Free chapter · Read without an account

Page54

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

.......a hankali Zahra ta kwantar da kanta a kafaɗar ab, kana cikin sakalci ta ce,"my Hot snake za ka barni na kwana ko?"idanunsa a kan tap dinsa ya ce,"no ba haka mu kayi dake ba pls idan kin kwana Ni kuma ya zanyi?"tura baki ta yi kafin ta ce,"yaya AB ba zan iya bacci a ko ina ba idan ba a nan ba"ta fada tana shafa ƙirjinsa zuwa cikinsa kana ta ture tap dinsa dake kan cinyarsa ta maye gurbinta tare cewa,"wannan gurbin Zahra ne bana kowa ba"tana mai zagaya hannunta duka biyu a tabayansa tare da kwantar da kanta a ƙirjinsa tana lumshe idanunnta,dogayen hannayensa yasa shima yayi mata kyakkyawar tarba har da guzurin sumba a goshinta,luf ta yi tana shaƙar ƙamshinsa da bata gajiya dashi a yan kwanakinnan harma da yawan feelings ɗinta akansa da ta ƙara ji daga jiya zuwa yau,a hankali take jin wata kewa na lullubeta sai take ji kamar wanda zata yi adadin wasu awoyi masu yawa bata gansa ba.

Mamaki ne ya kama AB lokacin da suka zo ya ɗagota dan su yi sallama amma sai yaga ashe har ta yi bacci,sai kace ba safiya ba,Jafar dake gaba ne ya yi gyaran murya tare da sanar dashi sun karaso gidan kaka,shiru yaji wanda dama bai sa ran tankawar ta sa ba,sai dai rashin jin motsin mutuniyar shi ya bashi amsar tambayarsa,hakan ya nunawa Jafar da josuwa kenan sai Zahra ta tashi daga bacci sannan zasu tafi,basu da ta cewa illa zaman jira.

Daga can nesa da gidan kaka kuwa wata bakar Corolla ce me baƙin glass fake a wajen dan mutane masu kaiwa da kawowa da zasu maida hankali kan motar to tabbas zasu fahimci cewa akwai abinda me motar yake jira saboda kusan mintuna talatin kenan da tsayuwar motar a wajen babu kuma wanda ya fito daga motar ko ya shiga motar,to amma dake safiya ce sai babu wanda ya maida hankali kan motar da kuma tunanin abinda motar tazo yi,abinka da anguwar kazo nazo a cakude take kowa neman na sawa a bakin salati yake yi dan haka ko da an kula da motar to ba a bata muhimmanci ba.

Su Adebayo da suke cikin motar kuwa, duk abinda ke faruwa a kan idanunsu,har zuwan da motocin AB su kayi suka tsaya masu tsaronsa suka fito amma shi da Zahra motar da suke ciki ko motsi ba ta yi ba,basu ji tsoro ba kuma basu ji a ransu cewa dalilin ƙin fitowarsu Zahra ya dangance su ba,saboda sun san sun yi kyakkyawan shirin da gano su zai yi matukar wuya,dan haka suma suka ci gaba da dakon jiran ganin fitowar Zahra.

Jafar ko sai waya ake masa saboda mutanen da suke jiransu, dan karfe tara daidai zasu shiga mittin da baƙi,gashi yanzu har tara saura kwata, sannan gogan ko a jikinsa dan da alama ma baya son ko kwakkwaran motsi wani ya yi dan kar a tashi gimbiya ƴar sarki.daga bangaren ab kuwa hasashen da Jafar ya yi tabbas haka ne dan ko shi ya kasa yin wani motsi me ƙarfi dan ya fahimci Zahra tana matukar jin daɗin baccinta.

Tara saura mintuna goma cif Zahra ta motsa tana mai ɗan buɗe idanunta kaɗan kaɗan har ta buɗe su gaba ɗaya,da sauri ta tashi zaune tana kallon AB da yake kashingiɗe idanunsa a lumshe kamar me bacci,shafa lallausar ƙasumbarsa ta yi tare da ɗan jan dogon hancinsa tana cewa, "yaya AB har yanzu bamu zo gidan kakan ba ne?"maimakon ya amsa mata sai kawai ya ɗora bakinsa a kan ɗan ƙaramin bakinta da yayi ja sai sheƙi yake yi,sai da ya tsatse bakin tas kana ya cikata taee da dage mata gira kafin cikin deep voice ɗinsa ya ce,"tun dazu muka zo bacci kika yi shi yasa bamu fita ba"kuma baka tasheni baa?" ta faɗa cikin dan mamakinsa,dage mata gira ya kuma yi ka fin ya sumbaci labbanta sannan ya buɗe mata kofar yayi mata alamar ta fita,a hankali tasa kafafunta a waje tana fita daga motar idanunta akansa har ta fita bata daina kallonsa ba,dan har ga Allah abinda ya yi mata ya taɓa ranta sosai duk sakarcinta yau aje sa ta yi tana kallon ab cikin wata irin so ƙauna damuwa kewa da bata sansu ba, kafin ta rufe kofar ta kuma kallon cikin idanunsa sannan a hankali kuma cikin nutsuwa babu wannan shagwabar da sakalcin cikin sanyi ta ce,"yaya AB idan muka koma gida zan gaya maka wani abu da nake ji akanka wata kil ko zaka fahimci menene a raina, kafin hakan yanzu ina mai fara sanar da kai cewa zan kasance cikin kewarka daga nan zuwa lokacin da zan kasamce tare da kai tunda ka zamarwa zuciyata tamkar wani mayen ƙarfe dake manne a zuciya da gangar jiki har da ruhi,sai kuma ta yi kalar shagwaba tare da marairacewa ta yi kasa da muryarat cikin wani salon da bata san ya a kayi ta yi sa ba, ta ce,yaya AB amma fa ba irin mayen ƙarfen da ka sani ba, wanda ana sa masa karfi yake rabuwa da abinda ya mannewa,Ni nawa mayen ƙarfen na musamman ne dan baya ciruwa kuma baya banbaruwa idan ya manne abu sai da su mutu tare,to kamar haka ta faɗa tana yin baya fusmarta dauke da wani kayataccen murmushi kumatunta duka biyu sun loɓa kamar ka zura yatsa,wata irin numfashi me huci ab ya furzar tare da dafe saitin zuciyarsa,ji yake kamar ya yi me saboda yadda kalaman Zahra suka ratsasa har suke neman yin tsiro, bashi da wani kuzarin motsi bare magana hakan yasa ya dinga bjnta da wani irin narkakken kallo har ta ƙule cikin gidan da baya da baya tana kuma daga masa hannu da murmushinta me kyau da ya ki barin fuskarta.

Josuwa da Jafar da suke a ƙage. su kayi saurin jan motar na bayansu suka take musu baya,gaba daya daga jafar har josuwa an tayar musu da tsumi dan gaba dayansu tunanin yin aure ne ya tafi da hankalinsu,shi ko AB ba karamin jarumta yayi wajen killace wancan yanayi nasa da Zahra ta barsa a ciki ba,ya dauko fuskarsa ta ko da yaushe ya aza, amma can cikin zuciya da gangar jiki jarumta kawai yake yi wajen danne feelings din Zahra dake neman kashesa.

Da gudu Zahra ta karasa cikin gidan tana kwallawa kaka kira,yarta kaka ta yi tana cewa ke ƴar nan ashe kuwa da gaske kawokin zai yi dan Allah wannan wace irin sangarta ce haka?"tura baki Zahra ta yi kana ta ce,to tunda bakya murna da zuwana bari na koma amma kafin na tafi ki fara Bani wannan kadan zogalen naki me dadi ba fara ci" rike baki kaka ta yi cike da mamaki ta ce,"Zahra yau kuma kece da cin kwaɗon zogale Allah mai iko?"Ni kam kaka kin daina so na ne duk kika cikani da wasu tambayoyi?Ni kawai ki min ko na taf.......sallamar da yaro ya kwaɗa a bakin ƙofar kaka ya katse Zahra daga abinda take son faɗa,duban yaron su kayi bayan ya gaida kaka da zahra ya dora da cewa, "wai ance zahra tazo inji mijinta ta yi mantuwa"duban kaka Zahra ta yi ta ce,"kinga yaya AB ya dawo sabida yaji a jikinsa kin koreni dan haka idan na fita bazan dawo ba tunda dama korata kike binsa zanyi ya Kaini gurin mama"da sauri kaka ta ce, "Allah ya baki hakuri je ki karbo sakon ki dawo zanyi miki kwaɗan zogalen har da na rama in kina so shalelen kaka" da sauri Zahra ta fita tana cewa haba kaka daga baya kenan Ni zaki yiwa wayo amma dai zan dawo na karɓa kwaɗan zogalen daga haka ta kai ƙarshen ƙofar kaka ta daina jiyo muryarta.

Zahra kuwa na fita taga mota ba irin ta ab ba dan kaf gidan babu irin wannan motar, hakan yasa ta ɗanyi slow,to amma da ta yi wani tunani sai kawai ta karasa jikin motar tana cewa "yaya AB mota ya canjo daga tafiyarsa??karasawar da zata yi taji an buɗe motar a lokaci daya aka janyota cikin motar tare da shaƙa mata wani abu da yasa ta tafi luuu kamar sumammiya,da gudu suka ja motar suka bar anguwar,bash ne ya fara ya shekewa da dariya yana cewa Finally Mr AB tazo hannu,sai suma suka ɗauka ƙyalƙyalƙyal kamar wasu sabbin kamu cikin farin ciki suka yi waya da siyam akan sunyi masara yanzu haka Zahra na tare da su.

Wata karar murna siyam ta yi tare da yin tsalle saman gadonta,tana juyi da burgima akai ranta fes, yanzu abu daya ya rage mata ta ji an kashe Zahra daga nan duk wani barinta ya gama cika ko iya haka ta tsaya bata da kaico tasan ba ta yi a banza ba tunda duka sun rasa bare ma tasan idan babu zahra dole ab ya haƙura da ita.

Waya ta kuma yi musu ta ce, su tabbatar sun kashe wayar Zahra sun cire layin idan ba haka ba za a iya yin tracking numberta a gano in da take,wani mugun tsaki Durga ya yi "yana cewa lallai yarinyar nan har yanzu tana wasa da aikin Durga nine zata koyawa aikina wai" ya karasa maganar da yin wata ƙwafa, daga nan basu tsaya a ko ina ba sai can wani kallataccen gidansa da ya saba yin irin wannan aiyukan na sato mutum ya kashe ko a yi masa jan kunne.

Ɗaki na musamman yasa femi ta kai Zahra dan a ransa ji yayi ba zai iya kuntatawa Zahra ba domin kuwa wani irin so ne da bai taba jinsa a kan kowane mutum ba yake yi mata, dan haka shi yanzu a shirye yake da yin komai dominta,duk kuma wanda ya nemi shiga tsakaninsa da ita zai iya kaisa garin da ba a dawowa.

Tun kaka na irga mintuna har dai taga abin ba na ƙare ba ne,ta ce,"kai yarinyar nan ko dai da gaske take tafiyar ta yi ne?"ta faɗa tana yafa gyalenta ta fita ƙofar gidan, rike baki ta yi cikin kakkabin shirmen Zahra ta ce,"kai amma wannan yarinya akwai shirmammiya, Ni gani ba waya ba bare na yi kiran mijinta yazo ya karɓa mata zogalen,dan tunda ta sawa ranta kulafucinsa idan ba ci ta yi ba hankalin mutane ba zai kwanta da rigima ba,ko da yake ma ina nan zai dawo karɓa mata in dai Zahra ce bari na je na tanadi kayan hadi yana zuwa sai na haɗa na bashi ya kai mata,su Zahra an kusa shiga sawun manya Allah dai yasa ta yi hankali,cewar kaka ta na kimawa cikin gidan bakinta a washe dan tashin farko ta gano meke damun mutuniyartata.

Misalin ƙarfe daya Amira ta fito daga makaranta,tana ƙoƙarin shiga motarta wayarta ta fara neman agaji, bata ɗaga ba har sai da ta shiga mota ta zauna sosai sannan ta ɗaga kiran, sallama ta yi tare da tambayar waye? duk da cewa tuni ta yi saven nomber sa amma saboda hali irin na mata yasa ta fuske ta yi kamar bata gane waye ba,daga can bangaren al'amin kuwa murmushi ya yi kana ya ce,"tunda baki gane waye ba bari na yi miki gwari_gwari yadda zaki fahimta, da farko dai Ni sunana al Amin yaya ga Zahra matar yayanki me shirin zama surukuwarki dan haka kai tsaye kina magana da me shirin ɗaukeki matsayin mata"kunya ce ta kama Amira dan haka sai kawai ta kashe wayar tana murmushi,bai rabu da ita ba,ya ci gaba da kira ita kuma bata daga ba saboda dalili biyu na farko bata san me zata ce masa ba na biyu kuma tuƙi takeyi,da taga dai yaki haƙura dole haka ta daga ta sanar dashi uzurinta, shi dinma hallau bai haƙura ba sai da ta yi masa alƙawarin idan ta koma gida ta kimtsa zata kirasa.

Ko da ta koma gida ta samu natsuwa Zahra ta fara nema, sai dai kuma wayar a kashe, sai da ta kira wajen so biyar ana tabbatar mata da cewa gaba daya layin ma baya lan waya, hakan yasa ta haƙura ta kira al'amin, amma fa haka nan take ji kamar ba lafiya ba,sai dai kyautata zaton lafiya yasa ta ɗan nutsuwa.

A bangaren Ammi ma tun wajen sha biyu take kiran Zahra dan taji lafiyarta itama dai a kashe wayar,tuna shiririta irin ta Zahra yasa Ammi ta yi tunanin me bi ma ta bar wayar a nan gida saboda ɗaukin fitar da zata yi,itama wannan tunaninne ya sama mata nutsuwa.

Ƙarfe goma suka fito daga mittin, yana shiga office bayan ruwa da yasha kai tsaye ita ya fara laluba a waya dan gaba daya mittin ɗinnan bai yisa a nutse ba dan ta riga ta birkita yar ragowar nutsuwarsa, gaba daya hankalinsa yana kanta kalamanta na ɗazu har yanzu su suke masa amsa kuwa a cikin kansa, duk ya runtse idanuwa jajayen lips ɗinta da take masa magana dasu suna motsawa a hankali ne suke masa gizo.

Shima a kashe ya samu wayar kuma shi ya tabbatar da cewa da wayarta ta fito,anan kusan tunaninsu daya da Ammi,amma duk da haka shi hankalinsa bai kwanta ba, lokaci_lokaci yakan kuma kira amma dai still abu ɗaya ake sanar dashi,gashi kaka bata da waya sai yau yaji takaicin da bai haɗawa kaka waya ba gaba daya ya manta sai yanzu da buƙatar hakan tazo ya tuna.karfe daya yaji ba zai iya jurewa ba, dan haka fitowa yayi da niyar tafiya gidan kaka ya duba da kansa amma sai su jafar suka yi saurin tararsa sunso ya barsu su je amma ko sauraronsu baiyi yana ganin har yanzu babu wanda yasan ƙololuwar inda Zahra ta kai a ransa bare sanin muhimmancinta.....

A firgice ta Zahra ta farka tana mai bin ɗakin da take da kallo dan dai ita a iya saninta bata taba sanin kalar dakin ba,da dai ta ji ta garau ai sai ta mike da hanzari ta nufi kofa,jin kofar a rufe ya tabbatar mata da cewa rufeta aka yi,komawa ta yi da baya sannan ta taho da gudu ta daki kofar wai ko zata bude amma babu alamar hakan,dan haka sai ta koma buga kofar da karfi tana cewa,"waye anan? da wani a nanne?waye ya kawo Ni nan? kuzo ku buɗe Ni".

Sosai yadda Zahra ke bugun kofar yana hankalinsu har da muryarta tunda ba wai nesa suke da dakin ba,Durga ne ya mike tare da nufar dakin,yana zuwa ya bude kofar.

Wani banzan kallo da na rashin sani Zahra ta fara wurga masa, kafin ta watso masa tambaya da cewa, "kai waye, kuma me yasa ka kawoni nan?"shiga dakin durga yayi tare da maida kofar ya rufe, sannan cikin son tausasa muryarsa ya ce, "Masoyine kuma soyayyace sanadin kawo ki nan gun" dariya Zahra ta saka kafin ta nunasa da yatsa tana cewa kai ɗan wahala kasan kuwa wacece Zahra kafin ka yi tunanin sato Ni?"

Kafin ya bata amsa sai ga Adebayo da su bash sun turo kofar sun shigo suna dariyar cinnasarar da suke ganin sunyi.

Zahra na ganinsu ta sa dariya tare da cewa au kace tare kuke da ƙungiyar kwartaye na dudduniya?? Adebayo ashe ka fito daga kurkukun? Har ina cewa zansa mijina ya fiddaka saboda lola ashe kai tuni ka haɗu da ƴan uwanka kwartaye,ya kamata ace Adebayo ya baku shawarar karku sato Zahra dan Zahra tafi ƙarfin sata wallahi idan baku sake Ni na tafi ba sai kun gwammace zamanku a gidan yari na shekara biyu" daga haka ta ja baya ta zauna a kan katifar dake dakin tana kallonsu ɗai dai kamar wasu fadawanta.

Gaba daya kallon kallo suka shiga yi saboda yanayin Zahra ba karamin mamaki ya basu ba,yarinya kamar iblishiya, duba fa ko ajikinta babu alamar damuwa a tare da ita,kafin su dawo daga duniyar mamaki sun tsinkayi wata muguwar ƙara me karfi da amo cikin kunnuwansu, wadda tasa suka fara rige_rigen yin takansu sai ga shi suna haɗa goshi suna gwaren neman hanya kamar wasu makafi....✍🏼

Team Zahra ina muku ya jiki fa🤣

Team siyam mu yi shagalin nasarar farko💃💃

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol