Free chapter · Read without an account
Page 55
Sai da suka fita gaba dayansu sannan suka fahimci daga ina ƙarar take fitowa,femi ce ta dakawa Zahra dake ta harba ƙafafu a ƙasa tsawa tare da cewa, "wannan wane irin shashashanci ne haka? wallahi idan baki rufe mana baki ba shegen duka zamu yi Miki dan Ni banga amfanin aje ki tsawon wannan awannin nan ba ba tare da kin fara gane kurenki ba",ihu Zahra ta kuma sawa kafin femi ta Ankara tuni zahra taja kafunta sai gata tim a kasa kan mazaunanta da ba wani tsoka garesu ba,hakan yasa wani mugun zafi ya shigeta dan kuwa ji tayi kamar ta zauna akan kashi ne,Zahra da ta yi aika aikan bata damu ba sai jifa da ta fara yi da duk abinda ta gani a dakin tana uhun a kawo mata kwaɗan zogale yunwa take ji,su bash ne su kayo kanta da miyar kai mata duka,durga ya yi saurin taresu ta hanyar sa hannunsa a hanyar kafin ya dubi wani yaronsa me suna tiger ya ce,"tiger maza kaje ka samo mana kwaɗan zogale a duk inda yake na baka awa daya"zaro idanu bash ya yi cike da mamakin durga kana ya ce,"oga bai kamata mu biyewa wannan shegiyar yarinyar ba dan ba kasan halinta ba ne abinda ya kamata muyi shine mu yi gaggawar kasheta tun kafin ta tona mana asiri da wannan ƙararta ta me kama da ta gyare".
Alamu yayi musu da su fita Dukansu, ba tare da ya ce komai ba,femi kuwa bata iya tashi ba sai bash ne ya dauke ta yana mita, yayin da take kallon Zahra kamar zata cinyeta idanunta sun kaɗa jajur saboda azabar raɗaɗin da mazaunanta ke yi mata,da gwalo Zahra ta bita tana ƙyalƙyala dariya ta samu abinda take so.
Suna fita ta fashe da kuka dan sosai ta fara azabtuwa da rashin ab ɗinta,tunaninta daya shine, idan kuma basu maidata gida ba ya za tayi kenan? Ya ab zai kasance da su ammi da mama kai da ma duk wani masoyinta?da wannan tunanin da take wani baccin ya kuma daukarta.
Kaka najin sallamar Jafar ta dauko kular da ta haɗawa Zahra zogale tana cewa, "ɗan halak ai nasan dole wannan rigamatun ta dawo da kai,haka nan ma Zahra ta yi rigima bare kuma da dalili ai yanzu kowa sai yayi hakuri"daidai tana fitowa kofar gidan, Ab na jingine jikin motar ya zubawa ƙofar gidan kaka ido dan yana da tabbacin cewa Zahra ce zata fito tunda ta ji muryar jafar,sai dai ga mamakinsa kaka ce ta fito tana faman washe baki ta ce,"jikana sai fa haƙuri dama na san bazata iya haƙuri da zogalennan ba shi yasa tun kafin ta dawo da kai na hada ina jiran zuwanka,ungo nan rike Allah ya raba lafiya oh Zahra da ciki to Allah dai yasa ta yi hankali kar ana fama yara na shirme uwa na yi"shifa Ab gaba ɗaya kansa ya ɗaure,dan haka kallon kaka kawai yake yana daukar zancenta ɗaya bayan ɗaya yana fassara shi a kansa,idan ya fahinta daidai kaka na nufin zahra tana da ciki ke nan?abinda bai gama fahimta ba dai shin ina zaran take?ina ta je da za a kai mata zogale?to ko dai gidansu ta tafi?,
Da yaga sai sa kansa cikin ruɗani yake sai kawai ya daure cikin kamewarsa ya fara gaida kaka da take ta zuba kamar an sata,amsawa ta yi bakinnan kamar gonar auduga tana kuma yi masa Barka da samun karuwa,shafa ƙeyarsa ya yi kafin cikin nutsuwa ya yiwa kaka tambayar da take ta cin ransa,ya ce, AM kaka ina ita Zahr ɗin take?dan ina ta kiran wayarta a kashe shi yasa na biyo naga ko lafiya??.
A'a me zanji kuma haka? wannan wane irin batu ne? Ko kaima ka.fara shirme irin na matar taka ne?Jafar ne ya matso kusa da kaka ya kuma yi mata karin bayani akan bayanin da ab ya yi mata, dan haka kai tsaye ta fahimci cewa dai Zahra bata tare da ab,cikin fara ruɗewa kaka ta ce,to idan bakwa tare da Zahra waye ya dawo ya ɗauke ta a mota bayan shigowarta bai fi da mintuna goma ba?sosai AB ya jingina da motar saboda jin kamar zai faɗi amma dai duk da haka bai karaya ba cikin karfin hali ya sanar da kaka shi tunda suka ajiye zahra ta shigo gidanta akan idonsa bai kuma dawowa ba sai yanzu,salati kaka tasa tana sanar dasu yadda abin ya kasance.
Da sauri Jafar ya zo ya budewa ab mota yana cewa, "muje can gida ina ga zamu sameta a can" shiga motar kawai ab ya yi amma ba wai dan yana gane wani abu ba,da sauri kaka ma ta rufe gida tana cewa, "a'a ku tsaya ni muje ai nima banga ta zama ba Allah dai ya takaita mana wahala yasa ta je can gidan nasu",kiran Ammi ne ya shigowa Ab ko ring bai fara yi ba ya ɗaga da zaton zata ce masa zahra na gidan,"babana kuna tare da doughter ne? tun wajen sha ɗaya nake kiran wayarta a kashe sai nayi zaton ko ta barta a nan amma hankalina ya kasa kwanciya tunda amira ma ta ce ta kira wayar a kashe shi yasa na kira ka ko kasan abinda ya samu wayarta?" numfashi me zafi Ab ya sauke kafin cikin wata irin murya da ammi bata taba jinta daga garesa ba ya ce,"Ammi d same ina kan hanyar zuwa can gida"cikin tashin hankali Ammi ta ce,"ban gane ba dama ba gidan kaka ka kaita ba?"kasa magana yayi dan haka sai kawai ya miƙawa jafar waya yana sauke wata irin numfashi tare da kwantar da kansa jikin kujerar motar.
Jafar ne ya yiwa Ammi bayanin komai cikin nutsuwa da son ta kwantar da hankalinta,amma ina lokaci daya yaji ruɗewa da tashin hankalin bayyane cikin muryarta, innalillahi kawai take ambata a haka ya kashe wayar yana fatan Allah ya taƙaita musu wannan tashin hankali da yake shirin tunkarosu.
Lokacin da Ammi ke yin wayar siyam da mama na zaune a falon suna cin abinci dan su kadai ne suka iya cin abinci a gidan,Amira ma da kyar yaya al'amin yasata ta ci kaɗan dan ya kwantar mata da hankali sosai, ya ce,bai kamata daga jin wayar Zahra a kashe su ɗaga hankalinsu ba tunda sun san halin kayarsu wata ƙila ma ta bar wayar gida da wannan ya samu amiran ta ci abinci, to kuma sai ga wannan tashin hankalin da ya karasa birkita su, annan ɗin ma dai alamin ne ya kuma basu kwarin gwiwa da cewa in sha Allah tana can gida babu abinda zai sameta.
Suna gama waya da Amira ya kira mama yana tambayarta cikin dabara,to shima anan hankalinsa ya fara tashi tunda a maganar mama ya fahimci cewa ko sanin Zahra ta je gidan kaka a yau din bata yi ba,kuma itama tun dazu take neman wayar Zahra dan ta gaya mata abin alkhairin da ab ya yi musu amma bata sameta ba,da kyar al'amin ya haɗiye tashin hankalinsa ya biyewa mama shima yana yiwa AB addu'a akan abinda ya yi ɗin, wanda shine yake da burin yin amma sai gashi ya rigasa samun ladan,cikin dabara ya zame ba tare da ya bar mama ta fahimci halin da ake ciki ba, dai-dai lokacin ne kuma kaka ta shigo bakinta dauke da sallama maman daddy ce dake wanki ta amsa tana washe baki da yiwa kaka sannu da zuwa,kaka bata samu damar amsawa ba ta tare ta da tambaya ke maman daddy zahra tazo gidannan yau?" Girgiza kai maman daddy ta yi ta ɗora da cewa,yo gaba daya ina gida da Zahla yazo zan seni,kaka shifa zahla de yazo waje a ke ganewa dan haka da yazo tun daga waje zaki ga alama koda shagon maman Sedik ne".
Kuka kaka tasa tana salati, da sauri mama ta fito tana tambayar kaka ko lafiya?, babu wani kwana_kwana kaka ta wassafawa mama duk abinda yake faruwa tun daga farko har karshe,jikin mama ne ya dauki rawa ba tare da ta ce komai ba ta zube a kasa dabar,maman daddy kuwa zani ta yafa akanta tana cewa,ina maman daddy yaga zama zahla ya bace,
Maman zahla ka kontar de hankali naka zahla ze kasance cikin salama zahla yana da masoya yana da kilkili babu abinda ze samesa,yanzu zamu fita nemansa in sha Allah"fita maman daddy ta yi ,ita ta sanar da su ab abinda ke faruwa a cikin gidan akan Zahra dai bata zo ba rabansu da ita tun jiya a gidanta,daga nan ta yi gaba tana shelantawa mutane.
Runtse idanunsa da suka yi jawur ya yi jijiyar kansa kuwa tuni ta fito tayi ruɗu ruɗu,wayar daddy ce ta shigo masa, bai iya dagawa ba Jafar ne ya daga,anan jafar ya tabbatarwa da daddy ba a ga Zahra ba,cikin tashin hankali daddy ya kashe wayar ya dannawa commissioner of police waya.
Gaba daya anguwar su Zahra ta ɗauka gidan kawayenta nadiya da Hafsah duk bata gidan dama ita Zahra idan kaga bata nan to bata wuce wadannan gidajen biyu in dai har ta ɗanyi nisa da gidansu kenan,duk inda aka je nemanta to tare da masu gidan zasu fito nemanta,gaba daya ƴan gidansu kowa ya bazama har inda aka san bata zuwa yau sai da aka je nemanta,lokaci ɗaya anguwar ta cika maƙil yara sai kuka suke yi suna kiran auty ZAHRA.
Da kyar kaka da Abba suka lallaɓa ab da ko magana baya iya buɗa baki ya yi sai kallo da ido,akan ya tafi in sha Allah za a ganta zamansa anan ba abinda zai ƙara sai tashin hankali da zai kara masa,josuwa da Jafar kuwa su kadai suka san halin ogansu shi yasa suka fi kowa tausaya masa,dan Jafar har kwalla sai da yayi masa dan yadda yake hango wutar azabar tashin hankali a cikin jijiyoyin kansa da idanunsa abin ba a magana,kai tsaye gida suka nufa dashi dan da alama ab sai abin da hali ya yi dan a halin yanzu ko sarrafa gabobinsa baya iya yi.
Suna zuwa gida Ammi ta rungumesa ita da Amira suna kuka,da kyar ya iya buɗa baki ya ce, "Ammi ki min addu'a Allah ya raya Ni tare da ZAHRA" daga haka ya wucesu a wajen cikin rashin sanin abinyi.
Daddy kuwa har lokacin yana tare da commissioner, ana kan bincike dan tuni ƴan sanda su kayiwa anguwarsu kaka ƙawanya tako ina babu shiga babu fita,bincike kawai ake babu ji babu gani.
Al Amin kuwa tuni ya yi shirin tahowa tunda dama akan gaɓar tahowar yake,sai dai bashi kaɗai ba saboda Mami zainab da ya Habib duk sunce zasu taho,dan haka gaba ɗaya suka rankayo, bayan sun sanar da ƴan uwa an fara addu'a ta ko ina akan Allah ya bayyana Zahra cikin aminci.
"Kai siyam baka da hankali ne? Ko ka san idan bamu nuna damuwar mu ba zamu iya shiga cikin zargi tunda an saka ƴan sanda cikin lamarin?,duk da cewa dai babu hannun mamanka a ciki"cewar mama kenan bayan sun shiga ɗakin siyam ɗin,harara siyam din ta watsawa mama kana ta ce, mama wai kina tunanin zan bari asirina ya tonu ne da har kike saurin tsame kanki daga sabgar? Dariya ta yi ba tare da ta ce komai ba ta shiga danna waya bayan ta tabbatar da cewa babu kowa a ta ko inan ɗakinta,ana ɗagawa kai tsaye ta fara magana a hankali tana cewa,"kai bash ya kamata kuyiwa wannan sakaran ogannaku bore dan banga alamar yana da niyar kasheta ba,idan ba zai kasheta ba ku ku saceta ku aikata tunda dama bashi ta yiwa abinda ta yi muku ba kune zaku dau fansa bashi ba"ta can ɓangaren bash da yake tare da oga durga, ya kuma sashi ya saka wayar a amsa kuwa ya kuma bashi umarnin da ya bata amsa, dan haka cikin bin umarni bash ya ce,"ey ai abinda muke shirin yi kenan gara mu kasheta tun kafin asiri ya tonu" kai dalla malam ni bana tunanin asirina zai tonu nafi tunanin makomata idan zahra ta kuɓuta dan haka ku yi abinda nake buƙata kawai"daga haka ƙit ta kashe wayar tana zagin durga da tsine masa.
Wani irin mugun murmushi oga Durga yayi tare da ambatar sunan siyam har wajen sau uku, daga karshe ya yi wata shegiyar dariya,lokaci daya kuma ya haɗe fuska tare da kallon bash ya nunasa da yatsa tare da cije baƙaƙen laɓɓansa yana cewa duk wanda bai fasa yi min bore ba baya buƙatar ci gaba da rayuwa dan haka bismilla",
Ko da Zahra ta farka da kwaɗan zogale tayi arba a gefanta, duk da cewa ranta babu dadi haka ga dauka ta dinga ci kamar ba gobe sai da ta cinye sa tas tasha ruwan dake wajen, sannan ta fara neman bathroom,cikin sa a ta samu ta shiga ta daura alwala tazo ta tada sallah,tana idarwa ana kiran magriba dan haka ta ɗora, addu'a take ta yi akan Allah ya bawa mijinta da iyayenta da surukanta da duk wani masoyinta haƙurin rashinta na lokacin da zata ɗauka a wajennan,wata budurwa ce bazata wuce femi ba ta kawo mata abinci, ko kallon abincin bata yi ba dan sam bai bata sha a wa ba,haka ta kwanta cike da kewar ab ɗinta,kuka tasa tana cewa, "Allah ya isana da yanzu ina jikin yaya dan kurmana in Allah ya yadda hakkinmu ba zai barku ba, a haka bacci ya kuma dauketa wanda sam bata gajiya da yinsa duk halin da take ciki kuwa a yau din.
Misalin karfe biyu na dare, Adebayo ya zare jikinsa daga makwancinsa ya fito cikin sanɗa,zuciyarsa babu abinda take hasko masa sai Zahra, tun da ya fahimci abinda oga Durga yake nufi da Zahra shi kuma ya ci alwashin ba zai barshi ya rigasa cika burinsa na kusan shekaru akan Zahra ba,dan haka ya gama shirin sa tsaf dan cimma mummunan manufarsa,dan duk sai da ya saka musu maganin bacci a cikin lemon da ya siyo musu yasan har ya gama Shagalinsa babu me zarrar farkawa,kai tsaye dakin da aka ajiye Zahra ya nufa tare da saka key din ya bude dakin.
Sai da ya lashe laɓɓansa har wani murmushin farinciki yake fiddawa na sanin cewa yau zai maida kwadayinsa.
Zahra da tun shigowarsa ta farka, tana kallonsa ya maida kofar ya rufe ya nufo ta,ko ɗar ba ta yi ba,tunda dama tasan abinda yake wa, dan haka a shirye take da ta yi maganin ɗan iska,a ranta ta ce, ƙaraso tsinannan kwarto yau macijinka ya gama yawo lola sai kiyi hakuri dan Adebayonki yau ya taro yakin ƙarshen duniya.........✍🏼
Zahra zata bamu samfur din yadda ake hukunta kwartaye😂😂
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*