Free chapter · Read without an account

003

by Aisha Muhammad Sanusi · AISHATUL HUMAIRA (Labarin Indo)

"Kai mai gari rufe mini baki, kasani daga yau sai yau karka kuskura koda wasa a kara kawo maka karar indo yar wajen iyalle ka karba har kai tinanin zakai mata hukunci, idan kuma ka kuskura ka aikata wannan hukuncin to na rantse da sarkin aljannu sai na kwakule maka idanu, na cire maka hanci, sannan na rabaka gida 6 naba yaran sarkin aljannu su gama min da kai,Mai gari kusan fitsari ya kusa saki da toh toh yake amsawa, tsabar firgicin da yake ciki ya rasa ta ina zai fara,cikin kakkausar murya indo tace" zan tafi amma ka tabbatar da cewa zan dawo da zarar kayi kokarin taba ta, sannan bazan barka haka ba, koma kai bacci, cike da jin tsoro ya kwanta yana raba idanu, daga iccen tayi ta kara sauke masa a kafa, bayan data toshe masa baki, daga nan ta fice daga dakin ta inda ta biyo ta nan ta koma, sannan ta tafi makwancinta, tana ta kalle kalle.WASHE GARI
Tin wuri ta tashi ba abinda tayi sai jikin bishiyar darbejiyan dake tsakar gidan taje ta zauna tana kallon giccin iyalle, Garba ne ya shigo yana kallonta cike da bacin rai amma ko kallonsa batayi ba, matsawa yayi kusa da ita yana fadin "ke baki iya gaisuwa bane, indo tana jinsa amma tai banza dashi domin yau yanda takejin kanta wallahi zata iya koma menene amma bazata yi masa kuka ba.
Kafcecen hannunsa ya daga ya shara mata mari, dagowa tayi tana kallonsa, fada ya fara yi mata ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba, ganin kamar ya tsai da ta ne yasa ta mikewa ta fice daga gidan, cike da mamaki yake kallonta domin tabbas yanzu indo ta daina tsoron ko wane abin halitta.Tafiya take daidai kofar gidan su salame ta tsaya, kanta tsaye ta shiga a zaune ta tarar da salame, zama tayi kusa da ita da wani mugun tsoro salame take kallon indo, domin ita har ga allah ta tsorata da lamarin indo, katse tinanin indo tayi tace "ki tashi mutafi kinsan dai habi tana can tana jiran mu saboda kinsan mu ne kawayen amarya ko, dai dai lokacin mahaifiyar salame ta fito daga bayi," ke kuma annoba me kika dswo kiyi mana a gida wallahi indo idan baki fita narantse sai na lahanta ki, indo cike da tsiwa tace" karki fasa kuma ai ba wajenki nazo ba wajen 'yar ki nazo, ke salame taso mutafi, ba yanda salame ta iya dole ta mike tabi bayan indo, domin idan ta kuskura tayi mata gardama tsabb zata kara dankara mata duka ba abinda ya dameta.Gidan su habi suka tsaya a lokacin tana cin kosai da kunu, ko gaisawa basuyi ba indo ta dauke kosan da kofin kunun ta koma gefe, tana ci tana jiran idan akwai wani mai magana a cikinsu, har tayi ta gama sannan ta ce "ke habi taso muje a karbo kudin, kuma na rantse harda ubana dik yar bura'ubar da bata bada ba, ba wanda zai bata abin ajo, ke habi kuma wannan ba ruwanki ki barni da su kawai, ita dai habi tasan hali shisa take ta daga kai kamar wata kadangaruwa.
Tafiya suke dai dai gidan mai gari suka tsaya, suna kokarin shiga, indo a gaba tin daga bakin kofa take fadin gafaranku dai masu gida, wuri suka samu suka zauna, indo ce ta kalli matar mai gari tace lafiya dai laure naga dik kin wani chanja, ke tsaya ina barki take,"laure tace ai bata nan tana makaranta, ba wanda ya kara magana tashi sukayi zasu tafi, indo ce tace suyi gaba ita kuma tai bangaren mai gari.A zaune yake yana firfita, idanunsaa ya dora kan indo take ya kau da kai yana kallin gefe, daga can yace" hajiya indo barkanki da hutawa ya mutanen gidan naku dan allah a gaishe min da iyalle, dariya ce taso kwace mata dan haka ba ta tsaya ko ina ba sai kofar gidan a lokacin ta saki dariya harda rike ciki."habi ce tace yadai indo me ya faru tsaki indo tayi" to ke kuma yar sa'idon jaraba, wallahi habi ki fita daga idona kuma muje wajen idi ya bamu rabonmu, daga nan sai mu biya shagunan kasuwa kowanne dan iskan ya bamu kudin ajo.Haka kuwa sukayi dan ko wane shago daga mai 20 sai mai hamsin, kafin wani lokaci salame da habi sai washe baki sukeyi, daga nan suka fara bin gidan kawaye suna karbar kudin, dik wadda bata bada ba ita da indo, dayake sun san halin indo sai su kwammace su basu kawai.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol