Free chapter · Read without an account

002

by Aisha Muhammad Sanusi · AISHATUL HUMAIRA (Labarin Indo)


Mai gari ne ya kalli indo yace ke indo haka akayi"dariya ta kyalkyale da ita tace eaa haka akayi mana mai garin garinmu.Mai gari ne yayi nuni take wani dogari ya fito da wata zabgegiyar dorina mai baki biyu, indo idanunta idan dorina ai tini ta tattara ya nata ya nata tai waje ta bar wajen, yayin da mai gari yace a bita a kamota dik inda taje.Gudu take suna binta, ta kasuwar garin ta biyo, tana yi tana waiwaye, a lokaci daya ta bace musu, sunyi nema sunyi nema har sun gaji abin har ba'a magana, haka suka hakura suka dawo domin fadawa mai gari. Indo kuwa samu tayi ta shiga rumfar idi mai shayi cikin inda ake ajiye bread nan ta samu ta rakube, idi shi tsoransa allah kada ma ta dauki wani abun, sai da ta dauki wajen mint 30 sannan ta fito,a lokacin rana ta take, kallon biredin idi tayi ta hadiye yawu, kallonsa tayi tana daukar daya, cike da bacin rai idi yace ke wallahi ajiye min biredi tinda ba ubanki bane ya siya min, wani kallo tsyi masa kallon baka da wayo, tare da fadin zo ka kwata, nufota yayi cikin sa'a kuwa ta tsugunna kasa ta debo ta watsa masa a ido,ta runtua na kare.Tafiya take tana yagar biredin dake hannunta, a lokaci guda ta cinye hade da sakin wata gyatsa, shafa cikin tayi sannan ta fara magana, amma gaskiya ban koshi ba, kuma ni bazan koma wannan gidan ba indai garba baya nan, kara na bari sai can anjima, tafiya take tana watsa kasa, can gaba kadan tazo shigewa ta hango tukunya a wani gida, murmushi ta saki tana dariya, shiga tayi tana zazzare idanu, Faranti ta hango da ludayi hakan yasa ta bude tukunyar, dafaffiyar shinkafa ce jellof taji alayyahu da manja, diba tayi sannan ta koma gefe ta fara ci hankali kwance, har ta gama cinyewa tasha ruwa sannan taji alamun mutum zai fito, da gudu ta fice daga gidan tana waiwaye. Haka tai ta gantali a cikin kauyen wakaza ganin dare yakiyi ne yasa ta tafiya gonar wuro tare da danewa bishiya, can kusan la'asar sannan ta sakko tai hanyar rafi.Sai can wajen magariba sannan ta fara kokarin shiga gidan nasu, ba kowa a tsakar gidan hakan yasa fa shige madafa, tuwon da iyalle ta gama ta kwasa ta fara ci kamar jaka, sannan ta shige makewayi daga baya kuma ta fito, a dai dai lokacin iyalle tafito, kallon ta take cike da mamaki. "ke yanzu indo haka kika zaba ko, wallahi ke da mai gari domin yanzun nan zan kira garba yazo yayi miki maganin abinda yake damunki, yarinya sai iskanci, murguda baki indo tayi" ke wallahi iyalle kin cika jaraba, kin san allah kika sake kika kira garba wallahi ai bata rufe bakinta ba taji shigowarsa, kallin kallo aka fara, a wani gudu tai tsalle ta dare katangar gidan ta gudu.Sai wajen 10 ta dawo daga dandali a lokacin bakajin sautin komai sai na tsuntsaye,mainakon tayo hanyar gida sai tayi hanyar gidsn mai gari, cikin sa'a kuwa fa dare katangar gidsn ta fada cikin gidan, turakar mai gari ta karasa, sai kuma ta juyo ta dawo zuwa tsakar gidan, wani mulmulallen icce ta dauko tare da burshi ne fuskarta da toka kamar fatalwa,dakin mai gari ta shiga shi kuwa sai shara bacci yake, kamar xaga sama ta daga wannan iccen ta rabka masa a kafa, a fisrgice ya tashi zaune yana fadin nashiga3, fitilar gefe ta kunna a lokacin ya ganta fara fat abinka da me bacci.Mai gari ne ya fara magana "dan allah kuyi hakuri ku Kuke ganinku ba mu muke ganinku ba, ku taimaka dan allah ku kyaleni, a lokacin da indo ta fahimci ya dauka cewa ita din aljana ce, sai ta babbake da dariya. 
 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol