Free chapter · Read without an account

Page 2

by Maryam · INUWAR GASKIYA

INUWAR GASKIYA

Na Marhama

Hajiya Rabi ta ci gaba da tafiya, Afnaan na binta a baya cikin nutsuwa.

Sun bi wani dogon corridor kafin su tsaya a gaban wata ƙofa da ke gefen bene na ƙasa.

Hajiya Rabi ta buɗe ƙofar.

“Ga ɗakin nan.”

Afnaan ta leƙa cikin ɗakin. Ba wani babban ɗaki ba ne, amma yana da tsafta. Akwai ƙaramin gado, wardrobe, kujera da kuma taga da ke kallon wani ɓangare na lambun gidan.

Ta shiga a hankali, ta ajiye jakarta a gefen gado.

“Na gode sosai, Hajiya.”

Hajiya Rabi ba ta amsa godiyar ba. Ta tsaya a ƙofar tana kallon Afnaan da wani irin yanayi da ya sa yarinyar ta kasa gane abin da ke zuciyarta.

“Ki saurare ni da kyau.”

Afnaan ta juya gare ta.

“Daga yau, za ki zauna a wannan ɗakin. Ba za ki fita daga gidan nan sai da izini ba. Zan kai sunanki wurin Mai Gidan, idan ya ga dama ya ba ki aiki, shikenan. Idan kuma bai ba ki ba, shi ma shikenan. Za ki tattara kayanki ki tafi.”

Ta yi ɗan shiru kafin ta ƙara da cewa:

“Kuma abu na biyu, ba na son yawan tambayoyi. Ki yi aikinki, ki kiyaye dokokin gidan, ki guji shiga harkokin da ba su shafe ki ba. Ba ruwanki da abin da za ki gani ko ki ji a gidan nan idan har kin Samu aikin . Kin gane?”

Afnaan ta sunkuyar da kanta.

“Na gane, Hajiya.”

“Da kyau.”

Hajiya Rabi ta juya za ta fita, amma sai ta tsaya a bakin ƙofar.

“Abinci za a kawo miki na rana. Kada kiyi yawo a gidan nan sai an kira ki.”

Ta fita ta rufe ƙofar.

Afnaan ta tsaya tana kallon ƙofar na ɗan lokaci, kafin ta fitar da numfashi a hankali.

Wannan gidan fa kamar ba gida ba ne, kamar gidan yari ne, ta yi tunani.

Ta zauna a gefen gado,  ta gyara hijabinta, sannan ta zaro ƙaramin hoton da ke cikin jakarta tana kallo take hawaye ya cika mata ido.

Muryar Hajiya Rabi taji a waje tana magana da wani.

“Ka kai wa Mai Gidan saƙon cewa akwai wata yarinya da ta zo neman aiki. Sunanta Afnaan Ibrahim.”

Wata murya ta amsa.

“Ya tambayi daga ina take?”

“Ban sani ba. Shi ya sa na ce ka kai masa saƙon. Idan yana buƙatar wani bayani, zai tambaye ta da kansa.”

Sautin takalma ya yi nisa.

Afnaan ta mayar da hoton cikin yar jakarta

Ta san cewa yanzu komai yana hannun mutumin da ta zo neman aiki a gidansa.

Abdulmalik Sani.

Mutumin da sunansa kaɗai yake sa mutane su yi shiru.


Bayan kamar awa ɗaya, an kawo wa Afnaan abinci. Ta ci kaɗan, sannan ta zauna tana jiran a kira ta.

Amma ba wanda ya zo.

Sa'o'i suka wuce.

Rana ta fara yin ƙasa, hasken da ke shigowa ta taga ya fara dusashewa.

Afnaan ta fara tunanin ko Mai Gidan ya ƙi ɗaukar ta aiki ne.

Sai ga ƙwanƙwasawa a ƙofar.

Ta miƙe da sauri.

“Shigo.”

Hajiya Rabi ce.

“Ki tashi ki gyara jikinki. Mai Gidan yana son ganinki.”

Zuciyar Afnaan ta buga da ƙarfi, amma ta ɓoye hakan a fuskarta.

“Yanzu?”

Hajiya Rabi ta ɗaga mata gira.

“Kin ji na ce yana son ganinki, ko kina son in sake maimaitawa?”

“A'a, Hajiya. Na ji.”

Ta ɗauki mayafinta ta saka, sannan ta bi Hajiya Rabi.

Sun bi corridor ɗin da ta bi da farko, suka wuce wasu ƙofofi har suka isa wani babban falo. Komai yana da tsada a wurin, daga kayan ɗaki zuwa hotunan da ke jikin bango.

A ƙarshen falon, wani mutum yana zaune a kan kujera mai launin baƙi, yana duba takardu.

Ba sai an gaya wa Afnaan ko wane ne ba.

Ta gane shi.

Abdulmalik Sani.

Ya ɗaga kai a hankali, ya kalle ta daga sama har ƙasa, sannan ya ajiye takardun da ke hannunsa.

“Ke ce kika zo neman aiki?”

“Eh, ranka ya daɗe.”

“Me ya sa kika zaɓi gidana?”

Afnaan ta ɗan yi shiru kafin ta amsa.

“An gaya mini cewa kuna buƙatar ma'aikata, ranka ya daɗe. Ina neman aiki ne domin in sami abin dogaro da kai.”

Abdulmalik ya jingina da kujera.

“Kin taɓa yin aiki a gidan wani mai kuɗi?”

“A'a, ranka ya daɗe.”

“Kin san dokokin wannan gidan?”

“Zan bi duk dokokin da kuka shimfiɗa.”

Ya yi murmushi kaɗan.

“Wannan amsa ce mai kyau. Amma ba amsa ce ta tabbatar da cewa zan iya yarda da ke ba.”

Afnaan ta sunkuyar da kai.

“Na fahimta, ranka ya daɗe.”

Ya juya ya kalli Hajiya Rabi.

“Ki koya mata aikinta. Zan ba ta dama ta nuna abin da za ta iya.”

Hajiya Rabi ta amsa, “To, ranka ya daɗe.”

Amma kafin su juya su tafi, Abdulmalik ya sake magana.

“Afnaan ko ma mene sunan ki?

Ta tsaya.

“Ki tuna abu ɗaya. A gidana, ba na son mutumin da yake son sanin abin da bai shafe shi ba.”

Ta juya ta kalle shi.

“Na fahimta, ranka ya daɗe.”

“Za ki iya tafiya.”

Afnaan ta bi Hajiya Rabi ta fita daga falon.

Ta yi tunanin ta samu abin da ta zo nema.

Amma ba ta san cewa daga ranar nan, za ta fara rayuwa a cikin gidan da kowane sirri yake da farashi ba.

Kuma wasu sirrin...

ba a barin su su fito da rai.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol