Free chapter · Read without an account

Page47

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

.......Ab suna shiga ɗakin ya kwantar da Zahra da har yanzu take lafke kamar me suman gaske,sai da taji alamun ya shiga bathroom sannan ta buɗe idonta guda ɗaya dan taga abinda yake shirin yi,daidai ya fito da ruwa dauke hannunsa cikin ƙaramin cup,da sauri ta maida idanunta ta rufe,yana zuwa ya ɗan yayyafa mata ruwan ƙaɗan a fuskarta,aiko sanyin ruwan yasa taja ajiyar zuciya tare da buɗe idanun a hankali kamar wadda ta farka daga doguwar suma,cikin nutsuwa da kamewarsa ya zauna a gefenta tare da ɗora kanta a saman cinyarsa yana kallon cikin idanunta da har yanzu take buɗesu tana lumshesu!,ɗora hannunsa ya yi a fuskarta yana shafawa kafin kamewarsa da muryarsa da bata yi girma ba ya ce,"zahr me yake samu ki"?juyawa ta yi rufda cikin ta cusa kanta a cikinsa tare da zagaya hannunta ta ƙugunsa sannan a hankali cikin karamin sauti ta ce,"yaya ɗan kurma nima kawai ji nayi na fadi kuma bana jin ciwon komai ajikina",ɗan jim ya yi kafin ya ce,"Tom bari na dubaki ko da wata matsala",umm umh ta fada tana maƙe kafaɗarta!,"me yasa"? ab ya bukaci jin dalilinta duk da yasan me take gudu,ta shi ta yi daga kwancen da take tare da mikewa tsaye tana cewa,"yaya AB bamu ci komai ba duka gidan bari na taso Amira mu je keching".

Riƙo hannunta ya yi tare da zaunar da ita saman cinyarsa, sannan ya ce, "ki bari bakya jin daɗi" langaɓe kanta ta yi idanunta har sunyi alamar hawaye,kafin ta ce, wani abu ya dagata tare da nuna mata hanya dan yasan tana fara magana zata rikice masa da rigima,sai da ya kaita har bakin upstairs ɗin ya tsaya yana hangota ta shige bangaren amira dan kiranta sannan ya juya ya koma ciki, tap ɗinsa ya ɗauka tare da zama a falon ya fara rage wasu aiyukannasa.

Sai da Zahra ta tabbatar ya koma sannan ta fito daga inda ta boye,da sauri ta shige keching ɗin ta fita ta kofar baya zuwa sashen masu aiki.

Siyam kuwa tun bayan gama tattaunawarsu da mama akan mamakin yadda a kayi Zahra tasan shitinsu,ta ɗauki mota ta fice daga gidan tana jin zuciyarta kamar zata fashe kanta har wani hayaƙi yake, saboda ɗaukar zafin damuwar rashin yadda zata bullowa Zahra,ƙawarta wata krista me suna suzan ta kira akan su haɗe a clup ɗin wajen gari, bata duba nisan gurin ba ta kuma bawa motar wuta ta figeta da masifar gudu.

Koda durga ya ƙaraso gidan bai tsaya sauraren kowa ba, kai tsaye shiryawa ya yi, tare da umartar yarannasa da su haɗe a clup ɗin wajen gari kamar yadda suke gabatar da Shagalinsu a can a duk lokacin da wani ya fito daga magarƙama ko wani abin farinciki ya samesu, ko sun gabatar da wani aiki lafiya ba tare da sun samu wata matsala ba,to duk suna yin irin hakan a wannan club ɗin da yake tamkar matattarar duk wani ɗan iska da gawurtaccen creminale, kai duk wanda yasan wannan club ɗin to haƙiƙa ba ƙaramin tantiri ba ne.

Tun daga nesa baba talatu ta hango Zahra,dan haka kafin ta ƙaraso ta cimmata,waje suka samu suka tsaya, sannan Zahra ta dubi baba talatu ta ce, "baba talatu ya a kayi kika san abin da su mama ke ƙullawa"? murmushi baba talatu ta yi!, kafin cikin ƙanƙan da murya ta fara cewa,"uwar ɗakina ai yau Ni naga tashin hankali da idona,dan wlh akan idanuna siyama ta zuba guba a cikin abincinku",ina kallonta ta taga har waya a ka kirata a lokacin ake sanar da ita bayanan gubar wai gubar bazata bayyana ba sai a hankali zata dinga kasheku ɗaya bayan ɗaya yadda babu wanda zai yi zargin wani abu bare ayi tunanin kasheku a ka yi, wai me kuka yiwa waɗannan mutanen suke son kasheku ey uwar dakina"?

"Baba talatu me zamu yi musu kuwa??"amma dai inaga nice na shafawa mutanen gidan kashin kaji, Ni suke son kashewa amma saboda son da mutanen gidan ke min yasa suma suke son kashesu, Allah yafi su kuma ba zai taba basu dama akan muguwar niyarsu ba,na gode baba talatu ina fata zaki ci gaba da tayani sa ido akan duka motsinsu kafin lokacin da zasu ɗibi kashinsu a hannayensu"?dan bana son tona musu asiri yanzu sai sun gama sanin wacece Zahra ƴar gidan yarbawa."

"In sha Allah uwar ɗakina zan baki gudunmawa ta ko wane bangare dan waɗannan bayin Allah ba abin yardawa bane" na gode,"Zahra ta faɗa tana barin wajen.

Bin bayanta baba talatu ta yi dan zuwa ta ɗora sanwar rana da wuri tunda babu wanda yaci komai a gidan,sai kuma taga Zahra ta tsaya a keching ɗin dan haka sai kawai ta shiga taimaka mata suka fara haɗa abincin.

Ƙamshin girkin Zahra ne ya fara tashin mutanen gidan daga baccin weekend ɗin da suka koma,duk da cewa basu fito ba amma kowa ya shaida girkin Zahra dan wannan girkin ba ƙamshin nasu baba talatu ba ne kamshin girkin ammi ne wanda ita ce da kanta ta koyawa Zahra dan haka ƙamshin girkinsu daban yake da na masu aiki,

Sai da Zahra ta kammala komai sannan ta danƙawa baba talatu amanar komai dake kan dinning ɗin sannan ta hade sama dan tsaftace jikinta,

Tana shiga falon ta dubi ƙaton a gogon dake girke a falon, wanda shi kuma a daidai lokacin ya buga ƙarfe sha biyu da rabi na rana,ƴar barandar falon ta buɗe ta shiga ba tare da tasan me zata yi a wajen ba.

Bata taɓa shiga wajen ba sai yau, dan haka wajen ba ƙaramin ƙayatar da ita ya yi ba,leƙawa ta yi kasan sai taga ashe wata yar garding ce ta hutawa a wajen, kuma daga wajen kana hango me shigowa da me fita duk da cewa an ɗan zagayeta da wasu itatu ƙamar na bukka,mama ta hango zaune akan kujerun da suka kuma kawata gurin da alama hutawa take yi,dariya Zahra tayi! Sannan ta ɗan juya bayanta inda zata bi ta koma cikin falon ranta fal tunanin ta yadda zata yi ta hana mama wannan jin daɗin,dariya ta kuma yi saboda abinda ta tuna da sauri ta fita tana cewa, "su Hajiya mama anga banza irin wanda babu a ƙauye,bata bi ta kan Ab da yake kwance saman coch ɗinsa me kama da gadon sarauniya ba ta yi ficewarta zuwa dounstais.

Saukowa ta yi fuskarta cike da fara a,ko baba talatu dake zaune a falon kasan cafet tana kallo bata kula ba ta wuce keching ɗin ruwan da ta wanke doya baba talatu ta ce, kar ta zubar akwai abinda suke yi da shi, shi ta ɗauka ta kuma ɗauko wata doyar ta feraye ta tsundumata cikin ruwan har bawon ta wanke ta cire doyar ta a jiye, dan diri_diri ta yi yatsanta kan lips ɗinta tana tunanin abinda zata kuma karawa dashi,"frg ta buɗe ta ɗauko ƙanƙara ta tsoma acikin ruwan sannan ta zuba kalar lemo Orange, dan taga fararen kaya ne a jikin maman dan haka zata yi kyau da ayi mata rinin maguzawa,ta fada tana dariya!sauri ta yi ta ɗauka ta fita daga keching ɗin dan kar AB ya tashi daga bacci ko ita maman tabar wajen,

"Uwar ɗakina ko na kawo taimako"? Mama ta tambayi Zahra dan tuni ta fahimci cewa Zahra wata salon muguntar zata yiwa waɗancan kafirawan farkon waɗanda suka ƙi gane cewa Annabi ya faku,girgiza kai Zahra ta yi tana saurin hayewa upstairs ɗin,komawa baba talatu ta yi ta zauna tana cewa,"koda yake wannan zamanma da nake yi ai babban taimako ne",

Cikin sanda Zahra ta bude falon, sai da ta fara leƙawa ta tabbatar AB ya tashi daga falon ma gaba daya sannan ta yi saurin shiga ta faɗa barandar,sai da ta fara yin addu'a akan Allah yasa mama tana nan bata tashi ba,tare da ƙara juya ruwan sannan ta cire ragowar ƙankarar da bata karasa narkewa ba.

A hankali ta zura robar da ruwan ke ciki dai_dai saitin inda mama ke zaune saboda jin daɗin iskar da take shaƙa me Ni'ima har bacci ta fara baki a hangame kamar shaddar gargajiya,dariya na cin Zahra ta juye mata ruwan gaba dayansu a kanta.

Wata muguwar zabura mama ta yi tare da yin wata yar dungure me tafiya da ka!,cikin azabtar sanyin da ya ratsata take cewa, "eho Allah ga maman siyam shedan na son gani baya nasa,Allah ka raba maman siyam da mutuwa lokaci nasa be yi ba, Allah ya bar maman siyam ya sika buri nasa kar ya mutu be ga jika nasa ba".

Zahara na jin haka.ta kwashe da dariya tare da saurin barin wajen, dakinta ta shige tare da shigewa toilet bayan ta boye robar a keching ɗin saman,kai tsaye ta fara wanka dan karma wani yayi zarginta,amma fa dariya har da hawaye duk ta tuna gwalanton maman siyam da yar dunguren da tayi sai taji kamar ta yi fitsari a tsaye saboda dariya.

Tsaf ya fito cikin shirinsa na fita Masallaci sai ƙamshinsa yake zabgawa me sanyaya rai sumar nan tasa a kwance luf sai sheƙi take baƙa siɗik da ita,kai tsaye dounstais ya nufa dan a tunaninsa har lokacin Zahra bata dawo ba,tun kafin ya gama sauka ya fara jiyo hayaniya da kukan maman siyam wadda ƙaikayin doya ya fara zautar da ita,da ɗan hanzarinsa ya karasa sauka ya fita wajen da yake jiyo hayaniyar zuciyarsa na addu'ar Allah yasa ba da Zahra ba ne.

Ammi da Amira da baba talatu ne suke ta kokarin riƙe mama daga ƙoƙarin cire kayanta da take yi,sun kasa riƙe ta saboda yadda duk ta jigatasu,babu abinda take cewa sai "wayyo jiki maman siyam ya na salubewa,jiki maman siyam yayi gobara,Ammi Amira ka duba min ko fatan maman siyam yananan"?Ammi ta ce, haba mama ki tsaya mu taimaka Miki mu duba ko wani abinne ya shiga jikinki,kamar ma ruwan doya ne ko"? Ammi ta tambaya tana ɗauke ɓawon doyar da ya manne a wuyan maman,Amira ta ce, "ai kam mama ruwan doya ne kuma duk yadda a kayi aljanu ne suka zuba matasu a jiki dan babu kowa a inda take zaune"ai mama najin haka ta kuma daka wani uban tsalle sai ga zaninta akasa daga ita sai gajeren wandonta burgujeje, gaba daya ma aikatan gidan da suka fito suna kallon ikon Allah suka fashe daga wajen suna dariyar da suke ta dannewa, wasu har da zama a kasa suna rike ciki saboda abin ba ƙaramin show ya bayar ba,

Ab kuwa ganin lokacin sallah zai wuce su, sai kawai yaja Daddy suka fita Masallaci tare da sauran securitys na gidan kamar yadda suka saba,dan hankalinsa ya samu kwanciya tunda baiwa Zahra a gurin ba,dan haka ya tabbatar haukan mama ne kawai.ya motsa ko kuma itama aljanunne da ita.

Lokaci daya club ɗin ya hargitse da ihu da shewa saboda bayyanar durga da muƙarrabansa.

Siyam kuwa binsu da kallo ta yi idanunta a lumshe tana ganin bibbiyu saboda shawuwar da ta yi.

Ƙa idar durga duk zuwan da yayi sai ya yi mu amala sabuwar fuska, dan haka yana zama a wajen zamansu na musamman ya fara wurga idanunsa dan lalubo wadda zata yi daidai da maida matarsa ta kwanakin da yayi a gidan yari,caraf idanunsa ya hango masa siyam da take ta langaɓe kai alamar dai abinta tasha yana kan yi mata aiki,bash ya nunawa ita tare da bashi umarnin cewa a ɗauko masa ita a Kaita dakinsa da yake sauka a club ɗin.

Babu wani bayani ko meman amincewarta bash ya daga ta cak duk kibarta da nauyinta a haka ya kaita ɗakin ya zubar da ita saman gadon, da ƙyar ta ɗago kanta tana nuna shi da yatsa tana son tambayarsa dalilin ɗaukota da yayi amma hakan ya gagara,fita bash ya yi ya barta a dakin tana ta ƙoƙarin son taga ta mike ta bar dakin.

Daidai lokacin da Zahra ta fito, a dai_dai su AB suka dawo, kuma har lokacin mama ba ta daina kururuwa da neman ɗauki ba, dan a halin yanzu ma rigar jikinta take neman cirewa bayan ta cire ɗaurin kanta,Zahra da ta yi kamar bata san me ke faruwa a gidan ba, ta yi saurin ƙarasowa inda suke ta fama da maman tana cewa,"ammi lafiya me yasameta"?Amira ce ta sanar da ita abinda ke faruwa,rike baki Zahra ta yi!, sannan ta dubi baba talatu tana cewa,"baba takatu dan Allah samo mana itaciyar darbejiya ko bulala me kyau idan za a samu ni nasan maganin matsalar yanzu zaku ga ta dawo daidai"to baba talatu ya ce tare da saurin tafiya samo bulala,aranta dariya take tana jinjinawa salon horaswa irin na Zahra dan itama bata rana dayan biyu wannan aikin nata ne....✍🏼

To yau kuma me zaki jawo mana sannu da aiki😂😂

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol