....kafin siyama ta karasa sai ganin mama ta yi a gabanta daga ita sai towel da alama ma ko tsarkin sabon kashin da ta yi bata yi ba ta fito saboda jin siyam ta ce zahra ce ta zubo musu abinci.
Siyam sai da ta firgita da ganin maman kamar an jehota da wannan ta samu damar mikewa tana dafa bango zata koma toilet din, cikin sauri mama ta janyota tana cewa siyam baka ga ta kasi ba fa saboda mun riga da mun yi die, ta fada tana dora hannunta aka daidai lokacin cikinta ya bada wani sauti ƙuuuuuuuuu, ai ko da gudu suka shiga rige rigen shiga toilet,mama ce ta rike rigar siyam ta baya tana cewa kazo ka wuce dakinka kayi tutunka a can.
Siyam cikin zafi da tsanar Zahra dake ruruwa a ranta ta ce", mama pls help wallahi idan na fita dariya zata yi min tunda dama ta shirya hakan,mama ta ce", baka isa ba fa siyam, wai ba kase ka zuba musu maganin over yadda zasu mutu ba? Ey na zuba musu,siyam ta fada cike da dauriya dan tuni ma ta fara yi a wando gashi mama ta hanata shiga ita bata shiga ba itama bata shiga ba, wannan wace irin masifa ce haka, tabbas ko da kashe Zahra shine abu na karshe da zata yi a rayuwarta to tabbas zata kashe tan.
Ammi ce ta dubi Zahra ta ce ku muje mu duba maman siyam da jiki, itama siyam din naga bata fito ta tafi office ba ina ga jikin maman ne ya motsa," dama Zahra kiris take jira dan haka ita kanta Ammin ta rigata ta tashi tana cewa aiko dai mama Nima bani shurun ya yi yawa ya kamata a duba su,dukansu suka tafi dakin mama.
Suna shiga Zahra ta toshe hancinta tana cewa subhanalla me yake faruwa a dakinnan? Ko dai sokawe a ka bude a dakin ko kuma an yi ambaliyar kashi", ta fada tana bin siyam da kallo saboda yadda ta yi tsamo tsamo kamar kazar da aka tsamo a ruwa,duk a don da aka sha don yin fatin murnar mutuwar su Ammi ya tashi a banza dan da ace suna da ƙuda babu abinda zai hanasa bin abincinsa ta hanyar yayyabe siyam da gadon mama.
Lafiya siyam me yake faruwa a nan? Ammi ta tambayi siyam din tana bin jikinta da kallo,wani mugun kallon tsana ta fara watsawa Zahra kafin ta dubi Ammi cikin dauriya da danne bakin cikinta na ganinsu lafiya babu wata alama da ta nuna sunci abincin ma bare a kai tunanin ya fara yin aiki,ta ce", Ammi cikinmu ne ya ɓaci", subhanalla garin yaya? Me kuka ci haka? Naka kamar ma har a jikinku ku kayi ko? Bata bawa Ammin amsa ba ta fita da gudu ta nufi nata dakin, amdaga karshe dai abinda take gudu ne ya faru dan kuwa zahra ta kasa danne dariyarta, cikin dariyar ta ce", ikon Allah wannan shi ake kira alhaki kuikuiyo kuma idan zaka gida ramin mugunta ka gina shi dai dai kanka dan karshe kaine zaka fada.
Amira ma ganin Zahra nayi sai kawai itama ta fara Tata da tun shigowarsu take danneta,harara Ammi ta watsa musu tana cewa bana son shakiyanci dama a na yiwa lalura dariya ne kuma fa bata wuce kanku ba" Zahra ta ce", yi hakuri Ammi wallahi abunne akwai show baranma idan mutum yasan asalin Film din tun daga farko,Ammi bata sauraresu ba ta fice tana laluben nomber AB wanda shi ne yake dubasu idan basu da lafiya,duk da bata da tabbacin zai duba su siyam ɗin,
Ammi tana fita suma suka bi bayanta saboda warin da yake neman sa su yin amai.
Koda Ammi ta kira Ab bai ce komai ba,sai kashe da wayar da yayi tare da sa kiran Dr sonie, yana dagawa ya bashi umarnin ya je gidan ya duba yana da mara lafiya.
Koda Dr sonie yazo ya duba su ya basu magani ya tafi gudawar bata tsaya ba, kusan dai ranar yini su kayi a banɗaki, lokaci daya su kayi zuruzuru kamar basu ba.
Sai bayan la'asar ne gudawar ta ɗan lafa har suka kwanta suna jinyar kansu,Zahra ce ta shiga dakin mama tana cewa mama ga abincinku da yau baku samu ci ba,ya kamata Ku dan ci tunda naga yanzu kun rage zirga zirgar", Allah ya isa segen yaro mugu kaine ka bamu abinsi ya lalata mana siki sine yanzu ka kuma kawo mana ya karasa kase mu," dan ware manyan idanunta ta yi sannan ta ce", a'a fa mama Ni meye kuka yi min da zan saka muku wani abu har yasa ku gudawa? Kawai dai kaikayine ya koma kan masheka amma kaikayin me sauki tunda bai kashe mashekan ba,dan haka idan zaki ci abinci kici idan ba zaki ci ba yunwa ta yi ajalinki," fita ta yi daga dakin ko ajikinta dan har yanzu gani take basu biya bashin rayukan da suke da kudirin dauka ba.
Dakin siyam ta shiga wadda ita saboda tsabar yadda bayanta yake radadi da azabar yajin gudawa ko zama ta kasa yi,a goho Zahra ta same ta saboda iska ta dinga dan hura mata wajen😄,kai siyam ta tasha azaba saboda ita tafi mama shan roman da yawa.
Kunshe dariya Zahra ta yi irin bata son ta fito dinnan ta ce", aunty siyam ya jikin ko na kawo miki abinci ne dan duk yau zawo bai barku kunci komai ba", a wani irin fusace siyam ta juyo tare da antayawa Zahra wani mugun ashar kamar wata yar maguzawa, zaro ido Zahra ta yi sannan ta haɗe hannayenta waje ɗaya tana cewa yi haƙuri aunty bani ce na kar zomon ba amma dai ke kika bani rataya,a gidan ubanki matsiyaciya kwadayayyiya me auren saurayin wata wallahi Zahra ki rubuta ki ajiye sai na rabaki da rayuwarki sai kin rabu da Ab ko da ubanki ne Sarkin Mayun bayelsa",
Waww abun ya yi kyau,Zahra ta fada fuskarta babu alamun bacin rai,ta ci gaba da cewa aini Zahra dashen Allah ce babu wanda ya isa kasheni sai lokacina ya yi kuma sanadin mutuwar Zahra ba a hannun gafalalliya irinki yake ba,tsinuwarki da zaginki babu abinda zai dame Ni dasu tunda nasan taki uwar da uban ma basu tsira daga zaginki ba,karewa ma tseren kashi kika dinga yi da uwar taki wanda ko da za a mutu ita Zahran yar gidan matsiyatan da kika ambata ba zata yi tseren yin zawo da mahaifiyarta ba,kuma mahaifiyar zahra tana da tarbiya da ilimin addinin da ba zai sa ta sa yarta ta yi kisa ba,kuma ki rubuta ki ajiye in dai baku yarda makaman yakinku ba to babu abinda zaisa zahra ta yar da nata,mu zuba ni da ku yanzu wasan ya fara tare da Zahra YAR GIDAN YARBAWA,marasa imani masu tseren zawo uwa da ya masu kashin wando kai amma dai anji kunya wooooo,zahra ta kai karshen maganarta da yi mata gwalo.
Mikewa siyam ta yi zata janyo Zahra dan idan ba dukan Zahra ta yi ba yau hankalinta ba zai kwanta ba,ai abun sai ya yi mata yawa da bakin cikin rashin aikin da maganin bai yi ba zata ji ko da maganganun da Zahra ke gasa mata wanda take jinsu kamar wutar karmami a kahon zuciyarta ko kuma da bakincikin kasancewar Zahra matar mutumin da tafi kowa kaunarsa a duk duniyar nan?ita siyam har yanzu a haukarta bata fahimci cewa Zahra ta sauya abincin ba tunda dai da idanunta taga suna cin abincin,kuma maganganun zahran basu sa ta fahimci cewa zahra ta san shirin kashe su suke yi ba.
Zahra na ganin siyam ta yunkura zata kamata ta yi saurin yin baya tana dan fiddo idanunta waje ta ce, wai Mr AB din zaki daka? Wannan kalmar ita ta kuma tunzura fushin siyam akanta dan haka kai tsaye ta dankota,Zahra na jinta hannun siyam ta daddage ta fasa kara, siyam bata damu ba ta daga hannu zata kaiwa Zahra Mari a kyakkyawar fuskarta wanda ita Zahra ta na sane ta bar siyam din ta kamata bata gudu ba.
Daidai siyam ta kaiwa Zahra Marin daidai lokacin aka bude kofar dakin take kamshinsa ya cike dakin wanda shine yake saurin bayyana cewa yana guri,siyam idanunta sun rufe hannu ta kuma sawa zata daki zahran amma a maimakon ta sami zahra sai kawai ta ji hannun yabi iska wato dai ta daki iska wanda har hakan yasa ta kai ƙasa saboda ta riga ta bada gaba ɗaya ƙarfinta a hannun.
Zahra kuwa jin an janyeta dukan bai sameta ba yasa ta kuma kankame wanda ya janyetan, a take kuma ta shaida ko waye ta hanyar shakar daddan kamshinsa,a hankali ta dago kanta dan son tabbatarwa saiko karaf suka haɗe idanu,cikin sauri ta maida kanta cikin kirjinsa saboda tsananin yadda kallon da ya yi mata ya shigeta...
Ita kanta siyam jikinta ne ya dauki rawa saboda tsoron ganin Ab din babu zato ba tsammani,cikin rawar baki ta nemi yin magana amma sai ya katseta ta hanyar juyawa da zahra dake makale kamar kadangaruwa a jikinsa tana tsoron kara kallon idanunsa da a yau suka kasa boye bacin ran dake cikinsu a karon farko.........✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*