Free chapter · Read without an account

007

by Aisha Muhammad Sanusi · AISHATUL HUMAIRA (Labarin Indo)

Kafin ta kai ga sa wukar tini taji saukar icce a kanta, a take a wajen ta sume, ba kowa bace illa salame data kwada mata icce, kallinta habi tayi sai kuma, lantana mai suffar aljanu inji indo amma ta fara lalubeta, anan taji kudin dakkosu tayi tace wannan ne da alama, ku huce mutafi mu kaso su, habi dai a tsure take dan haka tace aa kuzo mu kama mu wullarda shegiya domin wallahi idan ta tashi tasan a gidan nan akayi mata.
Kakkamata sukayi suka kaita lungun gidansu suka ajiyeta anan sannan suka tafi.Iyalle ce ta dawo daga bakin dandali tayi karo da indo, da sallallami ta tsugunna, daukar ta tayi sannan kuma tatafi gida, harda yar kwallarta, shinfida tayi mata ta kwantar da ita akan tabarma.Indo tin safe har la'asar bata farka ba hakan yasa iyalle jin tsoro, ruwa ta debo ta fara zuba mata akan ta tashi amma ko motsi batayi ba, dan haka ta fara jijjigata, tasan indo da nauyin bacci acewar iyallee wai indo bacci take, dan haka ta kara mata lokaci.Gaba daya yau kauyen kuwa kowa yau lafiya yake harkokinsa ba wanda ya tambayi ina indo.
Indo ana kiran sallar magariba ta mike tace "kutumar uba ai da gudu ta fita, gidan su habi taje basa nan, zama tayi a kofar gidan tana tinanin me ya kamata tayi ne.Gidan su dije da salame ta yashi taje amma babu su babu alamun su, hakan yasa tace" da ni kuke zancen, baku kadai ba harda iyayenku sai sun san wacece indo, tashi tayi tana gantalinta har magariba tayi, hakan yasa ta nufar dandali, anan ne ta hadu da barki, indo ce ta karasa kusa da ita tace "ke barki ina su habi ne, washe baki tayi da dik hakoran sun dafe tace," suna gidan su lantana wata uwar ashar ta saki tana girgiza kai, kafin kace me tini ta bar dandalin da wani mugun gudu.A daidai kofar gidan su lantana ta tsaya tana tinani me zatayi, hakan ne yasa kallon kasa, wata leda ta hango can nesa, zuwa tayi sannan ta tsugunna ta fara debo kasa a hankali, sai da ta cika ledar sannan ta karasa gidan, abinda take tinani ne kuwa ya auku, domin tukunya ce suka dora gefe kuma ga dije a zaune da lantana, shigowarta yasa lantana mikewa ta zuba da gudu tai dakin iyarta, dije ce tace sannu indo, bani banzan kallo ta wulla mata sannan ta bide tukunyar ta juye wannan yashin, kallon dijen tayi tace, "wato ke ga mayya ko, sai kici mugani kuma wallahi na kama habi da salame da lantana sai naci bura'ubansu, daga haka ta fice tana wakarta.Ganin kowa na tafiya kofar gidan mai gari hakan yasa indo tafiya tana cewa" kara naje ayi komai a gabana ko kuma a samu wani makiyin nawa ya aibata ni, tana zuwa ta zauna daga can nesa ba wanda ya hangota,mai gari ne yayi gyaran murya yace "mutanen wannan kauye ina fatan dik kun wuni lafiya, a gaskia muna cikin tashin hankali domin kogin dan marka, ruwan ya daina sha wuwa, hadi kuma ga gonakin mu da aljannu suka ciccire mana ciyawa,amma ina mai bada shawarar a kara hakuri komai zai daidai ta.Wani na kusa da maigari ne yace "aa mai gari bazaiyu muci gaba da zama a haka ba, kasancewar mu mutane ne kuma muna buqatar ruwa da sauran abubuwa, amma yanzu meye mafita, dikkanin mutanen wajen tsitt sukayi suna tinani, wani ne ya Mike yace" to allah gafarta malam mudai bamu da abinyi sai abinda kafada.Indo jin kowa yayi shiru yasa ta yin wuff ta dare gaban mutane, kafin kace me kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa da zagin indo, shi dai mai gari yasan gamon ba dadi shisa ma a take yayi tsitt, tsawa ta daka musu tace idan kuka bani abinda nakeso, ina tabbatar muku da cewa zan sa aljanu su dawo da kogin dan marka, jin haka yasa suka hada baki wajen furta me kike buqata ne indo, dariya tayi ta buga kafa tace wannan kuma ni zan yanke, dan haka a yau dik wanda ya shiga gidansa karka kuskura ka bude ko su dawo jikinka.A haka kowa ya yadda da abinda ta fada, sannan kuma kowa ya watse, indo dariya ta saka tana tafawa, tace "lalle wadannan anyi jahilai yoo inba jahilci ba ai daga jin wannan batu kasan karya nake, wohoho yo ni indo, daga haka ta shige ta fice.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol