Free chapter · Read without an account

Page60

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

da sauri Durga ya kashe wayar saboda hankalinsa da tunaninsa da ya dawo jikinsa.sai dai kuma tuni ya makara dan ƴan sanda dare da rana bibiyar layin Zahra suke dan gano inda wayar take,dan haka a wannan karon sunyi nasarar gano inda su Durga suke,ba tare da wani jinkiri ba suka cika mota suka wuce inda turaker ta nuna musu.

Zahra kuwa tana hawa sama ɗaki ta wuce ta ɓoye cinnakunta, tana fitowa ab yaja hannunta suka shige wani ɗan ɗaki da duk karanbanin zahra bata taba sanin dashi ba, text ya fara yi mata da wasu yan gwaje_gwaje wanda take suka tabbatar masa da abinda yake tunanin.juyowa ya yi tare da ɗaga Zahra sama yana juyi da ita har suka fito falon,zama ya yi tare da ita ajikinsa, kafin cikin nutsuwarsa da kamewa ya sumbaci goshinta da lips dinta sannan a hankali ya ce, "thanks my Hot Allah ya Miki albarka ya baki lafiya"zaro idonta ta yi tare da cewa yaya AB wani abu ne a cikin ko?Ai dama nasani shike nan na bani mutuwar dai zanyi da gaske"ta ƙarasa maganar cikin fashewa da kuka.shafa bayanta ya shiga yi yana cewa."no zahr ba mutuwa ba ce ƙaruwa muka samu, cikin haihuwa ne dake ko bakya so?"ciki kuma?" Ta tambayesa tana ɗora hannunta akan cikinta, cikin mamaki ta kuma cewa yaya AB ciki dai irin wanda ake haifar baby?"giɗa mata kai yayi yana kallon fuskarta dan karantarta.yanzu kana so kace min nima haihuwa zanyi a dinga ce min maman baby?"giɗa mata kai ya kuma yi, ji ya yi kawai ta rungumesa tana sumbatarsa kamar zata haɗiyesa,dama ya san a rina dan zahra akwai fasifar son yara, anan dai suka shashance suna nunawa junansu kauna da farincikin da suke ciki.

Ƴansanda sun samu nasarar cafke su Durga,femi dai basu samu damar kamata ba amma ba wai hakan yana nufin ta tsira ba ne,durga kuwa ko ajikinsa dan ya yi alkawarin ba zai taba bari a kama siyam ba har sai ya lalata rayuwarta kamar yadda ta lalata tasa ta hanyar shigo da zahra cikin rayuwarsa, dama shi Adebayo tasa ta kare ba tashi yake ba tunda a halin yanzu baya tunanin yana raye ma.

Su Abba kuwa tuni suka yiwa sabon gidansu tsinke dan dama rashin Zahra ne ya hanasu tarewa,kowa sai sambarka yake da gida yana ji dama shine,bakin kaka kuwa kamar gonar auduga za a ƙarasa tsufa da rayuwar jin daɗi,su Mami zainab ma basu Shirya tafiya ba dan sai an sa ranar su nadiya da Amira zasu tafi dan tuni soyayya ta yaki karfi a cikin kwana ɗaya ,dan dukkansu babu wanda ya tsaya ƙauren baki wajen bayyana abinda ke cikin ransa.

Wajen ƙarfe huɗu Zahra ta sauko fes da ita kana kallonta kaga me yaron ciki dan watanni huɗu,Ammi da Amira ta samu a falon suna tattaunawa akan batun turowar da al'amin zai yi,zama ta yi kusa da ammi tare da jingina kanta a kafadarta tana cewa "my Ammi me ake shirya mana ne?"shafa kanta ammi ta yi tare da cewa bikin ƙanwarki da yayanki mana kin san gulma tuni ta fito fili anyi ta walkiya mun gane fuskar kowa"wani dan tsalle Zahra ta yi kafin ta dire ta ji an tarota,ƙamshinsa da ta ji ya tabbatar mata da cewa sarkinta ne,kallonta Ab ya yi cikin nutsuwarsa kana ya ce," ki dinga bi a hankali yanzu ba da ba ne dolw sai kin rage wannan tsale_tsallennaki"daga haka ya juya ya gaida ammi cikin kulawa sannan ya fice daga falon dan dama masallaci zai tafi ya samu zahra na masa ganganci da kyautar da Allah ya yi masa.zahra kuwa zama ta yi tare da yin gum kamar wata saliha dan kuwa a karon farko dai yau taji kunyar Ammi,dariya Amira ta yi tana kallon Zahra da take wani dan kauda kai ita a la dole kunya taji,dariya amira ta kuma sawa tare da cewa lallai Ammi ɗiyarki fa ta kusa zama mom har an fara jin kunya"dakuwa Ammi ta yiwa amira sabida yadda zahra ta wani turo baki zata fara halinnata.

Wani irin kulawa ammi da Amira suka shiga yi da Zahra hatta da daddy ba a barsa a baya ba duk mintuna sai ya bugo waya yaji lafiyarta,dan ammi ba ta iya bari ya dawo ba ta kirasa ta sanar dashi abin farin cikin da ya samesu.

Ita ko Zahra gaba daya hankalinta yana kan dakin siyam so take kawai ta samu dama ta je ta aiwatar da kudurinta,ana cikin hakan al'amin yazo wajen Amira sai ya zamana daga ita sai Ammi a falon.

Cikin kulawa ammi ta dubi Zahra ta ce, doughter ko kina bukatar wani abu ne?"dan kariyar da kai Zahra ta yi kafin ta ce,ammi dan wake nakesonci kuma irin baki ba na baba talatu ba"miƙawa Ammi ta yi tare da cewa "shikenan bari na je na saka Miki bani mintuna talatin kinji".

Tana ganin ƙulewar ammi ta yi saurin mikewa ta shige corridor da zai kaita dakinsu siyam,a hankali ta shiga leka dakin siyam din ta kafar key,a sa a irin ta Zahra kuwa sai ta hango siyam daure da towel ta dauko kayan da zata saka ta ajiye akan gado daga bisani kuma ta shige bathroom wanda ya nuna alamar cewa wanka zata yi,hamdala Zahra ta yi sannan ta lallaɓa ta buɗe ƙofar ta shiga, cikin sauri ta ɗaga kayan da siyam zata saka ta juye cinnakunnan har a jikin siket da fant sai ta ta saka ta yadda bazasu zubeba har siyama ta gama sawa,mayar da kayan ta yi ta linkesu yadda ta gansu babu wanda zai ce an buɗesu ma,fita ta yi daga dakin ta koma falo tana fatan jin kururuwar siyam.

Cikin gaggawa siyam ta fito daga wanka saboda saurin da take yi zata fita,kuma fitar da zata yi ba alheri ba ce,saboda kawarta suzance ta samo musu wani mashahurin boka zasu je wajensa akan Zahra shi yasa take ta gaggawa,acewarta Gara ta yi komai cikin sauri dan kar fatan da mama take mata ya tabbata dan taga alamar mamantata tuni ta karaya da kalar takurawar Zahra, ba tare da tunanin komai ba ta dauki kayan ta saka, lokaci daya ta yi tsaf da ita, gaban mirror ta matsa zata gyara fyskarta sai kuma ta tsaya cak saboda wani azabar radadi da ta ji a kan breast dinta sosa wajen ta shiga yi.

Zahra kuwa tana can ta fara cin danwakenta kumnenta da idamunta kuwa gaba daya suna kan hanyar dakin siyam.

Siyam kuwa nacan azaba na cinta dan duk inda ta taɓa ajikinta cizonta ake yi gashi ta rasa abinda yake mata wannan cizon na mugunta, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara zarewa tun tana daurewa har ta fara fidda kayan jikinta tana ihun neman taimako.

Zahra na jin ihun siyam ta yi saurin ajiye spoon din hannunta tana cewa,"Ammi ga siyam can itama yau jinnunta sun tashi"cikin damuwa Amma ta mike tana cewa Ni kam na rasa a inda su ka jajibo wannan abu haka daga ita har uwarta ko kuma da abinsu suka zo oh?".

"A'a ammi kar ki shiga kin san muatanen nan ba kirki garesu ba suna iya shigewa jikin wanda baiji ba bai gani ba,dawo ki zauna a kwai sauran turaren da na yiwa mama ai kinga itama mama bata kuma yi ba tun ranar ko?"jinjina kai ammi ta yi tare da komawa ta zauna, ita ko Zahra cikin sauri ta bar falon ta je keching ta dauko turaren tare da kaskon gawayi dan dama tuni ta tanadi abinta mama na zaune ta zo ta wuceta,tana shiga ta tarar da siyam tunbur tana faman soshe_soshe har a gabanta ihu kawai take tana dukan kanta kamar sabon kamu,Zahra bata kulata ba ta ajiye kaskon tare da zuba turaren me uban yawa wanda tasan cewa ko kashewa siyam din ta yi zai jima kafin ya bar dakin,tana zubawa kuwa ya fara tashi gaba daya dakin ya turniƙe,cikin sauri ta koma da baya ta rufe siyam din ta waje, yayin da siyam ta fara wani irin numfashi tare da wani irin tari ko ganin gabanta bata iya yi saboda halin da ya turniƙe dakin shi yasa har ta kasa isa inda kaskon yake, zagin Zahra yake son yi amma bala in yajin da ya toshe hancinta da maƙogaranta yasa ta kasa ko magana sai uban tarin da take yi har da su amai.

A ɓangaren su Durga kuwa suna zuwa station din ya faki idanun ƴan sandan ya fice da wani irin gudu, irin gudun da manyan ƙwarin da suka saba da guduwa daga hannun yansanda ne kawai su ka iya sa,duk yadda suka so kamashi abin ya ci tura dan tuni ya tsere musu, gashi tuni sun karɓe wayar Zahra dake hannunsa babu wata dama ta ƙara bibiyarsa amma dai basu karaya ba dan sun sha alwashin sai sun sake nemosa.

Sai da ya tabbatar da cewa ya tsere musu, tserewa me yawa, sannan ya samu mafaka ya ciro wayarsa da duk ƙwaƙwar ƴansandan nan basu ganta a jikinsa ba,kunnata ya yi kai tsaye ya shiga neman siyam da ta zama ita ce target dinsa na ƙarshe, dan ya rantse ko da zai bari a kamasa tabbas sai ya gama da rayuwar siyam.

A daidai lokacin siyam na fama da kanta dan kuwa idan ka kalleta a wannan lokacin idan baka san me ta ke shukawa ba tabbas zata baka tausayi,Zahra kuwa ƙememe ta hana kowa zuwa inda take hatta da mamanta ƙin zuwa ɗakin ta yi, dan acewarta duk abinda ya faru da siyam ita ta jawa kanta tunda tun farko sai da ta bata shawara amma ta ki ji.

Tana ji wayarta na ƙara amma babu halin ɗagawa dan gaba ɗaya bata hayyacinta,sai da ta ɗauki kusan awa ɗaya a cikin wannan halin kafin ta fara dawowa hayyacinta, da ƙyar ta samu ta janyo wayarta da take ta jin karar shigowar saƙo tun kiran da aka yi bata ɗaga ba,gabanta ne ya faɗi saboda saƙon Durga da ta ci karo dashi,yana mai shaida mata cewa ta yi gaggawar fitowa ta samesa a address ɗin da ya tura mata a ƙasan saƙon idan ba haka ba kuwa zai tona mata asiri wajen yansanda, kuma idan ta sake ta gudu nan ma bata tsira ba dan yana dauke da wannan videon nata dan haka tazo a daren ta samesa,wani irin tsuma jikin siyam ya shiga yi gashi har yanzu bata dawo daidai daga cizon cinnaku ba, dan ƙasanta ji take kamar ya tashi daga aiki saboda a nan cinnakun suka fi cizonta fiye da ko ina,ashe basu mutuba ta amma ta samu waje ta shanya baki?ta yiwa kanta tambayar da babu me amsa mata. wasu kayan ta ɗebo ta saka, sannan ta fita tana faman bubbuɗe ƙafa dan ba zata iya yin tafiya irin ta kowa ba a wannan lokacin.

Tana fitowa Zahra dake falon ita kadai tana jiran sakamakon abinda ta yiwa siyam ɗin ya fito,ta tuntsure da dariya tana nunata da yatsa! kafin cikin dariya ta ce,"ke kuma lafiyarki ƙalau kike tafiyar yan kaciya da warin tusa?"ko kallonta siyam ba ta yi ba dan a yanzu bata da abin ce mata dan itama yanzu ta fara tsoron shegantakar zahra kamar yadda mama tuni ta kiyaya.

Barin falon Zahra ta yi tana ci gaba da dariyar tafiyar siyam,karo su kaci da ab ɗinta zai fita sallah magriba,take ta kanne dariyarta tana kallonsa cikin nuna rashin gaskiya,shima kallonnata yake dan tuni ya fahimci akwai abinda take aikatawa tunda yaga bata biyosa ba tun dawowarsa daga sallah la asar, bai ce mata komai ba ya rabata ya wuce sai da ya fara taka step din kana cikin deep voice dinsa ba tare da ya juyoba ya ce,"karki sake ki dawo kasannan"tuttura baki ta yi tana shugewa ranta fes tunda ta gama gabatar da aikin ta.

Lokacin da ab ya fito ya hango siyam na wata tafiya kamar ta yan shayi, kallo daya ya yi mata ya dauke kansa tare da shigewa masallaci a ransa yake ayyana cewa duk yadda aka yi wannan aikin Zahra ne,dan shi har ya riga ya canfa duk sanda yaga wani abu daga siyam ko mamanta to tabbas Zahra ce ta cika musu aikin yarinta, Allah ka shirya min Hot zahr ya fada can ƙasan ransa.

Siyam kuwa sai a lokacin ta samu ta fito daga babban gate ɗin mention din ta tare me nafef tare da bashi adireshin inda zai kaita, sannan ta shiga tana tsinewa Zahra da ab da Durga wanda bata san kiran me yake mata ba..........✍🏼

Kuyi hakuri da typing error banyi editing ba saboda jikin ba daɗi

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol