Free chapter · Read without an account
Page36
.......Cikin damuwa Ammi ta dubi siyam ta ce", siyam me ye kika yi hakan? Ko me Zahra ta yi miki bai kamata kisa hannu ki daketa ba,Gara ki bari ki fadawa mijinta yanzu gashi kin daki matarsa akan idanunsa,dakyar siyam ta hadiye miyan da ya tokare makogaranta ya ki wucewa idanunta kuwa kamar zasu yi aman wuta bakinta har huci ya ke ta ce,ammi ki yi shuru tunda baki san me ya hadamu ba,na tabbata ko da kin sani ba zaki bi gaskiya ba saboda idanunki sun rufe ko nace a sirin da aka muku ba zaisa ku gani ba,siyam Ni kike fadawa magana irin haka? Waye ya mana asirin? Me yasa kika kasa sawa ranki hakuri da abinda Allah bai ƙaddara ba,haba siyam sai kace ba musulma ba"
Amira da ke sawo kai dakin ma ta ce", wallahi siyam duk abinda ya faru da Zahra ba zamu kyale ba ko da yake shima nasan yaya AB ba zai barki ba,dan na fahimci tsanace kawai kika yiwa Zahra akan wani banzan Dalilinki Kum....Ammi ce ta katseta ta hanyar janta waje tana cewa babu ruwanki Amira bana son rashin kunya ban koya miki raina na gaba dake ba,daga haka suka fice suka bar siyam da karin wani tunzurin, ya yin da a zuciyarta take jin cewa yanzu ta fara neman yakin rayuwarsu dan wlh bazata barsu ba koda hakan zai kawo karshen nata numfashin to tabbatas ta yarda su yi mutuwar kasko,mu zuba Ni daku dan halak ka fasa...
A bangaren mama tana jin ta ɗan fara farfadowa ta ɗauki waya ta dannawa bokanta kira,ba tare da ta tsaya sauraren komai ba ta shiga zazzaga masa masifa akan cewar ya yaudareta ya ci amanarta ya bata maganin zawo a maimakon na farraku ko mutuwa,sai da ya ji ta ajiye numfashi daga zazzagar da take masa sannan ya ce kin gama? Ba tare da shima ya saurareta ba ya ci gaba da cewa kinyi na farko kuma na karshe idan ba haka ba duk ranar da kika kuma yi min irin wannan to kuwa zaki yi nadama,saboda ke matsiyaciya ce na baki magani kunje kunyi amfani dashi ba daidai ba amma saboda rashin kunya da renin wayo sai ki kirani kina min fada kamar uwata,to daga yanzu idan kinso zaki iya yanke alakarmu duk bata shafeni ba saboda ina da dubunku kuma sun yadda da aiki dan suna samun nasara tunda su ba jakar ƙwaƙwalwa garesu ba, daga haka kit ya yanke wayarsa yana huci da muzurai....
Kuka mama ta fashe dashi tare da yin wurgi da duk abinda hannunta ya ci karo dashi, wallahi ba zan kale wannan segen yaro ba dole na nemo safi me kyau ba irin naka na sa zawoyi ba,ta fada tana tashi da gudu saboda cikinta da ya kuma juyawa.
A can bangaren Oga AB kuwa,kai tsaye sama suka haye ba tare da ya tanka mata ko ya janyeta daga cukyikyiyar da tayi masa ba,yana shiga dakin ya zareta daga jikinsa tare da juyo da fuskarta da ta yi saurin kawarwa,kallon dai da take tsoro daga idanunsa shi ya kuma watsa mata take ta fashe da kuka tana mai cuno lebenta na kasa,dan tsuka ya yi yana mai watsa mata harara kafin cikin dakakkiyar muryarsa me dauke da yanayin gargadi da fushin da ya dan bayyana a cikinta ya ce ", kisa kike son yi ne? Me yasa kike haka? Kin san maganin da kika basu badan Allah ya kiyaye ba zai iya yi musu mummunar illa ko ma ya kashe su duka,rashin jinki watarana zai iya rusa mana duk wani zaman lafiya dan haka daga yau ba zaki kara sauka ko da bakin kofar falon nan ba ko ina nan ko bana nan stupid girl", ya karasa maganar cikin tureta daga kusancin da suka yi har tana faduwa kasa,bai kulata ba ya wuce bathroom saboda kiran sallar magriba da aka fara kwallawa.
Tana zaune a wajen ya fito ya shirya ya fice ba tare da ya kalleta ba bare ya bata umarnin yin Sallah kamar yadda ya saba mata,da kallo ta bishi idanunta na cika taf da kwalla, tashi ta yi ta tafi dakinta dan itama ta yi sallah,a ranta cewa daga yau babu ruwana da kai ba zan kara kulaka ba, dama ba zama ne ya kawoni ba to yanzu tafiyata zanyi na barku idan su siyam sunso su yi romanku kai da ahlinka su shanye ba damuwata bace,da wannan tunanin ta yi sallar har zuwa ishaa tana kammala addu'o'inta ta mike da hijabinta ajikinta sai takalmi da zura.
Har taje bakin kofa ta tuna da kayan duniyar da duk aka ce nata ne,dan jim ta yi sai kuma ta juyo ta dawo dakin tare da bude closed din tana cewa Wallahi Zahra bazata bar banza ba sai na kwashe komai tunda ko ba komai an kallan min jiki kuma an sha min baki dan haka duk wannan ba zai tashi a banza ba.
Manyan jakunkunan da ta gani a saman closed din ta janyo bayan ta taka stool din mirror,a nutse ta dinga dibar duk abinda taga ya yi mata, hakura ta yi saboda kar ta kasa dauka amma ranta akwai burin dawowa ta kwashe sauran tunda dai sun zama nata ko ba komai idan ta kyautata yammatancinta zata iya samun mijin Fulani ko zallar Balarabe wanda yafi AB ko mai da komai.
Kasa bude kofar falon da ta yi yasa ta hakura ta koma gefen kofar ta zauna bisa kan jakar da take daukarta da nishi ta rafka tagumi tana jira ya dawo ya bude mata ta tafi gidansu.
Tana jin alamar bude kofar ta dago kanta da sauri, a daidai nan Ab ya sako kai cikin nutsuwarsa da ke kara masa kwarjinin da Zahra ta ke tsoran kallon cikin idanunsa,ga mamakinta bai ma nuna ya ganta ba bare ya nuna wani mamaki na ganinta da uban kaya da hijab wanda dole ka gane cewa ita din me tafiya ce,juyawa ya yi ya maida kofar ya rufe tare da saka lambobin security din da bata taba sanin cewa da akwaisu ba.
Sakin baki ta yi tana kallonsa har ya shige can karshen falon inda ya saba zama a koda yaushe,zama ya yi cikin kujerarsa ta aiki tare da janyo tap din sa ya fara aikin dake gabansa.
Zahra dake kallonsa kai tsaye ta ji kamar ta fasa ihu,ga wani zafinsa da fushi da bata taba ji ba ya tsaya mata,cikin fushi ta mike ta kama hadle din kofar tana jijjigawa amma ko motsi kofar ba ta yi bare ta samu biyan bukata ta hanyar budewar kofar.
Da taga kofar ta ki buduwa sai kawai ta juyo idanunta na cike da hawaye tana kallonsa,har yanzu yana kan aikinsa. da wasa fuskarsa bata nuna alamar akwai wani abu da yake cakuda kansa da tunaninsa ba, tsaf ya shanye abinsa kamar yadda ya saba, wannan ne ya kuma tunzura zuciyar Zahra ta shiga watsa masa kayan da ta zuba acikin jakar kaf sai da ta rufe shi da kayan ya yi tamkar babu mutum a gurin sannan ta tsaya tana huci da kukan da sai yanzu ya samu damar fitowa saboda zuciyar da ta gama cinta.
A hankali yasa hannu ya dinga yaye kayan da suka yi masa rumfa tare da matsar dasu gefe,shayayyun idanunsa ya dago ya zuba mata su cikin yanayin kallon da ke sakar mata da kasala,kafin cikin nutsuwa ya rufe tap din yana mikewa dan barin wajen.
Fahimtar hakan da Zahra ta yi yasa ta daddage ta fasa ihum kuka tana diddira kafafunta cikin kukan take cewa ni ka bude min na tafi gida ba zan zauna anan ba.
Haka kawai kowa ya tsaneni kowa baya sona to Ni ka barni na tafi inda ake sona dama Ni bance zan zauna muku a gida ba,dan kawai kuna da kudi sai ku dinga yiwa mutum abinda kuka ga dama,to idan ma dan kaga na dau kayanku ne na fasa gashi nan na bar muku abinku har na lefen duka ku aiko ku karba dama ku ai yarbawannan marowata ne ba a cin kayanku,Kuma wallahi sai na fadawa Abba abinda ka dinga min dan abi min hakk......bata san ya a kayi ba sai kawai tsintar bakinta ta yi cikinnasa babu neman izininta ya shiga yin abinda take ikirarin zata fada a kwatar mata hakkinnata...
Duk yadda taso kwacewa hakan ya gagara karshe ma dai daukarta ya yi sukutum ya yi bedroom dinsa bakinsa na cikin nata yana mata shan sweet...cikin kankanin lokaci AB ya fara sarrafa Zahra da dukkan wani kuzarinsa da tunaninsa dake basa wannan ce hanya daya ta yin maganinta....
Haka kawai siyam ta kasa bacci ,babu abinda take sai kaiwa da kawowa, tabbas idan ta yi nawar kawar da Zahra AB zai maida Zahra cikakkiyar matarsa abinda bata fatan gani a rayuwarta dan da taga wannan rana Gara Allah ya dauki ranta ta huta da ganin ranar bakinciki ranar da zuciyarta zata buga ba tare da ta shirya hakan ba,babu abinda yafi daga mata hankali sai yadda taga tun hayewar da suka yi sama har yanzu Zahra bata kuma saukowa ba,koshi AB din da ya sauko sallah bai tsaya a kasan ba ya wuce duk da hakan ba sabon abu ne a wajensu ba,to amma tana matukar tsoron yanayin da ta gansa a ciki dazun.
Cikin sauri ta fito daga dakinta,sai da ta leka ko ina na coridow din kafin cikin sanda ta fito gaba daya ta bude dakin mamanta ta shiga tana fatan Allah yasa wuya bata sa ta yi bacci ba.
Aiko kamar yadda ta zata maman tuni ta yi baccin wahala da gwagwarmayar da tasha yau na sinturin zuwa banɗaki.
Dan jim ta yi kafin ta fara tashinta cikin raɗa.
A tsananin firgice mama ta tashi bakinta dauke da sunan Zahra,da sauri siyam ta toshe bakin maman tana cewa mama nice fa", murje idanunta ta yi tana cewa siyama me kazo yi baka yi bacci ba?mama banga ta bacci ba Zahra na can zata mallake min AB mama zuciyata bazata dauka ba.
Kai ya a kayi kasan ze mallake AB eye siyam?
Mama kina daki dazun baki san me ya faru ba,daga nan ta bata labarin abinda ya faru da Zahra ta shigo dakinta,ajiyar numfashi mama ta yi sannan ta ce", segen yaro Nima yazo daga nan ya wuce naka dakin to yanzu me kake so a yi?
Yauwa mama bari kiji abinda na shirya....ta kama kunnenta ta yi mata rada, jinjina kai mama ta yi tana cewa uwa baze yi gudu dansi ya yi rarrafe ba wannan sari ya yi yarona siyam," dariya siyam ta yi tana jin ranta fes dan sosai ta ji a ranta cewa a daidai wannan lokacin Zahra na tare da AB ana shirin yi mata sakiyar da ba ruwa.
Sosai AB ya ke son hukunta Zahra da al'amarin da yake ji zai yi sane kawai dan hukuncin,ita ko Zahra tun tana kokarin kubuta har dai ta bada kai bori ya hau dan kuwa yau sosai ta tantance zakin bakin AB Zahra da son zaki bata san lokacin da ta shiga sarrafa bakin AB da kanta a cikin nata ba,wani salon ma bata san tana yi ba,dan kuwa abin yana kai mata har can.
Zare rigarta da ya fara yi ne yasa ta dan motsa jikinta dan hanasa abinda yake kokarin yi,sai dai ina ta makaro dan tuni ya yi kasa da ita tare da kara manneta a naked kirjinsa da shi baisan ma lokacin da ya cire nasa rigar ba.
Haduwar fatarta da tasa ya basu wani hot shock da yasa gaba dayansu suka fidda wata irin ajiyar zuciya wanda a tunaninsu a boye su kayi ta.
Tudun lafiyayyan kirjinta ya hadu da lafiyayyan kwantaccen gashin kirjinsa ya kuma haifar musu da wata irin rawar jiki me hade da kasala da tashin tsigogin jiki,zagaya hannunsa ya yi ya dora akan sussulbar fatar gadon bayanta yana shafawa cikin wani irin yanayi da yake jinsa kamar a sararin samaniya ko kuma wanda yasha kayan maye,cusa fuskarsa ya yi tsakanin wuyanta da kirjinta tana Binta da wani irin zazzafan kisess masu kona ruwan kai,tare da sakar mata wani irin numfashi me dumi yana shaƙar ƙamshinta da ya riga ya manne da fatarta saboda yadda take nunawa turare rashin imani idan zata saka...
Wata irin sheshsheka Zahra ta yi saboda jin sanyin bakin AB a kan kirjinta tare da jin wani irin zummm har cikin kwakwalwar kanta...
A can bangaren siyam kuwa sun gama shiryawa tsaf mama na kwance a kan gadonta kamar gawa,siyam ta yi sanɗa ta fito falon bata bi ta kan sashen su Daddy ba wanda ko ma me ya faru sune farkon wanda ya kamata ace sun fara sani,kai tsaye ta haura saman upstairs din AB hannunta dauke da kakkauran savenpoon na karfe....
Daidai lokacin AB ya yiwa Zahra rumfa da faffadan kirjinsa idanunsa akan nata idanun da suke a runtse tana kokarin son tantance halin da zuciya da gangar jikinta suke ciki, addu'a ya yi tare da hade jikinsu guri daya yana mai kokarin kaiwa inda yake son kaiwa...✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*