Free chapter · Read without an account

006

by Aisha Muhammad Sanusi · AISHATUL HUMAIRA (Labarin Indo)

Abinda yake kawota makaranta kenan kullun ranar laraba da sassafe, saboda gidan malam ana suyan kaji, kuma ana raba naira hamsin, gashi ita har dana malam take hadawa ta debe bai sani ba, idan yara sun kawo na laraba.
Sallama take rafakawa a gidan malam iliya, amaryar malam iliya tana jinta ta fara kokarin boye soyayyin kajin, amma ina indo ta riga data gani, "amarya malam yace ki dakko mishi tawada a daki, amaryal malam bata fahimci komai ba dan haka ta mike ta tafi, indo ganin ta wice ne yasata sakin wata kafirar dariya, leda ta samo karama sai da ta cika ta da naman kajin sannan ta baro gidan tana fitowa bata jira dawowar malam ba tai hanyar gidansu.
Gaba a ya kauyen ya rikice, sakamakon ciccire misu shukoki da akayi, kowa zargin indo yake amma baka da ikon kayi magana, da kyar aka samu wani mutum da shi da samari 4 suka isa gidan su indo a lokacin ta dawo daga makaranta tana zaune tana yagar kajinta tana dariya, sallama ake tafkawa ba abinda tace illa "ku shigo, shigowa sukayi basu jira iyalle ba suka damki indo sai kofar gidsn mai gari.
Indo ana zuwa suka saketa ta zauna taci gaba da cin namanta, mai gari dik a tsure yake domin bai manta karonsa da aljanun indo ba,iyalle ce ta karaso tana fadin" dan allah kuyi hakuri ku kyaleta, babban ciki ne yace "aa ba wanda zai kyaleta wallahi sai ta biyamu, wani ne ya falfalo da gudu kamar yaci babu yace" ba indo bace ta aikata domin ita ma gonar gidansu sai da aka cire ta tsaff.Indo sai da ta cinye tsabb sannan tasha ruwa tai hamdala, kallon mai gari tayi daya kasa magana, sai kuma tacw "ni fa bani bace sarkin aljanu ne da tawagarsaya, domin jiya wajen karfe 2 na dare naji suna cewa a nome gonakin kowa, anan fa kowa idonsa ya duri ruwa, indo kuwa tashi tayi ma ta kara gaba ta barsu da zance da girgiza kai.
Gidan su dije ta wuce dan ganin ya lawan din, da sallama ta shiga tana yi tana wakar ta data zamar mata sabo, a kwance ta gansa ya mimmike kafa ga wasu uban shatin bulalu da sukayi masa rudu rudu, indo tana ganinsa take taji sanyi a ranta, karasowa tayi ta zauna tana fadin "sannu lawan me ya sameka haka, bai iya bata amsa ba saboda matsananciyar wahalar da ya sha a hannun aljanu. Dije ce ta shigo tana kiran, wallahi kogin dan marka ya lalace domin kuwa ruwan baya iya sha yiwa yayi jajawur, ya koma kamar jini inna, bata tsaya ba tace, kuma mai gari yace yana neman dik wani saurayi a kofar gidansa domin za'ayi bincike ne, kuma inna lawan ba yaji aljanun ba dan haka kawai ya tashi yaje.Indo ce ta hankada ta take taji ta a kasa, sai kuma tace "ke dallah shashasha mara hankali, lawan ya kuskura yace eyaga aljanu to wallahi kashinsa ya bushe domin suna dawowa a karo na gaba kashesa zasuyi, jin ance kisa ne yasa ta fara zaro ido tana fadin inalillahi, inna wai da gaske, innar ma taa yadda dan haka tace to yanzu ya zamuyi indo, dariya indo tayi tace "koda wasa karkuce aljanu ne suka kirbesa daga haka ta fice zuwa gidsn su habi.Tin daga kofar gidan take kiran mai suffar aljanu fito mana ga kawaarkj, yarinyar tanaji tasan itace amma sai tayi banza da ita, a zaune ta tarardasu ita da habi, habi na ganinta ta fara magana "dan allah indo ki taimaka ki bani kudin ajon nan dsn allah, indo ce ta kyalkyaale da daria tace" ke din banza ba kin turo mai suffar aljanu ta karbar miki ba jira nke tazo naga zata iya kwata, wadda aka kira da mai suffar aljanu a fusace ta tashi ta kama indo da fada, amma sai da indo ta mata duka, jin kamar tudu a kirjin budurwar ne yass indo lekawa ai kuwa idanunta suka hadu da nono, dariya ta kuma yi tace shegiya, wadannan yayan kwallon fa.
Ai da su kike gadara ko, ke habi dakko min wuka na yanke yan iska, ba habin ba hatta budurwar ta riga datasan ta gama yawo, habi hannu na raws ta mika mata, yaga rigar tayi tana saita wukar. 
​

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol