Free chapter · Read without an account

Page37

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

.....sai dai kuma ga mamakinsa ya rasa hanyar bi dan bai sani ba kuma bai taba tunanin abin zai bashi wuya irin haka ba.

Ita ko Zahra cikin wani irin mummunan tashin hankali ta shiga dukan kirjinsa tana cewa yaaa AB miciji a jikina miciji zai sare Ni wayyo Allah mama mutuwa zanyi micine a jikin....hade bakinsu guri daya yayi dan baya bukatar wannan sakarci da shirme na Zahra,harshenta ya kama yana masa shan sweet yayin da zahra aranta ta cigaba da maganganunta hankalinta tashe dan jin har yanzu abinda ta ke kira micijin bai daina laluben jikinta ba.

Hawaye kuwa tuni wani yake korar wani, cewa take shike nan na mutu dama yana sane ya min wayo da bani zumar bakinsa ashe dan ya kasheni ne,ji tayi a wannan karon ko zakin bakin bata ji saboda ta rayuwarta kawai take yi,jin yadda ya dan sassauta ruko da shan da yakewa harshenta yasa ta dan fizge bakinta tana cewa idan kana yiwa Allah da ma aiki kayi hakuri kar ka kasheni shi Abba bai san cewa da jinin mutane kuke yin kudinku ba, ya dauke Ni ya baku dan Allah kuyi hakuri dukanku wallahi Abbana ba kwaɗayayye ba ne tsautsayi ne dan Allah ka cire min macijinnan wallahi kato ne kuma a wajen fitsarina zai sare Ni",

Numfashi AB ya furzar shirmen Zahra na hawa kansa ga kuma yanayinsa da damuwar rashin samun hanya dan duk a tunaninsa abin ba zai dau lokaci ba, duk da cewa yana matsayin likita to amma rashin yin abin practical yasa duk kansa ya kulle,yana tunanin dole sai ya haska wajen ya nemo hanyar horas da Zahra dan ko kadan bai ji a ransa zai barta ba,hannu yakai wajen yana shafawa ko zai dace sai kawai yaji Zahra ta kuma sa kuka tana cewa innallaha ma assabireen Zahra yau kaddarar mutuwarki a hannun mutum ta ke, runtse idanunta ta yi saboda yadda tsigar jikinta ke wani irin mikewa saboda yadda Ab ke shafata da zuciya daya yana neman mafita,a hankali ya kuma birkitawa ya yi mata rumfa ya hade jikinsu waje daya a sonshi na kuma gwadawa a karo na biyu,ƙara Zahra ta saka jin AB na soka mata macijin a wajen fitsarinta tana cewa wannan wane irin maciji ne me naci ko da yake ba mamaki macijin tafi ne wallahi Allah sai ya min sakay....bata karasa ba shima ab Yana gab da samun nasarar gano hanyar kunnuwansu suka tsinkayo wani irin gigitaccen bugu wanda ya shiga har kwakwalwar kansu tamkar ana buga gangar shedan,ɗif suka yi gaba dayansu yayin da Ab ya dan runtse idanunsa da suka sauya kala daga ainahin kalarsu Zahra kuwa jin ba a daina bugun ba yasa ta birkice tare da kanmkame AB tana mantawa da batun macijin tsafi,cikin rawar jiki da na baki ta ce", yaya AB 'yan fashi da makami dan Allah kar ka bari su cutar damu kayi sauri kaje ka shuna musu macijin tsafinka dan Allah ka ji.....

Duk yadda bugun kofar da kuma maganar Zahra su ke hawa kansa hakan bai hanasa kasancewa cikin nutsuwarsa ba,a hankali ya zareta daga jikinsa ya mike tare da zura jallabiyarsa ya taka zuwa bakin kofar zai fita,dan juyowa ya yi yayi mata gargadin kar ta fito da ido kana ya fita daga dakin.

Jinsa kawai Zahra ta yi dan bata tunanin zata iya ci gaba da zama a gidan ma baki daya tare da wannan katon macijin da shi ko dan irin tsokar nan bashi dashi haka nan yake tamkar jijiyar bijimin Sa kuma baya kwanciya,da sauri ta mike ta zari doguwar rigarta ta zura tana yi tana waigen ta inda macijin zai kuma fitowa da sauri ta fita tana cewa Allah yasa dai ya ji shawarata ya Koresu da macijin....

Cikin kamewarsa da rashin nuna tsoro ya bude kofar falon. dai dai lokacin mutanen gidan da gigitaccen bugun ya tayar dasu suka karaso cike da tsoron abinda ke shirin faruwa hatta da masu aiki a wannan lokaci sun mike suna kaiwa da kawowa tunda ba damar su nufo sashen kai tsaye a wannan lokacin....

Siyam na ganin hakanta ya cimma ruwa sai ko ta yi kan Ab ta rungumesa cikin tashin hankali tana cewa shikenan mama ta mutu na rasa mamana bro AB bani da kowa yanzu mama ta mutu,,,daidai Zahra na fitowa idanunta suka yi mata mummunan gani siyam rungume da AB tana tumurmusa a jikinsa da sunan kukan mutuwar uwarta, a fusace Zahra ta karaso kusa dasu ta banbare siyam daga jikinsa tana cewa to dan kaikayi ya sheke mashekiya shine zaki rungume namijin da ba muharraminki ba dawo da ita zai yi da kika yi masa wannan iskancin?

Cikin kuka siyam ta kalli Zahra ta ce", amma wallahi Zahra baki da imani sai yau na kuma tabbatar da rashin kaunar da kike mana kuma Allah ba zai baki nasara akan abinda kike son aikata mana ba, daddy ne ya katse su da cewa wannan wane irin shashashanci ne kina maganar mahaifiyarki ta rasu kuma kin tsaya kina wasu surutan banza memakon kizo muje muga halin da take ciki dan mutabbatar da abinda kika fada ɗin,cikin kuka ta ce", shike nan daddy muje ta fada tana jan hannun AB da ya yi tsaye yana kallon ikon Allah fuskarsa babu wata alama ta sauyin yanayi daga dukkan abinda yake faruwa,da sauri Zahra ta kwace hannun tana cewa Ni kam yau na hadu da yar iskar mata uwarki ta mutu amma kina son yin kwartanci a gaban jama'a," jan hannun siyam da Ammi ta yi yasa ta hakura ta bita amma tabbas ta ji zafin maganganun Zahra da yadda AB ya yi tsaye yana kallonsu bai nuna tashin hankalinsa akan rashin mamanta ba bare kuma na abinda Zahra take yi mata tun fitowarta, wallahi sai na sabauta rayuwar yarinyar nan zan samu salama a rayuwata ko da mutuwa nayi ba zan kwanta cikin salama ba har sai Zahra ta ɗaiɗaice.da wannan lafazin a kan harshenta suka sauka kasan idanunta kuma na akan Zahra da ita take binta da kallon shakiyanci dan sosai ta ji dadin yadda AB ya bata hadin kai wajen kin bin siyam din.

Juyowa ya yi yana kallon Zahran wadda ta yi azamar bin bayansu saboda sauri har hada step biyu ta ke yi,a ranta ta kudurta cewa ita da saman nan har abada dakin Amira zata gudu kafin ta samu damar fecewa gaba daya.

Shi dinma saukowa ya yi amma bai bisu cikin dakin ba ya dai tsaya hannayensa goye a bayansa yana jiran jin sakamakon dalilin da yasa siyam ta yi wannan abun da ta yi ,wanda shi a karan kansa yake jin kamar tana sane ta yi hakan tunda ai bashi ka dai ne a gidan ba,kai a lissafima duk abinda zai faru a gidan shine na karshen ji saboda duk sunfi shi kusa.

Suna shiga dakin suka ga mama kwance a sankame kamar gawar gaske,kuka siyam ta kuma fashewa da shi tare da fadawa jikin maman tana jijjigata wai ta tashi kar ta mutu ta barta bata da wani gata sai ita, daddy ne ya matsa kusa dasu tare da kai hannu zai taba mama amma sai siyam ta yi wani irin juyi a zuwan kuka take ta tareshi ta hanasa tabata,Ammi ce cikin son rarrashin siyam din ta ce", dan Allah siyam ki daina wannan kukan ki bari muyi abinda ya kamata dan Nifa gani nake kamar bata mutu ba,daidai shigowar Zahra wadda idanta ya sauka akan mama sai kawai ta fara sharar kwalla tana cewa Allah sarki mama ashe ba mai cika buri ba ce.

Wani mugun kallo siyam ta watsa mata kafin ta ci gaba da girgiza maman tana kuka, daddy ya ce", wai siyam me kike nufi da ba zaki bari mu duba ta mu bincika ba kin kanainaye ta sai kara mata wahala kike idan mutuwar ta yi ki matsa mu tabbatar da mutuwar kafin duk abinda zai biyo baya", ai kamar ya kuma tunzurata dan ita siyam a son ranta ayi ta wannan hayaniyar har ayi assalatu ta yadda Zahra da Ab basu da halin kasancewa a tare tunda tasan yadda yake da aiki kuma gobe ranar shiga hospital dinsa ce dole ba zai zauna a gida ba.

Ganin da Zahra ta yi da gaske siyam bazata bari a gano makircinta ba yasa ta nufi toilet ba tare da kowa ya kula da ita ba,ruwa me sanyi ta debo wanda ya kusan yini a cikin boket yayi sanyi sosai ta dauko boket din gaba daya tayo waje,tana fitowa bata tsaya wata wata ba ta yi kan mama ta sheka mata shi gaba daya har sai da ya jika gadon sharkaf sannan ta matsa tana cewa ai daddy ba tsayawa zakuyi daka ta wannan ba idan ta ita ne sai dai maman ta sheka tana wannan sakarcin kukan da bashi da dadin ji a kunne dan wallahi kukan aunty siyam iri daya ne da kukan jaki,"

Wata irin sheshsheka mama ta yi tare da wuntsulowa tana mai sauke kanta kasa saboda yadda ruwan ya tafar mata har cikin tsakiyar kanta saboda babu inda bai bi ba, baki hanci kunne duka sai da ya samu hanyar wucewa tanan..

Wayyo wayyo wayyo abinda mama take fada kenan a gigice tana matsar ido da hanci.

Su daddy kuwa hamdala suka shiga yi da murnar dabarar da Zahra ta yi.

Siyam kuwa a fusace ta mike ta nuna Zahra da yatsa tana cewa waike wace irin mahaukaciya ce? Wannan wane irin dabbancine zaki zo ki zubawa mamana wannan uban ruwan me yawa ga sanyi muguwa me bakin hali kawai.

Zahra ta bude baki zata yi magana karaf suka hada ido da AB wanda ya shigo dakin daidai Zahra na shekawa mama ruwa,murguda ƙaramin bakinta ta yi tare da kawar da kanta cikin ƙunkuni take cewa kuma wallahi bazan koma dakin tsafi ba ehe.

Mama fa ta shiga wani yanayi da babu wanda ya fahimci halin da ta shiga dan su murna suke yi ta farka,Ammi ce ta ce", to AB dan dubata mana tunda an samu ta farfaɗo kaga meye yake damunta,Zahra na jin haka ta fashe da kuka tana murza idanunta kamar dai yadda yara tabararru suke yi,cikin sauri Ammi ta kamata tana cewa lafiya me ye ya sameki?

Cikin kuka Zahra ta ce", Ammi maciji ne a dakin ya AB wallahi kato kuma mun kasa kashesa muna ta kokarin kashesa ne siyam tazo,Ni dai ba zan koma sama ba dakin Aunty Amira zan koma",

Ai da gama maganar Zahra gaba dayansu hankalinsu ya dawo kanta daga Ammi har daddy da Amiran,shi ko AB saboda tsananin takaicin Zahra hannu yasa ya dafe goshinsa yana kallon wani waje daban.

Daddy ya kallesa ya ce", Abrahab garin yaya maciji ya shigo har dakinka ko dai wani abu ne ya tsoratata? Gyada kai kawai Ab ya yi yana mai barin dakin saboda idan ya cigaba da tsayuwa komai zai iya faruwa,ajiyar zuciya Ammi ta dan sauke kafin ta ce", doughter kiyi shiru babu wani maciji tsorata kawai kika yi",

Ni dai Ammi a dakin Amira zan kwana tsoro nake ji,Tom shike nan Amira jata kuje dakinki"Tom Ammi Amira ta fada tana kama hannun Zahra sai da suka je bakin kofar fita sannan Zahra ta waiwayo ta fakaici idanunsu daddy da suka koma kan mama ta yiwa siyam gwalo wadda saboda tsabar takaici da bakincikin da take ciki ta kasa motsawa daga inda take, saboda ta gane makirci Zahra ta yi dan kar AB ya duba mama.

Ammi ce ta ce", siyam tazo su kama mama su maida ita dakin aiyam din saboda gadon ya riga ya jike gaba daya,cikin wani irin tsanar ahlin gidan gaba daya siyam ta mike ta kama maman zuciyarta na wani irin suya, ba komai ne ya fi mata mata rai da su daddy ba sai ganin yadda suka rude suka tashi hankalinsu lokacin dq zahra ta fashe da kukan maciji yadda suka nuna damuwarsu ko lokacin da ta fadi mutuwar mama basu shiga wannan yanayin ba.. wannan dalili yasa ta kuma daukar dumi da su. dan yanzu bata ki ace sun yi gobara sun kone kurmus ba......✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol