Free chapter · Read without an account
WHEN PRIDE BEGGED
ZAYD ARMAAN
CHAPTER 110
WHEN PRIDE BEGGED
JIDDAAH BARKUM
—————-
Zayd ya yi shiru. Shi kansa yanayin jinin ya ba shi mamaki. Something wasn’t right. This didn’t look like menstrual blood at all, kuma yadda jikinsa ya cigaba da hautsinewa na wani irin rashin daɗi ya sa duk wani tunanin da yake yi a baya ya kau.
A hankali ya janye jikinsa daga kusa da Seeyama, ya ja da baya, yana ƙoƙarin fahimtar abin da ke faruwa. Ya sake kallon jinin da ke kan bedsheet ɗin, sannan ya sauke idanunsa zuwa jikinsa, kamar yana neman wani explanation da zai haɗa abubuwan da suke faruwa a daren nan.
Seeyama kuwa, kallonsa kawai take yi, hawaye na zuba mata kamar an kunna famfo. Hankalinta ya riga ya tashi. Ga burinta da ta daɗe tana jira ya kusa cika, amma a take komai ya rikide ya zama wani irin mafarki mai ban tsoro.
“Babe…” ta kira shi a hankali, muryarta na rawa. Zayd bai amsa ba. Ya haɗiye yawu, ya dafe goshinsa na ɗan lokaci, sannan ya miƙe a hankali. Amma bai sake yin wani yunƙuri na yin magana ba, sai ya juya ya nufi bathroom ɗin ba tare da ya ce mata uffan ba.
Seeyama ta bi shi da ido har ya ɓace a bayan ƙofar. Da ta ji ƙofar ta rufe, sai ta ɗora hannayenta biyu a kanta. “Na shiga ukuuuuu!” ta fashe da kuka. “What has just happened to me?! Wayyo Allah na! Wayyo mommy na!” Ta fara girgiza kai, tana kallon bedsheet ɗin da ke gabanta kamar za ta iya samun amsar tambayoyin da suka cika mata zuciya a cikinsa.
“daga ina Wnn jinin ya fito!” Ta share fuskarta da tafin hannunta, amma hawayen suka ci gaba da zuba. A yanzu ba ta ma tuna shirin da ta yi tun farko ba. Ba ta tuna irin farin cikin da ta ji ba lokacin da Zayd ya fara mayar mata da martanin ta. Abin da ya rage mata shi ne tsoro, ruɗani, da tambayar da take ta maimaitawa a zuciyarta.
What is happening to me?
Kusan mintuna talatin suka wuce kafin Zayd ya fito daga bathroom ɗin. Ya fito daure da towel a ƙugunsa, amma yanayinsa ya canja gaba ɗaya. Fuskarsa ta yi fayau, goshinsa na ɗauke da zufa, yayin da yake jan ƙafafunsa da ƙyar. Kowane mataki kamar yana buƙatar wani irin ƙarfi daga gare shi.
Ya ɗan tsaya a bakin ƙofar, yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa. Hannunsa ɗaya ya kama gefen ƙofar domin ya samu abin jingina. “Ya Allah…” ya furta a ƙasan murya. Wani irin ciwo ne ya mamaye mararsa, mai tsanani har ya sa shi kasa miƙewa yadda ya kamata. Ya dafe cikinsa da hannu ɗaya, ɗayan kuma yana riƙe da ƙofar, amma duk da haka ya kasa jurewa.
Bai kai ga ƙarasawa gadon ba ma, sai ya nufi sofa ɗin da ke gefe, ya zube a kai da ƙyar, ya kwanta rub da ciki. Hannayensa biyu suka kama mararsa sosai, yayin da ya matse idanunsa, yana ƙoƙarin danne wani irin nishi da ya kusa kubuce masa.
The pain was unbearable. Zayd Armaan, mutumin da ya saba jurewa komai ba tare da ya nuna rauni ba, yanzu yana fama da wani ciwo da bai fahimci asalinsa ba. Ya yi ƙoƙarin miƙewa, amma wani sabon zafi ya taso masa, ya sa shi sake kwanciya da sauri. “Damn it…” ya furta cikin raunin murya.
Seeyama, wadda har yanzu take zaune a kan gadon tana risgar kuka, ta ɗago kanta jin sautin muryarsa. Ta juya ta kalle shi, sai ta ga yadda yake murɗewa a kan sofa, hannayensa a manne da mararsa. Kukan nata ya tsaya na ɗan lokaci.
“Babe…?” ta kira shi cikin tsoro. Bai amsa ba. Ya matse haƙoransa, yana ƙoƙarin shawo kan ciwon. “Babe?” Ta sake kira, wannan karon tana tashi daga kan gadon. Amma kafin ta ƙarasa gare shi, sai ta tuna da jinin da ke nan a kan bedsheet ɗin, ta sake tsayawa cak.
A ƙarshe dai ta juya da sauri. Ta janye bedsheet ɗin daga kan gadon, tana rawar hannu, sannan ta tattara shi ta kai wajen washing machine. Ta jefa shi a ciki, ta kunna machine ɗin, kamar dai kawar da jinin daga gabanta zai taimaka mata ta kawar da wannan mummunan yanayin da ta tsinci kanta a ciki.
Bayan ta gama, sai ta fara wanke jikinta da sauri, tana bincika ko akwai wani rauni ko alamar jinin a jikinta. Amma babu komai. Jinin ya daina zuba gaba ɗaya. Ta tsaya cak, tana kallon jikinta cikin rashin fahimta. Ta sake dubawa, ta sake bincika, amma babu ko digo guda.
“Wayyyo…” ta furta, muryarta na rawa. Ta ɗora hannu a ƙirjinta, numfashinta ya fara sauri. “Yanzu kuma ina jinin ya fito? Dan Wnn ba period ɗina ba ne, kuma babu wani rauni a jikina… what exactly happened?” Ta girgiza kai da ƙarfi, kamar tana ƙoƙarin kore tunanin da ya fara shiga ranta.
“No, no, no… wayyo Allah na!” Ta sake fashewa da kuka, ta jingina da bango, tana jin kamar ƙafafunta ba za su iya ɗaukar nauyinta ba. “Na shiga uku! Ya Allah, me ya same ni?”
Sai a lokacin ne ta tuna da Zayd a ɗayan ɓangaren ɗakin. Da sauri ta share hawayenta, ta fito daga bathroom ɗin, amma abin da ta gani ya sa ta tsaya a bakin ƙofar. Zayd har yanzu yana kwance rub da ciki a kan sofa, hannayensa biyu a mararsa. Idanunsa a rufe, numfashinsa ba daidai ba, kuma duk da ƙoƙarinsa na ɓoye ciwon, a bayyane yake cewa yana shan wahala sosai.
“Babe!” ta kira shi, ta ƙarasa kusa da shi cikin firgici. “What are we going to do now?” Zayd ya buɗe idanunsa a hankali, ya kalle ta na ɗan lokaci. Ya so ya amsa, amma ciwon da ya sake tasowa ya sa shi lumshe idanunsa da ƙarfi.
“Just… leave me alone,” ya faɗa cikin raunin murya. Seeyama ta girgiza kai, hawaye suka sake cika idanunta. “No, babe! You’re not okay. Look at you!” Ta durƙusa kusa da sofa, tana ƙoƙarin ganin fuskarsa. “Please, tell me what’s happening. Cikinka ne yake ciwo? Should I call someone?”
Zayd bai amsa nan take ba. Ya ci gaba da dafe mararsa, yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa. A wannan lokacin, Seeyama ta fara jin tsoron da ya wuce damuwarta game da jinin. Domin komai ya faru a wannan daren, tana tsoron kar maganin ya masa illa dan ta sani ita da kanta overdosing tayi masa.
Kuma ba ta san abin da za ta yi ba. Ta kalli fuskarsa, sannan ta sauke idanunta zuwa hannayensa da suke manne da mararsa. Zuciyarta ta fara bugawa da sauri. “Babe… please, don’t do this to me,” ta raɗa cikin kuka. “I’m scared.” Amma Zayd ya sake matse idanunsa, ya sunkuyar da kansa, yana fama da ciwon da ya ƙara tsananta.
Seeyama ta ɗaga hannu ta rufe bakinta. Ya Allah… what have I done?
A hankali Zayd ya fara ƙoƙarin miƙewa, yana ɗan durƙusawa saboda azababben ciwon. Da ƙyar yake iya motsi, kuma shi kansa ya san babu yadda za a yi ya ci gaba da zama a wannan ɗakin bayan yana da wata mafitar. Ya matse haƙoransa, ya jingina da gefen sofa, yana ƙoƙarin tara ƙarfin jikinsa. Bayan ya samu damar miƙewa tsaye, sai ya fara tafiya a hankali zuwa inda jalabiyyarsa take.
Kowane mataki kamar yana ƙara tsananta masa ciwon. Ya isa wajen kayansa da ƙyar, ya ɗauki jalabiyyar, ya saka ta a jikinsa cikin wahala, sannan ya fara dafa bango a hankali har zuwa bakin ƙofa.
Seeyama, wadda take tsaye tana kallonsa cikin tsananin damuwa, ta miƙe da sauri ta nufi inda yake. “Babe, ina za ka je yanzu, a cikin daren nan?” ta tambaya cikin firgici, tana ƙoƙarin kallon fuskarsa. “Ko na ɗauko key ɗin mota mu je asibiti? You need to see a doctor! Ko kuma in ce, duka muna buƙatar ganin likita saboda ban fahimci abin da ke faruwa ba.”
Zayd bai ko kalleta ba. Ya buɗe ƙofar a hankali, yana riƙe da cikinsa da hannu ɗaya. Seeyama ta bi shi da sauri, zuciyarta na bugawa saboda yanayinsa ya tsorata ta matuƙa. “Babe, wait!” ta kira shi, tana ƙara matsowa. “Listen to me, please. You are not feeling fine. Ba za ka fita haka kai kaɗai ba!”
Zayd ya tsaya. A hankali ya juya kansa ya kalleta, idanunsa jajir, fuskarsa cike da wani irin yanayi da ya sa Seeyama ta kasa sake cewa komai. Ya zuba mata idanunsa na wasu daƙiƙu, sannan muryarsa ta fito a hankali, cikin rauni saboda ciwon da yake ji, amma kalamansa suka kasance masu nauyi.
“Zan zauna na mutu ne bayan abin da kika aikata min?” Seeyama ta zaro ido. “Babe…” “Ko ke kaɗai ce matata?” ya katse ta, wannan karon muryarsa ta ɗan ƙara kaifi duk da yadda yake fama da ciwon. “Don’t you dare come close to me.”
Ta tsaya cak. Kalamansa sun sauka a kanta kamar ruwan sanyi. Ta buɗe baki, amma babu wata magana da ta iya fitowa. Abin da kawai take yi shi ne kallonsa, tana ƙoƙarin fahimtar irin tsananin fushin da ke tattare da kallonsa. Zayd ya juya ya ci gaba da tafiyarsa, hannunsa ɗaya har yanzu a kan mararsa. Ya fita daga part ɗin ba tare da ya sake waiwayarta ba, yana jan ƙafafunsa a hankali duk da ciwon da yake ji.
Seeyama kuwa ta tsaya a bakin ƙofar, ta kasa motsi. Kamar wadda aka dasa a wajen. “Zan zauna na mutu ne bayan abin da kika aikata min?” Maganar ta ci gaba da amsa kuwwa a kunnenta, tana maimaituwa har ta fara jin kamar Zayd yana tsaye a gabanta yana sake faɗa mata ita.
Ta ɗaga hannunta ta rufe bakinta, idanunta suka cika da hawaye. “Wayyo Allah na…” Ta girgiza kai, ta koma baya da matakai biyu, har sai da bayanta ya taɓa bango. “Na shiga ukuuu na ja wa kaina da Kaina wajenta zai koma!” ta fashe da kuka. “Wace irin masifa ce na jefa kaina a ciki haka?”
Ta durƙusa a hankali, tana share hawayenta amma wasu suka ci gaba da zuba. Ta tuna yadda komai ya fara a daren nan, yadda ta yi farin ciki lokacin da ta ga Zayd yana mayar mata da kulawar da ta daɗe tana fata, da yadda a take komai ya rikide ya zama wani irin bala’i. Wallahi sai na kashe ki, you caused me all this, kece kika ja min, bazan barki ba, kece silar komai, ta fashe da kuka tana burguma a wajen kamar wata yar bori.
Ta dafe kanta da hannayenta biyu. Itace tayi min Wnn? Wallahi itace, itace, itace, ta bawa kanta amsaa. Tana sake fashewa kuka. Toh sabida me? Tambayar ta dawo mata a karo na babu adadi, amma wannan karon babu wata amsa da ta samu.
Ta ɗago kanta ta kalli ƙofar da Zayd ya bi, zuciyarta cike da tsoro. “Babe… please, don’t hate me,” ta raɗa cikin kuka, duk da cewa babu wanda zai ji ta. Amma daren ya riga ya canja komai.
Raihana kuwa, tun bayan da ta zauna a kan gadon nan, ba ta san tsawon sa’o’in da ta ɗauka ba. A ƙarshe dai bacci ne ya yi awon gaba da ita a wajen. Ta kwanta a rabe, wuyanta ma a karkace, alamar cewa baccin ba shiri ya ɗauke ta. Mayafin da ta saka ya zame kaɗan, ya rufe rabin fuskarta, yayin da hannunta ɗaya yake kwance a gefen pillow ɗin.
A hankali ƙofar ɗakin ta buɗe. Zayd ya shigo yana jan ƙafafunsa da ƙyar, hannunsa ɗaya yana riƙe da cikinsa, ɗayan kuma yana taimaka masa wajen dafa bango. Ya yi kama da mutumin da ya yi tafiyar da ba zai iya jurewa ba, duk da cewa daga inda ya fito zuwa nan ba wani nisa ne mai yawa ba.
Da ganin fuskarsa ka san yana cikin azaba, goshinsa cike da zufa, yayin da numfashinsa ke fita a hankali. Azababben ciwon marar da yake ji bai ba shi damar tafiya yadda ya saba ba. Da ƙyar ya rufe ƙofar bayansa.
Sai idanunsa suka sauka a kan Raihana. Ta kwanta a kan gadon kamar wadda bacci ya yi awon gaba da ita ba tare da ta shirya ba. Ko fitilar ɗakin ba ta kashe ba. Zayd ya tsaya yana kallonta na ɗan lokaci, fuskarsa ta rikida zuwa wani irin yanayi da ba wanda zai ce ya taba ganin shi a haka.
A hankali ya fara matsowa kusa da ita, yana ci gaba da dafa bango saboda ciwon da yake ji. Da ya ƙarasa bakin gadon, sai ya tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarta. She’s asleep. Ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya durkusa a hankali a gefen gadon. Ko zama ma yana buƙatar ƙoƙari a gare shi a wannan lokacin.
Ya ɗago hannunsa a hankali, ya janye mayafin da ya rufe rabin fuskarta, yana kallon yadda bushashen hawayen da suka bushe a gefen idanunta suka bayyana. Kamar ta yi kuka kafin bacci ya ɗauke ta. A hankali idanunsa suka sauka kan lips ɗinta jajurr dasu da suke a tsuke cikin bacci. Ya yi shiru, yana kallonta, kafin wata wawiyar ajiyar zuciya ta kuɓuce masa.
Ya daɗe yana kallonta haka, kamar zuciyarsa tana neman wani irin nutsuwa daga gare ta. Raihana tana kwance a bayanta, jikinta a miƙe, kamar wadda ta gaji sosai. Zayd kuwa, da ƙyar yake iya riƙe kansa, yana jin kamar ya afka mata kawai dan ya san idan ta tashi ya nemi wani abu rigima ce kawai zai sha, kila harda baqaqen maganganu.
A hankali ya sunkuyar da kansa, ya kwantar da shi a kan kirjinta, sannan ya kankame ya sosai yana shakar kamshin jikinta, take ya fara sauke ajiyar zuciya mai nauyi kamar yaron da aka dauke daga jikin uwarsa yana tsaka da shan nono. Wani irin yanayi ne ya mamaye shi, kamar ya samu wurin da zai ɗan huta daga azabar da yake ji.
A cikin bacci, Raihana ta ji wani abu mai nauyi ya sauka a jikinta, sannan ya kankame ta. Ba ta daɗe da yin baccin ba, kuma wannan motsin ya katse mata shi kwatsam. Da farko ta yi ƙoƙarin juyawa, tana tunanin ko pillow ne ya faɗo mata a jiki. Amma da ta ji numfashin mutum a kusa da ita, sai ta buɗe idanunta a zabure.
Abin da ta gani ya sa ta kusa tsalle daga kan gadon. Zayd ne! Ya kankame ta, kansa a kan kirjinta, kamar zai koma cikinta! “WAYYO ALLAH NA!” Ta miƙe da sauri, ta ture kansa daga jikinta, tana matsawa gefe kamar wadda ta taɓa wutar lantarki.
Zayd, wanda bai ma fahimci abin da ya faru ba, ya ɗago kansa da sauri. Ya kalleta cikin mamaki, yana ƙoƙarin fahimtar dalilin da ya sa aka ture shi haka. Raihana kuwa ta riga ta miƙe tsaye gaba ɗaya. Ta tsaya tana kallonsa da wani irin kallo, kamar ba ta gane wanda yake gabanta ba.
Zayd ya ɗan dafe gadon yana ƙoƙarin miƙewa. Ciwon marar da ya addabe shi ya sa ya kasa tsayuwa yadda ya kamata, don haka hannunsa ɗaya ya koma kan mararsa, ya dafe ta sosai. Raihana ta ɗan murtsike idanunta, har yanzu alamun bacci na bayyana a fuskarta. Ta kalle shi, sannan ta sake kallon ƙofar ɗakin, kafin ta dawo da idanunta kansa.
Cikin muryar bacci, amma cike da mamaki, ta tambaya: “Lafiya? Me haka?” Ta yi shiru na ɗan lokaci, kamar tana ƙoƙarin tuna abin da ya faru kafin ta yi bacci. “Ba ka ce sai da safe ba? Kwanakin ka a nan ya kare. Me kuma ya dawo da kai nan?”
Zayd ya zuba mata ido. Ya kasa yarda da yadda take masa magana, musamman ganin yadda ta ke maganar cikin hasala. Ya so ya yi magana nan take, amma ciwon da yake ji ya sa ya ɗan sunkuyar da kansa, yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa.
Raihana kuwa, ganin bai amsa mata ba, sai ta ɗan ɗaga gira. “Hello? I’m talking to you.”
A hankali Zayd ya miƙe tsaye, ko da yake ba ya iya tsayuwa da kyau. Hannunsa ɗaya har yanzu yana kan mararsa. Ya kalleta direct in the eyes, fuskarsa cike da wani irin yanayi da ya sa Raihana ta ɗan yi shiru. Sai muryarsa ta fito a sanyaye.
“I need you, please.” Raihana ta tsaya cak. Ta zuba masa ido, tana ƙoƙarin fahimtar abin da ya faɗa. Zayd ya haɗiye yawu, sannan ya ƙara da cewa cikin raunin muryarsa: “Na zo neman haƙƙin aure na ne dake kan ki.”
Raihana ta ɗaga gira ɗaya, tana kallonsa kamar ta ji wani sabon abu. “Haƙƙin aure?” Ta maimaita maganar a hankali, still tana kallonshi cikin rashin yarda. “Can you please listen to yourself?” Ta ɗan matsa baya, tana kallonsa daga sama har ƙasa, kafin ta ɗora wani azababben kishi da bata san daga ina ya taso ba ya tokare mata maqoshi.
“Wanne haƙƙinka ne a wajena? Nuna min inda yake, na ɗauko maka, please!” Ta yi maganar a dake ba wani tsoro dan hatta baccin da take ji tuni ta neme shi ta rasa. “Ka san baccin da ke kaina? Ka san da yadda ya ɗauke ni?” Ta ɗan qara ja baya kadan, tana kallonsa da idanun da tuni bacci ya kama gabanshi.
“Don Allah, I beg you, ka koma inda ka fito. Ka barni da abinda ya dameni.” Zayd ya tsaya yana kallonta. Da a ce a irin yanayin, da suka saba ne shi da ita, da ya mayar mata da magana cikin natsuwarsa ta yau da kullum. Amma a wannan daren, halin da yake ciki ya hana shi yin komai cikin sauƙi. Ya taune lips dinsa, ya ɗan sunkuyar da kansa, yana ƙoƙarin jure wani sabon raɗaɗin da ya taso masa.
Raihana ta lura da yanayinsa na ɗan lokaci. Murmushin da ke fuskarta ya ɗan gushe lokacin da ta ga yadda yake riƙe da cikinsa. Amma kafin ta iya cewa wani abu, sai ya sake ɗago kansa ya kalleta. Kuma a wannan karon, kallonsa ya sa ta kasa sake magana nan take.
Sai dai Zayd ya daure, ya fara takowa a hankali zuwa inda take tsaye. Raihana, ganin yana matsowa kusa da ita, sai ita ma ta fara ja da baya. Ta yi ƙoƙarin ɓoye firgicin da ya fara mamaye ta, amma yadda zuciyarta ke bugawa ya nuna cewa ba ta da nutsuwa ko kaɗan.
Duk da haka, Zayd ya ci gaba da matsowa. Mataki ɗaya. Sai wani. Har sai da bayanta ya haɗu da bango, ta rasa inda za ta ƙara matsawa. Ta ɗago idanunta ta kalle shi, sai ta ga ya kusanto sosai, ya tsaya a gabanta, amma bai bari jikunsu ya taɓa juna ba.
Ya zuba mata idanunsa, kallonsa mai zurfi kamar yana ƙoƙarin karanta duk abin da ke zuciyarta. Raihana ta kasa jure mayen kallon da yake mata kamar kura ta ga nama. Hakan ya sa ta yi saurin sauke kanta ƙasa, tana jin zuciyarta na bugawa kamar za ta fito ta bakinta.
Ya Allah, what is wrong with this man tonight? Ta haɗiye yawu, tana ƙoƙarin samun nutsuwa, amma sai ta ji hannunsa ya kama nata. Hannunta na rawa saboda yadda jikinta ya ɗauki karkarwa, amma Zayd bai damu da yadda ta dunkule hannunta ko ƙoƙarin kwacewa da take yi ba. Ya riƙe shi a hankali, sannan ya ɗora hannunta kai tsaye a kan mararsa.
Raihana ta zaro ido. “Me haka —” Bai bar ta ta ƙarasa ba. Ya sake matsowa kaɗan, ya sunkuyo da kansa, yana neman si hada idanu amma Raihana taqi kallonsa, sannan muryarsa ta fito a ƙasa sosai, kamar mutumin da ya kusa fashewa da kuka saboda azabar da yake ji.
“Don Allah, ki tausaya min.” Ya yi shiru na ɗan lokaci, yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa. “Idan na kwana a haka, zan mutu… I can’t take this anymore.”
Raihana ta tsaya cak. Duk da yadda zuciyarta ke mahaukacin bugawa da firgicin yadda ya kama hannunta ya ɗora a mararsa, ba ta iya hana wani irin ɓacin rai tasowa a zuciyarta ba.
Wato ita ce ya tuna yanzu? Ita ce ya raina? Ita ce ya mayar shara da zaiyi discarding abubuwanshi? Ita ce ya bar ta tana fama da tunaninta ita kaɗai, amma yanzu da yake buƙatar wani abu, sai ya zo yana roƙonta? Wato ita ya raina? Wacce ta taso masa da sha’awar uwar me, ya hana shi karɓar haƙƙinsa a wajenta, sai ita da ya raina? Wacce ta motsa shi daban, wacce zai sauke wa daban?
Lalle ma gayen nan ya bala’in raina capacity ɗinta! Wani irin haushi ya tokare mata maƙogwaro. Da sauri ta fisge hannunta daga kan mararsa, ta nade hannayenta a ƙirjinta, tana ƙoƙarin kare kanta daga sake kama hannun na ta.
Zayd ya kalleta, amma bai ce komai ba. Raihana ta ɗago kanta a hankali. Duk da muryarta na rawa saboda firgici da bugun zuciyarta, ta tilasta wa kanta kallonsa kai tsaye cikin ido. Sannan cikin muryar da ke nuna jin haushi, duk da ta fito ne cikin rawa, ta ɗago ta kalleshi cikin ido ba tare da ta yi ƙasa a gwiwa ba.
“Ita wacce ta saka a halin nan me ya hana ta cire ka a cikinshi? Ka koma can inda kuka fara ku ƙarasa! Ko ka manta cewa kwananinta ne ita ma? A matsayinta na budurwa, ka je ka gama kwana bakwai ɗinta cifffff! Nasan kafin su ƙare zaka samu abin da kake buƙata…”