Free chapter · Read without an account

Page 62

by Fatima Yushau adam · YAR GIDAN YARBAWA

"Yaya AB yanzu har ya kai ace kana rokon Allah kar ya baka me irin halina,Ni din me nayi? kawai dan ina saka ka magana bayan ma taimakonka nake saboda bakinka kar ya yi tsami"ɗafe kansa ya yi shi bai san ma ta ina zai fara tare rikicin ZAHRA ba,to ta ina ma ta ji addu'ar da yake ban da neman rigima?"kama hannunta ya yi ya zaunar da ita kana cikin lallashi ya ce, ban yi addu'a akan abinda kike tunani ba kawai nayi addu'a ne akan Allah ya saukeki lafiya"

Tura baki ta yi kana ta ce,to amma dai ai kana fada a ranka kana cewa Allah ya tsayar maka iya kaina idan ya kuma baka me irin halina ciwon kai zamu dinga saka ka,kuma ka rantse baka fada ba?" Ta tambayesa tana tsattsaresa da ido kamar me tuhumarsa ya aikata wani babban laifin. ɗage girarsa ya yi yana dan saki mata wani guntun murmushi kafin cikin deep voice ɗinsa ya ce,"Hot Zahra yanzu wannan fitinar taki ba dole na roƙi Allah ya sassauta min akan litle Princess ba me ye laifina a nan?" Kwaf_kwaf ta yi da idanunta kafin ta buɗe baki zata fasa kukan tabararta, da sauri ya tareta da wani irin salo ya haɗe bakinsu waje ɗaya wanda babu shiri ta haɗiye kukanta tare da miyansa da ya juye mata shi a bakin daga nan na bar musu dakin dan naga alamar cewa Zahra fa ta fetsare lamarinta sai du ai akan Allah ya bar ƙauna.

Komai ya lafa, rayuwa na ci gaba da garawa a hankali tare da kalubale da kuma nasarori,daga cikin nasarar da suka samu ,anyi auren Amira da alamin Habib da nadiya,Jafar da Hafsah, wanda shi da kansa ya sanarwa da Zahra ta samo masa shima a cikin ƙawayenta, hakan yasa Zahra bata yi ƙasa a gwiwa ba ta hadashi da Hafsah cikin ikon Allah suka hada kansu dan haka yanzu gaba daya aka hadasu aka sha biki.

A lokacin cikin Zahra ya shiga watan haihuwa jiran haihuwar kawai ake, yayin da ta wani bangaren babu abinda Zahra ta fasa ko ya ragu daga halinta sai abu daya shine yanzu babu wanda take wa mugunta tunda babu me takura mata ko me shiga sabgarta bare ta yi masa hukunci da kalar hukuncinta.

A bangaren gidan yarbawa kuwa yanzu basu da wata matsala domin Zahra ta yi musu tarbiya ta ko wace fuska karuwa suke da koyarwar Zahra,idan ka shiga gidansu yanzu ba zaka ce su ne ba saboda tsaf zaka samesa, gashi ko wacce an bata jari an bawa mijinta jari wasu kuma an basu aiki a Company,kaf unguwar yarbawa babu wanda bai samu albarkacin Zahra ba,maman Sadik kuwa da Zahra ta ce ta dinga lissafa kudin alewar sadaukar da yake zata dinga biyanta duk wata cewa ta yi, sam bata yadda ba dan ita ma yanzu tana ganin falalar sadakar tuni ta saba kuma cikin dadin rai take yinta,ko a nan ma Zahra na da kamasho sai dai fatan Allah ya bamu kadan alkhairi.

Dole Zahra ta koma da taimakonta ta wani bangaren tare da tallafar mijinta sarkinta da kuma surukanta abin alfaharinta,dan tuni ab ya mallaka mata wani cmp audugarsa da ke legos,wanda yaya Habib yake jagorantarsa, shi kuma yaya al'amin yana asibitin ab din wanda yake matsayin derecter,tare da mota da gida duk a matsayin tukyicin so da mutunci data kawo masa rayuwarsa.

Wata ranar juma a Zahra ta tashi da naƙudar da bata san ita ce ba,sai kuka da ta dinga yiwa Ammi wai cikinta na ciwo daga karshe dai ammi ta fahimci cewa nakuda ce Zahra ke yi, dan haka ta kwasheta suka tafi a sibintin kasancewar yau pri ab yana asibitin.

Tare da Ab a kayi nakudar duk da cewarsa likita bai iya yin komai ba saboda Sarauniya na ciwon na kuda,cizo da duka da ya kwashi kuwa yashasa har da su wutabalbal,a haka cikin ikon Allah Zahra ta sankato babynta me kama da babanta ko nace me kama da Ammi sak,Masha Allah abinda likitonvin suka dinga gada ke nan.

Ab kuwa sujud shukur ya yi ga Ubangiji, ga kuma Zahra lafiya kalau kamar ba haihuwa ta yi ba duk da cewa ansha gumurzu.

Ammi dakin gefenta tasaka Zahra tana kulawa da ita ga kuma kaka itama a gefe ga baba talatu ga mami zainab da tazo take zuwa kuma kullum wajen Zahra yar gata.

Ranar suna baby ta ci sunan umma rumana,suna kiranta baby nur,an sha shagali ranar anci an sha anyi hani an,mutane sun sha kyauta daga uban baby da kakan baby har da kakar baby Ammi,Zahra ta yi kyau tamkar wata zinariya, lafiya alhamdulillah an tashi daga taro cikin farin ciki sai fatan Allah ya raya baby nur.

Da dare kaka na tare da Zahra ana ta faman danbarwar bada nono kamar yadda aka saba tun haifar nur, kullum Zahra sai da kuka zata bata nono acewarta cizonta take yi.cikin nutsuwa da kamewa ya yi sallama kana ya shigo idanunsa akan baby nur da mamanta da take ta zubda hawaye fuskar a cakude da fushin shagwaba,gaida kaka ya yi kana ya zauna a gefanta,cikin kakadi kaka ta tashi ta fita tana cewa wata kila kai taga mutuncinka ta bawa diyartaka nono"jawota jikinsa ya yi yana cewa "ya akayi Ummu nur ya da hawaye haka kin girma fa yanzu wasu abubuwan sai dai mu barwa nur ko?"tura baki gaba ta yi kana ta ce,yaya AB cizona fa take kullum idan zan bata nono tsakani da Allah kai haka kake min idan zaka sha?"giɗa kai ya yi yana shafa kan baby nur kana ya ce, sorry Ummu nur ai ki mata uzuri ita yarinya ce,da lallashi da kulawa yasa Zahra ta bawa Nur nono ba tare da ta zare kafin ta koshi ba,sai ga yarinya na gyatsa alamun da suka nuna tunnzuwanta duniya bata sha nononta ta koshi ba.

A haka rayuwa ta ci gaba da garawa har Zahra ta yi arba in, a lokacinne kuma su mama da Abba suka tafi umrar da ab ya biya musu da alkawarin zuwa Hajj idan lokaci ya yi,kaka har da su kuka wai ita ce zata je garin ma aiki duk a dalilin jika, to dama haka Allah ke ikonsa ko Allah baiyi zaka samu arziki ta silar danka ba sai kaga idan kana da rabo ka samu har a jikin tattaba kunne,shi sanadi bashi da kadan kuma bashi da yawa, Allah ka bamu arzikin duniya da na lahira me amfani wanda al umma zata amfana ba wanda zamu ci mu ka dai ba.

Daddy da ammi sun nemi shawarar an da su koma gidansa su ci gaba da zama tunda yanzu ko mai ya daidaita dan haka yau suna idar da zallar nafilar da suka saba yi duk da dare da karatun Alqur'ani,ya yi kokarin sanar da ita bayan sun koma gadonsu sun kwanta.

Lokacin da Zahra ta gama saurarensa girgiza kanta ta yi! kana ta ce "a'a my Hot ba yanzu ba idan muka gama tara yaran muka samarwa Ammi masu sa ta magana sai mu tare, amma Ni yanzu gaskiya ba zan iya tafiya na bar ammi ba saboda daga Ni har ita ba zamu ji dadin zaman kadaici ba,dan duk macen da suruka irin Ammi to bana jin zata iya rabuwa da ita dan haka ka rabu dani tukunna ba yanzu ba"zai yi magana ta hanasa ta hanyar rungumesa tana cewa yanzu lokacin Hot zahr n ba lokacin surutu ba, kaima babyn Hot Zahra na ga alama yanzu ka fara gogewa a harkar magana"dan mintsili ya kai mata a gefen cikinta yana murmushi amma bai iya tanka mata ba,daga nan suka lula duniyar maji dadi da kullum basa gajiya da junansu,.

Zahra tana matukar samun kulawa wajen iyayen mijinta da kanwarsa, shi yasa kullum tsaf ab ke jinta dan bata barin ta samu wata tawaya da mijinta zai ji a tare da ita,Zahra duk sakalcinta ta yadda ta kashe ko nawa ne domin gyaran jikinta ta kowane ɓangare kuwa, ƙamshi a jikin zahra kuwa sai ka ɗauka cewa da shi a ka halicceta,hatta da baby nur kamshi ya zauna a jikinta.

Lola ma ta samu wani bazarin BEYERABE ta aura sun ci gaba da zamansu lafiya.

Ta ko wane bangare Allah ya sake budewa wannan zuri'a wanda kuma ba ko maine yaja hakan ba sai dimbin alkhairin su da temako wanda basa gajiyawa da yi a kullum ta Allah,(ku temaki iyayenku da na.kasa daku kuma Allah zai taimake ku,dukiyarsu zata habaka guzurinku na lahira zai nunku,ku sani cewa shi me bayarwa bai taba rasawa ba, Allah ya bamu mu bayar dan alfarmar shugaba Annabi Muhammad swa.

Bayan shekara uku....

Yau Zahra da kanta take tuki daga ita sai baby Nur ,sun dawo daga gidan ancle Habib,saboda zuwa hutun karshen shekara da sukayi, madiya da Amira da hafsa duka sun haihu amira namiji hafsa ma namiji ne sai nadiya da ta samu mace."la ammu kinga wani abu yana tafiya"Nur ta faɗa tana leke daga cikin motar,daidai lokacin Zahra ta yi hon a bakin mention dinnasu,sai da suka fito Nur ta kwace hannunta ta fita da gudu tana cewa sai na gano wanu abu me tafiya a waje"

Da gudu Zahra ta bita tana cewa "Nur karki fita Abbas ku tare min ita" Zahra take faɗawa securitys din gate din,amma ina kafin su yi wani yunkuri tuni yar ficiciyar yarinyar da ko tafiyarta bata gama kwari ba ta arce har da yi musu gwalo tana kada musu dan jikinta irin yadda uwarta take wa mutane idan ta yi nasara akansu,daidai lokacin Zahra ta ƙarasa sai fita itama ta yi tana kallon abinda Nur din ta biyu.

Na shiga uku Nur kadangare kika biyo dama, innalillahi shike nan Nur bake ba yin hakori idan hakoranki ya zube baza su taba fitowa ba saboda yaga hakoranki" take Nur ta tsaya tare da yin ƙwalƙwal da idanunta zata yi kuka ,kamo hannunta Zahra ta yi wanda ita tuni har ta fara hawaye.a haka suka shiga main falon Ammi inda suka samu Ammi da Ab wanda saukowarsa daga sama kenan cikin shigarsa ta jalkabiya marun me cizawa ya yi wani bulbul da shi masha Allah,

Da sauri Ammi ta taro baby Nur da take kuka shabe_shabe tana kallon Zahra ma da take share ƙananun hawaye kamar dai yadda Nur din take yi,ab kuwa zuba mata ido ya yi yana mika mata sakon rarrashi da tambaya ta ido,a kusa dashi ta zauna tare da kwantar da kanta a kafaɗarsa kana ta fara magana cikin kara karfin kukanta ta ce,yaya AB kaga Nur dinka daga dawowarmu ta fita waje wajen kadangare, gashi nan yanzu yaga hakoranta shike nan idan ta yi famfara ba zasu fito ba, tunda dama ance duk wanda kadangare yaga hakoransa to hakorin ba zai fito ba"ikon Allah wannan aikewa kuka daga ke har Nur ɗin" cewar ammi tana ji kamar ta fashe da dariya amma dai tana ta dannewa saboda ta san halin yan kayanta,ab kuwa kamata ya yi suka haura sama ba tare da ya ce komai ba,ammi kuma ya barta da rarrashin jikarta.

Lallashi ya yiwa Zahra me kyau da inganci wanda sai daga ƙarshe ya yi mata bayanin cewa abinda take tunani ba haka ba ne,sai a sannan ya samu lafiya akan mitar da take masa.

Zahra dai da lama ta haifawa an me irin halinta sai dai fatan Allah ya tsayar akanta😄

Lokacin haj na zuwa suka rankaya gaba ɗaya ahalin suka tsallake ƙasa mai tsarki,daga can kuma sarki da sarauniyarsa ta musamman suka wuce yawon buɗe ido ana sake baje SOYAYYA,daga nan ta kuma kunso wani cikin ,sai da ya yi wata biyar sannan suka dawo Najeriya...

Adebayo siyam,femi mama bash da sauran yaran da aka kama suna gidan yari suna girmar abinda suka shuka,dama Siyam da Ade tuni sun nakasa rayuwa su ke yi akwai ya babu,to dama wanda ya manta da Allah ai dole Allah ya barsa tunda su ko salla ba sa yi bare aiyukansu su dinga gyaruwa,to Allah ya rabamu da bin sharrin zuciya Allah ka bamu ikon aikata me kyau ka shirya mu bisa hanya me kyau,

Alhamdulillah

Alhamdulillah

Alhamdulillah

Allah ka yafe min kurarren da na yi a ciki wanda na sani da wanda ban sani ba,ya Allah ka bamu damar daukar abinda yake me kyua kasa mu ji tsoron aikata abinda yake mara kyau Amin ya rabbil alami ✍🏼

Mu hadu a kudurar Allah in sha Allah

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol