Free chapter · Read without an account
Page49
.......yadda yayi maganar cikin wata siga da sakin mata numfashinsa a kunnenta yasa ta ƙanƙamesa tana goga fuskarta akan kirjinsa da tuni ta buɗe ƴan maɓallan saboda rigimarta,lumshe idanunsa yayi yana mai ɗora hannunsa saman dogon gashinta me santsi na asalin Fulani,cikin sanyi_sanyi shagwaba_shagwaba ta fara magana fuskarta da bakinta na gogar ƙirjinsa numfashinta na sauka akai yana saukar masa da wani irin yanayi me wuyar fassara,"me ye na maka zaka ta min shiru"?dago yayi ya sumbaci lips ɗinta sannan ya ce,"bani abincin"da sauri ta tashi daga jikinsa ba tare da ta ce, komai ba ta nufi dinning ta hado masa ko mai a tsare kamar yadda Ammi ta koyar da ita tsarinsa akan komai nasa da ta sani.
A kusa dashi ta zauna bayan ta ajiye akan karamin Centre table ɗin dake gabansa, sannan a hankali ta ɗauki plet ɗin abincin ta ɗora a kan cinyarta tare da saka spoon ta ɗebo me yawa, sannan ta yi masa alama da ya bude bakinsa,kallon yawan abincin da ta ɗebo a spoon ya yi sannan ya kalleta ya yi mata alamar ta ɗan rage yayi yawa,maƙe kafadarta ta yi tana kallon spoon ɗin da lafiyayyar jelop rice ɗin da taji kifi da kayan hadi kamar sai ƙamshi take zabgawa, sannan ta kallesa ta kuma yi masa a lamar ya bude bakin,cikin fargabar lomar da kuma yanayin yadda zai samu test ɗin abincin ya buɗe bakinsa tare da lumshe idanunsa,a hankali zahra ta zuba masa abincin tana cewa wai yaya AB me ye kake wani fargabar cin abincin"?buɗe idonsa yayi yana tauna abincin cikin nutsuwa duk da yadda ya cika masa baki,zuba masa ido ta yi har sai da ya cinye lomar bakinsa yana sakar mata wani ɗan muskilin murmushi tare da ɗaga mata babbar yatsarsa alamun jinjina.
Washe baki ta yi fararen hakoranta jerarrun masu sheƙi suka bayyana,saboda sosai taji daɗin yaba mata da da ɗan kurmanta ya yi bayan bata taba zaton hakan ba,ci gaba ta yi da bashi wani ta ɗebo kadan wani ta ɗebo me yawa,da ya rasa yadda zaiyi da ita ta rage lomar da take basa, sai kawai tana zuba masa a wannan karon ya janyo fuskarta ya haɗe bakinsu ya shiga ɗura mata abincin,zaro manyan idanunta ta yi tana ɗan turasa amma ina bai cikata ba sai da ya tabbatar ta cinye abincin da ya juye mata.harara ta shiga antaya masa kamar idanun zasu faɗo, baice mata komai ba sai ɗage girarsa da yayi tare da yi mata nuni da ta ci gaba da bashi abincin,ajiye abincin ta yi tana tura baki tare da cewa, "na fasa kaci abinka da kanka"tana shirin barin wajen ya janyota ta fada jikinsa,baiyi wata wata ba ya haɗe bakinsu silently ya shiga bata wasu zazzzafan kisess masu ruda zuciya da gangar jiki, tuni Zahra ta shiga maida martani ga dan kurmannata dan kuwa sosai take jin daɗin bakinsa jinsa take kamar zuma take tsotsa.cak ya dauketa suka nufi daki ba tare da ya cire bakinsa daga nata ba,kwantar da ita yayi a jikinsa bayan ya shimfiɗesu saman gadon da yake ta tashin ƙamshin AB na musamman, cikin nutsuwa yake zame rigar jikinta da ta yi masa shamaki,haɗuwar fatarsu waje guda shi ya haifar musu da tashin tsigar jiki tare da ƙarin wani irin feelings,wanda hakan yasa gana daya suka.haukace da rikita junansu da zazzafar romance da wata irin fitinanniyar soyayyar da take bayyana tun daga ƙarƙashin zuciyoyinsu,se suke jin kamar zasu cinye junansu ne.
A wannan haɗuwar Zahra ta fara ɗanɗana daɗin micijinta, har ta fara maida martani da wani salon da ita kanta bata san ta iya ba,kuma bata taba sanin zata iya ba, samun kanta ta kawai tayi da bawa ab ɗinta duk wani jin ɗaɗi salo da matar kwarai ke yiwa mijinta a shimfida dan samun zuciyarsa da komai nasa,bata taba yi ba kuma bata taba sanin ya ake yi ba,so ne kawai da zallar ƙauna suke sarrafa yanayinta,sune suke sata a wata turba ta ƙara mallakar ɗan kurmanta ba tare da ta san da haka ba.
A bangaren ab ɗin shima bai da ilmin komai a wannan sabgar amma sai gashi yau so na sarrafa zukatansu, ƙauna na koya musu yadda zasu sarrafa junansu ta hanyoyi mabanbanta masu tsayawa a zuciya da gangar jiki.(ashe ba koya ake yi ba ashe ba sai an iya ake yi ba,in dai akwai so da ƙauna to tabbas an gama komai domin sune zasu zama jagora a reku,ku masu yinsa makafi ne sune masu idanuwa dan haka sai inda suka kaika suka sarrafaka,fatanmu su sarrafa mu a kan kyakkyawar turba me bullewa kar su zame mana makafin da zamu yi da na sani akan fadawa cikinsu, Allah ka iya mana da iyawarka ka hada mu da masoya na gaskiya wanda bazasu yi amfani da makantar SO su cutar damu ba,amin Ya Allah).
Maman siyam dai yau taga kanwar lahira dan kuwa ba karamin azabtuwa ta yi da wannan turaren da su Zahra suka sa mata ba,tuni hancinta ya fara zubda tsinkakkiyar majina me kamar ruwa atishawa kuwa ta yi sama da ɗari, ba ita ce ta fara shaƙar numfashi me kyau ba har sai da turaren ya gama konewa.daga nan ta yi laƙwas da ita sai kuma ta shiga tunanin anya kuwa ba aljanunne suka shefeta?? ba dan ko ita tana mamakin lamarin, idan ba haka ba daga ina aka watso mata wannan ruwan me kala da tarkace har da su doya, Zahran kuma da take tunanin ita ce ta yi mata gashi ta fito babu wata alamar ita ta yi kuma ta duba wajen bata ga kowa ba ko gifcin wani bare ta ce,mutum ne ya yi mata,kai gaskiya lamarin akwai ƙamshin gaskiya, sai kawai taji tsoro ya kamata hatta da ɗakin tsoronsa ta ji tana yi, gashi zahra ta daureta bare ta fita,haka nan saboda ta sawa ranta sai taji kamar ana motsi daga banɗaki, ai take ta saki fitsarin da take ta riƙewa na azaba to yanzu kuma ya zama na tsananin tsoro, anya kuwa ba wancan matsafinne ya tura mata aljanunba?? Tabbas hakan zata iya faruwa tunda ta gaya masa maganganu masu ɗaci,take cikinta ya kuma murɗawa dan tasan sheɗancin bokannata.
"To Malama tunda munzon kinga gidan ai sai ki juya ko"? Cewar siyam bayan sun karaso gidan sun yi fakin a ƙatuwar farfajiyar ajiye motoci,fitowa femi ta yi tana jin kwadayin shiga cikin gidan,dan tunda take bata taɓa ganin gida me kyau da tsari irin wannan ba bare har ta taka cikinsa,dan haka dole ta shiga ta bawa idanunta abinci,banza ta yiwa siyam ɗin tare da ɗan fara takawa dan tabbatarwa da siyam din cewa baza ta tafi ba sai ta shiga gidan,cikin tsawa siyam ta kuma yi mata magana tare da janyo ta baya tana cewa, "Wallahi kika sake kika kuma yin wani taku dan shiga cikin gidannna sai kin raina kanki, dan haka ki fita salin alin ko na sa security su fita dake yanzu"wani banzan kallo femin ta yiwa siyam kafin ta sheƙe da dariya sannan ta ce,"ai ke yanzu baki da zarrar yimin wani abu na tijara dan kuwa ina da babban makami a hannuna"femi ta faɗa tare da haskawa siyam video dake kan wayarta bayan tayi playin dinsa.
Wata kara siyam ta saka tare da kai hannu zata kwace wayar daga hannun femi,kafin ta samu damar hakan tuni femi ta maida wayarta cikin jakarta tana cewa, idan ma kin batar da wannan ai baki san inda taguwar suke ba,ke a ganinki video daya Oga durga yake yi?to idan baki sani ba ki sani wannan ita ce babbar sana ar durga duk macen da ta yi masa musu akan bukatarsa saida video yake yi ga masu sana ar Blue film dan haka kikama kanki tun kafin kema ki shiga wannan sahun".
Tun lokacin da siyam ta yi ihu Zahra take tsaye saman barander da ta zubowa mama ruwan doya,dan lokacin da siyam din ta yi kara Zahra ta fito daga ɗakin AB ɗaure da towel zata ɗakinta ɗauko wayarta, sai kawai taji ihun siyam,hakan yasa tayi saurin faɗawa ɗakinta ta ɗauko hijab ta zura ta fita barander dan taga abinda ke faruwa.
Taɓe baki ta yi tana shirin juyawa dan bata ga abin kallo a wajen tarkacen ƙawayen siyam ba, dai-dai tana shirin juyawa kamar ance da femi ta kallo wajen sai ko karaf idanunsu suka sarke da na juna,fasa tafiya Zahra ta yi tana kallon femin da bata fi watanni biyar da daina ganinta ba dan haka bazata taba manta fuskarta ba,harara ta watsawa femin a ranta tana cewa shegu taran kwartaye, daga haka ta yi juyawarta ta koma ciki.
Ba karamin shock femi ta shiga na ganin Zahra ba,dan haka cikin sauri ta juya tana kallon siyam da tun maganar da femin ta faɗa mata akan abinda surga yake yi da video tairaicinsu su ta ƙame a wajen hatta da kawarta ta shiga shock din maganar, girgiza ta femi ta yi tana cewa ke dalla ya akayi waccan ƴar matsiyatan ta samu matsayin shigowa gidannan"?cikin rashin fahimta siyam take kallon femi,ganin bata gane ba sai kawai ta fito mata a mutum ta ambaci sunan Zahra akan cewa ita take nufi,"surukar gidannan ce me ye kika sani a kanta"?siyam bata amsa tare da yi mata tata tambayar,jan numfashi femi ta yi tare da cewa lallai haduwa ta dake alkhairi ne dan dole ne ki taimakemu akan cika burunmu na son ɗaukar fansa akan wannan tsinannniyar yarinyar, kinga dole ki bamu hadin kai ko kuma ki tsinci videonki a social media dan haka ya rage naki ceton kanki ko ceton matar yayanki" daga haka femi ta juya zata fita daga gidan dan tasan dole ne siyam ta nemesu ko taki ko taso.
Da sauri siyam ta riko hannun femi tana cewa, "karki ta fi bukatarki bata bukatar dogon nazari a wajena domin mun kasance masu farautar abu guda, wannan yarinyar da kike gani baƙin cikinta ne ya yi sanadin zuwana wajennan har oganku ya ganni ya yi abinda ya ga dama dani dan haka wannan ma yana cikin fansata",da kyau cewar femi sannan ta mikawa siyam katin inda zasu haɗu dan tattauna matsalarsu tare da nomber wayarta a jiki,daga haka ta fice daga gidan tana sakin murmushin samun mafita.
Itama siyam ɗin duban kawarta ta yi fuskarta dauke da murmushin samun mafita, dan a yanzu ta tabbatar da cewa zata yi nasara akan Zahra tunda zata hada hannu da waɗanda su kafita rashin imani da shu'umanci,jin zuciyarta take yi fes kamar an wanke ta da ruwan ƙankara, cikin kwarin gwiwar da bata fita dashi ba tana hannun kawarta suka shige main falon fuskarta kamar gonar auduga.
Zahra kuwa na shiga ɗakinta closed ɗinta ta nufa bayan ta zare hijab ɗin dake jikinta,sai da ta fito da kayan da zata saka, sannan ta zauna a bakin gado tare da ɗaukar wayarta ta shiga lalubo nomber maman iyoka wadda ta bata kwangilar sawa maman Sadik ido,bugu daya maman iyoka ta ɗaga wayar tana gaida Zahra kamar wata babba,"maman iyoka ba gaisuwa na bukata ba ai nace ku daina gaidani amma kun ƙi ji,to ya batun maman Sadik fatan dai tanayin abinda nasa ta"?maman iyoka ta ce,"zahla gaskiya kayi maganin maman Sedik kullum yanayin sedeka amma rai nasi a haɗe, ba a so raina si yake yi ba"dariya Zahra ta yi tana cewa babu damuwa a haka zata saba har sai ta daina ƙunci, dan wannan kwanakin da na bata ba wai suke nan ba dan kar nasa zuciyarta ta buga ne yasa na faɗa mata kaɗan daga cikin yawan kwanakin da zata yi min sadakar,dan hak.....ji ta yi ya zame wayar daga kunnenta tare da kashewa gaba daya yana mai kafeta da idanunsa masu haske.
Kallonsa take kamar zata cinyesa saboda yadda yayi mata kyau cikin ƙananun kayan da yasa masu kalar sararin samaniya fuskarsa sai ƙyalli take tana fidda wani annuri,dage mata gira yayi tare da sunkuyowa ya sumbaci saman idanunta,dangane kai ta yi tare da lumshe idanunsa cikin kasalar da ganinsa ke saukar mata ta ce,"yaya AB kayi kyau sosai kamar wani ɗawisu"sumbatar lips ɗinta da baya gajiya da shansu ya yi tare da mikar da ita tsaye , sannan cikin nutsuwarsa ya ce, "thanks my Hot, zahr yaushe zaki daina rigima da neman tsokana ne,ko sai na baki baby tukunna zaki daina"?tura baki ta yi sannan ta ce,ni kam yaya AB ba zan iya haifuwa ba akwai ciwo"kayan da ta dauko ya shiga saka mata yana cewa karki damu babu wahala in sha Allah zaki haihu lafiya,dan nasan yau na aje babyna a nan wajen ya fada yana shafa Mararta.
Dora hannunta ta yi saman nasa tana dan sakin karamin murmushi,dage mata gira ya yi, ya raɗa mata a hankali cikin kunneta kina so ko"?dariya ta yi tare da rufe fuskarta da tafukan hannayenta, shima ɗin murmushi ya yi mai dan sauti tare da janta gaban mirror ya shiga yi mata kwalliyar fuskarta da yake matuƙar so,idan yayi mata line baƙin kasan taga baiyi ba to a maimakon a goge sai dai su tsaya su lalace wajen shanyesa da bakin juna, hakan yasa Ab yana sane ya dinga lalata lips din, da ya lalace sai ya tsotse da bakinsa da kyar dai aka kammala kwalliyar, sannan suka fito zuwa ƙasa dan shi Ab sallah la'asar zasu tafi da daddy, duk da dai yaso makara a lalace war da sukai wajen kwalliya.
Sosai siyam ta shiga tashin hankali ganin yadda mama ta yi kaca_kaca da kashi da fitsari, ga jikinta yayi ruɗu_ruɗu saboda susar ƙaiƙayi da tasha,idanunta sun firfito hancinta na yoyon majina saboda hayaƙin turaren Mayu da tasha,suzan ce ta tayata suka kwance mama tare da gyarata suna yi suna zagin Zahra da mutanen gidan.yau siyam bata taɓa abincin gidan ba da kanta ta yi musu girki suzan ta taya ta, sannan ta kai musu daki. Sai da suka ci suka yi hani an sannan ta bawa mama labarin abinda ya faru babu abinda ta ɓoye mata, to itama maman bata damu da abinda durga yayiwa siyam din ba, dan daga ƙarshe sun fassara haɗuwar a matsayin alkhairi tunda sun samu hanyar kawo karshen Zahra.
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*