Free chapter · Read without an account

Page 53

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

Ihu maman siyam ta saka lokacin da su baba talatu ke ajiyeta saman gadonta,saboda yanzu ko yaya ta yi wani motsi sai ta ji a jikinta,zama siyam ta yi a gefenta tana kiran likita dan yazo ya duba maman,ita da mama zata yadda ma wlh sechatery zata kira ya duba ƙwaƙwalwar mama dan da a alama ta fara motsi.cikin wahala mama ta buɗe baki ta fara bawa siyam labarin abinda ya faru da ita tsakaninta da aljanunta saboda ta kula da kallon mahaukaciya da siyam ke mata harma da sauran mutanen GIDAN.wani uban ashar siyam ta ɗura tare da mikewa tsaye tana yiwa mama kallon dama ke sokuwace??cikin kumfar baki ta ce,"mama dama ke ma ƙaramin tunanine dake?ashe abinda nake tunani akanki gaskiya ne?to idan ba kin samu taɓi akanki ba ya za ayi zahra tazo har inda kike ta raina miki hankali ko nace ta maida ki mahaukaciya kuma ki zauna akai?".

Zabura mama ta yi ta tashi har sai da ta runtse idonta tare da riƙe kugunta saboda wani azabar zafi da ya soketa,saboda azabar bakinciki da takaici kasa cewa komai ta yi sai hawaye, da ta tuna rawar salawaitun da ta yi a gaban jama ar gidan kuwa ai sai ta rushe da kuka,yau tsinuwar ma ta kasa yiwa Zahra dan a ganinta hukuncin zahra ya wuce ya tsaya a iya tsinuwa.

Zahra kuwa na can sun baje a main falo, tana naniƙe da kaka kamar zata koma cikinta,Ammi da suka gaisa basu guri ta yi sai Amira ce ta zauna ana hira da ita tana shan dariyar labarin da su nadiya suke bata akan Zahra cikin ƙusƙus dan kar yarbawa suji.

Su kuwa su maman daddy duk a darare suke,kallon gidan ma a fakaice suke yi suna tsoron sakin jiki Zahra ta gwada musu halinta da suka huta dashi kwana biyu,kallon lola Zahra ta yi tare da tuntsurewa da dariya tana cewa, sorry lola wallahi sai yanzu naji ina jin tausayinki akan rashin Adebayo ashe dama haka auren yake tuntuni baku gaya min ba? Shi yasa idan na sa ku aiki mazanku suna nan kuke kasa fitowa ko kuma ku fito da daurin kirji ashe Gara kuke kwasa yan jakar ub....kwaf kaka ta buge bakinta tana cewa dama Zahra har yanzu aure bai canja ki ba? wannan wace irin shegantaka ce haka?"tura baki ta yi tana cewa to kaka me nayi kawai dannece aure da daɗi?"la'ila masalli aka kaka ta faɗa tana tafa hannuwa baki sake da kunyar da Zahra bata rabo da basu ta ce, sai yanzu kika san haka? da da kike cewa baki so fa, kuma ko anyi kince sai kin dawo gida"tab ai wallahi kaka ba zan iya dawowa gida ba haka kawai na bar mayu masu idon mujiya su cinye min baki da macijin ɗan kurmana"me ye kuma maciji?"Kaka ta tambaya idanunta a waje don tunaninta macijin gaske Zahra ke nufi,kaka baki san maciji ba duk da kin haifi su Abba?" Zahra ta fada cike da gaɓunta tsakaninta da Allah,tari Amira ta fara sosai dan taga alama idan ba hakan ta yi ba da kaka da jikar zasu barar da hali a gaban jama a,ta yi sa a kuwa dan gaba daya hankalinsu ya dawo kanta,zahra da kanta ta ɗauko mata ruwa ta bata tasha tana mata sannu,su kansu su nadiya sunji dadin abinda amira ta yi dan idan ba haka ba babu wanda ya isa kwaɓar zahra a wajen da katoɓarar da take shirin yi ko ma muce take yi.

Abinci me rai da lafiya kusan kala huɗu su baba talatu suka jere a falon bayan sun shimfida babban tabarmar cin abinci,dan da farko har sun kai dinning amma sai Zahra ta ce su dawo dashi nan, saboda ƴan gidansu basu iya cin abinci akan dinning ba dan ko ita da tazo kafin ta iya sai da ta kwana biyu,ji ƙarya Amira dake kusa da ita ta faɗa,kallon Amira ta yi tana harararta kafin ta yi ƙwafa ta ce,ba zan rama yanzu ba har sai kin auri yaya al'amin", dariya kawai Amira ta yi suka ci gaba da jera plet saman table mat ɗin.suna fara cin abincin siyam ta fito ta tsaya tana musu wani kallon wulaƙanci kafin ta tsaida idonta kan kaka,dariya ta bushe da ita tana nuna kaka da yatsa kafin cikin dariyar ta ce, kai wannan mata akwai jaraba da ganin yadda kike loma kowa zai gane baki saba cin abinci ba bare akai ga irin wannan me rai da lafiya,to maza a ci banzar idan an gama a zo a ƙara gaba tunda babu gado"duk abinda take fada Zahra na jinta sai dai babu abinda ta fasa daga abinda take yi,gani ta yi kaka ta ajiye spoon dinta kafin ta yi magana ragowar ma duka sun ajiye jikinsu a sanyaye.

Wani kallo Zahra ta bisu da shi kafin ta bude baki ta ce,"me kuke nufi? Saboda ƴar karere ta yi muku magana zaku ajiye abincin da kuke da iko dashi?,to wai ma kun san wacece ita da har zata yi magana ku bar abinda kuke yi? To bari na gaya muku wacece ita,da farko dai wannan da kuke gani kwartuwace me leƙen dakin ma aurata kuma ba kowa ba ce a cikin gidan nan illa ƴar yayar daddy da ta gudo daga ƙauye ta bar mijinta saboda baya basu abinci shiyasa da suka dawo nan suka koma kamar Mayu suna cike gurbin yunwar baya, kwanannan suka gama gwaren shiga banɗaki ita da uwarta dan yin zawon da kwadayi ya jawo musu",aiko gaba daya suka sa dariya dan sosai labarin Zahra da yadda ta yi wajen bada labarin ya basu dariya, dan haka ransu fes suka ci gaba da cin abincinsu,kaka har da cewa ai da nasan nafita iko da gidan da ko kallo bata isheni ba,tunda nasan ko yau kika haihu ta wasu ta ƙare ta mu kuma ta soma" dariya suka kuma kwashewa da har da amira da wannan abu yayi mata daidai, dan fa ita sam bata kallon mama a matdayin yayar babanta sabida labarin da suka samj akan azabtarwar da ta yiwa daddy lokacin da iyayensu suka mutu aka barsu wurinta dan a lokacin baya da komai shi yasa duk abinda zata bashi sai ta yi masa gori, wata rana ma hanasa take yi gaba daya sai dai dan uwansa idan ya samo ya bashi,gashi bata samu haihuwa da wuri ba shi yasa take bala in son siyam Jamar me.

Siyam dake tsaye ta yi ba la'in mozanta ta kalli Amira tare da cewa ke kuwa wlh baki da zuciya kinzo an hadu dake ana ciwa ƴar uwarki mutunci kina dariya zan yi maganinku gaba daya,ke kuka Zahra ki sani abinda kika yiwa mama baki ci bulus ba ina nan take kanki sai kin gwammace baki zo duniyar ba"daga haka.ta juya fuuu kamar kububuwa,dariya Zahra ta yi tana kallon lola ta ce, sorry lola zansa yaya dan kurma yasa a fidda Adebayo dan kar kije ki bi maza a raba mana zunubin duk da cewa shine yaja duk abinda ya faru dashi"na gode zahla Allah ya kawo kazentar daki da wuri" cewar lola tana washe baki,ƙazanta kuma?" Zahra ta tambaya cike da rashin fahimta, jinjina kai ta yi tare da cewa "abin arzikin da nake shirin yi Miki ne har kin fara saka min da fatan ƙazanta eye lola?" Kaka ce ta yi saurin tare Zahra da cewa "a'a fa Zahra ba irin ƙazantar da kike nufi take nufi ba ,idan akace Allah ya kawo ƙazantar ɗaki to ana nufin haihuwa kenan"oh Zahra ta faɗa tana murmushi kana ta ce, "tom indai haka ne lola kisa ranki a inuwa kamar Adebayo ya dawo ya gama in sha Allah"Allah yasa suka amsa suna ci gaba da Shagalinsu.

Sai ƙarfe biyar motar da ta kawosu ta dawo ɗaukarsu, Zahra kamar ta bisu dan kuka tasawa kaka sai ta bita,rarrashi Ammi ta fara ita da kaka amma tamkar suna zuga Zahra,siyam dake jikin windownta tana kallonsu fata take da addu'a Allah yasa ammi tabar Zahra ta bisu,da suka rasa gane kan Zahra sai Ammi ta kira ab a waya ta sanar dashi abinda ke faruwa.

A lokacin AB yana tare da baƙin da suka yi masa saukar bazata dan basu iso ba sai ƙarfe huɗu, da baiyi niyar ganinsu ba,to amma duba da yanayin buƙatuwar da suke ciki yasa ya sauraresu shine har a lokacin suna tare suna mittin akan issues ɗin da ya kawosu,dafe kansa ya yi cike da damuwa gashi bai gama ba bare ya koma gidan,"kayi shiru ammi dake kan layi har lokacin ta faɗa,numfashi ya ɗan saki kana ya ce,Ammi su tafi kawai idan na gama abinda nake sai mu biya mu ɗaukota"ɗan jim Ammi ta yi kafin ta magantu da cewa,anya kuwa babana wannan hukunci naka ya yi,? duba fa kaga yamma ta yi,da dai ka canja shawara ka taho yanzu sai ka rarrasheta ko ka kirata a wayarta ka rarrasheta ko zata haƙura"ok kawai ya faɗa ya kashe wayar.

Kiran wayar Zahra ya shiga yi, Zahra dake kankame da kaka Bama tasan inda ta cilla wayar ba,Amira ce ta mika mata wayar, ba tare da ta matsa daga jikin kaka ba ta karba wayar ta sa akunnenta,a hankali kamammiyar Muryarsa me sanyin amo ta ratsa kunnenta yana kiran sunanta da salon da ya saba kiranta, sorry Zahr ki yi hakuri da kaina zan kaiki gidan kaka gobe in Allah ya kai mu, ko bakyaso ki je ki daɗe tare da ita kamar yadda su kayi? Ko yanzu baki san zan sa kawo Miki su ba idan kika yi hakuri haka zan ta yi miki bazata ina saki cikin farinciki kinji my nurr"gyada kai ta yi sannan cikin Muryarta da tasha kuka ta ce,kayi alkawari zaka fita dani goben ka Kaini?" Insha Allah oya maza share hawayen" da sauri ta shiga goge fuskar ta kamar yana kallonta tare da cewa "yaya AB yaushe zaka dawo?" Ba jimawa in sha Allah" Allah ya dawo da kai lafiya i miss You my Lollipop ɗin snake Dina,"ammi da sauri ta kuma bawa Zahra tazara tana kawar da kanta daga kusanta su kuwa su kaka dama da wannan damar suka samu suka shige mota bayan Ammi ta yi musu sha tara na arziki ita kanta Zahra ba a barta a baya ba dan kaya ta dinga basu har dasu atamfa da takalma tunda bata da kudin da zata basu,kuma da ta basu sai da ta yi musu kashedi akan dan su yiwa mazajensu kwalliya ta basu,ga kuma kudi masu yawa da Ab yasa Ammi ta basu haka suka bar gidan suna godiya zahra har da ɗaga musu hannu.

Wani wawan tsaki siyam taja tare da sakin labulen ta koma,har ranta bata so Zahra ta hakura da fitar nan ba,to amma da haka zata samu nasara tunda basa son damuwar zahran tasan zata yi nasara akan burinta.

Ab bai samu shigowa gidan ba sai wajen karfe sha daya, a lokacin har Zahra ta gaji da kumburin fushinta ta yi bacci,bai tasheta ba kai tsaye wanka ya fara ya kimtsa sannan ya dan tsakuri abinci kaɗan ya sha fruet,daga nan ya wuce dakin,ya dan jima yana kallon fuskar ta dake cike da fushi sannan ya raba jikinta ya kwanta yana janta jikinsa.

Washe gari da safe, ya dauka Zahra zata yi masa korafin rashin dawowarsa ko tayi masa darun da bata yi ba, amma sai yaji shiru dan tuni ita ta manta ta shiga sabgarta da sangartar da ta saba yi masa, wannan halin da ya fahimta na Zahra a yau ba ƙaramin daraja ya ƙara mata da so ba.(Ƴar uwa ki fahimta idan kina da yawan ƙorafi da rashin kau da kai akan lamurran mijinki to ki gyara dan mita da korafi akan abinda bai kai ya kawo ba ko abinda bai taɓa faruwa ba,yana kawo raunin so da rashin ganin daraja wajen miji be careful ƴar uwa).

Yau dai a ƙasa suka karya Wannan shine dalilin da yasa siyam tasan Zahra zata je gidan kaka,dan haka cikin sauri ta bar dinning ɗin ta koma daki ta kira su Durga ta shela musu komai,ba tare da bata lokaci ba suka shirya fita tare da Adebayo tunda shine yasan gidan kaka da gidansu, femi kuma ita ce tasan mension dinsu ab dan haka kai tsaye motarsu Durga a babban layin mention ɗin su ab suka tsaya, amma fa sunsha gargadi wajen siyam dan ta tabbatar musu suka bari gerd ko securitys ɗin layin suka kama su karsu sa sunanta a ciki,dariya durga yayi yana cewa, "wannan yarinyar bata san suwaye suke tare da durga ba kuma bata san aikin durga ba,amma idan taji labarin kwamushe matashiyar yarinya zahra zata fahimta, kuma zata daina kawo min raini da yi min kallon sakarai,kafin na tafi mataki na gaba a kanki".

Yadda suka ga tsaro a layin kawai yasa suka ɗan tsorata dan haka su kayi saurin sauya shiri.

Har kofar motar Ammi da Amira suka rakosu duk da cewa Amira taso zuwa to amma yau itama zata shiga school dan haka dole ta hakura ta bawa Zahra sakon gaisuwa gurin kaka.

Siyam bata bar jikin window ba har sai da taga fitar motocin AB sannan ta saki ajiyar zuciya tana yiwa kanta fatan nasara.......✍🏼✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol