Free chapter · Read without an account
Page50
Ranar karasa yininsu su kayi cikin farinciki,dan gani suke kamar burinsu ya cika,sai dare suzan ta tafi da niyar gobe zata dawo dan suje inda zasu hade dasu femi,mama duk halin da take ciki hakan bai hanata shiga farinciki ba,dan sosai Zahra ta addabi rayuwarsu shi yasa yanzu mama ta kuma zaƙuwa akan rabuwa da Zahra alaƙaƙai acewarsu.
Washe gari da sassafe siyam ta tashi ta gama komai nata,ta zauna zaman jiran karasowar suzan,zuciyarta cike da zaƙuwa da wannan haɗuwa da take ji kamar itace zata kawo ƙarshen matsalarta.
.....yau AB hospital zaije ba Company ba, dan haka karfe bakwai na safiyar ya gama shiryawa cikin cot dinsa ash da suke ƙara masa kyau da kwarjini,har ya gama shiryawa Zahra na baccin gajiya dan fa ab ɗinnata ba na wasa ba ne sosai yake bukatar samar da baby a cikin kwanakin nan dan haka ya dage da nema,juyi ta yi cikin bacci tare da ƙara damƙe fulon da take zaton Ab ne,a hankali take buɗe idanunta saboda jin kamar ba Ab dinne a tare da ita ba, daidai yana ƙarasowa gabanta tare da sunkuyo da fuskarsa ya sumbaci lips ɗinta,lumshe idanunta tayi tana ɗan tura bakinta kaɗan idanunta akansa,shafa fuskarta zuwa lips ɗinta ya yi kafin a hankali ya buɗe baki cikin kamewarsa ya ce,"wake up my realty"a hankali ta zaro harshenta ta lashi saman lips ɗinsa da yake ta sheki kamar ya saka lipstick, sannan cikin shawagwaba da sanyin murya ta ce,shine ka shirya zaka fita ka barni da ban tashi ba sai dai naga baka nan"? Hannu yasa yana taya ta tashin da take kokarin yi,sai da ya mikar da ita tsaye sannan cikin calming ya ce, "sorry habibty"maƙale kafaɗa ta yi idanunta na kawo ruwa sannan cikin Muryar son fashewa da kuka ta ce,to waye zai min wanka"?hucin bakinsa ya furzar Sannan ba tare da ya ce komai ba,ya fara zame mata ƴar guntuwar rigar baccin dake jikinta.
Da sauri ta shige jikinsa tana cewa, "noo ya Ab"ɗage gira ya yi yana ƙoƙarin ɗagota daga jikinsa,ƙin yadda ta yi tana kuma shige masa tare da girgiza kanta a ƙirjinsa wai bata so ya ganta, murmushinsa ya yi da ba koda yaushe yake samuwa akan kyakkyawar fuskarsa ba, sannan a hankali ya yi mata raɗa wanda hakan yasa ta shiga masa kukan taɓara tana turza kafafunta aƙasa,daukarta ya yi cak ya nufi bathroom da ita yana zuwa ya sakata a jakuzin,aiko kuka ta fashe da shi tana cewa ya fitar da ita,dole ya maidata cikin bap bayan ya tara ruwa masu dumi.
Zai fara cuɗata ta yi saurin rike hannunsa tana cewa,"yaya Ab ka tafi kawai tunda ka riga ka shirya karka bata jikinka"zuba mata idanunsa da suka sauya daga farinsu ya yi,kafin a hankali ya sa hannunsa kan fatar kirjinta yana shafa mata shower jel ɗin da ya zuba a tafin hannunsa,riƙe hannun ta kuma yi saboda sauyin da ya fara kawo mata cikin jikinta, kallonta ya yi da idanunsa da suka shige ciki yana jin wani abu me karfi na bin jinin jikinsa,zare hannunsa ya yi ya yi baya,ajiyar zuciya Zahra ta saki tana wani cije lips ɗinta kamar me jin ciwo,a tunaninta ya tafi sai ganinsa ta yi ya dawo toilet din naked ɗinsa kamar yadda ya kawota.
Kafin ta samu damar yin magana ya shige cikin ruwan tare da janta jikinsa yana manne kirjinsu waje ɗaya,kankamesa Zahra ta yi tana wata irin sheshsheka kamar zata shiɗe,haɗe bakinsu waje ɗaya yayi cikin wani shauƙi da kazar kazar na son cimma abinda zuciya ke muradi,wani irin salo me tafi da zuciya ab ya shiga yiwa Zahra, babu inda baya sha baya tsotsa a jikinta,ji yake duniyarsa na wani irin juyawa a sararin samaniya kamar wanda yasha kayan maye.
Lokacin da femi ta koma gida, bata boyewa su bash komai daga labarin Zahra ba, Adebayo har da su taka rawa dan shi fa har yanzu yana maitar Zahra, babu abinda zai huce masa fushinsa a kanta sai ta hanyar dandanar zumarta da a sanadin a hakanne ya yi rayuwar gidan maza,shima dai bash kusan abinda yake kwaɗayi kenan dan haka duka sunyi tarayya akan son cimma abu guda.
Suma da wuri suka shirya karfe takwas suka bar gidansu zuwa inda suka yi zasu haɗu da siyam dan dukkansu a ɗoke suke,shi kansa Durga ya ƙagu yaga Zahra dan kuwa a ƙankanin lokaci ya fahimci inda Adebayo da bash suka nufa,dan tun a labarin fyaden da Adebayo ya bashi a kurkuku ya san cewa yarinyar za ta yi zafi dan haka take shima ya fara kwadayin zahra.
....a safiyar yau din ma dai Zahra tasha maguza wajen gwarzon mijinta Ab,da kansa ya yi mata wanka ya naɗota cikin towel kamar jaririya,sabon shiri ya yi musu tare da zahra sannan suka fito gaba daya suna ƙamshi kana ganinsu kaga couples.
Da Jafar suka fara cin karo a falon yana ta faman duba agogo, dan tun kira ɗaya da yayi bai kuma gigin yin wani kiran ba,a yanzu kam yasan dole wasu al'amuran su sauya tunda akwai Zahra,shi yasa shi dakansa Jafar ɗin yake ƙoƙarin sauya schedules nasu dan kawai ya samarwa AB ɗin lokacin samun nutsuwa da iyalansa,cikin sauri ya sunkuyar da kansa yana masa Barka da fitowa,amsawa yayi cikin kamewarsa fuskar nan a dinke sai dai kana hango zallar mutsuwa da kwanciyar hankali a cikinta,yau dai Zahra bata harari Jafar ba an gaisa cikin kwanciyar hankali (Allah yasa hankali aka fara)cikin sauri Jafar ya karbi tap da wayar Ab guda dake hannun Zahra ya fita daga falon.
Dan kallon dinning Zahra tayi tana cewa, me ya hana su fitowa yin breakfast"?bai bata amsa ba sai janyota jikinsa da yayi ya dora lips dinsa kannata ya shiga bata kyakkyawar sumba. Daidai lokacin siyam ta fito cikin wani taku na ƙasaita da faɗi,turus ta yi tana kallon yadda ab yake juya harshensa cikin bakin zahra kamar sai haɗiye,wani kakkauran miyau ta haɗiya kafin ta karaso tana yin gyaran murya wai dan su san da ita a wajen,sai dai ta yi a banza dan kuwa sai da AB ya tsotse lipstick din da ya sa mata tas sannan ya saketa,kafin cikin kamewarsa da rashin hayaniya ya ce, "ki kula"daga haka ya juya fita daga falon cikin takunsa wanda yake nuna mazantaka da kuzari a tare dashi,ko da wasa bai kalli inda soyam take ba bare tasan yasan da ita a wajen,itama Zahra bata kalleta ba ta fara takunta cikin rausaya jikinta kamar wata tarwaɗa tana taku kamar sarauniyar ɗawisu.
Wata ƙwafa siyam ta yi daidai lokacin Zahra ta shige corridor da zai kaita dakin Amira,a fusace ta fita, aranta tana cewa zaki gane kurenki ne wannan abin da kike yi duk na karshe ne sai dai kiyi sa a lahira ƴar gidan matsiyata kawai.ko kallon inda motocin AB suke ba tayi ba, ta shige Tata motar a fusace ta figeta ta bar gidan zuciyarta a cunkushe duk da tana jin cewa yaune zata kawo karshen matsalarta.
Yana shiga mota Jafar ya miko masa wayarsa da ya fitar da wani dan kyakkyawan gida me tsari wanda a ƙalla zai iya cin zaman mutum biyar ba tare da takura ba,ya ce,oga ga gidan da aka samu acikin anguwar ina ga wannan zai yi saboda akwai bangare guda da kaka zata zauna sannan a kwai wani bangaren na baki dan duk sai da na shiga na duba komai, sannan gini ne me inganci dan sai da muka yi magana da wadanda aka bawa kwangilar ginin gidan"karbar wayar Ab ya yi yana duba tsarin gidan kallon sakonni ya yiwa gidan sannan ya mikawa Jafar wayar ba tare da ya ce, komai ba.shuru tun Jafar na jiran amsa har ya sare da jin ta bakinsa sai kuma can bayan ya mula dan kansa ya ce,idan ka tabbata komai yayi zaka iya tura kudin, a sa dukkan abinda ya dace yadda babu abinda zasu bukata" in sha Allah oga za ayi komai fiye da yadda ka zata"jafar ya fada yana kiyasta irin murna da farincikin da zahra zata shiga idan aka nuna mata wannan gidan matsayin na iyayenta.
Zahra na shiga dakin Amira ta sameta duƙunƙune cikin bargo tana kwasar bacci,zama tayi a gefenta tare da ɗan bugun filon da amiran take kai,bude ido amira ta yi tana dan hararar zahra kafin cikin yanayin bacci ta ce, "haba matar yaya ya zaki dameni ina bacci bayan ke kin aje min wayarki a nan yayanki ya kira daga jin mace bai santa ba ya dameni da surutu" zaro ido Zahra ta yi tare da janyo wayarta tana cewa,kai ba dai yaya alaminne ya kirani ba"? "Ohon muku ke da shi"Amira ta faɗa tana juyawa dan ci gaba da baccinta,Zahra kuwa kai tsaye kiran yaya al'amin tasa,ringin biyu ya ɗauka yana cewa, kin san zaki yi nisa da wayar kika kirani,kuma na kira wata kanwar mijinki me daɗin murya ta dauka"dariya Zahra tasa tana kallon Amira da ke cikin bargo kafin ta ce, kai yaya al'amin ko dai kana ciki ne?? Wallahi yaya idan kana so baka zanyi dan suma haka su kayi mana basu jira cewarmu ba suka ɗaukeni suka bawa ɗansu dan haka faɗi ranar da kake son a daura auren"dariya alamun yayi cike da mamakin wawtar Zahra da bata karewa dan kana jin yanayin maganar tata zaka san cewa da gaskiyarta ta yi ta har zuciyarta,sai da ya yi me isarsa dan a koda yaushe baya gajiya da jin shirmen kanwartasa dan kuwa tana matukar sakasa cikin nishaɗi, sannan ya ce,"ok zahra karki damu yadda su kayi mana tabbas haka zamu yi musu amma dai yanzu ki fara antayo min hotonta da nomber ta kafin karshen wata nazo"tsalle Zahra ta yi tana cewa, "yeeee yaya yanzu zan tura maka yau Allah ya kawo ranar ramuwa"daga haka suka kashe wayar komi bata tsaya ba ta tura masa nomber Amira da hotonta,duk Amira najinta amma bata ce mata komai ba,duk da cewa ita tasan yaya al'amin ɗin a hoton da ya Turawa Zahra bayan ta yi waya,samun kanta ta yi da sakin murmushi har da wani rufe fuska kamar tana gaban almain din.
Nadiya Zahra ta kira suka sha hira sannan ta roketa akan su zo,idan kuma basu zo ba to zata rabu dasu ta sake wasu ƙawayen,sosai nadiya ta bawa Zahra haƙuri dan ita kanta tasan sunyi mata laifi a dai yadda suke bai kamata ace tun kai Zahran yau wajen wata hudu amma basu kara zuwa ba,duk da cewa su bangaren su tsoro suke ji kar ace kwaɗayine ya kaisu, sun manta alakarsu da Zahra saboda gudun maganar mutane.
Daga nan Hafsah ta kira, itama dai korafin da ta yiwa nadiyar shi ta yi mata,ita ma kuka hafsan hakuri ta bata akan ceqa in sha Allah zasu zo a kusarnan,daga nan suka yi sallama, haka zahra ta ci gaba da kiran yan uwanta harda yarbawan da suke mutunci da su.
Da ta kira kaka kuwa kuka ta fashe mata dashi tana cewa ta daina sonta tunda itama tunda aka kawota bata zo ta ganta ba, dama ita mama ba a maganarta dan acewarta bazata yi ta yawan zuwa gidan surukai ba,dakyar kaka ta lallasheta da cewa itama zata zo in sha Allah wai da bari ta yi idan zahran ta haihu sai ta taho gaba daya,dariya zahra ta fashe da ita tana ɗaukar maganar kaka shirme.
........siyam sai da ta jinjina ƙarfin kiyayyar su femi akan Zahra, saboda yadda ta tarar har sun riga su zuwa dan ita bayan fitarta sai da ta biya ta ɗauki suzan.zama ta yi tana ƙarewa Durga kallo a fakaice,yanzu wannan ƙazamin mutuminne ya haikemin?? Ta fada a ranta tana jin kamar ta shaƙo wuyansa ya mutu ta huta da takaici,a nan kowa ya gabatar da kansa da abinda Zahra ta yi masa, daga nan suka shiga tattauna hanyar da ya kamata su bi wajen ɗaukar fansarsu.
Hoton Zahra Durga ya buƙaci gani dan tun ɗazun dauriya kawai yake dan kar su gano meye a ransa su ki buda masa hanyar da zai kaisa ga Zahra,cikin rauwar jiki siyam ta bude wayarta tare da fiddo hoton Zahra da ta ɗauka ba tare da zahr ta sani ba,mikawa Durga wayar ta yi,shi kuma yasa hannu ya karba fuskar nan babu annurin da wani zai iya kawo masa wasa,zubawa hoton ido ya yi yana kallon Zahra duk da cewa kamar a tsorace a ka dauki hoton amma hakan bai hana bayyanuwar kyawunta da tsarin dirin jikinta ba,wani irin kakkauran miyau ya haɗiya, kafin cikin dauriya da waskewa irin ta gogaggun ƴan duniya ya dago kansa daga kallon hoton yana binsu da kallo daya bayan ɗaya,daga karshe ya dire kallonsa akan siyam tare da cewa,"sace ta zamu yi dan haka ki tura mana duk wasu bayanan da zasu bamu sa ar ƙwamusheta ba tare da wata damuwa ba"ya faɗa yana miƙa mata wayarta.
Wata zabura siyam ta yi tana cewa, "wane irin sacewa kuma"? Salan ku saceta ta samu hanyar guduwa, kun san kuwa kafirin wayon yarinyar nan sai kace wadda aljanu suke sarrafawa"??
Wani banzan kallo Durga ya watsa mata kafin ya mike yana cewa, idan ke ce zaki koya mana aikin mu to ki fita daga cikin team dinmu, amma fa ki sani mune da nasara akanki daga haka ya bar wajen yana cewa su bash, "daga yau aiki ya soma"
Dukansu binsa su kayi da kallo, kafin Adebayo ya saki wani makirin murmushi yana cewa wannan shine daidai mu saceta mu gasa mu cinye ba wanda ya ji ya gani".........✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*