Free chapter · Read without an account

Page58

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

.......da ƙyar Ammi ta ɓanɓare Zahra daga jikin ab dan ta hana kowa ya taba shi,tunda suke basu taba ganin kukan tashin hankali na gaske ba na sakalci ba a gurin Zahra,rungumeta ammi ta yi tana shafa bayanta cikin damuwar da ta yi mata dabaibayi tun batan Zahra.

Mama kuwa ƴarta tazo ta kama suka shige daki dan tasan a wannan halin da ake ciki babu wanda zai kula ya ce,likita ya duba mata siyam ɗin,cikin kuka siyam din take cewa,mama na shiga uku ya a kayi Zahra ta kuɓuta ba ance sun kama da wuta sun kone ba? mama masifa ta dawo tsugunne ba ta ƙare ba, wallahi zahra sai na ga bayanki ko kuma muyi mutuwar kasko,bazan taba yarda da faɗuwa ba,Kum......da sauri mama ta toshe bakinta tana cewa "kai baka da hankali sai an jika asiri naka ya tonu? Kai me yasa baka da hankali da tunani memakon kayi tunanin halin da zaka siga idan zahla ya gane da hannunka? Ni fa ina tunanin Zahla ya ganeka Gara ka gudu tun kafin ya tonaka",girgiza kai siyam ta yi kafin ta ce,"haba mama Ni zan gujewa Zahra ai babu inda zani domin nasan ba tayadda za ayi ta san cewa dani a cikin wannan sabgar tunda ba gaya mata zasu yi ba,dan haka ki barni kawai ni da ita shege ka fasa"dariya mama ta yi tare da cewa aiko kaine segen dan na sani kaine zaka fasa zahla ba zai fasa ba"wani kallo siyam ta yiwa mama kafin ta yi ƙwafa kawai ta fita daga ɗakin ta koma nata goshinta na zubda jini.

Acan falon kuwa Ammi janye Zahra ta yi dakyar da lallaɓa suka koma ɗakinta,domin idan tana wajen ba zata bari a duba AB ɗin cikin nutsuwa ba.

Ajiyar zuciya Dr sonie ya sauke bayan dawowarsa daga kan Ab,sai da ya tsane fuskarsa da hanky sannan ya dubi Jafar da daddy ya ce,"in sha Allah ba sai munje hospital ba zai farfaɗo nan da wasu mintuna zuwa one hour, shock ne ya shiga bayan jin wata magana da ta firgitasa ainun amma anyi sa a nazo da wuri dan da ya kai awa daya a haka sai dai muyi haƙuri dashi,amma yanzu na shawo kan matsalar zai farka, amma duk da haka sai anbi wasu hanyoyi dan samun ɗorewar lafiyarsa,dan haka a daure a bar wani abu da yake so kuma zai faranta masa zuciya idan ya gansa a kusa dashi wannan matakin ne kawai zai taimaka mana wajen kare zuciyarsa daga barazanar bugawa da take yi,"in sha Allah Dr" cewar daddy da Jafar, daga nan Dr sonie ya fita tare da Jafar shi kuma daddy ya zauna kusa da ab yana kallon fuskarsa da ta fada kamar wanda ya yi jinyar shekaru.

Lokaci ɗaya masu aikin gidan suka shiga farin ciki da sanin dawowar Zahra sai gashi walwalar kowa na dawowa Sai kuma jiran farfadowar oga wanda shima suke masa kyakkyawan fata da sa rai.

Bacci ne ya kwashe Zahra,bayan Ammi ta lallabata tayi wanka,ko kaya bata sa ba daga ita sai towel din da ta daura ta yi kwanciyarta tunda ita baccinta na yanzu ba shirya masa take ba yake zuwa.

Sai a lokacin ammi ta dan samu nutsuwa ta kira Amira ta sanar da ita cewa anga Zahra gata yanzu ma bacci take,wani ihu Amira tasa tana ambatan alhamdulillah wanda hakan ya jawo hankalinsu mama kanta,cikin farin ciki ta rungume mama tana cewa "alhamdulillah mama Zahra ta dawo gida anga Zahra yanzu haka tana dakin Ammi tana bacci"sujudur shukur mama da Abba su kayi a tare suna mai mika godiyar su wajen Ubangiji Mai amsa addu'ar bayinsa dan sun san wannan nasarar tana daga maida komai garesa da suka yi,sai ga bakin kowa na washewa kowa fuskarsa ta cika da walwala,take Amira ta ce,abinda ya fi dacewa kawai su wuce gidan gaba daya, haka kuwa a kayi gaba ɗaya suka rankaya zuwa mension Abrahab.

Ragowar mutanen anguwa da yan gidan su Zahra kuwa cewa su kayi zuwa gobe ko jibi sai su je su yi jaje da barka,sun san zuwa lokacin Zahra ta huta ta samu kanta yadda ya kamata.

Daddy ne yasa Jafar ya buɗe ƙofar baya ta falon bakinsa saboda ab Yana main falon ba damar jama a su shiga tunda har lokacin bai farfaɗo ba,Ammi kuma ta bawa baba talatu umarnin da su kai abinci falon bakin dan tasan duk wanda zasu zo ɗin basu samu nutuswar cin abinci ba, yanzu ne kowa zai sa wani abu a cikinsa cikin kwanciyar hankali.

A bangaren me nafef kuwa tuni an sakesa saboda bincike ya tabbatar da cewa bashi da sa hannu a sace Zahra kuma bai san komai game da hakan ba,dan haka suka sallamesa ya yi tafiyarsa.

Ta ɓangaren Durga kuwa abinda ya damu su femi bashi ya damesa ba,dan shi ta Zahra yake tashin hankalinsa na rasata ne ba na tunanin asirinsu zai iya tonuwa ba ne kamar yadda su femi suke cikin wannan tararrabin. bash kuwa har yanzu bai san inda kansa yake ba saboda mummunan harbin kunamar da yake dawainiya dashi,tunda suka kira likitansu ya dubasa babu wnada ya kuma bi takansa kowa damuwarsa daban da ta dan uwansa,femi bayan tsoron kar asirinsu ya tonu har da na tunanin maƙudan kuɗaɗen da ta yi asara dan har ta fara hangowa kanta sabuwar rayuwa a sabuwar duniya.

Kamar wadda aka mintsina haka ta farka daga baccin saboda mafarkin ab da tayi, dama baccin na dole ne da bata iya sarrafa kanta idan ya so ɗibarta amma da bazata taɓa bari ya ɗauketa ba, saboda ɗan kurmanta na cikin halin tsakiyar rayuwa da mutuwa, a hankali ta sauko daga saman gadon ammi ta miƙe tsaye tana kallon ɗakin kamar zata ga ab din a cikinsa, idanunta ne suka sauka kan hijab ɗin Ammi akan gadon,cikin rashin ƙarfin jiki da na zuciya ta ɗauki hijab din ta saka kana ta fito daga ɗakin.

A hankali take takawa kamar wadda kwai ya fashewa a ciki,idanunta ta zuba masa zuciyarta na wani irin bugawa da ƙarfi kamar zata huda kirjinta ta fito saboda yadda ta gansa a kwance saman doguwar kujerar falon me fadi me kama da katifa kamar gawa, cikin rawar da kafafunta suka fara yi ta ƙarasa kusa dashi tare da kwanciya a jikinsa tana taɓa ƙirjinsa dan son ta tabbatar da rayuwarsa ko akasin haka,jin numfashinsa na fita tare da bugun zuciyarsa yasa ta saki wata ajiyar zuciya me ƙarfi tare da shigewa jikinsa tana mai haɗe fuskarta da tasa hancinsu da bakinsu na gugar juna ta ce,"my Hot man Please wake up zahrs she's back to U, u are not going anywhere I promise my Hot snake" ta faɗa tana ƙarasa dora bakinta kan nasa tana cewa "i miss my sugar lips daga haka ta fara tsotsar harshensa a hankali tana kallon fuskarsa da ta yi wani fayau sai haske da dogon hanci.

Kamar mafarki yake jin komai dan haka sai yayi luf domin baya son wannan kyakkyawan moment din ya shigesa,jin yadda zuciyarsa da gangar jikinsa ke karɓar saƙon Zahra sai hakan yasa shi buɗe idanunsa a hankali wanda kana gani kasan cewa yana tsoron gushewar yanayinne, da sauri ta janye bakinta daga nasa fuskarta cike da farinciki ta ce,"yaya AB dan Allah kar ka sake komawa wallahi waccan muguwar ƙarya take yi ban mutu ba saboda nice na sa musu wutar dan na samu na gudo, yaya ab nayi kewarka sosai"ta faɗa tana kuma rungumesa hawaye na zubowa daga idanunta,dakyar ya ɗaga hannunsa da yayi masa nauyi ya ɗora akanta yana ɗan yamutsa sumarta da take ta ƙamshin mayukan wanke kai da turarukan gashi wai dan duk ya tabbatar da cewa ita ce ba mafarki yake ba.

"Zahrr kece da gaske ba mafarkin da nake ta yi tun jiya ba ne yau ma na sake yi?"dariyarta me kyau wacce ke cike da KURUCIYA da sakalci ta yi sannan ta ce,yaya Ab ɗauke Ni mu tafi sama kar kwartayen GIDAN nan su leƙo su ganan min macijina da suke son kwace min saboda ina son ganin lafiyarsa daga nan kaima sai ka samu amsarka"

Dafe kirji siyam dake laɓe jikin labulen corridor da ya raba su da falon ta yi tana cewa, "ji tsinannniyar yarinya ko ta ganni ne?" Cikin sanɗa ta juya ta koma ɗakinta tana kukan da tasan cewa babu ranar daina sa sai ranar da ta ga Zahra bata duniya.

Cikin wani irin zafin namansa da ya dawo a lokaci ɗaya ya miƙe tare da ɗaukar ta cak ya nufi sama da ita ba tare da jin jiri ko kasala ba,sakala hannunta ta wuyansa ta yi tana kallon fuskarsa tare da cewa,"yaya AB kana cin abinci kuwa? Fuskarka du ta faɗa kayi haske"girgiza mata kai kawai yayi dai-dai suna shiga tsakiyar falon, ƙoƙarin sauka ta fara yi,sauketa ya yi yana kallon inda take nufa, keching ta nufa tana cewa "yaya AB yunwa nake ji kaima kuma nasan kana jinta" wayarsa ce ta yi haske alamar kira, ɗagawa yayi saboda ganin Ammi ce,sai da ta fara furta alhamdulillah sannan ta ɗora da cewa ga abinci nan nasa Amira ta kawo muku daga haka ta kashe wayar tana sakin murmushin jin dadi, dan lokacin da suke hayewa saman ita kuma tana shigowa falon dan duba Ab din da zahra da tarar bata dakinta.

Yana sauke wayar daga kunnensa ya bi Zahra keching din, dai-dai tana kokarin ɗauko tukunya ya tare ta ta hanyar janyo hannunta kafin cikin muryarsa da ta yi kasa sosai ya ce,ki bari ga Ammi ta aiko abinci dan naga kin zama acici kwana biyu,biyosa ta yi tana cewa yaya AB Allah cikina yanzu baya koshi duk abinda naci da nayi mintuna ake kwashewa ko dai asibiti zamu je?" Kafin ya bata amsa sun hada ido da Amira da har ta gama jere abincin a kan Centre table ɗin falon,sakin ab ta yi suka rungume juna da Amira cikin farinciki,kafin Zahra ta fara zaro surutun shirmenta tuni Amira ta bar falon tana cewa sis idan kin huta zamu haɗe akwai labari me daɗi" daga haka ta bar falon ta bar zahra da tura baki ita ala dole ta ji haushi,kamota ya yi jikinsa yana sunsunar wuyanta da gashinta da suke fitar da wani sihirtaccen ƙamshi, yayin da hannunsa guda yake ƙoƙarin cusa shi cikin towel ɗinta wanda garin haka towel ɗin ya kunce gaba daya ya yi kasa dan dama tuni ta cire hijab din dake jikinta a keching.

Kallon siyam mama ta yi cikin jin haushin rashin daukar shawarar da bata yi,ta ce "wallahi siyama Ni na gaya maka yaronnan lubu_lubu ya yi maka ya sani cewa da kai ne aka sacesi,amma ya yi suru saboda akwai abinda yake siryawa irin nasa na mugunta kafin ya tona maka asili amma ka ki yarda, nace ka haɗa kayanka ka bar gari ka ƙi ji, to babu ruwan mamanka du abinda ya faru kar kase da mamanka asiki"cikin tsawa siyam ta dakatar da mama da cewa,"mama ki rabu dani na gaya maki bazan gujewa zahra ba sai dai koni kashi a gidan nan zuciya na ba zai dauka ba i can't see d girl in dis world"jinjina kai kawai mama ta yi tare da bar mata ɗakin tana mamakin tosewar kai irin na siyam da har yanzu ya kasa gane waye zahla.

Cikin murmushi Ammi ta zauna tana cewa,"ai yanzu dukansu sun farka mu da ganinsu kuma sai dai gobe in Allah ya kaimu"dariya yaya Habib ya yi yana cewa "to Ammi ai kin san dama haka zata faru idan suka ga junansu,ni naga ma azarɓaɓin zuwan mu wallahi amma dai tunda duk suna lafiya ai shikenan",gaba daya falon aka sa dariya sabida sigar da ya habib ya yi wajen yin maganar, nadiya kuwa duk a takure take saboda kallon da yaya habib yake binta dashi, shi dama yaya al'amin da amira tuni suka bar falon wanda dama tun jiya kowa ya fahimci abinda suke nufi to sai kuma ga Habib shima ya fara nuna tasa alamar akan nadiya.

Da sauri ta sunkuya zata dauki towel ɗinta amma sai ya rigata ya daukesa tare da jefa kan kujerar dake nesa dasu,shigewa jikinsa ta yi cikin gunguni da tura baki ta ce,"yaya AB yunwa fa nake ji"a hankali ya yi mata raɗa cikin kunneta yana hura mata iskar bakinsa ya ce,"a haka nake son ganin my Hot zahr muje kici abinci acici"bata sakesa ba a haka a tafi da ita suka zauna tana maƙale dashi duk dan kar ya kalle mata jiki.

Sosai Zahra ta ci abincin dan sai da ya tabbatar ta koshi sannan shima ya samu ya ci ya dan cike gurbin yunwar da ya diba, daga nan ya ɗora da madara me sanyi da zuma, Zahra kuwa ta bakinsa ya shiga ɗura mata tana sha tana ƙyalƙyala dariya saboda waiwayin da yake mata a kan ƙirjinta da ta gaji da kudundunewa ta bar masa kayansa,a haka ya kwasheta zuwa bedroom ɗinsa yana ci gaba da shayar da ita madarar dake bakinsa.

A hankali ya kwantar da ita saman bed din, kana ya bi bayanta ya kwanta saman jikinta yana kallon naked jikinta da yake ɗaukar hankalinsa matuka, domin wani irin ƙyalli da santsi fatarta ke yi kamar wanda aka yi mata wanka da ruwan kwai, madarar dake hannunsa ya shiga zubawa a jikinta yana bin gurin da harshensa da ya ɗau sanyin madarar yana lashewa,yana zuwa saman wuyanta ya burkitota tare da tsiyaya madarar a wuyanta zuwa kan dukiyar fulaninta tare da sa bakinsa akai,Zahra kuwa jin yadda Ab ya saka harshensa akan ƙirjinta yana mata wani irin lasa da waiwayi da harshensa yasa ta sakin wani irin numfashi me huci wanda ya kuma susuta ƙwaƙwalwar ab, Muryarta ita ta kuma neman zautar dashi saboda yadda Muryar ta fita da wani rin sautin dake ɗauke da shauƙi da kuma kalaman da ta yi amfani dasu wajen yin maganar."wayyo yaya AB Kar ka bar rayuwataaaaaa.........✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol